Auren Wata Uku Book Complete By Sameena Aliyu.doc

Author :  Sameena Aliyu Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   17 / 52

48K to 51K   out of 153.1K words

take.

Mommy ta k araso a birkice tana tambayarta meke faruwa.

Anisa ta d ago tana dubanta dan tinda taga Haidar yazo gidan gashi taji ana batun Aure. Bugu da k ari akan idonta Mommy ta shige d aki tana magana da Amminta a waya Wanda ta tabbata bazai shige zancen auren suke ba. Shin iyayenta basu fahimci irin son da take ma Haidar bane. Idan har ba auren Haidar zatayi ba toh ma zaman me take a gidan. Take ta mik e tana kuma fashewa da kuka ba tareda tace da Mommy komai ba.

Mommy tabi bayanta da kallo kafin ta tab e baki tace  Sangarcin sun motsa kenan. Bata kuma bi takan Anisa ba taci gaba da sabgoginta dan yau Ji take tamkar kaf damuwarta na gidan duniya Ya yaye.


**

Asshe ta dubi Umma wacce ta cakare cikin tsadaddan leshi d anubansu, Tai far da idanu  Wow Umman Ummul kinga kuwa yanda kika fito kikai kyau.. Kyaunki na asalin k abilar Fulbe Ya kuma bayyana.. Gaskiya kud i zasu amshe ki.. Kin ganki kuwa wa zaice kin haifi Ummul..

Umma ta ci gaba da wahse baki tana juyi gaban madubi tana duban kanta  Allah ko Hajja Asshe.. Toh ai gwara kar na Saba tinda ba samun irin wann tufafi zanyi kullum ba.

Asshe ta kuma murmusawa  Inji waye.. Ai saidai ki dinga kyautan su ma. Ke ai yanzu kin girmi irin wad nn ma saidai na order daga k asar waje.. Kekam fah yanzu kin zarce sa anninki  Yarki taci sunanta Uwar alkhairi ta bud e Miki k ofofin alkhairi.. Ke fa yanzu da matan gwamnoni zaki dinga jerawa..

 Na shige tsaran Yaya.. Umma tace tana kuma washe baki.

Asshe tace  Waye kuma Yaya..?

 Tani kishiyata.. Umma ta bata amsa.

Gajeren tsaki Asshe tai tace  Saidai ta soma kiranki da Yaya daga yanzu dan kin Riga kin amshe girman. Ummul d inki ta k wace Miki girman.. Ta aje mata hanshak in handbag shak e da kud i  yan dubu dubu ciki tace  Wann naki ne ki razani Tani dasu. Dan tinda Asshe ta gane Suwaiba ba kwad ayayya bace burinta kawai shine ta burge kishiyarta harma da sauran jama an dake tsangwamar  yarta su shiga taitaynsu sann Ummul d inta Tai irin auren da yaran Tani basuyi ba ta k udiri niyyan cika ma Umma wann buri nata. Dan sosai matar ke sakata nishad i.

Asshe ta fice tana fad in bara ta duba Hilala ko ya shirya dan shine zai kaisu.

Umma ta jinjina Kai tana kuma murmusawa. A fili take furtawa bayan Asshe ta fice  Tani kenan.. Dake da  ya yanki Kun gama mana wulak anci.. Yau idanunki zasu gane Miki abin mamaki.. Yau zakiyi nadaman duk wasu abubuwan da kika jima kina min cikin gidan nan.. Ummulkhairy da kike aibatawa Har kina ambatonta da Ummulsharri toh yau sharrinki zai koma kanki Tani.. Ki jira bayyanata.!



SameenaAleeyou=???
*AUREN WATA UKU..!*



*16*






*??Sameena Aleeyou&
'




Safiyar Washe gari gidan Hajja Fannah suka fara nufa ko an samu wani bayani gameda Umma. Saidai har kawo wann ranar babu Umma babu labarinta babu wani bayani tak amaime da ita. Ummul sai juya wayar Umman take cikin hannunta nokia k irar 3310 duk taji jiki ta kod e. Hawaye suka kuma gangaro mata. Gashi sun tadda Hajja Fannah ma bataji dad i ba kwance take lik is dan tin bayan tafiyar Hisham jikinta ba dad i k ok ari kawai take. Ummul ta dubeta tace  Hajja ko dai asibiti zamuje.?

Hajja Fannah ta murmusa cikeda jin dad in yanda Ummul ta damu da damuwarta  A a Ummul, ba sai naje asibiti ba.. Zuwa anjima zazzab in zai sauk a in sha Allah.

Ummul ta jinina kai suna masu mata fata da addu an samun lafiya itada Khulsum.

Khulsum ce ta soma mik ewa yayinda Ummul ma ta mik e suna mata Sallama da fad in zasu biya Asibiti wajen Abba su dubasa daga can zasu k ara komawa police station ko an samu wani batu gameda mahaifiyarsu.

Ummul ta d an dubeta  Hajja zamu iya barinki ke kad ai naga kaman yau jikin naki da d an nauyi.

Hajja Fannah ta murmusa tana mai mik ewa zaune sosai dan hankalin Ummul d in Ya kwanta  Kinji Ummul nifa zazzab i ne ke damuna nasan kuma bazai shige typhoid d in nan da ya sakani gana kwana biyu ba. Banison zuwa asibiti ne su tara min magani dan bana shiri da had iye k waya Shiyasa ko Hisham ban sanar dashi ba dan nasan yanda kika dage naje asibiti haka shid inma zai dage. Toh kafin ku min taron dangi gashi can na dafa ruwan zogale ma inata sha dan nafi gane wann. Ta k arashe cikin k ok arin nuna jarumta irinta maras lafiya.

Ummul ta murmusa kad an. Sosai take jin Matar har cikin ranta. Sun mik e suna kuma mata Sallama ta k araso hannunta rik eda  yan kud ad e ta mik a masu  Ungo nan kuyi kud in abun hawa.

Dukansu biyu girgiza kai suke suna fad in a a ta barshi.

Ta d an b ata fuska tana fad in  Au baku d aukeni uwa ba kenan idan har zan baku abu kuk i karb a. Ta dubi Khulsum  Ungo nan karb a maku ita Ummul ai tasan karonmu. Idan bata amshi kyauta na matsayin malamar ta ba ai ta amsa matsayin  Yata. Can k asar zuciyarta kuwa Matar D anta ta kirata.

A dole dole suka amsa dukda dama basuda ko sisin da zai kaisu asibiti wajen Abba balle Har su tafi police station maganan case d in Umma.


Suka kuma mata godiya had ida fatan samun lafiya kafin suka fice.


Suna tafe cikin adaidaita Khulsum ta dubi Ummul  Adda mai zai hana mu fara zuwa police station d in tinda kinga asibiti ko munje ba Lallai Mama da yaranta su bari mu shiga wajen Abba ba.

Ummul ta girgiza kanta  A a Khulsum, koda zasu hanamu mu je d in dai. Muji ya jikin nasa Ya kwana tinda idan muka tafi maganan neman Umma ba Lallai mu dawo da wuri ba har sai munji yanda al amarin Ya kwana. Kinsan ofishin  yansanda cases da yawa. Inaji a jikina da izinin Allah yai za a samu Umma. Ta k arashe cikin tsananin rawar murya irin na Wanda Ya gama karaya amma tawakkali Ya hana furta hakan.

Khulsum ta jinina kai tana amsawa da Allah Ya sa a samu Umma ya kuma bawa mahaifinsu lafiya. Ummul ta amsa da Ameen daidai sansa mai adaidaita Ya diresu k ofan asibiti.

Suna dosowa haraban ward d in suka hango Mama da Badi a. Ga Azeema a gefe harma da mijin Azeemar Habibu. Sai wallahi tallahi suke baka ma gane mai suke fad i dukda wai k asa k asa sukeyi basa d aga murya kar ajisu a fatattake su.

Azeema fad i take  Wai kuna so kuce mun tun yammacin jiya kud ad en suke hannun Tasi u kuma wayansa a kashe.?

Habibu yaci gaba da salati yana tafa hannu. Ya dubi Mama wacce ko iya cewa komai batayi. Huci kurum take. Fuskar Tasi u ne kawai ke mata gizo cikin ido. Allah ya gani da zataga Tasi u yanzu a gabanta zata iya shak esa Har sai an k wacesa.

Cikeda zak ewa Habibu yaci gaba  Wann ai zancen banza kenan.. Ta Ya za a ce kun kira shi Tasi u kun dank a masa ragamar komai irin haka. Mai zai hana baku tuntub i ita Azeema ta kirawo nata mijin matsayin shaida ba..Wann ma ai ba magana bace tinda kud in nan ba kud in Bad ia bane ita kad ai.. Ehe kud i ne na magada.. Kuma shago da ba shagon sata ba ya ma za ace an sayar cikin rahusa haka. Nawa kowacce zata samu cikinku.?

Badi a dake aika masa mugun kallo tace  Toh wai kai Malam naka a wanne.. Ko harda kasonka ne cikin gadon.?

Azeema ta katseta  Ai naga gadon na uban Tasi u ne da kika gayyatosa Ya kwashe kud ad en Ya gudu. Toh wllhi na ranste da Allah bazata tab a sakuwa ba wai bindiga a ruwa. Wllhi yanzu zan kirawo Yaya Salima tinda duk abinda ake itama bata sani ba. Na ranste da Allah sai an mana kashin hakkinmu ehe. Ko kuma wllhi na gayyato maku hukumar hisba nace Kun saida gadon mahaifinmu dake kwance gadon asibiti.! Ta k arashe sai huci take.

Habibu sai bud e hannaye yake yana kuma ingiza Azeema. Fad i yake Ahtoh magana kenan a fito masa da hakkin matarsa.

Azeema ta Ciro waya da zummar kiran Salima kenan suka sinkayo kukan Mama. Ta kamo bakin mayafi tana matse idanunta  Ni Tasi u zai tona ma asiri a garin nan.. Na rufa masa asiri yana d an wiwi na d auki  ya na basa a tunanina zaiyi hankali ashe ni ce  yar wiwi.

 Mama ba fah kuka zakiyi ba, nemo Tasi u Ya kamata kuyi yanda ya shiga Ya fita dan wllhi muddin Tasi u baizo ba daga nan ofishin hukuman hizba na nufa na zayyane masu komai. Kun raba gadon mahaifinmu da ransa.! Azeema tace tana huci.

Habibu yai saurin shiga tsakiya kaman wani alk ali  A a a a baza ayi gaggawan gayyato hukuma ba tinda abin duka na gida ne. Kamata yayi a binciko yanda Tasi u yake duk rintsi. Yanzu zan tafi yanda shi Tasi un ya cika zama na tuntub i abokansa tinda dai baza a samesa a gida ba. Na tabbata baiyi nisa ba. Ya k arashe yana mai wucewa cikin sauri.

Ummul da Khulsum suka dubi juna cikin tsananin shock. Mama da Badi a saida shagon Abba sukai kenan ko mai hakan yake nufi.? Innalillahi wa inna ilaihi raji un.

Suna a haka aka zo neman kud in magungunan Abba wanda kusan kwana biyu kenan yana skipping wasu treatments d in masu matuk ar mahimmanci.

Mama sai ta hayyayako ta soma bala i tana fad in ta gaji da zaman asibiti ma jinyar da yak i ci yak i cinyewa.

Nurse yace  Yanzu babu kud in da za a masa jinyar.?

Azeema tace  Kurma ne kai baka ganin tashin hankalin da muke ciki ne.. Damfararmu fah akayi..

K arasowan su Ummul suna tambayan mai ake nema gameda jinyar mahaifinsu yaja hankulan su Badi a. Ita kam Mama har yanzu fah bata wani gane mai ake ciki ba hankalinta kacaukam naga Tasi u da kud ad enta.

Badi a tace  Kud in jinya ake nema ko zaku biya ne tinda wancan karan ma ku kuka biya. Sai aje a sake saida jiki a kawo kud i. Ko mazan ne babu.?


Khulsum ta dubeta Har lokacin mamakinsu bai saketa ba  Da dai a kiramu b arayi marassa imani masu saida k addaran mahaifinsu da ransa gwara ace jikinmu muka saida muka biya kud ad en jinyarsa. Kin fahimta B arauniya matar b arawo.!

Badi a ta nufota a zafafe tana fad in  Ke ni sa anki ne dan ubanki.. Sai na gurje bakin ki yanzu a nan..!

Saida aka shiga tsakanin Khulsum da Badi a.

Nurse yace  Yanzu haka Dr zaizo babu abinda aka buk ata.. Shin ba hanyar da za a bi a samu a saya magungunan..?

Kaman daga sama suka sinkayo wata murya  K warai akwai hanyar da za a saya!

Mama dake shirin barin wajen dan batada lokacin cecekucen rashin kudin jinyar Malam da malaman asibiti burinta kawai ta isa ta cimma Tas u. Nan tai birki jin wann murya dai tai ma me muryar farar sani. A hankali take k ok arin juyowa har dai ta karkato gaba d aya.

Mama ta daskare. Ta shiga mutsuka idanunta tana duban wacce take gani gaba gareta  Suwaiba.! Ta furta cikin tsananin mamaki.

Suwaiba ce fah.. Suwaiba Amaryar Malam Isubu nata take gani sanye cikin tufafi na alfarma. A gidan Uban wa Suwaiba tayi arziki dare d aya. Karfa hausar nan da ake cewa dare d aya Allah kan yi bature ta tabbata kan Suwaiba. Ta kuma mutsuke idanunta dan har lokacin gani take kaman gizo ne ba gaskiya ba. Wai Suwaiba shashashar matar Malam Isubu ce haka kaman wata matar shugaban k asa ko gwamna.

Khulsum da Ummul ma da mugun mamaki suke duban mahaifiyar tasu wacce kaman an canzata. Suka dubi juna suka kuma duban Umma shaye da tsananin mamaki, cikin tsananin shock suka furta  Umma.!

Umma taci gaba da takowa gaba garesu. Azeema da Badi a ma da mugun mamaki suke duban Umman.

Kai tsaye nurse d in Umma ta nufa tace  Nawa ake nema..?

Nurse d in Ya d ago takardan na list d in abubuwan da ake buk ata Ya soma karantowa.

Kafin Ya gama karantowa Umma ta d aga masa hannu alamun dakatarwa lokaci guda ta bud e tsadadden handbag d in dake rik e hannunta ta Ciro sabbin kud ad e  yan dubu dubu sai walk iya suke. Mama ta zaro ido waje ganin dubabe bugun habuja suna walk iya suna kashe mata ido. Wai Suwaiba ke fiddosu.

Ko k irgawa batai ba ta mik a ma nurse d in  Ungo nan.. A saya duk abinda ake buk ata, idan yayi canji ka rik e canjin idan kuma akwai abinda bai isa ba ka sanar Dani.. Ko menene.. Ta k arashe tana gyara zaman tsadaddan mayafin dake bisa kanta.

Nurse ya murmusa  A a Hajiya saidai na Miki jagora ki biya da kanki.

Umma ta jinjina kai yayinda Umma ta take masa baya.

Tin daga k afafu Mama ke dubanta Har zuwa tsadadden leshi da yan kunne da sark a dake kwance wuyanta. Wann ko taron manyan matan gwamnoni Suwaiba taje a haka ai ta cinye taro.

Akan idonsu Umma ke gudanar da komai da taimakon nurse d in kafin daga bisani ta amso receipts ta dawo yanda ta baro ahalin mijin nata Wanda kowa shock Ya hanasa aiwatar da komai. Baga Mama da yaranta ba baga Yaran Umma ba wanda zasu iya cewa Har yanzu basu tabbatar idan mahaifiyarsu bace.

Ko takan Mama batabi ba ta dubi su Ummul wacce suma kansu ta koma masu tamkar bak uwa. Kallon rashin sani ne ko na mamaki suke bin mahaifiyar tasu dashi. Tsakiyan yaranta ta shiga wato Ummulkhairi da Ummukhulsum ta kamo hannayensu tace  Mujenku kuga mahaifinku..

Tamkar rak umai da akala haka Umma ke janyo su Ummul da???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? Khulsum. A haka suka zo suka shige gaban Mama da yaranta wanda suka koma kaman an dasa su.

Har suka shige cikin ward d in Mama da yaranta basu daina binsu da kallo ba.

Suna shigewa Mama ta dubi Azeema tace  Ke wanke ni da mari dan ubanki.

Azeema ta dubeta a yatsine  Ban gane na wanke ki da mari ba Mama..

 Nace ki mareni na tabbata ba mafarki nake ba.. Ba Suwaiba bace Ke min gizo ba. Inji ba itace yanzu ta shige gaba na ba ko.? Ku amsa min mana.. Na shiga uku ni Tani..

Bata kai aya ba taji zafi Ya tsunkuri  yar yatsarta na k afa. Badi a ce ta take mata  yar yatsar cikin k ok arin dawo da Mama hayyacinta.

Mama ta saki k ara tana d ingile k afarta  Wayyo kunama ta cijen.!

Badi a tace  Ba kunama bane ta cijeki, take maki k afar nai ki tabbata ba mafarki kike ba..

Azeema tace  Mama wllhi Umman su Ummul ce. Amma nima nafi zaton canzata akai.. Mama ina ta samo kud ad e irin haka dare d aya.. Kinga Har fari da shek i ta k ara dare d aya. Mama kin kaw ga suturan dake jikinta. Wllhi iriinsa matar Gwamna ta saka ranan da za a rantsar da mijinta.. Mama Ina matar nan ta samo kud i haka wai.?

 Yo Ina zan sani ina tareda ke a nan.. Mama tace tana kuma lek en bayan Umma a tsarace.

Badi a ta tab e baki tace  Kar canzawarta ya zautar daku. Abu ne a bayyane matar nan dama barikinta kawai take son yi auren mahaifinmu ya taka mata burki.. Yanzu da take ganin zai Mutu shine ta baje kolinta da kyau zatai barikinta mai dalili..

Azeema tace  Kai wllhi amma fah ta mun kyau, kinga shegen mayafin da ta watsa. Irin mai walwalin nan fah da ake talla online.. Inama ta bani aro naje dashi Bikin k anwar Habibi na yak i shegun danginsa.

Bata kai aya ba Mama ta hamb are bakinta  Kud in shan jini da tsafin zakije a baki.. Toh Idan shaye shaye kike kije Azeema.. Kije Suwaiba ta shanyeki.. Ni nayi imani itace ta asirce Ummul mazan dake nemanta ke gudu sabida Allah Ya rufa masu asiri da sauran kwanakinsu. Shi Fa izu dake kwanansa Ya k are gashi ta lashe kurwansa. Yanzu kuma abun yazo kan Malam Shiyasa data mik a sa gashi a kwance kafi gawa.. Kuma yanzu ba sai anjima ba zan fiddata daga cikin asibitin nan..

Fiuuu Mama ta shige ta nufi ward d in yaranta na biye da ita.

Bata damu da majinyata dake kwance wajen ba Mama ta shiga kururwa tana fad in Suwaiba mayyace yar K ungiya asiri ne na shan jini.. Ta tsafe  yarta Ummul tana amfani da ita tana cinye mutane kaman yanda Fa izu d an  yar uwan Malam Isubu ya mutu. Bai isheta ba yanzu ta mik a mijinsu zata cinye.. Sai dukan k irji take tana fad in wllhi bazaayi ma mijinta amfani da dukiyar  yar shan jini irin Suwaiba ba.

Sauri sauri wasu nurses da cleaners suka tafi kiran securities. Hango securities d in da Mama tai ya sanyata had iye kalamanta.

Securities suka k araso suna muzurai suna fad in

17 / 52