Auren Wata Uku Book Complete By Sameena Aliyu.doc

Author :  Sameena Aliyu Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   10 / 52

27K to 30K   out of 153.1K words

d an kauda fuskarta tana matsan k wallan da suka cika idanunta. Ta jinjina kai a hankali tana shafa bayan Ummul alamun kwantar da hankali  Yi kuka Ummul.. Kukan zaisa kiji relief& 

Saida ta bata lokaci tana kukar da abinda ke k unshe k irjinta kafin tai gyaran murya  Let them say whatever they want. Su fad i duk abinda suke so. Amma koda wasa kar kiyi abinda zaija miki matsala a rayuwa. We are all human beings, kuma Allah ya haliccemu daban daban. Level of tunaninmu bazai zama daidai da juna ba. Ko a makaranta ne cikin aji d abi un yara da halayyarsu ya banbanta. Akwai yaron da kana koyar dashi abu bugun farko ya d auka. Wani kuma sai anyi da gaske ya gane. Akwai fast learners akwai slow learners. Malaman makaranta da suke koyar da yara suka san d abi unsu su zasu fad a miki wann. Akwai yaran da suke fuskantar wani ciwo da iyayensu ma basu san suna dashi ba kaman irinsu Attention deficit hyperactivity disorder (ADHD). Sai kiga a gida anata jibgan yaro ace jaki ne baya son karatu baya gane karatu wanda ba haka bane ya samu d an wani matsala ne da idan aka tafiyar dashi sannu a hankali yanda yake d in idan abun ba mai tsanani ne sosai sai kiga ba sai anje ga ganin likita ba. Wata uwar fah da kanta take abusing d an da ta haifah ko ince wasu iyayen. Kar kice d an rik o ko goyo a a D an suka haifa zasuyi abusing a nasu tunanin wai soyayya suke masa. Wani yaron tsananin matsi da tak ura da tsanani shi yake traumatizing d insa. Kiga uwa ta dasa ma yaranta tsoronta. Yes ta haifar da fair tsakaninta da yaranta duk wai ita a dole tarbiya take masu batasan ta kashe kanta bane a staye. Bai jima ba na gani da idona ba jiyau ba wani yaro yayi hanging kansa sabida tsoron yayi laifi. Kuma kar kice wani babban laifi a a minor laifi ne amma sabida tsoronta da ta haddasa masa yasa ya d auki rayuwarsa. Toh kinga dik ire iren wad nn sukan haddasa ma yaro ya dinga wasu d abi u kaman na mai tab in hankali tin yana k uruciya har kawo girma. Ba ace kar ka tsawatar ma yaranka ba amma idan aka tauna sai a d an sake haka shi yaro yake. Sann ire iren wad ann cututtuka na kwak walwa akwai mutanen da dama manyan mutane da suka zama madubi ga al umma sun fuskanta a lokacin k uruciya idan kika bibiyi tarihinsu kafin nasarorinsu. . Akwai mutane masu special needs cikinmu  yanadam. Mutanen da suke buk atan kulawa ta musamman. Ba zallan wanda muke ganinsu da nakasa ta zahiri a fili ne suke buk atan taimako na musamman ba. Wato mutane masu disability da muke iya gani mu tantance. Akwai wasu d abi u da zaki kula mutum nayi wasu lokutan kaman d an tab in k wak walwa. Abun minor ne baiyi tasiri a jikinsa ba. Idan aka ja yaro jiki ko mutum mai irin wann matsalan ka tafiyar dashi yanda ya dace sai kiga abun yayi sauk i ba sai an kaiga neman magani ba. amma mutanen da suke rayuwa dasu sai susa abun ya girma har ya koma kaman hauka. Sai kiji ance miki mutum ya koma hauka tuburan. Mutane suna hantaran shi mutum mai irin wann matsalan. Ko kiga daga an ganshi sai a fara dariya ana manna masa hauka. Mutane suna kiransa da sunaye barkatai Wawa, a a shashasha lusari maras hankali. Dama k wak walwar nasa da gaske akwai d an matsala sai kiga yayi giving up ya yarda da abinda mutane ke fad a akanshi sai kiga ya fara abu irin na masu tab in hankali. Irin wad ann sune mutane masu Emotional and mental health needs. Wasu zaki samu through life experience suka had u da wann matsalan. Wasu zaki samu stress ne ya maidasu haka. Some have history of abuse musamman idan cin zarafin da suka fuskanta a lokacin k uruciya ne. trauma or neglect. Wasu an wofantar dasu. Dik suna contributing kiga mutum ya samu wann Matsalar. Wasu kuma biological factors ne ma ana gadon cutan sukai ko kuma dai cuta ne kawai daga Allah. Amma a matsala irin na mahaifiyarki zai iya zama Desperation na ganin ta aurar dake ko ta halin k ak a zai iya haifar mata wann matsalan kinga kuma rashin tawakalli da karban k addara yanda tazo ma Bawa ya shigo ciki. A akasarin lokuta desperate individuals sukanyi wasu bubuwa wanda normally thinking person bazai fahimta ba. Because they are desperate sukan aikata wasu abubuwa da yafi kama da hauka or illogical. A wasu lokutan Yakan sa mutum ya cutar da kansa har ma yakaiga yayi yunk urin kashe kansa.

Ummul ta dubeta sai ta tuna sanda Umma tai yunk urin fad awa rijiya zata kashe kanta dikdai sabida k addararta.

Muryar Hajja Fannah ya dawo da ita  Ni ba likita bace sann kuma ban karanci halayyan d an adama ba. Ina fad a miki wasu abubuwan ne base on experience. Ni uwa ce da ta raini d anta ba uba. Mun fuskanci k alubale da dama a baya wanda yasa na zama exposed da ire iren matsalolin nan.. Ta d an numfasa kafin taci gaba  Ko ma wanne matsala mahaifiyarki ke fuskanta Ummul kija mahaifiyarki a jiki. Kar ki tab a hantararta koda ta kasance mai tab in hankalin ko shashasha kaman yanda mutane ke fad i. Iyaye ko a bola suke yawo iyaye ne. Allah yakan k addari rayuwar wasu cikin rayuwarmu domin ya zame mana jarabawa. Kibi umarnin Allah kiyi mata biyayya cikin abinda babu sab onsa. Kiyi k ok arin tafiyar da ita yanda take d in. Na tabbata ko haukan ne, ko ganganci ne ko ma menene Allah bazai tab a bari ki tab e ba matuk a kin fawwala masa lamiranki kuma baki fasa addu a da neman zab insa ba. Ta kuma kamo hannayenta  Dik tsanani yana tare da sauk i. Inada yak inin Umma ba b acewa tai ba. Khulsum zata dawo gida Abba kuma zai samu lafiya cikin yardar Ubangiji. Tashi muje ba zama zamuyi ba.

Suna k ok arin mik ewa sukaji sallama.

Hajja Fannah tai birki tana dubansa. Tilon d anta da aiki ya rik e mata shi can birnin tarayya.

Bai kulada budurwar dake zaune gefe saman kujera ba ya k araso ya rungume mahaifiyarsa yana fad in yayi kewarta.




SameenaAleeyou=???

*AUREN WATA UKU..!*




*10*





*??Sameena Aleeyou&
'





Sautin kukan Ummul dake fita a hankali ne ya d auki hankalinsa. Ya d an kaikaito yana dubanta. Kanta a kife saman gwiwoyinta.

Ya maida dubansa ga mahaifiyarsa  Hajja wacece wann..?

 Kaga Hisham jeka aje jakanka. Zuwa kai akan gab a daidai lokacin da nakeda buk atan hakan dikda zuwan ba zata ka min.

Zai kuma magana ta shiga turasa tana fad in  Kaje kawai ba lokacin bayani bane yanzu.. Allah yasa da motarka kazo.


Ya jinjina mata kai yana mai nufan hanyar d akinsa. Yana tafe yana waigowa yana duban Ummulkhairi da har lokacin kanta a kife yake.

Fitowan Hisham yai daidai da mik ewarsu tsaye. Yai mutuwan tsaye yana kallon budurwar. Fuskarta fayau alamun kuka da damuwa. Bai tab a ganinta tareda mahaifiyarsa ba balle yayi tunin ko  yaruwarsu ce. Danginsu ma gaba d aya ai suna Maiduguri so baya tunanin  yaruwar mahaifiyarsa ce.

Yai tsaye daga gefe yana sauraron mahaifiyarsa dake kuma kwantar ma budurwar hankali.

Agogon hannunsa ya duba yaji ana kiraye kirayen sallar la asar. Ya d anyi gyaran murya wanda yasa Hajja juyowa tana dubansa. Sai ta maida dubanta ga Ummul tace  Yanayin kinnan anya ma kuwa kin saka wani abu cikinki Ummul.

Girgiza mata kai tai. A hankali cikin Sanyin muryarta ta furta  Kiyi hak uri Hajja na k oshi bana jin yunwa. Bazan iya cin komai ba.

Hajjah Fannah ta fahimceta dan wani tashin hankalin ya wuce gaban komai. Dafata ta d anyi  Maza shiga d akina kiyi sallah. Zan shigo na sameki.

Ta jinjina mata kai tana mai shigewa jiki a sanyaye.

Hisham ya kasa janye idanunsa daga barin dubanta har ta shige. Ya rage daga shi sai mahaifiyarsa. Ya d an bud e hannayensa yana d aga gira kafin tai masa tayin abinci  I m still full.. Don t worry about me. Ya shiga nuna k ofan d akin yana tambaya a hankali  Hajja who is she..?

Kunnensa guda ta kamo ta shiga janyosa tana fad in  Ban gama da kai ba zaka sanar dani dalilin da ya hanaka sanar dani kana tafe.

Ya d an saki k ara yana k ok arin dafe kunnensa  Yi hak uri Hajjata.. Idan na sanar dake kuma ai bai zama bazata ba.

Ta murmusa tana dubansa. Su duka biyun duban juna suke cikeda shauk i  Watau dai bazaka daina min bazata ba. Kaidak bazaka girma ba.

Ya murmusa  Na jima wann karon banzo na ganki ba shiyasa. Suka soma sabon gaisuwa Hisham na kuma tambayarta wacece wann budurwar.

Ta d an dubesa  Naga alama ka k agu kaji ko wacece ita. Yanzu dai kaje kayi sallah police station zaka kaimu..

Ya d an dakata da nad e hannun rigarsa da yake  Hajja police station kuma.. Meke faruwa ne wai.?

Ta d an lumshe idanunta had ida furzar da huci  Je kayi sallah Hisham.

Ya jinjina mata kai kafin yasa kai ya fice yana tunanin mai zaikai mahaifiyarsa ofishin  yansanda.


A natse take sanar da Hisham abindake faruwa game da kama  yaruwar Ummulkhiairi da akayi. Mahaifinta dake kwance gadon asibiti ga kuma mahaifiyarta da suke tsammanin b acewa tai. Saidai bata sanar dashi sanadin faruwar komai ba. Tinda ba huruminsa bane. Wann ma dole ne ta sanar dashi.

Hajja ta mik e  Jiramu a waje muna fitowa. Barin duba Ummul d in. Ta fad i tana nufan k ofan d akin da Ummul ke ciki.

Ta tadda ta ida sallar. Ta linke abin sallan kafin ta dubi Hajja dake tsaye tana jiranta. Hajja ta sakar mata murmushin k arfafa gwiwa kafin ta sanar da ita bak on da ta gani D anta ne dake aiki can Abuja. Yazo hutun aiki ne. Yanzu haka yana waje yana jiransu zai kaisu police station ayi belin Khulsum sann ayi filing report na missing person idan har b acewa Umma tai.

Ummul ta jinjina kai a hankali tana ma Hajja Fannah godiya. Hajjah Fannah tace ta daina mata godiya ita  ya ta d auketa.

Koda suka fito Hisham na tsaye jikin motarsa yana waya. Sam ita bazama tace ta iya tantace shi ba dan har lokacin ba wai ta dawo cikin hayyacinta bane. Karfin hali ne Kauai. Tasha jin labarin ana cewa Hajja Fannah nada D ah saurayi amma baya zama garin kano zuwa yake lokaci zuwa lokaci domin ya duba mahaifiyarsa. Duk zuwa gidan da take bata tab a arba dashi ba sai wann karon.

Back seat Hajjah Fannah ta bud e mata ta shige yayinda ita Hajjar ta shige mazaunin mai zaman banza gefen d anta.

Suna tafe saman kwalta suna kowa yayi jigum jigum. Hisham bai saba zama haka shiru da mahaifiyarsa ba. Zai iya cewa they are best of friends shida mahaifiyarsa sabida tsananin shak uwa dake tsakaninsu. Yau d in duk sai yaji babu dad i. Sai ya sata kallon Ummul ta cikin mirror yanda ya hangi Siraren hawaye basu daina sauk a saman k uncinta ba.

Ji yai ya kasa janye idanunsa daga barin dubanta. Rabin hankalinsa naga kwalta rabi naga Ummulkhairi.

Hajja Fannah takai dubanta ga mirror yanda Hisham ke satan kallon Ummul. Bata kuma cewa komai ba sai d an sauk e ajiyan zuciya da tai. Sosai yarinyar ke bata tausayi.

**
Lexus ce bak a wul taketa kutsawa cikin k ungurumin daji. Kai da gani kasan ba lafiya ba kaga motan manyan mutane irin wann na ratsawa cikin daji.

Saida sukai tafiya mai nisa daga bakin kwalta zuwa wani k ungurumin k auye da yake tsakiyan daji kafin Mommy ta juyo ta dubi driver dinta tace ya fita ya basu waje zasu tattauna. Driver yai yanda Mommy tace. Juyowa tai tana Duban k anwarta Asshe dake zaune gefenta cikin motar  Asshe kin tabbata aiki yakeyi mai kyau...

Asshe ta murmusa "Aunty Kwaise kenan. Ni ina zama ya ganni kishoyoyi sun sakani tsakiya. dole na kutsa nasan duk wani malami mai tashe da yake aiki kaman yankan wuka. Sha yanzu magani yanzu.

Asshe itace kanwar Mommy dake aure garin Kano. Mijinta D an kasuwa ne da kasuwancinsa ya zaga garin Kano harma da wasu jihohin Arewa. Su uku ne wajen mijin nasu tanada uwar gida da amarya itace ta tsakiya. Itace kuma mahaifiyar Anisa sai d an uwan Anisa mai suna Hilal.

Zaune sukai gaban gasunk umin bokan da ya ari sunan malanta ya yafa. Sumarsa furfura ya cika kama daga kansa dake rufe cikin hulan sak i har izuwa sajensa da ya zagaye fuskansa.

Wani k aton faranti ne gabanshi mai lallausan yashi a ciki. Hannunsa guda nad e cikin doguwar carbin da takai tsawonsa koma tafi. D an bukkan kuwa ko ta ina shirgi ne da tsummokara.

Asshe ta gyara zama  Allah gafarta Malam itace  yaruwata da kwanaki na labarta maka tana so a mata aiki akan d anta.

Hannu guda ya d aga ya dakatar da Asshe yaci gaba da jan doguwar carbin yana furta wasu kalmomi da basu iya tantancewa.

Lokaci guda yasa hannunsa ya shafi k asan ya zana wasu layi kusan guda uku.

Sai ya soma jinjina kai yana duban farantin  Naga AURE cikin rayuwar d anki.

Asshe da Mommy suka dubi juna.

Mommy ta girgiza kai cikin rashin fahimta  Aure kuma Malam..?

Mutumin ya jinjina mata kai cikin tabbatarwa.

 Malam anya kuwa..? Aure cikin rayuwarsa..? A gaba kenan dan a halin yanzu ko maganar mace baya so a masa balle aure da aje iyali.

Wani kwanon sha ya d auko wanda tsatsa tai mata dabaibayi ta ko ina ya nuna mata cikin kwanon mai cikeda ruwa. Take fuskar Haidar ya bayyana.

 Wann ba shine D anki Aliyu ba..?

Mommy tai saurin jinjina kai alamun eh  Eh.. Eh shine Malam.

Ya kuma kad a kai  Tabbas D anki yayi Aure ba tareda saninku ba..


Mommy ta dafe k irji cikin d imauta  Na shiga uku Ni Kwaise..! Ta dubi Asshe jikinta har rawa yake  Asshe tsanar da Haidar ke min har yakai yai aure ba tareda sanina ba.. Innalillahi wa inna ilaihi raj iun..!

Bokan ya katseta  Shi kansa baisan yayi auren ba.!

Suka dubi juna itada Asshe shaye da mamaki.

Asshe ta girgiza kai cikin rashin fahimta  Malam mai haka yake nufi ya za ayi yayi Aure bai sani ba.?

 Koda yasan da Auren baya cikin hayyacinsa akayi Auren. Aure ne da aka k ulla akan sihiri. Aure ne da aka k ullashi a Fadan dodon tsafi. Aure ne da aka masa k ulli uku mai K arfi.. Aure ne da akayi sa dan a masa farrak u da Iyayensa.!

Jikin Mommy ya d auki rawa. Zufa ya shiga keto mata ta ko ina  Malam.. Auren sihiri fah kenan. Na shiga uku ni Kwaise.. Haba biri yayi kama da mutum. Na fad a Haidar baya cikin hayyacinsa. Malam wace shed aniyar ce ta shigo rayuwar d ah na dan ta rabamu..?

Ya kuma zana k asa yana fesa ruwan bakinsa saman yashin  Saninta bazai miki amfani ba dan D anki bazai tab a bud e baki ya sanar dake gameda wann auren nasa ba.

Mommy ta soma girgiza kai  Malam duk yanda za ayi a karya wann mugun sihiri da aka masa. Ni kuma nayi alk awarin ko nawa ne zan kashe domin na dawo da d ah na cikin hayyacinsa.

Girgiza kai ya soma yana aje wani igiyan guru saman tray d in  Abinda k asa ya hasko min shine an bisne wann asiri a wani waje yanda ita kanta wann matar da yake tareda ita matsayin matarsa bata san yanda tukunyar sihirin yake ba. Wani wanda yakeda burin ganin bayan d anki da ma ahalinki gaba d aya ya mallaki tukunyar ya mata ajiya mai nisa. Dan a yanda k asa ya hasko mun ita kanta wann matar da umarnin wani take aiwatar da komai.. Har sai wann tukunyar ya fashe kurwan d anki da aka d aure ciki ya kub uta.

Zufa yaci gaba da karyowa Mommy  Na shiga uku ni Asshe waye mai burin ganin bayan ahalinmu irin haka..? Yanzu Malam ba yanda za ayi a fasa wann tukunyar.?


Ya kuma zana k asa sau uku sai kuma ya d ago ya dubi Mommy  Da sihiri ake karya sihiri.. Akwai hanya d aya tak da za abi a karya wann sihirin.

Daga Asshe har Mommy rige rigen tambayar hanyar suke.

 Wani Auren shi zai karya wann Auren.. Sabida asirin ajikin d anki akayi..!

Mommy ta girgiza kai  Kana nufi idan yayi wani auren shikenan asirin zai karye.

Shiru yai kaman mai nazari sai kuma ya jinjina kai  Aure ne ba kaman ko wani Aure ba. Aure ne da yake k unshe da sharudd a.. Aure ne da za ayisa domin warware wani auren. Aure ne da ba ko wace irin mace za a aura ba sai macen da ta cika k a idodin da zan sanar daku. Aure ne da yakeda iyaka wa adin da zai rayu. Aure ne da zai wanzu a tsakanin watanni uku tak.. AUREN WATA UKU..!




SameenaAleeyou=???
*AUREN WATA UKU.!*



*11*






*??Sameena Aleeyou&
'



Mommy da Asshe suka dubin juna cikin k ullewan kai.

 Malam sharud a kuma.. Wasu irin sharud a kenan..? Sann Kaman ya AUREN WATA UKU.? Asshe ta tambaya tana dubansa.

Ya kuma d auko wasu layu da guru

10 / 52