Auren Wata Uku Book Complete By Sameena Aliyu.doc

Author :  Sameena Aliyu Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   20 / 52

57K to 60K   out of 153.1K words

ya kusa datse duk wata alak ar dake tsakaninsu. What exactly is going on..? Kasa nemo amsar da Tai ya sanyata k arasawa saman kujera ta zauna tana kuma fad awa duniyar tunani.

**

Ita dai tana Jin yanda makeup artist d in keta faman zuzuta kyaun da tai amma bata tanka ba. Dan physically ne kawai take wajen amma tinaninta da hankalinta basu a wajen. Duban fuskar nata take cikin madubi Wanda dukda makeup d in ba mai tsanani bane. Amma abinka da wacce bata saba ba sai take ganin kaman an canza mata kamanni ne . Dama tin can ita ba gwanar kwalliya bace balle yanzu da take tsaka mai wuya. Bata tab a tsammanin Umma zata tafi da nisa har haka ba. Tana jin sanda su Umma da Aunty Asshe suka shigo sai faman zuzuta kyaun da tai suke. Lafaya ne Wanda kallo guda zaka masa ka tabbata Ya amsa sunansa kalan peach Wanda Ya dace da skin color d inta da bai cika haske ba haka nan kai tsaye baza a kirata bak a. sai black long sleeve shirt daga ciki, an kwantar da lallausar bak ar sumarta da Ya sha gyara daga gefe.

Asshe ta k araso da sauri ta mik ar da ita tsaye  Wow! lallai za a haifo mana Fulata shuwa. Yauwa  yar albarka Uwar alkhairi.. Maza muje masu hoto suna parlor suna jiran fitowarki.

Ummul ta d ago ta dubi Umma amma sai taga Umma ta kauda kanta gefe alamun bazata saurare ta ba. Cikin sanyin jiki ta soma jan k afafunta tana biyeda Asshe wacce ke rik e da ita. Can k asar zuciyarta bata komai sai ambaton Allah domin ya shiga lamuranta.

Suna fitowa parlorn suka tadda masu d aukan hoto har kusan mutum uku. Tai tsaye tana duban masu hoton wanda k arasowarta kawai suke jira komai nasu ya zama ready. Ji tai kaman kar ta k arasa wajen amma sai maganar Aunty Asshe ya fad o mata  Kud in Aurenki shine kud in aikin mahaifinki Ta d an d aga k wayan idanunta sama cikin k ok arin hana hawayenta zuba. Tamkar kazar da k wai ya fashe ma a ciki haka take takowa cikin parlorn. Ta k arasa ta zauna yanda masu d aukan hoton ke nuna mata. Lokaci guda zuciyarta na karanto mata  Komai da kike gani na faruwa akwai dalilin faruwarsu Ummulkhairi.. Ita rayuwa jarabawa ce gaba d ayanta. Allah yayi tanadi wa masu hak uri kaman yanda yayi alk awari.. Watak ila kasancewar Umma a matsayin mahaifiya a gareki shine babban k alubalenki a rayuwa.. Kiyi hak uri kiyi mata biyayya.. Har abada bazaki tab e ba. Da wann batu na zuciyarta taji k warin gwiwa na d an zuwa mata.

Umma ce mai nuna mata styles d in da zatayi har gyara mata zama take tana fad in tai murmushi kyaunta ya bayyana. Kuji fah.

Izuwa lokacin Ummul ta daina mamakin Umma sai addu a da take wa mahaifiyar nata cikin zuciyarta.

Aka d auki hotuna aka gama dikda cikin idanunta akwai alamun hawaye a duka hotunan amma kam tayi kyau TabarakAllah ma sha Allah inji Aunty Asshe. Fad i take d ansu yayi dacen mata.

Bayan Asshe da Umma sun keb e Umma tace  Toh yanzu meye abu na gaba Hajja Asshe.?

Asshe tace an tura ma mutumin da zai wanke hoto can Abuja ya kai ma  yaruwata. Yau zasuga Amaryarsu Ummulkhairy a hoto kafin su ganta a zahiri.

Umma ta lumshe idanu had ida sauk e ajiyan zuciya. Lokaci guda ta d aga hannuwa sama  Ubangiji kasa an dace.. Allah yasa Ummul d ina ta dace.. Allah na rok eka ka jefa k aunarta cikin zukatansu a kallon farko..

Asshe ta murmusa ta dafa Umma  Anma dace in sha Allahu. Kinsan dai ance wai gani ya kori ji Shiyasa za a aika masu hotunan Ummul su gani su shaida amma  Yaruwata da D anta basuda matsala. Yanzu Abu na gaba sai maganan kai lefe da saka rana.. Inaso duka ayi su a gobe ne. Amma kafin nan dole mu samu magabatan Ummul ayi magana.. Kinaga dangin mahaifinta zasu amince su bamu aurenta.?

Umma tai shiru kaman mai nazari. Cikinta ya bada wani sauti k uuu.! Ita sai yanzu ma ta Tina da za azo wann gab ar. Ta soma  yan kame kame. Sai kuma ta nusa tace   yanuwansa basa jituwa dashi abinki da gidan da  yanubanci ya raba kai. Yaruwarsa mace ce guda d aya tak, kuma itama Sun raba gari tinda jimawa. Kuma mace ai bata bada aure. Kaf  yanubansa ne gidan Wanda ba wani ganinsa da gashin ido suke ba.. Idanun Umma suka kawo ruwa murna na Neman komawa ciki take duban Asshe  Toh.. toh.. Yanzu mai zai faru idan suka k i amincewa su bada auren Ummul..?

Saurin katseta Asshe tai  Haba Suwaiba kin faro abu da zafinki kar ki badani mana& Keda kike da babban makami.. Bakiga yanda kika aje Kishiyarki a yanda ya Kamaceta bane..? Ai kud i Sune jigon rayuwar nan Suwaiba. Idan kud i na aiki toh na tabbata Miki zasu bada auren Ummul ba tareda wani b ata lokaci ba dan nayi imani kaf d insu fama suke da rayuwar nan ta yau..

Umma ta jinjina Kai  Kuma fah kince wani abu dan ko yau d in nan da naje nai rabon kud in ina ganin Baballe ya amshe Wanda na bawa D ansa ya soke a aljihu.. Kunya ce ta hanasu nasan suma da Sun shiga layin rabon kud in..

Asshe tace  Ah toh kin gani ko. Ke fah yanzu sai abinda kika ce a wann gidan. Ta k arada  Ita kuma Ummul zata zauna a nan a mata  yan gyare gyare na amare.. Mai gyara na musamman na d auko daga can gida Maiduguri.Kuma kinga dai yaro ne d an gayu Wanda rabin rayuwarsa turai ne Ya saba cin karo da matan turawa da wayayyun mata da suka goge. Kinga kuwa dole duk wacce zata je matsayin matarsa ta wanku da kyau ta kuma k ara samun gogewa gudun kar a samu matsala dukda ko a haka aka kai masa Ummul na tabbata baza a samu matsala ba amma kinsan ance idan kanada kyau ka k ara da wanka. Kinsan sha anin d an yau. Ta d an gyara tsayuwarta  Sann zamanta a can gidan naku wani tsautsayin na kuma giftawa Wanda bazamuyi fata ba. Kinga Har kawo wann lokacin kishiyar ki batasan abinda ake shiryawa ba.

Umma tai karaf tace  Ai Kinga wann  yaruwar tata da ta fice ko bala inta kad ai Ya isa ya iya jawo wani matsalan tinda kinga a nan take ce mata su gudu. Toh kafin ta koma can na shafa cikin dare naji sun gudu gwara ta zauna a nan asiri na a rufe a kula da ita idon masu ido bai ganta bakin masu baki bai tofa ba.

Asshe ta jinjina kai  Cikin kwanaki k alilan komai zai kammala da yardar Ubangiji Ummul d inki ta shige d akin aurenta mafarkin ki ya zama gaskiya.

Umma sai ta fara hawayen farin ciki tana fad in shikenan burinta yana gab da cika. Allah zai cika mata wann buri nata daga k arshe.

Asshe ta girgiza kai kafin ta fice ta bawa Umma waje tai mai isarta.


A haka Ummul ta k araso ta tadda Umma wacce itama hawaye ne kwance saman fuskarta.

Ta k urawa mahaifiyarta ido. Sai kuma tasa bayan hannunta ta share hawayen dan taji kaf tattaunawar da su Umma sukai.

 Alfarma d aya zan rok eki Umma. Ta fad i cikin rawar murya.

Umma ta dubeta wann karon hawaye ne saman k uncinta.

Ummul taci gaba  Ki kaini wajen Abba na gansa nai masa Sallama kafin ku killaceni a wann gidan.

Umma ta jinina mata kai tana sakin murmushi ta kamo hannayen Ummulkhairi  Zamuje Ummul. Zamuje kiga mahaifinki. Sann zan baki labarin duk abubuwan da suka faru dalla dalla tin daga lokacin da Tani ta fatattake ni naje na nemo kud ad den jinyar mahaifinku.

Bayan Umma ta labarta komai dangane da had uwarsu da Asshe da irin duk wani taimako da Asshe Tai mata. Da buk atan Asshen na nema ma d ansu aurenta. Jinina kai Ummul tai ba tareda tace komai ba dan kalamai sun k are saman harshenta. Abinda yai mata saura hawaye ne Wanda suma d in batada tabbaci idan basu kusan k arewa ba.

Driver ne ya d aukesu Ya kaisu Har asibiti wajen Abba.

Mama dake zaune a haraba tana hangosu ta mik e cikin sauri ta nemi wajen b oyo ta b uya yayinda Ummul da Umma suka shige d akin.

Umma ta dubi Ummulkhairy tace  Zan barki ki gana da mahaifinki Ummul. Ku biyu.

Ummul ta jinjina mata mai tana goge hawayen da suka kwararo mata.

Ummul zaune gaban gadon mahaifinsu Wanda idanunsa ke lumshe, ta saka bayan hannunta ta share hawayen da suka gangaro mata, abubuwan da suke faruwa da ahalinsu sai gifta mata suke a k wayar idanu. Ta d aura hannunta guda saman na Abba. Cikin rawar murya take furta  Abba tinda ka kwanta komai bai k ara daidaita ba.. Umma ta canza Abba.. Sai kuma tai shiru tana share hawayenta  Abba koda bana nan& Ban sani ba ko zamu sake had uwa ba ko bazamu sake had uwa ba. Abba ka yafe wa mahaifiyata a bayana. Dan Allah ka yafe ma Umma.! Kuka ya hanta ci gaba da magana.

Da k yar kukan nata Ya tsagaita kafin taci gaba  Abba bazanso wani wanda ba kai ba ya aurar dani. Watak ila Umma ta hana maka wann damar ne domin ceto naka rayuwar.

Muryarta yaci gaba da rawa  Abba banida wani zab i.. Rayuwarka na kan gab a a nan.. Watak ila wann shine maslahan ahalinmu. Watak ila komai zaizo k arshe. Watak ila ni ce matsalar. Watak ila idan nayi nesa daku zaman lafiya da kwanciyar hankali zai wanzu tsakanin ahalin. Abba zanyi duk wata sadaukarwa sabida ahalina. Ka yafe mun Abba. Kuma ka yafe wa mahaifiyata . Ta k arashe tana mai kifa kanta gefen Abba hawaye na kuma kwararo mata.

Mama dake lab e bayan window ta waje taji duk abinda Ummul tace. Wato Suwaiba ta shirya aurar da Ummulkhairi ne a sirrance..? Shin wann shine dalilin canzawan Suwaiba..? Aiko idan haka ne sai taga ta yanda za ayi wann aure.. Idan Suwaiba tasan wata bata San wata ba. Toh amma ta ya zata b ata auren tinda Suwaiba bata nuna masu mijin Ummul d in ba.? Kar dai Suwaiba ta samo attajiri ne ma Ummul d inta.. Idan har al amra sukaci gaba da tafiya a haka kenan fah Suwaiba zata zamto sarauniya a gidan. Sai abinda tace. Harta  ya yan cikinta su Azeema sai Sun gagareta. Tin yanzu ma komai ya canza balle abubuwa suci gaba da tafiya a haka.. Uwa uba Har kawo wann lokacin basu saka Tasi u a idonsu ba... Dawowan Suwaiba dik shi ya karkata masu hankali ta kasa aiwatar da komai gameda b cewan Tasi u. Toh inaga Abubuwa sunci gaba da tafiya a haka.? Yanzu ita fah zata tashi a tutan babu kenan ga Suwaiba ta dawo da sabon sauyi..

Mama ta koma gefe saman benci ta zauna had ida buga uban tagumi. Kallo d aya zaka mata ka fahimci duniyar tai mata atishawan tsaki. Sai faman sauk e tagwayen ajiyan zuciya take tana canza salon tagumin ta. Babu babban abinda ya bata takaici kaman da ya kasance yanzu dik abinda suke ci daga wajen Suwaiba ya fito.. Shikenan Suwaiba fah ta amshe girman nata. Abinda yai saura kawai shine Suwaiba ta umarceta ta soma kiranta da Yaya.

Saiga Mama na hawaye tana fad in har abada bazata bari Suwaiba tai nasara akanta ba. Idan abinda zata aiwatar k arshe shine hana yuwan auren Ummulkhairi ta shirya yi. Da dai ta bari Suwaiba tai galaba akanta gwara tai komai dan nasara nata ne da yaranta ba na Suwaiba da nata  ya yan ba. Da wann tunani ta mik e tagajan magajan domin kaw zama bai ganta ba.

*
Kan Ummul na kife gefen mahaifinta tana ci gaba da cazgan kuka mai ban taisayi.

Umma ta k araso ta dafata.

Ummul batace komai ba Har Umma ta ta k araso wajen.

 Tashi kije Ummul direba yana jiranki. Ki sani bazan bari ki koma gidan mahaifinki ba har sai ranan Aure gudun kar wani abu ya gifta. Kindai san matsalarki da abubuwan da mukaita fuskanta a baya na fashe fashen Aurenki. Wann karon ban shirya ba ma wani k ofa ya lalata Aurenki ba. Naga Tani bata nan a nan, zan zauna wajen Abbanku Har Tani ta dawo. kuma zan karanto masa komai koda bazai bud e idonsa ba na tabbata kunnuwansa da zuciyarsa zasu saurareni.

Ta murmusa tana duban Ummul  Na tabbata a yau mahaifinki ya farka ya ganki a d akin Aurenki zaifi kowa farin ciki sann wann kad ai Ya isa ya zama silan yaye damuwar dake k unshe cikin zuciyarsa.

Dubanta kurum Ummul Tai ba tareda ta iya cewa komai ba. Har yanzu dai a idon Umma itace matsalar ahalinsu da k addararta.

Ta kuma juyowa ta dubi Abba hawaye suka kuma gangaro mata. A hankali ta isa ta tofa masa addu o i kafin tasa kai ta fice jiki a mace.
**

Abuja..

Zaune suke gaba d aya a nan lambun dake farfajiyan gidan. Mommy Daddy harma da Anisa.

Mommy dai bata sama bata k asa gaba d aya kana ganinta zaka hango tsantsan farin cikin da take ciki.

Ta dubi Anisa tace maza ta sami one of the mades su shirya wajen cin abincin mutum guda.

Daddy ya dubeta  Are you expecting someone.?

Mik ewar da Anisa zatai ta hango shi ya nufo garden d in. Looking handsome as always. Zuciyarta yai wani irin yankewa.

Mommy ta fad ad a murmushinta tana nuni da Haidar dake k arasowa  Oh! He s here already. Ta maido da dubanta ga mijinta  Ya kamata mu rinka samun lokaci irin haka na musamman domin ahali. After all, amarya za a kawo mana very soon.

Baice komai ba yaci gaba da abinda yake. Dan yanzu ya kula Kwaise batada zance sai na auren D anta.

Haidar ya k araso Mommy na masa sannu da zuwa. Sai nan nan dashi take. Wani sabon kula da soyayya take nuna masa abinda bata masa a baya ba. Kaman tayi ma wofi haka ya d auki abun tinda yasan ba dan Allah take ba.

Koda Anisa ta kawo plate karb a Mommy tai tana k ok arin serving d insa sai haba haba dashi take tana tambayarsa me za a zuba masa.

Cikeda k osawa Haidar Ya rik e hannunta Ya amshi plate d in  Mommy please that s enough, I can do it myself. I ve been doing it since childhood.

Jikinta ya d anyi sanyi ta soma Tina ita dai tin tasowarsa tin yarinta bata tab a tambayarsa yunwan cikinsa ko lafiyarsa ba. Masu aiki da Nannies Sune suka San lafiyarsa, cinsa ko shan sa. Har yayi ciwo ya gama bata san yayi ba kuma ba matsalar ta bane. The only abu da take tambaya ta kuma tada hankali akai shine karatunsa na boko da sakamakon da zai birge mahaifinsa. Idan kuwa bai kawo sakamakon da zai birge mahaifinsa ba ranan zai wuni ne a d aki mai duhu kuma a kulle cikin tsananin horo.

Mommy ta gyara zama ganin table d in Ya b ata shiru sai sautin cutlery dake tashi cikin plates.

Ta d an murmusa tana duban Haidar  Ya labarin aiki.. Ina nufin sabon project d in naku.. Kun fara ne.?

Yasan so take tai creating hiran da zai had asa magana da mahaifinsa. Ya d an girgiza kai kad an  Still ironing out the details.. Ya d ago yana dubanta sosai tinda yasan tasan komai  In a couple of months, Mommy. Let s say two to three months.

K arasowar wata mai aiki rik eda k aton frame a rufe Ya katse Mommy. Mai aikin ta k araso cikeda ladabi ta tsaya nan bayan Mommy rik eda frame d in tana sanar da ita security ne Ya shigo dashi.

Mommy ta jinjina Kai tana mai nuna mata yanda zata ajiye.
Ta maidoda dubanta ga Ahalinta tana kuma fad ad a murmushinta  Na had a mana wann cin abincin ne a tare domin na gabatar mana da wani mihimmin abu. Musamman gareka Haidar. Ta k arashe tana mai isa jikin frame d in.

Ta shiga bud ewa sannu a hankali tana mai furta  Kyakkyawar Amaryar mu. Matar D anmu Haidar. Sirkarmu wacce zata zamto silan dunk ulewar ahalinmu.

Cak ya tsaya da abinda yake. Lokaci guda yana mai matse fork and knife dake rik e cikin hannunsa. Bai iya janye idanunsa daga saman plate d in ba haka nan bai dubi hoton da mommy ke nuna masa ba wacce ta ambaceta da matarsa.

Girgiza kai Daddy yai yana tunanin matarsa ta zauce da wann auren da take yunk urin yima d ansu. Ya d auki tissue had ida goge bakinsa. Ya dubi Mommy kafin yace  Are you in your right state of mind. What s the meaning of this Kwaise.?

Mommy tace  Gani ya kori ji Engr. Matar Haidar ce. Idan ba a hoto ba nasan bazaije ya ganta ba har sai Randa aka kawo mana ita gidan. So kafin a kawota yak i amincewa yace gaibu na auro masa. Gwara na samu dalilin kafa hujja. Look kalla kaga, zasu dace da Haidar.. Asshe ta iya zab e. Ta k arashe sai duban hoton take tana murmushi.

Daddy dai kallon wacce ta samu matsala yake mata. Lokaci guda ya

20 / 52