Auren Wata Uku Book Complete By Sameena Aliyu.doc

Author :  Sameena Aliyu Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   35 / 52

102K to 105K   out of 153.1K words

kad an ganin Anisa ta tsareta da ido  Fine, naji.. What do I get in return dan wann karon shiri babba zamuyi wanda bazata iya tsallakewa ba.

Anisa ta jinjina Kai tana murmushi  Idan har kika taimaka min na zama matar Haidar komai mai sauk i ne Leenah. I promise not to let you end your life Washing clothes with bleach just to keep them white.

Leenah ta jinjina Kai tana murmushi  Lokaci yayi da zakiyi abinda kike tsoro Anisa.

Anisa ta dubeta cikin rashin fahimta  Kaman yaya..?

Leenah tace  Your ultimate goal is to get rid of her for good. Right.?

Anisa ta jinjina Kai  K warai kuwa.

Leenah ma ta jinjina Kai  Good..! Then make her disappear for good..

Anisa ta kuma girgiza Kai  But how.?

 Kill her Neesa.! Poison her once and for all.

Anisa ta zaro ido waje  A a Leenah.. What what if our plan fails again..? Kaman dai sauran..?

Leena ta dubeta  Anya da gaske kin shirya Anisa..?

Anisa ta dubeta a d an tsorace  Mai a zai faru idan bataci poison din ba.?

Leenah ta murmusa  Ba ko wani poison bane ake ci Anisa. Wani shak ansa ake a iska. A hankali yake lalata lungs kafin a ank ara sai gawan mutum. Kinga irin wann babu wanda zai zargeki. Ta k arashe da murmushi saman fuskarta.

Anisa ta murmusa  Yayi. Yanzu ya za ayi mu samu.?

Leenah ta murmusa  Wann mai sauk i ne ki bar min komai a hannuna. Nasan kudi bazai zame miki matsala ba.

Anisa taita murna tana mata godiya. Akan haka suka rabu washe gari suka had u a mahad a.

Leenah ta ciro wani mistitsin kwalba cikin jakanta ta mik a ma Anisa. Anisa hannu na rawa ta amsa dan kwalban da wani ruwa mai kaman acid ciki.

Anisa na juya kwalban Leenah ke mata bayanin yanda zatai amfani dashi.

 Cikin turaren da take yawan amfani dashi zaki zuba kad an. Muddin tana shak an wann turaren bazata wuce kwanaki uku tana numfashi ba.

Murmushi Anisa tai. Cikin zuciyarta take fad in Yazo gidan sauk i dan ta kula Ummul tana yawan shafa turaren humra da ta kai mata a kwanakin baya Wanda ta sauya turaren da Mommy ta bata dashi. Tabbas zata zuba mata a ciki.

Leenah ta dubi Anisa had ida gyara zamanta  A baya nayi zaton Hajiya Kwaise bazata tab a bari D anta ya auro d iyar talakawa ba. Nafi tunanin iyayen Haidar zasu nema masa aure ne daga babban ahali. A well known and influential family. Like business partners d insu ko d iyar manyan  yan siyasa kodai d iyar masu mulki. Amma na sha mamaki yanda ta auro ma d anta wann yarinyar.

Anisa ta jinjina Kai  Ba ke kad ai kike mamaki ba Leenah. Shiyasa zuciyata ke tabbatar min akwai wani Abu a k asa k ark ashin wann auren. Massive love d in da Mommy ke nuna ma yarinyar yafi komai d aure min kai. Ko ni nan da nake tamkar  yarta sann mahaifina is a successful businessman banyi zaton zata bari d anta ya kawo mata ni matsayin sirka ba sanin ko wacece ita. Nafi zaton zata tafi da nisa sai gashi ta k are a  yar talaka. Ke da ganin wann al amari kinsan akwai lauje cikin nad i. And believe me I vow to find out whatsoever she s hiding.

Leenah ta jinjina Kai  Ta haka ne kawai zaki fahimci komai Neesa. Idan kika kashe yarinyar.

Anisa ta jinjina Kai tana tabbatar da kalaman Leenar.

Daga bisani godiya tai ma k awarta Leenah sukai sallama Leenah na fad in sai taji result.

Koda Anisa ta koma gida cikin hikima da dabara ta zuba wann ruwan lungs poison da Leenah ta bata cikin turaren Ummul.

Ta dawo d aki tai relaxing tana sakin murmushin nishad i. Nan da kwanaki biyu zuwa uku mataalarta zai kaw. Saidai a fidda gawan Ummul daga gidan. Dan ta tabbata wann karon Ummul bazata haye tuggunta ba.

A fili take furta  Mommy ki gama duk wani shirin da zaki mata. Haidar gawar Amaryarsa zai dawo ya tadda. Tana Ida fad in haka ta fashe da dariya.



SameenaAleeyou=???


*AUREN WATA UKU..!*




*30*







*??Sameena Aleeyou&
'

Tinda jirginsu tai landing a Nigeria Dareen ta rasa sukuni. Ta kula akwai mihimmin abinda yasa suka yanke hutun nasu suka dawo gida Nigeria. Toh amma rashin sanin mak asudin dawowar tasu shi yafi komai d aure mata kai. Da fari tayi zaton project d insa yasa ya dawo amma daga bisani ta kula kaman dai abun nada alak a da ahalinsa ne musamman ma mahaifiyarsa. Meyasa duk irin aikin da suka tabbata anyi kan Haidar d in da iyayensa kaman bai wani tasiri tsakaninsa da mahaifiyarsa ba. Kaman dai Har yanzu shid in koda bai nuna ba can k asar zuciyarsa yana kwad ayin Ya mata biyayya. Dan taga call history nasu a wayarsa shida mahaifiyarsa. Kuma tinda sukai wann wayar ya yanke decision d in dawowa gida. Tabbas ya zama dole ta koma wajen Dodon kobuku ta sanar dashi halinda ake ciki. Tana so aimata aiki na musamman akan mahaifiyar Haidar wacce take ji a jikinta ita d in nema take ta zame mata barazana. Sann wann zuwan da zatai bazata bari Shadow ya sani ba. Aiki ne da za a mata ita kad ai. Ya kamata ta saka rana ta tafi gida Ilorin dan ta gana da Dodo Kobuku. Ta k arashe tunanin tana kallon fuskar Haidar dake kwance yana baccin gajiyan hanya. Fuskar tasa tayi fayau tamkar Wanda baida wata damuwa. Ta murmusa zallan k aunarsa takeji na bin duk wani vein na jikinta. Ta Shafa fuskarsa a hankali. Can k asar zuciyarta take furta  You are mine Haidar Maitama. Ni kad ai na. I won t allow anybody to come between us. Not Shadow, not even your own parents. Idan shiga tsakaninku is not enough zan b ullo maku ta wani hanyar. Idan ta kama na kashe rai ne akan ka zan kashe. Koda mahaifiyarka ce dan na kasance dakai zanyi Haidar. Kaid in nawa ne. Ni kad ai.! Ta k arashe tana tsura masa ido.

**

Tin farar safiya take gidansu Leenah, ta kasa zaune ta kasa tsaye. Zuciyarta ya cika da tsoron abinda ka iya zuwa ya zo. Yau kwanaki uku kenan da ta zuba poison din cikin turaren Ummul. Ta tabbata izuwa wann lokaci komai zai iya faruwa dan gaba d ayan ranan ma bataji d urin Ummul d in ba. Ta dubi Leenah dake zaune hankalinta kwance tana kallon American movie ta k araso ta zauna kusan Leenah zuciyarta sai tsinkewa yake  Hey.! What if she s dead by now.? Ko kuma ta shirya min wani makircin tinda kinsan makira ce ta gaske..! Anisa tace duk a tsorace.

Murmushi Leenah tai tana jefa popcorn a bakinta  You know what Neesa, you should stop being paranoid idan ba haka ba a banza zaki sa ko wani Abu ya sameta a zargeki. And if that happens believe me I won t come to your aid. So ki kwantar da hankalinki ki tashi ki koma gidan ki tabbatar da abinda ya sameta. Ta k arashe tana duban Anisa.

Jikin Anisa har lokacin a mace yake sanin ko wacece Ummul d in tinda ta tsallake tuggunsu har guda biyu. Idan ta tsallake wann din ma ba abin mamaki bane. Babban abinda yafi bata tsoro shine wann ya k unshi kisan kai ba kaman sauran ba. Bata kuma cewa komai ba sai zama da tai can gefe tana ci gaba da tunanin abin yi. Dan tsoronta d aya ji take kaman idan ta koma gida Ummul zata kamata, reshe zai kuma juyewa da mujiya kaman ko yaushe. Da kyar ta iya tashi tai Sallama ma Leenah ta nufo gida duk jikinta a mace.

Daga can nesa tai tsaye tana hangen sashen Ummul amma bata shiga ba dan har lokacin zuciyarta bai daina bugawa ba. Sauri sauri ta nufi nata d akin tana tambayan maids ko Ummul ta shigo. Nan wata maid ke sanar da ita bataga shigowarta ba. Da haka Anisa ta nufi d aki duk a tsorace take. Tana shiga ma kwanciya tai saman gado ta sanar sa maid d aya ko Mommy ta neme ta tace mata ta dan kwanta bata Jin dadi.

Kwanciyarta da kad an ta hango mota bak a k irar Mercedes GWagon. Gabanta yai wani irin tsinkewa dan wann motar tasan ta Haidar ce. Yaushe Ya dawo.? Da gaske shine ciki.? Kodai idonta ne ke mata gizo.? Da gaske Haidar ne Ya dawo.? Take taji jirin gaske na neman kada ita sanda ta diro daga saman gado. Ta isa jikin window a guje dan tabbatar ma idonta.

Shid in ne dai looking handsome as always a cewarta. Gani tai ma ya k ara k warjini da kyau. A hankali ta furta  Haidar& Mai ka dawo yi..? Meyasa bazaka jira ta cika ba.? Meyasa zaka dawo yanzu..? Ji tai tana son sanin halinda Ummul ke ciki kafin Haidar Ya cimmata. Sauri sauri tai nufin fitowa daga d akin sai kuma taja ta tsaya kaman wacce ta tuna wani abu zuciyarta na kuma bugawa. A hankali ta koma da baya ta zauna zuciyarta bai daina bugawa ba.

A b angaren Haidar kaw tsaye ya hange mahaifiyarsa gaban tsohon hotonsu Wanda akai tun yana k aramin yaro d an shekara 10 Wanda bayan shi baya tunanin sunada wani family picture tare.

Hawaye take tana Shafa hoton, at same time tana ci gaba da furta  I want nothing but the best for you.. I know I ve never been a good mother to you.. But please give me a chance Haidar.. Ka bani dama na gyara kurakuran da nai a baya. Just this once.. Kuka ya hanata ci gaba da magana.

D an kauda fuskarsa yai cikeda k osawa dan yasan hakan bazai wuce d aya daga cikin acting d inta ba. Yasan bazai wuce ta hangi motarsa ne ko taji shigowarsa shine tazo gaban picture d insu take wann wasan kwaikwayon nata in order to gain his sympathy.

 Nice performance Mommy.! I m here already. I guess the show is over. Yace yana k arasa shigowa parlorn.

Mommy ta juyo cikeda mamaki tana dubansa. Ta kuma mutsuka idonta. Sai taji murmushi na zuwa saman fuskarta.

 Haidar.. My Son..! Ta furta cikin rawar murya hawaye basu daina ambaliya a fuskarta ba.

Sai Ta isa da sauri ta rungume shi kukanta na k aruwa. Tsam ta rik e sa cikin jikinta. Tana hawaye take furta  I knew it.. I knew You d come back to me.. To your family. Nasan zaka dawo garemu Haidar.. Nasan bazaka bani kunya ba. Sabida kai d in D ana ne..

Duk sunbatun nan da take ji yake ta cika masa kunne. Yai k ok arin cireta daga jikinsa da k arfin gaske.

 Don t get it wrong Mommy. Idan na dawo na dawo ne kawai sabida project d in amma ba sabida ke da k udirinki ba. Yace yana duban mahaifiyar tasa dake tsaye gabansa tana kuka cikin sanyin jiki.

Mommy ta jinjina kai  Even so Haidar. I m glad ka dawo sabida project d in. Nafi kowa farin cikin dawowarka. Your wife is waiting for you Aliyu.. She s been waiting for you for the past two weeks..


Bata kai aya ba suka soma sinkayo hayaniyar wata  yar aikin gidan tana ihu tana kiran Mommy.

Gaba d aya Haidar da Mommy suka juyo a tare sanda maid din ta shigo tana haki.

Anisa da hayaniyar ya sanyata fitowa ba shiri ita ta tari maid din da tambayar meke faruwa ta shigo haka tana ihu.

Cikin haki take sanar dasu ta shiga kai abinci section d in Ummulkhair amma ta tararta a kwance lifeless.

Mommy da taji batun bagatatan saurin k arasowa tai tana jijjiga mai aikin tana tambayarta mai take cewa. Mai aikin ta kuma nanata binda tace.

Babu shiri Mommy ta fice ba tareda ta bi takan kowa cikinsu ba ta nufi sashen Haidar.

Yayinda Anisa taji kama an yaye mata duka damuwarta. Daga k arshe dai burinta Ya cika.

Yanda Mommy taga Ummul kwance k asa tamkar maras numfashi sai ya kuma gigitata. Ta shiga jijjigata tana ambaton sunanta.

Mik ewa tai cikin kuka tana fad in ma aikatan gidan su kira ambulance amma kafin tai wani aune sai ganin Haidar tai ya ciccib i Ummul d in Ya nufi motarsa da ita yana Anisa ta isa ta bud e mata bayan motar.

Mommy ta biyo bayansu cikin sauri Har lokacin hawaye take.

Anisa jikinta duk a mace ganin Haidar ya d auki kucakar nan ya sakata motarsa harma cewa yake ta bud e masa motar.  Kan uba toh wllhi ka d auki wofi domin kuwa fanko ce wajen gawa ce Babu rai. Ta fad i haka cikin zuciyarta.

Mommy ce ta shiga bayan motar ta d aura kan Ummul saman cinyarta yayinda Anisa tai maza ta shige gaban Motar Haidar ke driving.

Yanda hankalin Mommy ya tashi dole ta baka tausayi. Dan kuka take da gaske tana fad in Ummul ta tashi kar ta tafi ta barsu ga mijinta Ya dawo gareta.

Daga Anisa Har Haidar d in sumbatun Mommy ya cika masu kunnuwa cikin motar. Allah Allah suke a isa asibiti ko sun huta da sunbatun Mommy.

Suna isa Ya kuma d aukanta suka nufi cikin asibitin da ita. Take Likitoci suka amsheta aka nufi ER da ita.


Nan suka zauna suna jiran ba asi daga Drs. Har lokacin Mommy kuka take yayinda Anisa ke addu an Allah yasa a fito da sakamako mai dad in sauraro a kunnuwarta ma ana ta mutu.

Ganin Mommy bazata daina kuka ba yasa Haidar mik ewa Ya zira hannayensa cikin aljihun wandonsa. Kukan da Mommy take irritates him musamman idan yaji tana ambaton yarinyar ta tashi mijinta ya dawo gareta. Gaba d aya ji yake zuciyarsa a cunk ushe. Meyasa ma bazai tafi ba.? Zaman me yake a asibitin.? He did what he had to do sanda yaga yarinyar kwance lifeless. Ya kawota asibiti. Toh zaman mai zaici gaba da yi.? Yai gajeren tsaki sanda ya kuma duban Mommy dake ci gaba da matsan hawaye. Wani b angare na zuciyarsa na sanar dashi ka zauna ko dan mahaifiyarka. Ya kuma yin tsaki wai shi Haidar ke yin abu dan mahaifiyarsa matar da bata da wani buri bayan taga ta k untata masa. Ya kuma yin gajeren tsaki yana mai duban k ofan ER din.

Can gefe ya matsa dan baya son sauraron kukan da Mommy take.

Anisa sai satan kallonsa take da duk wani motsinsa.

Wayarsa ce ta soma ruri Ya fito da ita daga aljihu nan yaga Dareen ke kiransa. Bai amsa ba sai Ya maida wayar aljihu Har ta k arashi ringing d inta.

Hankalin Anisa sosai ya kuma tashi ganin Haidar baibi takan wayarsa ba sann ga damuwa k arara Ya nuna saman fuskarsa. Mai hakan yake nufi .? Ba dai Haidar damuwa yai da wann kucakar ba Wanda ko wayarsa Ya kasa amsawa. Dan ita duk a nata tunanin damuwar halinda Ummul ke ciki ne ke d awainiya da Haidar d in tsaban abinda ta raya ma ranta kenan. Zuciyarta sai wani irin k una yake mata tana ci gaba da addu an Allah yasa a fito masu da gawan Ummul kowa ya huta.


A can gidan Haidar d in kuwa hankalin Dareen yayi dubu Ya tashi. Haidar d inta ne ke ignoring calls dinta yau. Mutumin da ko important meeting yake zai excusing kansa ya d aga kiranta musamamn da taga an d auki lokaci bai returning call din ba. Ita kad ai sai safa da Marwa take tana jin zuciyarta na mata d aci. Tana a haka taga wayan Shadow na shigo mata.





SameenaAleeyou=???
*AUREN WATA UKU..!*




*31*






*??Sameena Aleeyou&
'







Tana d aga kiran ta sinkayo muryarsa daga d aya b angaren  I heard that you re back in the country.. Ya akai banji hakan daga bakinki ba..?

Shiru batace dashi komai ba sai hucin da take dan gaba d aya zuciyarta a cunkushe take tinda ta kasa samun Haidar a waya. Muryar Shadow ya kuma dakan dodon kunnenta  Dareen are you sure you are not hiding something from me.?

 Toh mai zan b oye maka. Yes mun dawo amma ban samu chance na sanar dakai hakan ba. After all, jiya ne kawai muka dawo k asar. Is not as if na shafe kwanaki ne da dawowa bakaji daga gareni ba.

Katseta yai  Don t you dare take me for a fool. I know you so well. Na sani idan kina shirya wani abun.. Let me warn you Dareen. Idan kika shirya wani abu a bayan ido na believe me zaki d and ani kud arki.

Tai murmushin takaici  Is that a threat.?

Murmushin shima yai  You know me so well. I don t keep people around with threats. Idan har zanyi abu lokaci d aya nakeyi ke kinfi kowa sanin hakan.

Yai gyaran murya kafin yaci gaba  Ina Haidar..?

Ta kuma furzar da huci  How would I know.? Ya fita bai sanar Dani ba.

 You should know Dareen. Because that s what you are there for. Ban ajiyeki tareda dashi ba just for you to have fun with him kin fahimta.

 Oh excuse me! You don t own me.. And you are not the one calling the shots here. Ni ce nake rayuwa da Haidar a halin yanzu& Barazana kawai kake da kake cewa tulun da aka d aure kurwar Haidar aka shata layin k iyayya tsakaninsa da iyayensa na wajenka.. Kuma bari kaji from now henceforth bazan bari ka cutar da Haidar ba. Babban kuskuren da ka tapka shine da ka min sanadin shiga rayuwarsa. A halin yanzu Haidar dani are one.. He s my husband da nake sonsa

35 / 52