Auren Wata Uku Book Complete By Sameena Aliyu.doc

Author :  Sameena Aliyu Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 52

15K to 18K   out of 153.1K words

clearing throat d insa.
 A ko wace ma aikata I believe ana samun sauye sauye da banbancin ra ayi tsakanin shugaba da ma aikatansa. Which is what makes the company stand firm on its feet..

Babu wanda zaice bai zama impressed da yanda Haidar ke amsa tambayoyin da ake masa with so much courage and determination.

Mutumin ya jinjina kai  So does that mean da gaske ne kenan kaida Mahaifinka baku samun jituwa har a wajen aiki..?

Haidar yai masa k uri dan ya gane turosa akai yai masa tambayoyin da zasu tunzurashi. Tafukan hannayensa ya d an had e waje guda  I m not here to tell a story about my personal life. But Being the son of the president of this company doesn t make me different from others. If I don t receive any VIP treatment it s because that s the company s policy. And I believe this is why the company remains on track despite all the challenges.

Ya kuma jinjina kai.  One more question Engr.  Is it true that your company is going bankrupt.. And the economy is at the state of crisis.?

Haidar ya d an rage girman idanunsa kad an yana duban mutumin, lokeci guda ya d an gyara zaman suit d insa  Let s call this a business perspective. Some times failures lead to future successes. I can assure you, MB (Maitama Builders) does not& and will never fear challenges.. Ya k arashe yana mai mik ewa lokaci guda mai gabatarwan ma ya mik e yana mai mik awa Haidar d in hannu alamun musabiha  Mun gode da bamu lokacinka da kai Rankayadade.


Alhaji Gimba ya dubi Daddy  Look, duba kaga yanda yake amsa tambayoyin with so much focus and determination. He has all the potentials and skills to take this company to a greater heights. I m super optimistic about him.

Daddy dai baice komai saima mik ewa da yake k ok arinyi.

Alhaji Gimba ya rakashi da kallo yana mamakin Allah yai baiwa wa mutum da samun d a irin Haidar Wanda yake d aya tamkar ga dubu amma ya kasa gani ya kuma kasa appreciating. Sosai lamarin abokin nasa ke d aure masa kai yanaji inama nasa d an ya kasance kaman Haidar.
**

Hisham ya kuma duban Haidar had ida girgiza kai  Ban fahimceka ba Haidar.

 Meye baka fahimta ba..? Haidar yace yana duban Hisham d in.

D an gyara tsayuwarsa Hisham yai  Kanaso kace min gadar zare yaso k ulla maka da ya shirya wann interview d in..? Kanaso kace min ya shirya hakan ne just for you to fall into his trap and create more scandals.? Kana so kace min shi kake zargi da yi ma Kampani zagon k asa.?

 He gave me all the reasons to suspect him.

Hisham ya kuma jinjina Kai  Amma zanji mamaki idan haka ya kasance duba da kusancin shi da mahaifinka.. So what are you planning now..?

 Of course I ll play his little game. Shiyasa ma na halarci interview d in. Ya k arshe yana k ok arin mik ewa.

Hisham ma ya mik e suka soma takawa.

 If that s the case, I ll support you Haidar har gaskiya ta bayyana.

Ba tareda ya dubi Hisham ba yace  I d rather do it alone. This is my battle and I ll fight it alone.. I ll make my Dad swallow all his words a lokacin da zan kamo wuyan mutumin da ya aminta dashi matsayin babban mak iyinsa. Each and every insult da ya jefeni dashi sai na sashi ya cinye kalamansa. And hakan zai faru ne kawai idan ya d aurani Akan project d in nan. So I ll do whatever it takes to make sure ya mallaka min ragamar wann project din.

Hisham yai still yana duban Haidar d in  Haidar kana magana kaman fansa kake so akan mahaifinka. Haidar.. Anya lafiya kake.. Mahaifi fah ya wuce wasa.?

 Wani mahaifin kenan.. Amma wani suna ya tara..! Yana ida fad in haka ya bud e motarsa ya shige.

Har ya bace ma ganin Hisham bai daina mamaki ba. Al amarin Haidar da mahaifinsa ya soma zarce tunaninsa.

***

Kano.


Tinda Abba ya shigo gidan hannunsa na hagu ke dafe da b angaren k irjinsa. Ya kuma duban Umma dake zaune gefensa ta rapka uban tagumi tana masa sannu.

Ya amsa yana mai gyara zamansa bayan yasha maganin da ta kawo masa.

Saida ya daidaita zamansa sosai kafin Ya soma magana  Suwaiba Ya kirawo sunanta.

 Na am Abban Ummul. Ta amsa duk jiki a mace ganin yanayin Abban.

Abba yaci gaba  Magana nake so muyi amma ina so ki kwantar da hankalinki.

 Toh Abban Ummul.. In sha Allah zan kwantar da hankalina.. Nidai burina ka samu lafiya..

Abba ya d an b ata lokaci kad an kafin yace  Ai na sanar dake yanda mukai da manemin auren Ummulkhairy. Wato Alhaji Kamilu mak ocina a kasuwa.

Umma ta jinjina kai  Eh kwarai anyi haka..

Abba ya kuma jinjina kai  Wato Suwaiba bayan shi Alhaji Kamilu yazo yaga Ummul kwanaki uku da suka shige. Washe gari da safe kaman yanda kika sani sun taho har nan k ofar gidana shi da wani abokinsa sun bada sadaki.. Alhaji Kamilu ya bada sadaki naira dubu d ari a matsayin sadakin ita Ummulkhairy lakadan

Umma kam tsaban farin ciki bata tsaya taji k arshen zance ba ta shiga gud a tana fad in Ummul dinta tayi goshi  yan bak in ciki saidai su Mutu.

Abba ya lumshe idanunsa kad an yana jin zafin k irjinsa na k aruwa. Daurewa yai ya d an bud e murya yai mata tsawa kad an data saurare shi.

Umma ta kuma wahse baki tana gyara zama  Yi hakuri Abban Ummul.. Farin ciki na ne ya gaza b uya. Ummul d ina lokaci yayi. Ai ni dama tin a nan wajen ka kirawo yan uwanka a nan cikin gida suka zama shaidu aka d aura.

 Suwaiba ki dubi girman Allah ki saurareni. Ya kuma fad i cikin tsarewa.

Ta saka hannayenta biyu ta kame bakinta  Na tuba.. Nayi shiru Abban Ummul.. Ina sauraronka yaushe suka nema a saka lokacin biki..? Ni wllhi na ma basu wuk a da nama su saka ko gobe ne.

Abba ya sauk e ajiyan zuciya a hankali yana girgiza kai kafin yaci gaba  Toh kinsan kwanakin baya kasuwa ta d an ja mun baya har na amso bashin hatsi a nan cikin kasuwa..

Jikin Umma ya soma sanyi amma sai tace  Kasan mutane yanzu idan Sun bika bashi sunyita korortoto kenan kai kace duniya ka amsa wajensu.. Su kwantar da hankulansu lokacin biyansu yayi in sha Allah..

 Ki saurare ni Suwaiba.

 Toh Ina sauraronka Abban Ummul.. Tace tana gyara zamanta.

Abba yaci gaba  Toh shekaran jiyan da suka kawo sadakin sai shi Wanda yake bina bashin hatsi Ya taho mun da buk atan kudinsa. Lallai Lallai shima yana neman kudinsa zai amfani dasu. Kuma nima nasan yanda Kasuwa ta koma a halin yanzu. Wasu lokutan Har ka fita ka dawo ba a zuwa saye. Godiyan Ubangiji ne kawai amma al amarin k asar sai addu a. Hakan yasa na d auka cikin sadakin Ummulkhairy na biya tinda gadarana sadakin  yatace. Banida hanyan biya sai wann sadakin. Na cira ciki na biya.. Yau kwatsam da naje Kasuwa Alhaji Kamilu ya tareni da batu mai tada hankali.

Ai bai kai aya ba Umma ta soma girgiza kai tana fad in  Dan Allah. Dan tsarkin mulkinsa da buwayarsa Abban Ummul ka rufa mun asiri ka mun sutura.. Kar kace min shima ya amshe sadakinsa.. Wayyo ni Suwaiba na shiga uku na Mutu na lalace..

Abba ya kifa kansa yana girgizawa yana jin yanda Umma ke fad in ta shiga uku ta Mutu ta lalace. Takaici da ya cika shi ganin tak i sauraronsa sai kuka take tana jefa kanta a uku. Abba yace  Aima baki gama jefa kanki a uku ba Suwaiba sai kinji irin wulak anci da kwance zanin da bawan Allahn nan ya mun a cikin kasuwa.!

Umma ta d ago idanunta masu zuban ruwa tana dubansa hannayenta duka biyu dafe da k irji yayinda Abba yaci gaba da fad in  Tinda nake a rayuwata ba a tab a min irin tozarci da wulak ancin da bawan Allahn nan ya min ba. Suwaiba, Alhaji Kamilu dai ya amshe sadakinsa ba yanda banyi ba ya bini bashin sauran kud ad ensa amma sai cewa yai bazai iya jira ba dan haka yasa yaran shagonsa suka kwaso kaya a nawa shagon darajan kud ad ensa makotanmu a kasuwa masu burin su ganmu a rana duk suna kallo. Wann wulak anci da mai yai kama Suwaiba..

Kukan Umma ya k aru mik ewa tai ta fice tana rera kuka tana fad in Ummul zatayi ajalinta.

Daga Ummulkhairy har Khulsum a tsorace suka nufo waje jin Umma na ambaton zata fad a rijiya.



SameenaAleeyou=???
*AUREN WATA UKU..!*




*08*






*??Sameena Aleeyou&
'


Yaran Umma suna kuka suna rok onta ta sauk o daga saman rijiya Mama na kuma ingizata  Suwaiba ko ki fad a ko kar ki fad a da alama dai bak in cikin wann  yar naki shi zai ajalinki.. Wayyo ni Tani zanyi kewarki Suwaiba. Ashe tafiya zakiyi ki barni.. Na yafeki duniya da lahira Suwaiba. Ta shiga rangad a ma Badi a da bata jima da zuwa gidan ba kira tana fad in ta fito tayi bankwana da Suwaiba tafiya zatayi ta barsu.

Suwaiba ta dena kururwar da take tana duban Mama da mamaki  Yaya bazaki hanani fad awa ba.. Rijiya fah zan fad a..

Mama ta kamo bakin zani tana goge hawayen da babu su  Yo ko na hanaki ko ban hanaki ba wancan  yar taki mai bak in k addara zatayi ajalinki Suwaiba. Ta shiga doka kiran Badi a wacce bata jima da zuwa gidan ba.

 Badiatu.. Badiatu! Badiatu..!! fito kiyi sallama da Suwaiba.. Suwaiba dai lokaci yayi..!

Badi a ta d age labule fuska a yatsine tana kuma turo kallabi gaban goshi  Toh Mama ki barta ta fad a mana.. Idan bata fad a ba ai bata tabbata shashasha ba.!

Khulsum ta harzuk a  Uwa bata fi uwa ba Anty Badi a kar ki sake gangancin zagar min mahaifiya..

Badi a ta malamalo ashar had ida zame d aurin kanta tai d amara dashi tayo kan Khulsum tana fad in kafin uwarta Suwaiba ta fad a rijiya sai ta fara jefata ciki taga uban da ya tsaya mata.


Ai sai Umma tai tsalle ta duro daga saman rijiya ta shiga janye Khulsum wacce Baid ia Ke k ok arin janyota Mama na tayata. Abu sai ya koma kaman dambe Mama ta shige ma  yarta Umma ma ta shige ma nata  yar wacce taga haik an rijiya za a jefata.

Ummul kaw fashewa tai da wani irin kuka sosai ganin wann tashin hankalin dik sabida ita ake.

Tana tsaka da kuka tana rok onsu suyi hak uri su daina ta hangi Abba na rarrafowa daga d akinsa hannunsa guda dafe da b angaren k irjinsa. Ta kirawo sunansa cikin kid ima tana mai nufansa.

Hakan yaja hankulansu. Nan take suma sukai Kan Abba suna ambato sunansa. Tuni idanunsa sun kafe suna kallon sama baka iya ganin bak in k wayan idon.


Sai kuma suka koma kururuwa suna neman agaji.

Kaf mutanen gidan aka rasa mai kawo masu d auki dan dik a nasu zaton wasan kwaiwayo ne da suka saba.

Sukai masa caa akai kowa yana ambato Sunansa suna rok onsa ya tashi. Umma sai masa fifita take da bakin zani yayinda Mama ta kawo ruwa cikin kofi tana mik awa Umman. Fad i take  Suwaiba duba mana kiga yana numfashi.

Umma na kuka take fad in  Haba Yaya kar kiyi tunani haka. Abban Ummul na numfashi.. Taci gaba da rera kuka tana rok onsa ya tashi kar ya tafi ya barsu.

Kaf  yanuwansa maza dake zama cikin gidan aka rasa mai zuwa ya dubasa balle a kaisa asibiti. Dama gidan Sun gaji gaba na  yanubanci tin daga iyaye da kakanni. Yan wann d akin babu ruwansu da yan wancan d akin. Shi Abba kusan shine babba cikin mazan dake rayuwa a gidan sauran yeyyen nasu duk mata ne suna gidajensu. Shi a d akin mahaifiyarsa shi kad ai ne namiji. Hasalima su biyu mahaifiyar tasa ta haifesu. Daga shi sai kaw  yaruwarsa k anwarsa mai suna Inna Dije. Inna Dije da mijinta basu jima da komawa garin Dutse na jihar Jigawa ba yanda mijinta ke aiki. Hasalima mijin nata d an asalin jihar Jigawa ne amma yayi zaman Kano yanda yaga Inna Dije k anwa ga Abba ya aureta. Sun zauna tsawon lokaci a Kano kafin iftila in rashin tilon d ansu ya samesu. Tin bayan rasuwar D ansu basu kuma zaman Kano ba hakan kuma yai daidai da canjin wajen aiki da mijin Inna Dije ya samu. Sann tin bayan wann lokacin Inna Dije bata kuma saka k afarta a garin Kano ba.

Wasu dattawan unguwar masu ganin mutincin Abba su suka Kaisa wani k aramin asibitin gwabnati mafi kusa. Mama da Umma sukai masu godiya.

Jigum jigum sukai gaba d aya suna jiran ba asi daga wajen likitoci.

Daga yanda suke zaune Mama ta kafe Umma da yaranta dake zaune daga d aya b angaren suna hawaye. Sai cika take tana huci dan wann dik dalilin Suwaiba da  yarta ke faruwa. Ta sauk e idanunta kan Ummul wacce ta kasa daina kuka maras sauti. Kaman wacce aka sinkara ta soma furta  Wann duk laifinki ne Ummul.. Idan Abbanku ya rasa ransa ki sani alhakin mutuwarsa zai ratayu ne a wuyanki.. Kece nan kikai silan mutuwar mahaifinku..!

Umma ta d ago tana duban Mama shaye da mamaki  Yaya ya zaki ce haka.? Ta ina Ummul ta zama Sila..?

 K warai kuwa ita ce Sila dan bak in cikinta da abunda ke faruwa da ita su suka taru suka haddasawa mijin mu ciwo ehe.!

Badia dake koke Koke tana ambato sunan mahaifinta ta k arasa a guje ta shiga janyo Ummulkhairy tana fad in shegiya mai bak in k addara kafin ki kashe mana uba sai and fara kasheki kowa ya huta. Daidai lokacin su Azeema da Salima sauran yaran Mama dake gidajen aurensu suka iso ai nan suma suka aukawa su Khulsum. Fad a dai yaci gaba a asibiti. Har saida ma aikatan asibitin suka tasamma koransu.

Da kyar dai aka raba bangarorin guda biyu fada. Kowa suka koma gefe suna aika ma juna mugun kallo.

Can da jimawa wani Likita ya fito. Suka mik e gaba d aya suka nufesa.
Sukai ma likitan caaa da tambayoyi kowa naso a soma amsa nasa. Mama da yaranta su Salima na yi Umma da Khulsum na yi. Ita dai Ummul ita kad ai ce baka Jin bakinta.

Likita ya zuba ma sarautar Allah idanu yana duban wann ahali Wanda majinyacin da suka kawo baya buk atan irin wann hayaniya da tashin hankali nasu. Ya d an girgiza kai yana k ok arin kwantar masu da hankali amma sai yaga kaman basa gane wann yaren. Tsawa ya daka masu yace duk suyi shiru ko su fice su bar masu asibiti.

Bayan Likitan ya kebe da Mama da Umma Ya dubesu yace  Ku sani yanzu ba lokacin tashin hankali bane. Lokaci ne da mijinku ke tsananin buk atar kwanciyar hankali. Ko kunsan mijinku na d aukeda matsanancin ciwon zuciya mai haifar da Kumburin zuciya.!

Ai sai suka rikice Umma kuka Mama kaw mik ewa tai dafe da k irji  Likita kumburin zuciya fah kace.?!

Likita ya jinjina mata Kai  K warai Hajiya.. Kuma ciwonsa ya wuce matakin farko.. Hasalima zamuyi k ok ari ne mu turasa can babban asibitin koyarwa dan a can ne zaifi samun kula sunada k wararrun likitoci da ya shafi ciwon zuciya..

Umma ta share hawayen da suka zubo mata tana tuna ranan da mijin nasu yai masu wasiya da hak uri da zaman lafiya  Likita yanzu mai zai faru da mijinmu..? Tai maganar cikin tsananin rawar murya mai cikeda rauni.

Sauk e ajiyan zuciya yai yace  Kwararrun Likitocin da suka shafi b angaren ciwon zuciya ne kad ai zasu iya sanar daku abinda zai faru.. A halin yanzu bazan iya ce da ku komai ba.. Zuwa gobe da yardar Allah zaa tafi dashi can asibitin koyawar sai Likitocin zuciya su dubasa. Amma ku kwantar da hankulanku ba wani abin tashin hankali ana warkewa cikin k udarar Ubangiji. Kuyi hak uri na fad a maku gatsau sabida Kun Kai hak urina bango ne shiyasa. Ku kwantar da hankulanku ku had e kan ahalinku ko dan samun lafiyan mijinku.. Please do this for your husband. Ya k arashe yana dubansu su duka biyu.

Mama tace  Sunan maganin ka fad a Likita.?

Ya d an murmusa kad an had ida girgiza Kai  Cewa nai kuyi hakan domin mijinku.

Suka jinjina Kai a tare Likitan ya k arada  Kar ku damu babu abinda zaku biya mutanen da suka kawo sa nan sun biya komai. Saidai idan an kaisa can babban asibitin koyarwa dole zaa bukaci kud i ko nace kudade masu yawa.

Daga haka Sallama likitan yai masu suka fito jikkunansu duk a sanyaye.

**


Abuja.


Hisham ya dubi Haidar wanda ya bada hankalinsa sosai ga laptop d in dake gabansa wanda da gani ko ba ace kasan aiki tuk uri yake domin achieving goals dinsa. Ya d an Sauke ajiyan zuciya  I hope he approves the new proposal.

Shiru Haidar yai idanunsa kan computer din har lokacin. Yeci gaba da juya pen d in dake mak ale cikin yatsunsa guda biyu  I know my Dad, he s so meticulous& So everything should

6 / 52