Auren Wata Uku Book Complete By Sameena Aliyu.doc

Author :  Sameena Aliyu Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   22 / 52

63K to 66K   out of 153.1K words

the fact that your company needs me.. And you need me too.. Kuma shine dalilin da yasa ka kirani kake sanar Dani duka shirye shiryenka.. So Daddy, deny it all you want. But the truth is that I m very much important to you.. And your company is nothing.! Absolutely nothing without me.! Yana ida fad in haka ya mik e zuciyarsa na masa zafi.


A daidai k ofan fita daga sashen ya had u da Alhaji Gimba na shigowa. Alhaji Gimba na ganinsa ya fad ad a murmushinsa. Bai damu ba idan Haidar bai gaishesa ba. Shi dai bazai tab a cire hope Akan Haidar d in ba. Alhaji Gimba yaci gaba da fad in  Congratulations to you and your team. Naji dadin wann al amari kuma inada yak inin company bazatayi danasanin zab en gwarazan da zasu jagoranci wann aiki irinku ba..I trust you and your team. Ya d anyi fasali kafin yaci gaba  Wann aikin kampani ne so ina shawartanka kar ka bari wani ma???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?tsala da kake dashi tsakaninka da mahaifinka yasa kai ma aikin rik on sakainan kashi ko ka yanke hukunci cikin fushi. Na yarda da Kai amma tunasarwa yanada kyau. The company s future relies on your hand Aliyu. And we have high expectations of you.. Let s set our differences aside so we can reach our common goal. Ko dan mu ba ma abokan Adawa kunya. Ya k arashe murmushi saman fuskarsa.

Tinda ya soma magana Haidar da hannayensa ke sakale cikin aljihu yake dubansa lokaci guda yana nazarinsa  Trust me, it s just a matter of time before we find out who the real traitor is.

Murmushi Alhaji Gimba ya kuma sakar masa kafin yai nuni da parlorn  Baringa mahaifinka. Have a good evening. Ya fad i yana mai shigewa cikin parlorn.

Lumshe idanunsa kad an Haidar yai had ida furzar da huci  Fake life fake people. Everything around this family is fake nothing is real. Lokaci guda yasa kai ya shige cikin sassarfa zuciyarsa na masa wani irin k una.

Ya fito daga sashen mahaifinsa kenan ya hangi k atuwar mota ta shigo cikin gidan shak e da kaya ta nufi nasa b angaren. Yabi motar da kallo kafin ya nufi hanyar sashen nasa. Nan ya hangi Mommy da Anisa sai nuna ma masu interior d in yanda zasu jera kayayyakin suke. Ga tsaffin Kayan duka an fito dasu.

Yai tsaye yana dubansu da mamaki. Can Anisa ta hangosa. Sai ta matso kusan Mommy tai mata rad a a kunne  He s here Mommy.

Mommy ta d ago tana tambayan wane kenan. Ganin Haidar ya sanyata fad ad a murmushinta. Ta k arasa da sauri ta kamo hannunsa  Haidar my son, today is the happiest day of my life.. An d aura aurenka yau Haidar.

Sai yaji abun banbarakwai. Shi ya ma mance da wani batun aure da yarjejeniya. Wani irin duba yake mata irin na da gaske take.? Da gaske auren suka masa sabida son zuciya irin nasu.

Mommy taci gaba da fad in  Wann shine Mafarin had in kan ahalinmu da yardar Ubangiji. Cikin ikon Allah komai zai daidaita. Bakinta ya gaza rufuwa har mamaki Anisa take yanda Mommy ke matuk ar d aukin wann aure. Taci gaba da nuna ma Haidar kayayyakin  Look duba kaga. I know you have high taste so I ordered everything to your taste. Ta saka hannu ta tallafo fuskarsa  Yau d in ina Jin na cika wani gurbi na zama uwa a gareka D ana. Burin ko wata uwa kenan taga D anta yakaiga cikan kamala.

K ok arin cire hannun Mommy daga fuskarsa yake Jin tana wasu irin sunbatu  Mommy will you please stop.! Enough of this drama. Ya dakatar da ita kafin yaci gaba  Quit the act already! Stop acting like you care.. Like you are responsible.! Like you are doing your motherly duties wad anda kika makara bakiyi ba tun a baya. It doesn t suit you at all Mommy.! Ya k arashe jijiyoyinsa har fitowa suke.

 Haidar. Ta ambaci sunansa kaman mai shirin kuka.

Dakatar da ita ya kumayi  Mommy you and I both know ba auren tsakani da Allah bane. Ba don ci gaban rayuwana matsayina na d anki kikai ba. You are doing all this for your own advantage. Ya d anyi fasali  Mommy my day is bad enough, thanks to my Dad. bazan bari ki k ara mun wani akai ba.! Yana ida fad in haka yasa kai ya fice daga gidan a gaggauce.

Jiki a matuk ar sanyaye Mommy ta juyo. Anisa ta k araso ta taddata.

 Mommy seems like ke kad ai kike son auren nan a gidan nan. Shin bazaki hak ura da auren nan ba kawai tinda Wanda akayi dominsa baya so. Kawai ki d aga waya ki kira Ammi ki sanar da ita an fasa tin kafin a kawo matar cikin gidan nan. Dan na tabbata wann auren ba mai d orewa bane.

Mommy ta harereta  Ke dalla rufe mun baki. Bansan shashanci, Wann aure da kika gani mutuwa ce kawai zata raba matar da Aliyu. Idan kinga auren ya Mutu ki tabbata matar ta Mutu ne.! Tana ida fad in haka tasa kai ta shige tana neman layin Asshe dan Jin mai ake ciki.


Anisa ta tab e baki tana mamakin wann irin al amari.

**

Kano&


Dik maganganun da Hilal keyi cikin motar ba sauraronsa take ba. Hasalima bazata iya tantance mai yake cewa ba da za a tambayeta. Damuwarta kawai su isa ga  yaruwarta tai k ok arin shawo kanta su gudu tinda babu idon Umma. K aran bud e gate ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da tai nisa ciki. Zuciyarta sai tsinkewa yake tana addu an Allah ya bata ikon shawo kan Addarta Ummul cikin sauk i. Tana ji a jikinta wann aure babu wani alheri cikinsa.

Hilal yana Ida parking tai saurin kama handle tana kokawan bud ewa.

Ya tsareta da idanu  Easy kar ki balla min marfin mota bayan kin b ata min da tab o..

Bata amsa shi ba dan bata da lokacinsa. Tana Jin sanda motar ta fita a lock tai saurin bud ewa ta fito. Sauri sauri ta nufi cikin gidan har kaman zatai tuntub e.

Hilal ya bita da kallo had ida tab e bakinsa kad an kafin ya nufi bangarensa.

A daidai mashigar gidan Khulsum taji ance da ita  dakata..!

Cak taja ta tsaya sakamon muryar taji ya dakatar da ita.

Umma ta gani ta tsaya tayi k ebebe rik e da kunkumi tana duban Khulsum d in.

 Umma..! Khulsum ta fad i mamaki kwance saman fuskarta.

Umma ta jinjina kai  K warai ni ce nan.! Tai maganar tana kuma k obarewa bakin k ofa.

 Umma.. Me kike a nan..? Khulsum ta tambaya cikeda mamaki.

 Ke zan tambaya mai kike a nan..? Wani munafuncin ne Ya kawoki..? Awho kinzo ne ki kashe mata auren Tun kan ta tare ko..?

Mamaki Ya hana Khulsum furta koda kalma sai duban Umma da take. Da k yar ta iya furta  Umma a ina uwar amarya ta tab a yima  yarta rakiya d akin miji.. Haba Umma fisabilillahi, bayan auren rashin galihu da kikai ma  Yaruwata shine saida kikai mata rakiya. Shin baki gudun maganganun mutanen ne Umma..?

 Allah tsari gatari da saran shuka.. Aure auren gata nai ma d iyata irin Wanda kaf lungun ku ba a tab a samu ba. Ki koma ki tambayi  yan lungun naku kiji wani irin aure akaima Ummul. Aure na bajinta auren da na tabbata bazaa daina kambabasa ana labarinsa ba. Ke harta da masu shigewa saida suka shaida.. Kuma ban rako Ummul ba saida zuciyata ta tabbatar min zaki iya zuwa& Gashi kaw kin zo d in kaman yanda nai tunani.. Zuwanki na sani ba Alheri bane.. Dan na tabbata kaman yanda nai alwashin aurar da Ummulkhairi haka Kikai alwashin lalata mata aure. Tinda ba yau kika saba korar mata maza ba. .Ke ni fah akan auren nan wllhi Khulsum sai mu raba gari dake.! Ta k arashe tana sakin huci.

Khulsum ta jinina kai a hankali tana duban mahaifiyar tata  Umma kin kaw ji abinda kike fad i..? Tai maganar cikin rawar murya.

 K waraiii kuwa.. Wllhi sai kiyi yamma nai gabas muddin kikai yunk urin lalata auren  Yaruwarki Wanda Babu kalan fad i tashi da banyi ba dan ya tabbata. Tsaf zan yafeki Khulsum muddin kika kawo mishkila.

Hawaye suka gangaro ma Khulsum  A a Umma. Abun bai tsanani haka ba. Har kullum ke mahaifiyata ce banida tamkar ke.. Bazan b ata auren Adda Ummul ba.. Na Miki alk awari Umma.. Amma dan Allah alfarma d aya nake so kimin..

Yanda Umma ke dubanta a dak ile sai ka rantse ma wata tsararta take jifa hararan.

 Umma dan Allah ki bari nai Sallama da Adda.. Na rok eki..! Ta k arashe tana had e tafukan hannayenta biyu waje guda alamun rok o.

Umma bata amsa ba sai k ofan waje da ta shiga nuna mata  Fita.. Wuce ki fita.. Wllhi idan ni na haifeki kuma na haifi Ummul bazakiyi Sallama da ita ba.. Shige ki fita nace kar na bud e idanuna na ganki..

Khulsum ta dubi mahaifiyarta da mamaki  Umma kin Sallamanin kenan..?

 Idan haka kika d auka.. Kije duniya da yawa..

Innalillahi wa inna ilaihi raji un Khulsum ke nanatawa cikin zuciyarta. Wai mahaifiya ke fad a ma  yarta haka.. Anya Umma ita ta haifesu..? Anya akwai iyaye irin Umma..? Anya mutum zai d auki D ah a cikinsa tsawon watanni tara Ya haifosa duniya yaci gaba da rainonsa rana tsaka Ya k isa sabida wani buri nasa na duniya..? Anya akwai irin wad ann iyayen..? A iya saninta harta dabba yasan dadin d ansa. Meyasa tasu mahaifiyar ta zama haka..? Shin dama ana jarabtan bawa da iyayensa..? Ashe ba iyaye bane kawai ake jarabtarsu da yaransu ashe Yaran ma akan jarabcesu da nasu iyayen.. Ta lumshe idanunta hawaye suka gangaro mata. A hankali take ja da baya hawaye na gangaro mata tana duban Umma.


Umma kaw bayan ta tabbata Khulsum ta fice cikin gidan ta koma harda ce ma maigadi idan wann yarinyar ta dawo ya koreta.

Suna zaune parlor itada Asshe bayan k awayen Asshe Sun watse. Asshe ta dubi Umma tace  Yarinyar nan taki akwai fitina, sam batai halin  yaruwarta Ummul ba.

Umma ta tab e baki  Ai mutane biyu ne mabanbanta halayya. Fitinanniya ce ga taurin kai tsiya da masifa yacce kikaga k anwar Ubanta. Bata rage ma Dije komai a d abi a ba.

Asshe tace  Wacece Dije..?

Kafin Umma ta kaiga bata amsa suka sinkayo wata murya daga k ofa  Ni ce nan Dije k anwa d aya tilo ga Isubu..!

Daram.! Daram!! Daram.!!!

Haka k irjin Umma ya bada wann sauti cikin sakan guda.



SameenaAleeyou=???
*AUREN WATA UKU.!*




*20*






??Sameena Aleeyou&
'





Inna Dije taci gaba da takowa cikin parlorn. Yayinda Umma keta faman k ifta idanu, zuciyarta bata daina tsinkewa ba.

Daidai saitin Umma Inna Dije ta k araso ta tsaya. Umma ta kasa d ago idanu ta dubi Dije.

 Dole ki kasa d ago idanu ki dubeni Suwaiba. Idan Har kinada sauran kunya bazaki dago ki dubeni ba..

Umma ta soma girgiza kai hawaye na zubo mata Har lokacin bata d ago idanunta ba.

Fincikota Dije tai tana fad in  zo nan.. Yau sai naji uban da ya tsaya miki a garin nan Suwaiba har kike buga wasanki da sunan wauta da shashancin gangan..!

Ta kuma janyo Umma a zafafe. Hajja Asshe tai saurin raba tsakaninsu  Inaga dai ya kamata ayi komai gaban idona.! Ta k arashe tana duban Inna Dije data cakumo Umma.

Umma ta k walalo idanu waje Jin zaa kwance mata zani gaban Hajiya Asshe. Ta had e hannu biyu waje guda alamun rok o  A a Dije.. Kar kiyi haka.. Wann matsala ne da ya danganci ahali..

Inna Dije ta murmusa tana duban Umma  Dole kice matsala ce da ya danganci ahali Suwaiba.. Sabida bakiso a bankad o sirrikanki gaban sirakanki ko..? Kin masu rufa rufa kin aura masu  yarki da lak anin mahaifinki ya fad a kanta cewa ita d in bazata tab a aure ba.. Sabida wani babban Dalili Wanda nida ke muka binne hakan tinda jimawa..!

Umma ta zaro idanu waje tana duban Inna Dije da Jin wani batu Wanda ta kasa fahimtar ina ya dosa..

Asshe ma idanu waje take duban Umma da Inna Dije cikin tsananin d aurewar kai  Wa.. Wani batu kenan..?!

Dije ta murmusa cikeda cin nasara. Cikin zuciyarta take ayyana lokaci yayi lokacin d aukan Fansan rasa tilon D anta Fa iz da tai a dalilin Ummulkhairy.

Umma ta kuma girgiza Kai  Dije wa.. Wani dalili ne wann.. Kuma.. Wani magana muka tab a binnewa mu biyun Wanda ni ban sani ba.?

Dije ta murmusa  Suwaiba kar ki fara mana dramarki a nan.. Dan kinsan tar nake kallonki.. Kin shashantar Dani Karon farko na rasa Fa iz dalilin  yarki bazan kuma bari ki shashantar Dani ba..!

Umma ta kuma girgiza Kai hawaye na Neman b allo mata.. Zatai magana Asshe ta dakatar dasu  Wai meke faruwa ne..?

 Abinda yake faruwa shine D anku ka iya zama gawa na gaba kaman dai yanda Fa iz d ina ya mutu..!

Asshe ta mik e tana kuma zaro idanu dafe da k irji  Na shiga uku gawa fah..! Haidar ne zai zama gawa na gaba..?!

Dije ta dubeta sosai tace  K warai kuwa.. Domin Ummulkhairy da kike gani ba mace bace..!

Innalillahi wa inna ilaihi raji un.! Shine abinda Asshe take nanatawa tana ganin duniyar na Neman juye mata  Ba mace ba..? Mecece toh..?! Na shiga Uku ni Asshe me na aura ma D an  Yaruwata..?!

Umma na kuka take girgiza Kai tana duban Inna Dije jin irin sharrin da ake ma  yarta akan idonta  Dije kiji tsoron Allah..!

 Idan banji tsoron Allah ba tsoronki zanji ko tsoron mushurikin mahaifinki wanda ya maida Ummulkhairy yanda take a yanzu..!

Izuwa lokacin kan Asshe ya gama k ullewa.. Ta dubi Umma dake duk e wajen tana hawaye tace  Ke Suwaiba..! Fad a mun.. Meke faruwa..? Wacece  yarki..?

Umma bata iya cewa komai ba sai kuka tana girgiza Kai..

Inna Dije ta kuma murmusawa  Ai bazata iya sanar dake komai ba domin kuwa batada amsar baki.. Amma ki tambayeni ni zan sanar dake komai.. zan sanar dake Wacece Suwaiba da badak alan data k ulla a doron k asa..!

Asshe ta d ago tana duban Inna Dije cikin tsananin shock.

Lokaci guda Inna Dije taci gaba  Yarinyar da kuka aura ma D anku ba mace bace.. Domin kuwa a lokacin da Suwaiba ta samu cikinta ba cikin  Ya mace tai fatan samu ba.. Mahaifin Suwaiba ya kasance gasunkumin malamin tsubbu ne Suwaiba ta tafi wajensa amsar taimako a lokacin tana d auke da cikin Ummulkhairy kan cewa ya bata lak anin haifo d a namiji... Sabida Sun mance Allah shi kad ai yake halitta mahaifinta bai isa ya sauya halitta ba.. Wann dalili yasa aka haifo Ummul a idon duniya mace ce mai kyau son kowa k in Wanda ya rasa.. Amma a zahiri ne kawai. A magana ta auratayya namiji bazai tab a amfana da Ummul ba domin kuwa ita d in an tsafeta tun a ciki.. Hakan na nufin Ummulkhairy bazata tab a aure ba.. Idan kuma tai toh fah duk mijin da ta aura zai mutu. Idan bai Mutu kafin ta kaisu ga aure ba kaman dai yanda Fa iz d ina ya mutu toh zai mutu idan wata alak a ta auratayya ta gifta tsakaninsu.!

Duniyar Asshe ya shiga juyawa.. Innalillahi wa inna ilaihi raji un.. Meke shirin faruwa dasu.. Shin ta yaya zata sanar dasu suma auren warware asiri kawai na watanni uku sukai da Ummulkhairy Wanda sai ya mu amulamceta wann sihirin da aka masa ya karye.. Ta ina zata soma sanar da  Yaruwarta abinda ke faruwa.. Lallai tana tsaka mai wuya..!

Muryar Umma ne ya katse mata tunanin yanda take fad i cikin kuka  Haba Dije..! Dije kiji tsoron Allah.. Ki tuna akwai mutuwa.. Dije har zaki iya tsara wann babban k arya kan D iyar D anuwanki.. Dije baki tsoron hakki.. Baki tuna yau idan babu mahaifin Ummul ita amanace a gareki..?!

 Rufe mun baki annamimiya..! Ke Har akwai maci amana irinki ne Suwaiba.. Kin mance Ya aurenki ya kasance ne na tuna miki Suwaiba..?

Umma ta kuma kifa kanta a k asa kuka na kuma zuwa mata. Lokaci guda Dije taci gaba  Talla kike kawowa cikin gari a lokacin Tani da mahaifiyarmu wato sirkarta kenan basu jituwa mahaifiyarmu tana so Yayana Isubu ya k ara aure kafin ta bar duniya sabida yara mata da Tani ke haifa masa. Mahaifiyarmu tana son samun jika namiji daga wajen D anuwana Isubu.. Ke Suwaiba kika yaudari Tani kikace a garinku mahaifinki malamin zaure ne kuma yana bada lak anin mallaka, Tani ta biyeki kika kaita Har rugarku da sunan tana neman lak anin mallaka. Shakuwa ya shiga tsakaninku kika d auki Tani tamkar Yaya. Tani ta daukeki tamkar k aramar k anwa ta baki dukannin yardarta. Kika zamto mata ingiza mai kantun ruwa.. Kika zaga Tani kikaci amanarta. Maganin bakin jini keda Ubanki kukaita tura ma Tani Wanda zaisa mijin Tani ya tsaneta ya soki. Haka ne..?

Idanun Umma suka kuma firfitowa waje tana jin sirrikanta kaf Dije na fito dasu. Dan wann b angare da Dije take fad i bata da haufi gaskiya ne. Cikin rawar murya irinta mai kuka take furta  Amma nayi nadama kuma mahaifina ya daina wann aikin kafin ya bar duniya Dije.

22 / 52