Auren Wata Uku Book Complete By Sameena Aliyu.doc

Author :  Sameena Aliyu Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   2 / 52

3K to 6K   out of 153.1K words

samu  Yaruwar ki ya samu d iyarki sann ne zakiji ciwon da nake ji.. Wayyo Allah.. Wayyo ni Suwaiba laifin mi nayi aka jarabceni da  ya irinki Ummul.. Ke ba wani tawaya bane tattare dake d an hasken nan baki rasa ba. Ke duk wani abin da mace zatai tink aho dashi daidai gwargwado Allah ya baki amma a rasa Wanda zai aureki kowa da yazo sai Ya gudu.. Haba Ummul..! Ta kuma fashewa da wani kukan..

Idan da sabo sun Saba da dramar mahaifiyarsu. Khulsum ta girgiza Kai. Tinda aka soma amsan kud in auren  yar uwarta Ummulkhairy ana fasawa cikin damuwa da tashin hankali mahaifiyarsu take. Batada da burin da ya wuce taga Ummulkhairy tayi aure ta bar gidan ko ba dan komai ba sai ko dan gori da maganganu da take fuskanta Kama daga kan Abokiyar zamanta har izuwa kan ahalin gidan dama sauran jama an unguwa. Mahaifiyar Ummulkhairy ta kasance irin mutanen nan ne masu saka damuwan maganganun mutane a ransu. A akasarin lokuta mutane suna mata kallon sakarya wacce batada wani wayo ko cikakken hankali. Sann tin Ummulkhairy tana k arama taci burin ta aurar da ita da k anan shekaru saidai Allah bai nufa hakan ba. Haka zatai mata wanka tai mata ado tin tanada k ananan shekaru taita mata wak e tana karanto baitika tana mata rawa tana fad in saura k iris ta aurar da ita saura k iris ta kaita d akin miji. Koda Mama kishiyarta zataita yab a mata maganganu da fad in ta jira dai taga girman  yar tata sam bazata tab a tankata ba. Umma Ta kasance irin mutanen nan ne masu san Barkwanci Wanda kowa ya mata wann shaidar Wanda hakan kesa wasu ke mata kallan shashasha a akasarin lokuta. Ko fad a Abokiyar zamanta ta tareta dashi wasa take maidashi Sam batada abokin fad a kaf unguwar balle gidan. Hakan yasa halinsu itada Khulsum yasha bam bam. Domin kaw albasa batai halin ruwa ba. Dukda kuwa cewa Ummulkhairi ma bata dauko barkwancin ba. Sai sanyi wann kuma wajen mahaifinta ta dauko.

Burin Ummulkhairi shine cikan burin mahaifiyarta. ta samu mijin da zai aureta koda bata sonsa zatai hak uri ta zauna dashi dan burin mahaifiyarta ya cika. Burin mahaifiyarta shine Ummul d inta tai aure ta tafi d akin mijinta.

Mahaifiyar su Ummulkhairy ta kasance itace mace ta biyu a gidan mahaifinsu. Matarsa ta fari itace Mama Tani yara uku gareta kuma duk sunyi aure suna d akin mazajensu. Badi a itace babba sai Salima sann autarta wacce Ummulkhairy ta girme mata da shekaru uku itama tuni tayi aure tana d akinta. Autar Mama tani sunanta Azeema. Mama ta kasance d aya daga cikin matan unguwar Wanda basu da aiki sai aibata duk macen da Allah ya jarabceta da JINKIRIN aure ko mutuwar aure. Nan zakaji bakin Mama tana alfahari tana fad in ita nata yaran kaf suna d akin mazajensu kai kace wayonta ne ya kawo hakan ko dabararta.

Mahaifinsu baida wani karfi saidai basu rasa abinda zasu saka bakin salati, saida manja da mangyada yake a kasuwa dukda dai jarin ba wani mai yawa bane amma sunfi k arfin abinda zasu saka a bakin salati daidai talaka. JINKIRIN auren Ummulkhairy ba shine ke tada hankalin mahaifinsu ba kaman yanda ake maganan aure magana yabi iska. Dukda ya kasance Dattijo kuma mai k ok arin danne damuwarsa ya fawwala wa Ubangijinsa lamuransa can k asan zuciyarsa na damuwa da al amarin  yarsa Ummulkhairy saidai Sam baya nuna hakan. Kullum cikin cewa yake Allah ne bai nufa ba. Ga manema Sam basu fasa nemanta ba domin kaw d iyarsa tubarkallah ce batada makusa saidai ace d anadam tara yake dama bai cika goma ba. Yayi imani lokacinta ne kawai baiyi ba.

Gyara zamansa yai yana sauraron kukan da Umma ke ci gaba da yi tana fad in  Abban Ummul dan girman Allah ka nemo min mafita wllhi bansan ya za ayi na sake fuskantar mutanen unguwar nan ba. Toh ma da wani fuska zan sake fita ana nunani ana k irga fashin auren Ummul da akai.. Dan Allah ka nemo min mafita Wayyo ni Suwaiba.. Ta k arashe tana kuma rusa wani kukan.

Abba ya girgiza Kansa, ya kasance mutum maras San hayaniya kaman dai  yarsa Ummulkhairy. Shi irin mutanen nan ne da zakai abu su kauda idanu suyi kaman basu gani ba sann irin mutanen nan ne masu nuna kulawa da k auna kan duk Wanda Allah ya hukunta kasancewarsu tare Kama daga iyalansa har zuwa kan  Ya yansa da danginsa dukda kuwa k annensa dake zaune cikin gidan basu d aukesa bakin komai ba hasalima gaba suke dashi. Hakan baisa ya fasa masu nasiha da wasilci da zumunci ba.

Cikin b acin rai ya tsame hannunsa daga cikin kwanon tuwon dake gabansa ya katse Umma da fad in  Haba Suwaiba! Ya isa haka nan.. Shin yau ne aka fara amsar lefen Ummulkhairy ko sadakinta..?

Batace komai ba sai gunjin kuka da take ci gaba.

Ya kuma girgiza Kai  Toh tinda ba yau bane na farko sai ki kwantar da hankali dan na tabbata bazai zama na k arshe ba tinda dai kink i amincewa  yarki ta koma makaranta tai karatu kaman yanda ita Ummul d in ke so.

Cikin zuban hawaye ta d ago tana duban mijin nata  Yo wani karatu fisabilillahi .. Aima shekarun ta Sun wuce shekarun zaman aji.

 A ina kika tab a ji an girma ma neman ilimi Suwaiba..? Waima dakata Suwaiba. Da kika damu kika daga hankali duka nawa Ummul d in take ne..?

Umma ta dago a zabure jin yace nawa Ummul d in take. Tai karaf tace  Ta fah haura talatin Abban Ummul.
Taci gaba  Yo wani ilimi zata nema ya wuce ilimin zama a gidan miji da naketa k ok arin bata.. Allah na tuba abu kaman jifa ko sa hannu.

Abba ya kuma katseta  Kinga Suwaiba na rabaki da wann gurb ataccen tunani.. Ki je kina jefa kanki cikin damuwan abinda Allah bai d aura Miki ba.. Ko an fad a Miki bansan kina amso ma Ummulkhairy Neman Taimako bane.. Nasan komai kawai ina kauda ido ne ina Miki uzuri.. Amma ki sani kar kawar da idanun da nake bana magana yasa kije ki auka ga sab awa mahaliccinki kiyi shirka.. Ki natsu ki san mai Kike ciki.. Allah yana sane da duk abubuwan da suke faruwa.. Addu an da zaki mata Har sai yafi na Wanda zaki saka wani ya mata domin kaw ke mahaifiyarta ce.. Idan har da gaske so kike tai auren kaman yanda kikaci buri. Sai ki rage bacci ki tashi cikin dare ki Kai kokenki ma Ubangijin duka. Ki zubda hawaye a yanda zuban hawayen zai amfani domin kaw wajen Allah ne hawayenki keda amfani ba mutanen da zasuyi murna da ganin hawayen naki ba. Haba Suwaiba kiyita korototo kina kin shiga uku..? Da irin wann korototo da ambaton uku da kike ma kanki toh fa babu abinda zaki gani sai ukun..

Ta kuma kamo bakin zani tana share hawaye  Haba Abban Ummul dan Allah ka fad a alkhairi..

 Kece zakiyi ma kanki karatun ta natsu ki dinga fad in alkhairi gameda  yarki ko dan rayuwarta ta inganta. Domin kuwa su  ya ya amana ce Allah Ya bamu kuma za a tsaida mu a tambayemu akansu ranan gobe. Ya k arashe yana mai janyo kwanon tuwon sa.
**
A can d aki kuwa Khulsum ce ta duk a gaba ga Ummulkhairy, tayi zaman rak umi tana fuskantar  yaruwar tata da tin shigowarsu gidan take aikin abu guda wato kuka.



SameenaAleeyou=???

*AUREN WATA UKU*



*04*





*??Sameena Aleeyou&
'




Tafiya yake cikin mota sautin Marin da mahaifinsa ya shata masa bai daina k uwa a dodon kunnuwansa ba. Shi ba wai zafin Marin bane ya tsaya masa a rai, Marin nasa da yai gaban employees d in Kampanin kuma masu aiki under department d in da yake running shine abinda yafi komai k ona masa rai. Ya sani shi dai a idanun mahaifinsa baya yin komai daidai sabida haka wann ba sabon abu bane wajensa. Ba a wajen aiki ba a gida ba.. Amma meyasa zai wulak antasa gaban ma aikatansa irin haka..? Ya cije labb an bakinsa kad an zuciyarsa na kuma k una. Mahaifinsa ya tsanesa baya k aunarsa, kai duka iyayen sa guda biyu basa sonsa basa k aunarsa. Shi zai iya cewa tun tasowarsa baida wani good memories da both mahaifansa wato mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa. Mahaifiyarsa tin tasowarsa cikin tilasta masa da tsaurara masa take wajen ganin yayi abinda zai burge mahaifinsa ya kumayi alfahari dashi. Saidai duk abinda yayi baya burge mahaifin nasa. Kullum cikin nuna masa baiyi daidai yake ba. Kullum cikin kusheshi yake da jifansa da kalamai masu muni. Tsakaninsa da iyayensa akwai wani Katanga da yai ma soyayya shamak i dashi. Baisan soyayyan iyaye ba. Ya taso ne cikin tilastawa da k ok arin burge mutanen da bai tab a birgewa ba a cewarsa. Yai gajeren tsaki yana mai kokarin kauda tinanin.

A farfajiyan gidan yai parking motarsa jikin wani tapkeken roundabout da furanni suka k awata tsakiyarsa ga ruwa na kwaranya daga tsakiya. Cikin sassarfa ya nufi cikin gidan har lokacin zuciyarsa bai daina masa zafi ba.


Zaune ya taddata a parlornsa ta mik e santala santalan fararen k afafunta da suka sha ado da k unshi . Sai faman karkad a k afafun nata take tana tururi ita kad ai alamun dai isowarsa take jira.

Baiji mamakin ganinta a parlorn tinda yasan kullum cikin controlling rayuwarsa take.

Baice komai ba sabida ransa da yake a mugun b ace.

Har yasa Kai zai shige ya sinkayo muryarta  Ai na zaci daga can bazaka dawo nan ba tinda ka zama sallamamme .

Cak ya tsaya yana saita numfashinsa a hankali  Couldn t you wait for me first to at least do something wrong kafin ki fara aibatani. Ya k arashe daidai sanda mahaifiyarsa ta k araso gabansa ta tsaya suna fuskantar juna.

Ganin ciwo a fuskarsa ya sanya yanayinta canzawa. Alamun rauni ya bayyana saman fuskarta  Haidar.. Me ya sameka.. Ina ka samo rauni..? Ta tambaya cikin nuna kulawa.

Murmushi mai ciwo ne saman fuskarsa. Lokaci guda ya girgiza Kai yace  Don t act like you care Mom. Kin San hakan zai faru. Am I right.?

Ta d an tsare fuska  Wani irin magana ne nasan haka zai faru.. Had arin mota Kai ko me.. Tinda dai nasan baka shiga sabgan mutane balle nace fad a Kai da wani..

 Babu ko d aya Mommy.. Yai fasali yana mai shafa raunin da mahaifinsa yaji masa a labb ansa  Meyasa ciwo a jikina zai d aga miki hankali da girma na idan bai d aga miki hankali a lokacin k uruciya na ba.?

Ya kafeta da idanu. Jin tayi Shiru batace komai ba yasa shi murmusawa kad an da gefen bakinsa  Of course you don t have the answer. Well, zaki iya kiran wann a matsayin tukuici na mahaifina. All thanks to you, your Majesty, Mommy.!

Ta furzar da huci kad an  Mai ya had aka da mahaifinka..?

 A usual stuff.. Banyi daidai ba, Dikda bana tunanin Akan wann ne kawai.. Ya d an daidaita tsayuwarsa kafin yaci gaba  Nafi zaton kece kika bashi shawarin yai mun wulak ancin da ya mun.. A naki tunanin ta haka ne kawai zaisa ki fahimci mai kike son fahimta gameda D anda kika dasa rashin yarda da daidaito a tsakaninku tun yana k aramin yaro. Na sani ku biyun baku zama on the same page with each other unless wann abun will hurt me deeply. Ko ba haka bane Mommy.? Ya k arashe yana dubanta.

Furzar da huci tai had ida girgiza Kai  It s for your own good Aliyu.. Dik Fad i tashin da nake inayi ne domin ka zama mutumin K warai sann rayuwarka ta inganta.. Bazai yuwu bayan tsayin dakan da nake Akan D ah na na zuba ido rana daya komai ya rushe ba. Aliyu ka daina kwana a gida.. Ka tsiri wasu d abi u da ba naka ba.. Some strange behaviors wanda a baya bakayi. A baya baka tab a maida mun magana kan duk abunda zan umarceka.. But now.. You ve changed.. Completely Haidar.. Ina kake kai kudaden da kake fitarwa daga kampanin mahaifinka.. So kake ka hadani fada dashi..? A nashi tunanin nice nake daure maka gindi kake abinda ka so.. A nashi tunanin nasan duk halinda kake ciki.. What he was wrong about shine yanzu Aliyun da ya sani ya banbanta da Aliyu na wanda baya boye mun komai.. D ah na mai biyayya a gareni koda na kasance mai tsauri akanshi.. Haidar din da baya mun musu koda munada banbancin ra ayi.. Ta danyi fasali muryarta na rawa tana kuma matsowa kusansa  Aliyu nasan ba shaye shaye kake ba tunda bakayi ba a lokacin da tak ura da tsanani zasusa kayi. Sann bana tunanin mata ne suka d auki hankalinka tinda shima bakayi a baya ba lokacin da ya kamata ace kayi idan kai me yi d in ne& Toh menene ya dauki hankalinka a duniyar nan.. Haidar please..

D aga mata hannu yai alamun dakatarwa  Kin rasa wann daman akan D anki Mommy tuntuni..

Ya dan juyo yana dubanta kafin yaci gaba cikin rarrabewar kalmomi  What I do with my life is none of your Business& You said it right. Ni ba wann k aramin yaron da kike kullewa a d aki ki hana masa lokutansa na k uruciya ki tilasta masa cinye takardu koda baya so.. Ya d anyi fasali kafin yaci gaba  Kin mance ne na tuna Miki Mommy.? That unhappy little boy ya girma Mommy. Kuma zai yanda yake so da rayuwarsa ba yanda ke kike so ba.. After all, duk abinda kike yi kinayi ne sabida benefits d inki.. Ba abu guda da kikeyi domin ci gaba na.. Kinayi ne kawai domin amfanin kanki.. Burinki shine ya mallaka min company sabida watak ila akwai abinda kike tsoro ko kuma yake Miki barazana da rasa dukiyarsa wanda ni ban sani ba.. Shiyasa kike amfani Dani domin na zame miki makamin ki.. D anki ba komai bane a wajenki face weapon. Yes, I am nothing to you face makaminki. Haka ne Mommy..? Jinjina kansa yai jin bata amsa ba  Wace irin uwa ce take haka ma d anta Mommy.? Ya k arashe idanunsa cikin nata.

Dikda zuciyarta dake harbawa bata bari tsoro ya bayyana saman fuskarta ba. Saima girgiza Kai da take  Don t you dare question my motherhood.. You ve no idea what it takes to be a parent..! Ta k arashe tana sakin huci.

Jinjina mata kai yai  Eh bansan mene zama iyaye ba kuma bana so nai experiencing daidai da dak ik a guda. Kinsan dalili sabida ban taso naga misali mai kyau wajen mutanen da ya kamata na gani daga garesu ba..  Ya d an kuma matsowa had ida sassauta murya  Kin gama sanin duk abinda ke faruwa cikin rayuwar D anki.. Do you know why..? Ya tsare mahaifiyar tasa da idanu kafin yaci gaba  Because I m not that scary little cat da kikai traumatizing d inshi da son zuciya irin naki. Bazaki sake amfani dani domin cimma burinki ba.! Daga haka sa kai yai ya shige cikin huci.

Tabi bayansa da kalamansa na kuma dakan dodon kumnuwanta har zuwa tsakar kanta. Salati kawai take.. Meke faruwa da ita..? Meke faruwa da D anta. Ko zamanin yarinta zamanin da take kulle Haidar cikin d aki mai duhu bai mayar mata da maganganun irin haka. Hasalima duk abinda zata masa shiru yakeyi. Ya koma kaman mai tsoron mutane, dik yanda mutane suke baya zama baya kuma cewa um balle um um. Akwai lokacin da har sukai zaton ko ya kurmance ne har saida aka had a masa da therapy kafin maganarsa ya dawo. Ita tsoro abun ya soma bata. Yafi kama da aikin asiri.


Yana tura k ofan d akinsa ya hangi Anisa  yar k anwar mahaifiyarsa dake aure garin Kano tsaye closet d insa rungume da rigarsa ta lumshe idanu. Jin an turo k ofa ya sanyata bud e idanunta suka kuwa had a idanu.

 What are you doing in here..? And can you explain why you are holding that..? Yai mata nuni da rigarsa dake cikin hannunta da idanunsa.

Ta saki murmushin yak e  Na shigo na gyara maka d akin ne.. Mommy tace kwana biyu baka kwana a gida.. Nima d in jiya da dare na shigo garin..

Baiyi mamaki ba dan Mommy ta turo Anisa d akinsa. Yasan kad an ne da aikin Mommy ta turo Anisa tai mata binciken k wak waf cikin d akinsa dukdai dan ta gane what s been going on cikin rayuwarsa.

 Get out.. I need to change.. Ya fad i yana mai shigewa cikin d akin lokaci guda yana k ok arin undressing Kansa. Suitcase ya ciro Anisa tana gani ya shiga ciro kayansa yana sakawa ciki.

Mamaki ya cika Anisa da ganin yanayinsa. Tasan bai iya fushi ba dukda kuwa ba kasafai kake gane normal days d insa ba. Definitely dai wani abu na faruwa dashi. Ta girgiza kai kad an. Sauri sauri ta fito ta nufi wajen da Mommy Ke tsaye tana tsaka da salallami. Anisa d iyar k anwar Mommy ce mai suna Asshe dake zaune a garin Kano. Daren jiya tazo gidan dama takan d an zo tai masu kwanaki lokaci zuwa lokaci.

 Mommy wai lafiya.. Wai meke faruwa ne a gidan nan..?

Har lokacin Mommy bata amsata ba ta kasa furta koda kalma. A haka Haidar ya k araso ya shigesu ya barsu nan tsaye suna binsa da kallon mamaki.

2 / 52