Auren Wata Uku Book Complete By Sameena Aliyu.doc

Author :  Sameena Aliyu Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   49 / 52

144K to 147K   out of 153.1K words

da nake masa bai kai na sangartasa Har haka ba. Nima nawa iyayen ba haka suka mun ba. Dan haka bazanyi ma nawa d an kisan gwani ba. He must learn to take responsibilities. Kuyi shawari da D anki. Kodai ya kama Sana a ya hakura da karatun yayi auren ko kuma ya ci gaba da karatu kafin yayi auren.! Yana ida fad in haka ya mik e zai fice. Sai kuma ya juyo ya dubi Hilal  Kana jina, ka dawo da duka kud ad en da na baka da sunan makaranta. K wandala ban yarda ka bari wajenka ba. Kar ka bari na sake maimaita maka ka dawo mun da kud ad ena.! Yana ida fad in haka yasa kai ya fice.

Asshe taji duniyar na juya mata. Ta k araso gaban Hilal dake duk e wajen  Ina jinka.. Wace yarinyar ce ta d auke maka hankali haka..?  Yar waye.. Waye mahaifinta a garin nan.?!

Ya d ago yana murmushi mai ciwo yana duban mahaifyarsa  Ammi is that really what matters now.? Kar ki damu kinfi kowa sanin ko wacece ita da kuma ahalinta..! Yana ida fad in haka ta mik e ya fice cikin sassarfa. Zuciyarsa fal damuwan yanda zaiyi Ya maidama mahaifinsa kud ad ensa kafin wa adin da ya basa Ya cika.

Yana ficewa Asshe ta mik e tana tunanin abun yi. Wacece ta d auke mata hankalin D a haka.? Khulsum.! Sunan da zuciyarta ya raya mata kenan. Ta soma girgiza kai tana zagaya parlorn. Suwaiba ta gama da ita da halinta dole ta nemo hanyar da zata raba Hilal da wad ann harababbun mutane kafin su gama da ita. Dije.! Ita ce ta fad o ranta. Dije ce kawai zata zamto makamin da zata yak i Suwaiba da ita.

Saurin ficewa tai ta nufi nata sashen. Saidai tana isa ta tadda wayar Anisa na shigo mata.

Labarin hadarin su Haidar da Anisa ta sanar da ita ya kuma jagula mata lissafi.

Asshe ta shafe goshinta tace  How s my sister doing Anisa..? Yaya  yaruwata take.?

Anisa takai dubanta ga Mommy wacce Daddy ke rik e da ita Sun nufi mota. Da kyar ya shawo kanta zai kaita gida ta dan huta Tai sallah. Saida yai mata alk awarin dawowa da ita asibitin ma kafin ta amince ta bisa.

Ta numfasa daga nan yanda take tsaye tana wayar  Your sister needs you Ammi.. Gata nan ta kasa barin asibiti. Ta kasa cewa komai ta kasa cin komai sai kuka da kiran sunan Haidar take. Ammi ya kamata ko mai kike ki bari ki zo Abuja.. Ki raba Haidar da annobar da kika lik a masa kafin tai ajalinsa.. Dan tinda ta shigo ahalin tashin hankali ne ke kunno kai na yau daban na gobe daban. And worse part d in shine ta lashe Zuciyar Mommy bata ganin laifinta. Tana mata wani irin soyayya da bazai bari ta bud e idonta ta gane cewa ita d in annoba ce kuma had ari ce ga rayuwar Haidar.. Ammi only you.. Ke kad ai ce zaki iya raba wann jarabbabben aure da kika nemar ma Haidar. Dan idan ba kece kika bud i baki kikace Ummul annoba ce Mommy bazata tab a yarda ba.!

Zufa yaci gaba da karyo ma Asshe dan yanzu wani masifan da ya b ullo mata ya wuce gaban tasa k afa ta tsallake. A halin yanzu ba rayuwar Haidar bane kawai akan layi harda rayuwar nata d an Hilal. Dan tayi imani tsautsayi da masifa ke bibiyan Suwaiba da ahalinta.. Bazata tab a bari Hilal dinta Ya fad a cikin wann bala i ba. Nan take ta sanar da Anisa zata kira Mommy amma bata jin zata samu zuwa duba Haidar a daidai wann lokacin domin kuwa wani wutan zata kashe. Dole ta saka ma Suwaiba birki.

Anisa tace da mamaki  Ammi yanzu ita Ummul d in Har tanada  yaruwa da Hilal ya k yalla ido kanta.? Ammi wai mai kika gani so special gameda mutanen nan ne kam da kika jajibo mana su..? Ammi yanzu kina so kice mun Abba yace Hilal ya maida masa kud ad ensa.?

Asshe tace  Wann ba matsala ta bace Anisa. Tinda nasan D anuwanki kobon mahaifinku bazai ciwo ba zai maida masa. Da ace kece sai na damu.

Anisa ta katseta  Ammi you are wrong.!

Asshe tace da mamaki  Mai kike nufi.?

Anisa taci gaba  Ammi.. Bana jin Hilal yanada kud ad en maida ma Abba yanzu. Tai maganar kanta staye.

Da mamaki Asshe tace  Kan mai zaki ce haka.. Kinsan wani abu ne..?

 Ammi Hilal ya tura mun kud ad en dake account d insa.!

Da mamaki Asshe tace  Ke ban fahimceki ba mai kike nufi..?

Take Anisa ta labarta komai yanda Leenah taita karb an kud ad e wajenta ita kuma tana tambayar Hilal.

Asshe ta koma ta zauna gijif saman gado tana dafe kai  Kin kashe ni Anisa..! Take zuciyarta ta soma ayyana mata Yanzu idan Hilal bai maida masa kud ad en ba dole k arshe zai fad i gaskiya cewa ma Anisa ya bada. Idan aka isa nan.. Magana zai fito fili.. Komai zai bayyana. Mijinta zai San ta tafi gidan boka. Aunty Kwaise zata San ta ha inceta akan auren Haidar da Ummul. Wani b angare na auren da  yaruwarta bata san dashi ba zai bayyana. Snn  yarta Anisa zata shiga uku. Gaskiya zai bayyana cewa ita ce sanadin rufe Aunty Kwaise da akai. Ahalin zai tarwatse .. Bazata bari hakan ta kasance ba.. Bazata bari ba.

Gaba d aya Asshe ta daburce ta susuce. Ta yanda take shiga ba ta nan take fita ba. Daga ita Har Anisar kuka suke. Ko wanne na jingine laifi ga d aya b angaren.

Anisa na kuka take fad in  Ammi.. Mommy bazata sake stanata ba ma sai taji cewa had arin da ya samu Haidar inada hannu ciki..!

Cak hawayen Asshe suka k afe  Na shiga uku.! Anisa mai kika zama..? Kin lalata komai kin b ata komai keda nace kar ki aiwatar da komai ba tareda umarni na ba.!

Anisa na kuka take fad in  Har yaushe zan jiraki Ammi.? Har tsawon wani lokaci zaki d iba kafin ki fitar da Ummul daga rayuwar Haidar.. Duk abinda na aiwatar sabida son Haidar nayi. Ammi I couldn t wait for you to act.. I had to do it my way.. And I ended up screwing everything up as always.!

Ta share hawayenta tana huci  But there s no going back Ammi.. Abinda ya faru ya Riga ya faru. Idan kikai wani abu foolish ko kika tona asirina wajen Mommy. Ba ni kad ai Mommy zata yak a ba Ammi..  Yaruwarki will wage a war against you zata tsaneki ne..  Yaruwar da ta rik eki har kawo Aurenki..  Yaruwar da ta d aukeki Aminiya abokiyar shawari. The best solution shine ki bar min komai a hannu na.. Ki tsaya a kano ki kashe wutan da Hilal ya kunna.! Tana ida fad in haka ta kashe kiran.


Wani irin kuka Asshe ta fashe dashi duniyarta tai mata d aurin goro. Ta d aura hannu biyu akai tana fad in  ya yanta biyu zasuyi ajalinta. Cikin duka abubuwan data aiwatar Bata tab a tsammanin zai backfiring da yaranta tsamo tsamo ciki ba.

Mik ewa Tai tana tunanin kuka bai ganta ba. Take ta danna kiran Dije.

Dije tana ganin kiran Asshe tai wata murmushi da gefen fuska. Cikin zuciyarta take ayyana kin kira akan gab a.


Saida ta Lek a ko ina ta tabbata babu mai ganinta kafin ta d aga kiran. Babu b ata lokaci Asshe ta sanar da ita dalilin kiran.

Inna Dije ta sanar da ita tana gari ta tsammaci ganinta washe gari kafin ta juya Dutse tinda dama a washe garin take shirin komawa. Da wann sukai sallama. Washe gari kuwa kaman yanda suka tsara. Bayan Inna Dije tayima su Umma Sallama cikin mutunci ta nufi gidan Asshe..


Asshe ta dubeta ta kuma gyara zama  Ni da ke munsan sirrikan juna.. Haka ne.?

Dije ta murmusa  K walliya munsan abinda muka sani dai.

Asshe ta furzar da huci  And we have common enemy here.

 A a a a yimin da yaren da nafi wayo.. Mai kike nufi.? Ta k arashe tana fiddo idonta waje.


 Ina nufin munada mak iyiya guda d aya.. Ita ce Suwaiba.!

Inna Dije ta murmusa  Anzo wajen.. Ai ni a halin yanzu kallon  yaruwa Suwaiba take min ba mak iyiya ba.

Asshe ta girgiza kai cikin rashin fahimta  Ban fahimceki ba.. Kina so kice mun keda Suwaiba Kun sasanta..? Kin yafe mata duk abubuwan da tai maki a baya.. Ciki harda mutuwan tilon D anki.?


Inna Dije ta murmusa tana kurban soft drink d in da aka tarbeta dashi  Waye yace miki Dije tana yafiya..?
Ta kuma gyara zama  Ni da kike gani bana mantuwa kuma bana yafiya. D aukan fansa farilla ne. Na bama Suwaiba abinda take son gani ne a yanzu dan ta haka ne kawai zan cimma burina kanta.!

Asshe ta jinjina kai  Toh idan kuwa haka ne bakida Wanda kike dashi da zai taimaka Miki ki kai Suwaiba k asa kaman ni. Nikeda makullin auren Ummul a hannuna.! Nikeda makullin tashin hankalin da zai tarwatsa Suwaiba ya kaita k asa.. Ni keda makullin AUREN WATA UKU.! Ta k arashe idonta tar cikin na Inna Dije.

Murmushi Inna Dije take tana dubanta  Maiyasa kika kirani.?

 Kiranki nai mu taru mu had a k arfi da k arfe mukai Suwaiba k asa. Dan bazan tab a bari nawa ahalin Ya tarwatse sabida ita da zuri arta ba. Bazan bari Alakan D ana da mahaifinsa Ya samu nakasu ba. Bazan bari Na rasa mijina ba. Bazan bari na rasa D ahna ba. Bazan tab a bari D ana ya auro jinin Suwaiba ba. Bazan tab a bari na had a zuri a da Suwaiba ba.! Ta k arashe tana huci.

Inna Dije ta murmusa  Idan kina so na taimakeki fayyace min komai.

Taryan taryan Asshe ta karanto mata yanda Tai da mijinta harma da D anta Hilal da kudin da ya tura ma  yaruwarsa Anisa dan ya rufa mata asiri da cewa da maifin Hilal yai Ya maido masa kud ad ensa Har kawo auren da Hilal d in yace yana son yin Wanda ba kowa yake so b????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  a face  yar Suwaiba.

Inna Dije ta sauk e ajiyan zuciya  Idan Har kina so kiyi ma Suwaiba da ahalinta iyaka da zuri arki zab i d aya kike dashi a nan.


Asshe ta girgiza kai cikin rashin fahimta  Wane zab i kenan.?


 Ki fitar da Tani kishiyar Suwaiba daga kurkuku.!


Asshe ta d ago da mamaki tana duban Inna Dije  Tani kuma.? Meyasa zan fitar da ita.. Maiyasa zan fitar da matar da Suwaiba ke fad i tashi wajen ganin ta fitar da ita.? Maiyasa zan taimaki Suwaiba.?!


Murmushi Inna Dije tai tana mai fitowa kad an daga cikin kujeran  Banida tabbaci kan tuban Tani. Da gaske ne ta canza kokuwa wasa da hankalin Suwaiba take kaman yanda nai. Tani a halin yanzu Babu abinda take buri kaman ta shak i iskan  yanci.. Ina mai tabbatar Miki idan har Tani tasan cewa kece Kika fiddata Babu abinda zaki umurceta ta gaza miki shi. Zaki mallaki Tani a tafin hannunki.! Ta k arashe shu umin murmushi irinta gogaggun mata saman fuskarta.

Asshe tai shiru kaman mai nazari. Tabbas fitar da Tani zai mata amfani ta wata fuskar bayan mallakar Tani da zatai. Zata jifi tsuntsu biyu d dutse d aya. Zataja layi ma D anta Hilal da hakan.. Tinda ta tabbata ba zaiso mahaifinsa yasan cewa ya tura ma  yaruwarsa Anisa kud ad en makarantar sa ba. Idan Hilal yai alk awari baya tab a sab awa musamman tsakaninsa da  yaruwarsa. Yana k aunar  yaruwarsa da zai iya zaban ya shiga matsala sabida nata asirin ya rufu. Idan ta fitar da Tani hakan na nufin ta samu igiyan d aure Hilal.

Ta murmusa tana duban Inna Dije wacce itama can k asan zuciyarta da nata manufan akan fidda Tani da take so Asshe tai.


 K warai na fahimceki kuma na amince. Idan Har fitar da Tani daga kurkuku na nufin rugujewar Suwaiba na amince zan fitar da ita.

Inna Dije ta jinjina kai  Suwaiba bazata san kece kika fidda Tani ba. Zan ci gaba da shashantar da ita.. Abin zai kasance kaman dai ni ce nai ma Tani hanyar fita daga kurkuku. Hakan zaisa Suwaiba ta kuma yarda da sakin jiki Dani. A sauk ak e zamu kaita k asa.

Asshe ta murmusa tana jinjina kai.. Nan take suka shirya komai da yanda zasu gudanar da komai.

**

Bayan kwanaki uku da faruwan wann al amari Tani ta shak i iskan  yanci. Duk a tunanin Umma Inna Dije ce Tai hanya aka fidda Tani ba tareda tasan cewa Asshe ce ta biya Bakauye kud ad ensa harda tara.

Tani taita kuka tana godiya ma Suwaiba da Dije da alk awarin zama da kowa lafiya.

A b angaren Hilal koda mahaifinsa Ya tutsesa da maganar kudi Asshe tai karaf tace taimako yai ya fidda sirkar Haidar da aka lak a ma sharri daga gidan kasu. Taci gaba da matsan hawaye tana fad in  Alhaji ni bansan wane irin Zuciyar taimako Hilal keda shi ba. Kaf kud ad en yayi amfani dasu wajen d aukar ma surkar Haidar Lawyer da biyan tara. Ina laifin Ya sanar damu ko iyayen Haidar ko shi Haidar d in halinda ake ciki.. Ni yanzu na yanke shawarin zan d aga koda k adarata..


Katseta yai da fad in  Ba sai kin saida komai naki ba.. Dama so nake nasan mai yai da kud ad en.

Ya dubi Hilal  Taimako abu mai kyau ne koda ace wasu ka taimaka ba Dangin matan Haidar ba. Amma ka sani komai yanada tsari da hanyar da ya kamata abi a aiwatar duk kyaunsa.. Kud ad en nan da kai taimako dasu ka kai munzanin da zaka iya nemansu. Ka d aukesu matsayin bashi na baka. Zaka tafi kasuwa kai aiki tuk uru ka nemesu da guminka sann ka biyani kud ad ena. Yana ida fad in haka Ya mik e ya fice yana sab a babbar riga.

Hilal ya sauk e ajiyan zuciya yana mai lumshe ido. Ya bud esu ya dubi Amminsa cikin mamakin yanda ta tsara zance ma mahaifinsa.

Kafin yai wani magana ta dakatar dashi  K warai na fitar da Tani tinda nasan burinka kenan ka fitar da ita ka burge Suwaiba. Sann abu na gaba nasan cewa kud ad en da ya baka na makaranta ka turasu ma Anisa. Kuma nasan ko mai zai maka bazaka tab a cewa ma Anisa ka bayar ba. Abinda nake so kai a nan shine ba kai ba  yar Suwaiba.! Ka nemi  yar gidan ko waye ka aura amma ba  yar Suwaiba ba.!


Hilal ya girgiza Kai yana duban mahaifyarsa  Kinyi haka ne dan ki d aureni Ammi..? Sabida haka kika zab i taimaka masu.?

 Burinka kenan ai ka fitar da Tani koh..? Toh na cika maka wann burin.. Saura nima ka cika min nawa burin ka fita daga hark an Suwaiba da zuri arta. Idan kuma ba haka ba yanda nasa kudi na fidda Tani sai na sa kud i na kulle Suwaiba.! Idan auren kake so da gaske ka nemi  yar gidan ko waye ni zan tsaya maka koda mahaifinka bai tsaya maka ba. Amma banda  yar Suwaiba ehe.!

Ya girgiza Kansa  Kiyi hak uri Ammi.. You don t have to go this far.. Kimarki ya wuce haka a wajena.. Maganar aure kuma ki kwantar da hankalin ki na jinginesa , har sai na nemi na kaina kaman yanda Abba yace. Da yardar Allah.! Yana ida fad in haka yasa kai ya fice.

K arshe dai Asshe ciwon k arya ta kwanta gudun kar taje duba Haidar.
**

Abuja..



Yau kwanan Haidar ak alla biyar kenan a coma an doshi sati guda. Babu alamun farkawarsa. Duk wani masoyinsa Ya duk ufa addu a gareshi da rok ar masa sauk i wajen Ubangijin komai. Babu kaman Mommy da Ummul.. Mommy yini take asibiti yayinda Ummul ke kwana wajensa.

Yau suna zaune saman doguwar sofa dake fuskantar gadon da Haidar ke kwance bisa, na urar nasara Sun masa k awanya. Su duka biyun Sun saka shi gaba sun tsura masa ido.

Mommy taci gaba  A lokuta da dama mukan mance wasu ni imomin da Allah yai mana na d an lokaci ne ba mai tabbata ba& Allah yakan mana kyauta da samun wasu mutane cikin rayuwarmu. Kaman  ya ya, Iyaye, miji, mata da sauran makusanta. Wann kyautar ba mai tabbata ciki.. Ba Wanda yasan adadin kwanaki, watanni, a a shekaru nawa zakuyi tare kafin Allah Ya amshe wann kyautar.. Shin kayi appreciating wann kyautar.? Shin ka sauk e nauyin da aka d aura maka na hakkoki..? Ta juyo tana duban Ummul da idonta masu rauni  Ina rok on Allah yasa da sauran rayuwar da zamuyi tareda Haidar a gaba.. Ina rok on Allah Ya tashi kafad unsa Ya raya mun shi cikin aminci Ya zamo majib icin Al amaransa.. Ta kamo hannayen Ummul cikin nata baya ta share hawayen da suka gangaro mata  Ina rok on Allah Ya nuna mun zuri ar Haidar kafin na bar wann duniyar Ummul.. He s all I have.. I can t lose him..! Ta k arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka.

Ummul ma hawaye ne suka ciko idonta. Ta shiga jinjina kai cikin k ok arin k arfafa ma Mommy gwiwa, hawaye na gangaro mata 

49 / 52