Auren Wata Uku Book Complete By Sameena Aliyu.doc

Author :  Sameena Aliyu Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   9 / 52

24K to 27K   out of 153.1K words

ya tab a maku gadonku ina raye ehe.!

Yaranta suka rangada shewa suna kuma ingizata.

Daga Umma har Khulsum da Ummul Cak kukansu ya d auke suka ma nemi kukan da suke suka rasa. Innalillahi wa inna ilaihi raji un.. Wacce irin duniya muke rayuwa ciki.? Ace iyalanka daka rayu dasu ahalinka Wanda kafi kowa kusanci dasu ba damuwarsu ya zaayi ka samu lafiya ba. Ashe damuwarsu mai zaka Mutu ka bar masu ne..? Shin ina allan attajiran dake tara dukiya kota halin k ak a su Mutu su bar ma magadan da ko tausayinsu basa ji balle suyi masu addu a.. Innalillahi wa inna ilaihi raji un. Matarka da  ya yanka.. Hasbunallah wa ni imal wakil.. Muyi ma kanmu karatun ta natsu tun munada dama kafin dama ta kufce mana. Mu Gina ma kawunanmu ayyukan alkhairi. Mu d ibi dukiyoyin mu muyi aikin alkhairi dasu tun munada dama. Mu Gina ma kawunanmu sadaka mai gudana har bayan rayuwarmu dan ba Lallai abinda ka bari su maka ba. Allah ka bamu  ya ya masu albarka Wanda su kansu zasu zame mana sadaka mai gudana Ameen.

Wann rana da jimami Umma da yaranta suka yini.

Ummul ta dubi Umma su duka biyun idanunsu a kod e  Umma yanzu ya zamuyi. Haka zamu bari Mama da yaranta suyi yanda suke so..?

Khulsum dake gefe ta k ura ma waje guda idanu tace  Mai kuke tunanin a gidan da cikin Umma ma gaba suke da juna balle  yanuba..?

Umma ta kuma goge hawayenta dan ta d ago ina maganar Khulsum ya dosa.

Ummul ma tai saurin d agowa ta dubi Khulsum sai kuma ta dubi Umman  Umma ko Inna Dije zamu kira mu sanar da ita halin da Abba ke ciki..?

Shiru Umma tai kaman mai nazari kafin ta girgiza Kai tace  Har yau babu Wanda yasan abinda ya haddasa gaba da k iyayya tsakanin mahaifinki da tilon  yaruwarsa da suka fito ciki guda.. Mahaifinku ya b oye mana bai sanar damu abinda ya rabasa da Dije ba.. Amma ya datse alak a da ita kuma itama ta datse alaqa damu.

Khulsum tai saurin d agowa ta dubi Ummul wacce keta k ok arin danne marayan kukan dake taso mata jikinta har rawa yake tamkar wacce ta tuna wani abu.

Lokaci guda Khulsum ke ci gaba  Tin sanda Ya Fa iz tilon d an Inna Dije ya rasu Abba da Inna Dije basu kuma zama  yan uwa ba.

Take Ummul tai boasting cikin kuka mai tsanani ta mik e ta nufi uwar d aki.

Umma ta dubi Khulsum  Maiyasa Khulsum.. Maiyasa zaki ambato mata Fa iz& Meyasa zaki d ago mata wann mik i.. Sai kuma muryarta ya soma rawa. Cikin rawar murya take furta  Tinda Fa iz ya koma ga mahaliccinsa ahalinmu bai kuma daidaito ba.. Tabbas da Fa iz nada rai duk abubuwan da suke faruwa watak ila da basu faru ba.. Tabbas da Fa iz na nan a raye da yanzu Ummul d ina ta jima a d akinta.. Allah sarki Fa iz ka tafi ka barmu da tarin k alubale da iftila i.. Tabbas rashinka babban gurbi ne a garemu.. Ka tafi da kurwar ahalinmu Fa iz& ! Ta k arashe cikin tsananin kuka.

Khulsumu ta k araso ta rungume mahaifiyarta. Cikin rawar murya take furta  A a Umma duk abinda ke faruwa tuntuni rubutacce ne.. Allah ya nufa hakan dole sai ya kasance.. Wann itace k addaran ahalinmu.. Auren Adda Ummul kuma ko ya Faiz na raye ko baya raye bazai tab a faruwa ba sai lokacin da Allah yaso. Umma kiyi k ok ari kiyi tawakkali da sannu Allah zai kawo mana mafita kinji Umma ta& In sha Allah Abba zai samu lafiya kuma farin ciki zai dawo cikin ahalinmu da izinin Allah.!

Umma ta rungume  yar tata kuka na kuma kufce mata.

Tamkar wacce aka sinkara haka Umma ta janye jiki daga na khulsum. Ta shiga girgiza Kai tana duban Khulsum d in  Yaya tayi gaskiya Khulsumu, Anya ba wani mugun k addara bane yake bibiyan  yar uwarki..? Meyasa Fa iz ya Mutu kafin yakai ga aurenta.? Meyasa tin bayan da Fa iz ya bar duniya duk wani maneminta basa kaiga aure maganar ke watsewa.. Shin Anya ba alak ar Ummulkhairy da Fa iz bane yai Ajalin Fa iz..? .. Anya ba wann dalilin bane ya raba tsakanin  yan uwa biyu..? Ina nufin mutuwar Fa iz shine ya raba tsakanin Mahaifinku da  yaruwarsa.. Anya ba Ummul ce tayi sanadin Fa iz ba.?!



SameenaAleeyou=???
*AUREN WATA UKU.!*




*09*





*??Sameena Aleeyou&
'

Saurin rik e bakin Umma Khulsum tai tana girgiza Kai  Haba Umma wace irin magana ce wann.. Umma magana kike fah kaman bakiyi imani da k addara ba..Umma na zaci ciwon Abba ya dawo dake hayyacinki daga wann rashin tawakkalin.. Haba Umma saikace ba musulma wacce ta yarda da k addara ba..

A zafafe cikin zuban hawaye Umma ta katseta  Ki gaya mun cikin abunda nace wanne ne ba haka ba..?! Ki gaya mun Khulsum..! Taci gaba da kuka mai sauti tana girgiza Kai  Bak in K addaran Ummul shine yai ajalin D an  yaruwar mahaifinku Fa iz..! Bak in k addaran Ummul shine ya raba tsakanin mahaifinku da  yaruwarsa.! Bakin k addaran Ummul shine ya jefa mahaifinku halinda ya tsinci Kansa ciki..! Bak in k addaran Ummul shi yake sa ko wani namiji ya guje ta..! Bak in k addaran Ummul shi ya jefa ahalinmu cikin yanayin da muka tsinci kawunanmu ciki..!

Kaman daga sama sukaga Mama ta d age labulen parlorn. Ta jinjina Kai tana duban Umma  Na gode ma Allah da yasa kika furta duka wad ann da bakinki Suwaiba..  yarki Ummul itace tai sanadin Fa iz.. Yaron kirki aka lik a masa annoba aka rabasa da rayuwarsa.. Toh wllhi kinji na ranste Miki da Allah bazan bari  yarki ta kuma kusantar mijina ba balle ta lashe nasa kurwan.. Kai kaf d inku babu mai kusantar min miji..

???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Khulsum dake faman sakin huci goge hawayen dake kwance saman fuskrta tai ta k araso gaban Mama  Wllhi wllhi banga Wanda ya isa ya hanamu ganin mahaifinmu a asibiti ba..

Badia ce ta k araso ta tsaya gaban mahaifiyarta tana murmushi tana duban Khulsum dake ci gaba da sakin huci. Lokaci guda ta d ago hannunta dake rik e da wayar salulanta. Take tai playin recording d in muryar Umma da tai sanda take fad in Ummul ce tai sanadin mutuwan Fai z harma da ciwon mahaifinsu. Tana gama playing suka kuma sakin murmushi itada Mama. Mama taci gaba  Ko Kotu aka tafi wann kad ai ya ishemu shaida& Badia shige mu tafi wajen mahaifinku.. Daga haka sa Kai sukai zasu shige Khulsum ta yunk ura zatabi bayansu Umma tai saurin dakatar da ita tana girgiza Kai hawaye na fita mata dan kukan nata ya daina fita da sauti.

Khulsum ta dubi Umma. Ta rasa k unci ne ko takaicin mahaifiyar nata ne k unshe cikin Zuciyar  Haba Umma.. Haba Umma, kinga ga irin abinda nake fad a Miki.. Yanzu makirar matar nan zatayi amfani da wann damar ta iya cutar da mahaifinmu.. Umma dan Allah wai sai Yaushe zaki daina maganganu marassa kan gado fisabilillahi.. Umma a gabanki matar nan da yaranta suke lissafin mai Abba zai Mutu ya bari. A bayyane take so suke mahaifinmu ya Mutu.. Umma mai zai faru idan sukai amfani da wann damar suka k arasa mahaifinmu dake kwance gadon asibiti.. Umma kin cuce mu wllhi idan Mama da yaranta suka k arasa Abba ba kowa ne Sila ba face ke.!

A guje Umma tabi bayan su Mama tana rok onsu su rufa mata asiri kar sukai ma hukuma muryarta da Badia ta nad a cikin wayarta.

Takaici ya kuma Kama Khulsum dan tasan yanzu Mama da  yarta Badia Sun samu makamin shashantar da Umma dole su tilasta mata yin duk abinda suke so musamman da sukaji tana tsoron wai sukai recording d in da Badia tai ma hukuma. Khulsum ta bud e murya tana kiran mahaifiyar tasu. Lokaci guda take furta  Umma ki bi bayansu su Kai ki ma hukumar kinga  Yaruwata ma ta huta da muggan kalaman da kike jifanta dasu duk wayewar garin Allah.!

Tau!!! Taji sauk an mari saman k uncinta. Ta d ago da mamaki tana duban Ummulkhairy data d auketa da Marin. Lokaci guda take furta  Shin Kinsan girman mahaifiya Khulsum..! Shin Kinsan matsayin mahaifiya..? Shin Kinsan darajarta Akan  ya yanta..?

Cikin huci Khulsum take duban Ummul lokaci guda take furta  Akan na fad i gaskiya shine zaki mareni.. Mahaifiyarmu tana buk atar mai tunasar da ita.. Mahaifiyarmu tana buk atan mai nusar da ita..!

 Ya isheki Khulsum.! Ummulkhairy ta dakatar da ita kafin taci gaba  A haka ne zaki nusar da ita kina d aga mata murya kina fad in ta cucemu mu  ya yanta har Kina cewa taje hukuma su kamata.. Mahaifiyarki Khulsum.?! Tai birki tana girgiza Kai tana duban Khulsum cikin rashin yarda  Mahaifiya ce zaki fad a mata haka.. Ina karatunki na islamiya ya tafi..? Kin mance cewa ko nasiha za a ma iyaye cikin kwantar da murya da lallama ake. Kin mance k issan bawan Allah Junaid da ya keb e kansa a wajen gari yana bautan Allah. Mahaifiyarsa tazo ta kirasa yana ibada bai amsa ba. Akai haka har sau uku a na uku tace Allah ya had asa da sharrin  ya mace daga k arshe wann bawan Allah saida ya had u da sharrin mace. Karuwa taje tai . Bayan Allah ya wanke shi daga sharrin karuwa da ya fad a . Daga baya mahaifiyarsa ta fad i cewa wann bakin da tai masa shine ya kamasa.. Kinga darajan mahaifiya dukda ba sab on Allah yake ba bautan Allah yake saida bakinta ya bisa saida yai tasiri akansa.. Wann itace Uwa Khulsum.. Ba a wasa da al amarin iyaye..

Khulsum ta jinjina Kai tana hawaye  Na yarda Miki  Yaruwata.. Shin koda ace mahaifiyarka zata apka ma b ata sai ka k yaleta..? Ummul sanin kanki ne rayuwar Umma akwai gyara cikinta.. Sanin kanki ne Umma bata yarda da k addara ba.. Shin bakiji yanda ta d aura alhakin komai akanki ba har Mama da yaranta suka sami hujja.. Ummul rayuwar mahaifinmu na cikin had ari a wann gab ar dole na nusar da Umma kuskuren ta..

Cikin sanyi jiki Ummul ke duban Khulsum. Sai kuma ta girgiza Kai tace  Watak ila gaskiya Umma ta fad a.. Itace ta haifeni.. Tafi kowa sanina..

Khulsum ta k araso ta dafa  yaruwarta  Ubangijinki da ya halicceki yafi kowa saninki  Yaruwata.. Dan Umma tana mahaifiyarki bai zama hujja akanta ta dinga kausasa harshenta Akan k addararki ba.. Sabida Dani dake da Umma dama duk wani mahalik i bamuda ikon canza k addararki.. Allah shi yake k addara rayuwar mu yanda yake so ya kasance.. Iayakacin namu shine addu a Allah yai mana tsari da k addara mai muni.. Ki daina kuka  Adda Ummul.. Da sannu Ubangijinmu zai daidaita mana al amranmu ya kuma bawa mahaifinmu lafiya.. Kuma na Miki alk awari zan bawa Umma hak uri nai mata nasiha cikin lallama da kwantar da murya. Sai suka rungume juna suna kuka mai ban tausayi da tsuma zuciya.

Shiru shiru Umma bata dawo cikin gidan ba. Ummulkhairy tace subi bayan Umma su dubata.

Koda suka fito ma wayam basuga Umma ba. Ummul da Khulsum sukai tsaye suka jimami.

Khulsum tace  Kar dai Umma tabi su Mama ne..? Mai zai faru yanzu Adda..?

Ummul ta rasa abin fad i. Sukai tsaye suna duban mutane masu giftawa.

Daga can nesa suka hango mashin d in mijin Azeema ya nufosu ga Azeema zaune d amas saman babur d in.

Suka k araso sukai parking. Ta dafe shi ta sauk o sai karairaya take  Yauwa Habibi, da alama mun kusa mallakan mota dan na gaji da babur din nan. Kar ka damu na maka alk awarin da an bani kaso na na gado zan biya maka duk bashin da ake binka..! Ta k arashe tana aikawa su Ummul wulak antaccen kallo.

Khulsum ta dubi Ummul mamaki kwance saman fuskrta. Wai mahaifin su ke kwance gadon asibiti Azeema ke wann maganar. Daga ita har mijin nata kaman sunga kashi haka suka dubi su Ummul.

 Habibi bara na shiga na fito da kaya na mu tafi tinda mun hadu da Mama a hanyar asibiti. Azeema tace bayan ta dira daga bayan Babur d in. Haka ta k araso ta shige ta gaban su Ummul tana watsa masu wulak antaccen kallo.

Khulsumu tai saurin Shan gabanta  Adda Azeema kinga Ummanmu tareda Mama ne.?

Azeema taja tai birki tana watsa ma Khulsum banzan kallo  Ajiyanta kika bani da zaki tambayeni ko na ganta..?

Ummul ta girgiza Kai cikin sanyin muryarta tace  A a Azeema gani mukai ta biyo bayan Mama kuma munji kince kin hadu da mama a hanya Shiyasa muke tambayarki..

 Mahaukaciya ce ita ko k aramar yarinya ce ita..! Tinda ku kanku kunsan cewa mahaifiyar taku b elb el ce sama Sama ce sai ku nemi igiya ku d aureta a gida ko ku Sakata a turu maganin hauka&  Kafin takai aya taji saukan tagwayen maruka d aya bin d aya.

Azeema ta malmalo wani ashar tana duban Khulsum dake sakin huci wacce itace tai Marin.

Cikin huci Khulsum taci gaba  Baa haifi wacce zata ci mutuncin mahaifiyata na barta ba bari kiji na fad a Miki..!

 Ni kika Mara Khulsumu.. Toh wllhi yau idan baki kwana cell ba wllhi ba sunana Azeema ba.. Dan uwarki Suwaiba sama sama daga kaina kin gama rashin kunya..! Ta k arashe tana ihu tana k walla kiran Habibi..

Kan kace me mutane sunyi caa a wajen.

Babu shiri Mijin Azeema ya ko k araso yana fad in wllhi baiga ballagazar da zata marar masa mata ya barta ba. Fad i yake wllhi sai ya d aure Khulsum.. Kan kace mai ya d ale mashin d insa ya bar wajen.

Ummul sai kuka take tana rok on Azeema tai hak uri ta bari suji da ciwon mahaifinsu da kuma b acewar mahaifiyarsu.

Azeema kaw sai tsalle take tana jijjiga tana fad in wllhi yau bataga uban da ya isa ya hanata d aure Khulsum ba.

Bakin Khulsum bai Mutu ba fad i take wllhi Azeema ta kuma gigin zagar mata mahaifiya sai ta k ara mata da wasu marukan. Kuma idan ta haifu kar ta fasa rufeta a gidan yari.

Wasu daga cikin  yan gidan masu goyon bayan Azeema sai dad a ingizita suke. Wasu kaw cewa suke Ummulkhairy da  yaruwarta kullum cikin jaza masu fitina suke. Idan kaji ana bala i da rikici a gidan toh ba kowa bane face su biyun.

Allah sarki Ummulkhairy idan ka ganta dole ta baka tausayi. Jim kad an motar police ya k araso tafiya da Khulsum.

Mijin Azeema na gaba yana fad in idan zai kashe k arshen kud insa sai ya k watarwa matarsa hakkinta.

Ummul kaw ganin za a tafi da  yaruwarta da gaske ya sanyata saurin k arasawa tana rok on Habibu mijin Azeema da yai hak uri ya taushi Zuciyar Azeema ko dan halinda mahaifinsu ke ciki a asibiti.

Haka akai ayari anai masu rakiya yayinda wata  yarsanda ta tasa k eyar Khulsum zuwa cikin motar su.

Ummul ta kamo  yaruwarta tana kuka shar shar tana rok onsu dan Allah su k yale mata  yaruwarta.

Sergeant d in ta bige hannun Ummul tana tsawa wa Khulsum ta shige mota.

Azeema da mijinta suka d ale babur suka take masu baya.

Durk usawa Ummul tai a wajen wani irin marayan kuka ma taso mata. Hannayenta biyu ta d aura akai jikinta kaw har wani irin rawa yake. Innalillahi wa inna ilaihi raji un..! Wann wani irin jarabawa ne.. Wani irin iftila in rayuwa suke gani.. Ba a gama da wann ba a fad a wann..! Ta rintse idanunta hawaye na kuma ambaliya a fuskarta. Da wanne zata fara mahaifinta dake kwance asibiti.? Mahaifiyarta da bata san ina ta tafi ba.? ko kuwa  yaruwarta da aka tafi da ita police station.?  Hasbunallah wa ni imal wakil..! Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifli khairan minha..! Ta furta cikin tsananin rawar murya. Ta mik e tamkar zautacciya tana Neman ta hanyar da zata nufa.

Batasan ina take tafiya ba k afafunta kawai take jefawa. Bata tsinci kanta a ko ina ba sai gidan Hajja Fannah.

Da tsananin mamaki Hajja Fannah ke duban Ummulkhairy wacce ko magana bata iya yi.. Hajja Fannah tai saurin kamo hannun Ummulkhairi  Subhannallahi Ummul meke faruwa..?

Ummul bata iya amsata ba saima kifa kanta da tai cikin jikin Hajja Fannah marayan kuka na taso mata.

Hajja Fannah ta rungumeta sosai cikeda tsananin tausayinta. A haka suka nufi cikin gidan.

Ta zaunar da Ummul saman kujera wacce ta koma tamkar mutum mutumi bata um bata um um sai hawaye dake ci gaba da gangarowa saman kumatunta.

Hajja Fannah ta mik e da zummar kawo mata ruwa ganin ta mata tambayar duniya kan ta sanar da ita meke faruwa ta kasa. Idanunta suna kafe waje guda sai zuban ruwa da suke.

Amma koda ta kawo ruwan ma kasa sha tai har lokacin idanunta na duban b angare guda ga hawaye na kwaranyo mata. Hajja Fannah ta kyaleta bata tak urata ba har saida suka d ibi lokaci a haka kafin Ummul ta soma fad in  Komai ya hargitse, sunce ni ce sila.. Sunce bak in k addarata da haukan mahaifiyata shi yai sanadin ciwon mahaifinmu.. Hajja Umma ta tafi bansan ina ta tafi ba.. Abba yana asibiti amma sun hanani ganinshi.. An.. An kama Khulsum& Tana ofishin  Yan sanda..! Sai tai boasting cikin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Hajja Fannah ta

9 / 52