Auren Wata Uku Book Complete By Sameena Aliyu.doc

Author :  Sameena Aliyu Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   23 / 52

66K to 69K   out of 153.1K words

Ke shaida ce mahaifina bai Mutu yana wann mummunan sab o ba. Dije Allah Algafur ne kuma mai rahama.

 Ke yimin shiru! yau ne kika san Allah Suwaiba.? Ashe kinsan da haka kika rufe ido kika doge sai kinga auren Ummul kaman lokacin baya da kika doge wajen ganin kin haifo d a namiji.? Kaman yanda burinki na farko bai ta bata ba Suwaiba haka burinki na biyu ina nufin ganin  yarki Ummul a d akin aure kaman ko wace  ya mace bazai tabbata ba.!

Dije na huci taci gaba  Kusanci da yarda da Tani ta baki da shi kikai amfani kika aure mata Miji. Mahaifiyarmu babu irin soyayyar da bata Miki ba Dik a tinaninta zaki haifo mata jika namiji.. Wanda hakan yasa kukaje kukaita tsibbace tsibbacenku keda mahaifinki dan ki haifo d a namiji..Idan kin mance na sake tuna miki da cikin Ummul mahaifiyarmu ta bar duniya bataga abinda kika haifa ba Wanda ta k wallafa ran D a namiji zaki haifo.. Bayan mutuwar Inna wato mahaifiyarmu mahaifinki ya Mutu shima. Daga nan ne Tani ta fara cuzguna Miki& Kika koma mata tamkar baiwa.. Duk abubuwan da kikai a baya basu isheki ba Suwaiba har saida kika saka mutanen da basuda hakki ciki.. Idan ni na rasa Fa iz Watak ila sabida tsanar da na Miki a baya.. Su wad ann mutanen mai suka Miki kika jangala masu Ummul...? Suwaiba dole ki haukace da son ganin  yarki tayi aure kota halin k ak a tsoron kar tsafin da mahaifinki ya jefi  yarki dashi a lokacin da kike d auke da cikinta ya tabbata.!

Girgiza Kai kurum Umma take tana hawaye ganin Dije ta d aureta ko ta ina.. Babu bayanin da zatai ta wanke kanta. Dije taci gaba  Ke fah akan cikan burinki Suwaiba babu Wanda bazaki ci Amanansa ba. Koda kuwa wann mutumin ya Miki halarci kaman yanda Tani ta Miki..!

Asshe ta shiga jinina Kai bakinta yana furta  Tabbas haka ne..! Sai yanzu nake fahimtar komai.. Tani taso nusar Dani gaskiya na rufe idanuna.. Ashe ita ce mai gaskiya.. Tabbas na Miki rana Suwaiba.. Babu abinda ban Miki amma kika zab i ki b oye mun wann bala i dake k unshe jikin  Yarki.. Da niyyan taimako na nema ma D an  yar uwata auren  yarki.. Ashe ke akwai k ulli cikin zuciyarki.. Kin cika butulu Suwaiba.! Muryar Asshe ya soma rawa hawaye na gangaro mata  Ki sanar Dani mai zan fad a ma  Yaruwata da ta aminta Dani Akan Tilon D anta ta mallaka min wuk a da nama.! Ki sanar Dani Suwaiba..! Ta k arashe kuka na kuma b allo mata.

Umma na girgiza Kai tana hawaye take fad in  Ki yarda dani Hajiya Asshe.. Wllhi cikin maganganun Dije akwai Wanda sam ba gaskiya bane.. D anta had arin mota shine ajalinsa amma ba auren Ummul d ina da Ya tasamma bane.!

 Wani gaskiya kike dashi da har zan yarda dashi..? Asshe ta katseta cikin d aga murya.
Lokaci guda taci gaba  Wann auren babu yanda zaije..! Bazan saka rayuwar D an  Yaruwata Akan layi ba.. Za a Warware wann aure tun kafin  yarki ta bar gidan nan.. Zan kira  Yaruwata na sanar da ita komai.. Ita zatai umarni ma D anta ya datse auren Amaryar da aka aura masa wacce ko saninta bai ba..! Tana ida fad in haka ta mik e zata nufi sama..

Umma ta bita a guje ta duk a gabanta ta kamo k afafunta tana kuka sosai take fad in  Ki rufa mun asiri dan girman Allah Hajja Asshe.. Dan Allah kar ki bari a warware wann aure.. Dan Allah kar ki bari a maida sadaki.. Wllhi Ummul mace ce kaman ko wace  ya mace.

Asshe ta fuzge k afarta  So kike na kashe D ah na Akan cikan makahon burinki Suwaiba..! Aure dole a warware..! Tana ida fad in haka ta kuma fuzge k afar ta ta nufi sama a fujajan kaman zata kifa.

Hannu biyu Umma ta saka aka tana kuka maras sauti tsoron kar Ummul taji muryarta tasan abinda ke wakana. A fili take furta ta shiga uku ta Mutu ta lalace.

Daga yanda Dije ke tsaye tana dubanta murmushi ta saki. Cikin zuciyarta take furta  Da kyau Dije.. Fansan ran Tilon D anki kike d auka.. Aima baki shiga uku ba tukuna Suwaiba.. Dan yanzu ne aka fara buga wasan.. Ba ke kad ai bace kika iya buga wasa.. Saima kin ci karo da duk tanadin da na miki..


Asshe tana haurawa zama tai gijif saman gado tana jin wani irin tashin hankali na ziyartarta. Yanzu ta ina zata fara b ullo ma wann al amari..? Mai zata soma sanar da  yar uwarta bayan d inbin kud ad en da ta asma daga wajenta..? Ta sanar da  yaruwarta d iyan mutane masu mutunci mai irin matsalar da boka yace a aura ma Haidar ta samu dukda kasancewansu talakawa amma sunada dattako. Sabida Hajiya Kwaise bata amince D anta ya kasance da d iyar matsiyata marassa dattako k ark ashin kalmar aure ba koda kuwa na tsawon watanni uku ne kacal. Shin ta yaya zata soma gabatar da wann ahali masu dabaibaye da matsala Wanda tashin hankali yai ma rayuwarsu marfi, dangin tsiya dangin matsafa. Ba a nan ta tsaya ba Ita kanta yarinyar an tsafeta tin a ciki.. Sann ita d in barazana ce ga rayuwar Haidar. Ta rintse idanunta tana jin tashin hankalinta na kuma ninkuwa.. Meyasa Tai komai a gaggauce..? Meyasa bata saurari Tani ba..? Meyasa Tai zaton kishi ne kawai da Hassada yasa Tani gaza zaune wajen ganin auren bai tabbata ba..? Ta Ware idanunta sanda zuciyarta ke ambato mata .  Mutuwar Kwasko kenan Haidar zaiyi da wann yarinyar da kika aura masa. Shin AUREN WATA UKU zaki ambaci auren ko Auren ajali.? Tabd ijam! Wann shi ake kira cuta ta d au cuta.!

Ta kuma mik ewa tsaye zufa na kuma tsartsafo mata. Zuciyarta ta shiga amsa mata d imbin tambayoyin da sukai karan tsaye cimma Zuciyar nata  Me kike tunani a auren da aka faro bisa umarnin boka..? Me kike tunani a auren da ba a nemi zab in Allah cikinsa ba..? Me kike tunani cikin auren da ba a d aukesa umarni daga Allah ba..? Me kike tunani cikin auren da ba a ginasa bisa ginshik in auren ba..? Ma ana ba ayi sa domin cika sunnar ma aiki (SAW) ba. Dole abubuwa su biyo baya.. Dole bazaku ga da kyau ba. Kaman yanda kika rufe ido kikai ma  yar mutane auren Mutuwa da D anku haka nan wann matar da kika d auketa shashasha tai auren mutuwa ma d anku da nata  yar. Tirk ashi. Lallai yau akeyinta.

Asshe taja wani irin gauron numfashi tana mai kuma mik ewa tsaye daga zaune. Lokaci guda take furtawa a fili  Me zan aikata ni Asshe.. Me zan sanar da  Yaruwata..? Zata fahimci k arya naita shera mata kenan ina amsar mak udan kud ad e hannunta..? Shin waye zai fanshe kud ad en da na amsa hannun Kwaise da sunan AUREN WATA UKU ma d anta. Shin ma ta ina zan iya mayar mata da kud ad en da ta bani na yak in nemo ma Haidar matar wata uku..? Dan nayi imani nawa mijin ba biya zaiyi ba dan shi mutum ne da mata bata cin kud insa sai wacce yake yayinta. Nida  Yaruwata kuma k ar tasan k ar ne akan kud i. Zamu iya samun matsala ta tarwatsewar ahali akan kud ad en da ta tafka asara ba tareda ta samu biyan buk ata ba. Uwa uba taji auren mutuwa na shirya ma tilon D anta Wanda ita kanta ta saka nata Auren cikin had ari domin ta ceto sa daga mugun asirin da aka jefesa dashi. Mijina will come to know everything. Duk abubuwan da na aikata harda zuwa wajen boka da AUREN WATA UKU da na k ulla Wanda Ya k unshi kisan kai. Zai rabu dani rabuwa ta har abada. Even my children will leave me. Kowa zai gujeni na zama banida tsuntsu banida tarko. Kishiyoyina su samu abun yawo Dani. Lallai ina tsaka mai wuya ni Asshe. Suwaiba ni ta cuta a duka wann al amari. Gashi garin k ok arin gyara ahalin  Yaruwata ni zan tarwatsa nawa ahalin da farin cikina. Toh amma rayuwar Haidar ake magana a nan. Ta shiga girgiza kai tana mai furtawa a hankali  A a.. A a bazan bari hakan ta kasance ba.. Haidar s life is at stake here.. Bazan bari a kai masa ajalinsa ba.. I need to do something immediately.. I need to come up with something& I just.. Can t sit back and do nothing.. Amma me zanyi..?


Batakai aya ba wayarta ta soma ruri Hajiya Kwaise ke kira.



SameenaAleeyou=???..
*AUREN WATA UKU.!*




*21*






*??Sameena Aleeyou&
'




Jikin Asshe Ya kuma yin lak was dan gani take kaman Kwaise ta riga ta san komai. Cewa Ajalin D anta zata kai mata matsayin makarin asirinsa.. Har wayar ta kusa tsinkewa kafin Asshe ta iya tattara daidai gwargwadon natsuwan da yazo mata a wann lokacin. Murya a raunane ta d aga kiran  Aunty Kwaise..

Daga d aya b angaren Mommy ta kaste ta  Asshe duk yanda za ai Amaryar wata uku ta iso Abuja a gobe.. Asshe a yanda na hango tsananin k iyayya a idon Haidar Ya kuma haifar min da tsoron rasa D ana. I can t afford to lose him Asshe. Haidar shi kad ai ne D ah na zanyi komai zan sadaukar da komai nawa dan na kub utar dashi da ahalina daga sharrin shed aniyar can. Asshe bana so a sami wani mishkila. Ki kula da matar wata uku da kyau tamkar k wai a hannun yaro tinda kinsan amfanin ta wajenmu. Rayuwar d ana tamkar yana had e ne da nata rayuwar. Har sai lokacin da zata karya wann asiri da aka jefesa dashi. We need to make sure ta iso a gobe cikin k udurar Ubangiji.

 Amma.. Amma.. Aunty Kwaise..

 Asshe Babu wani Amma.. I cant afford to lose my son completely& Just do as I say.. The house is set. Everything is ready. Isowarta kawai ake jira na rik e Haidar a gida kaman yanda yake bisa yarjejeniyar mu dashi. Engr ma cikin satin nan zai tafiya, Business trip. Akan Auren Haidar na hana kaina bin mijina tafiyar da zai d aukesa makonni kinga kuwa na shirya ma wann aure. Na shirya karya asirin da akai ma Haidar. Mommy ta k ark are wayar nata tana kuma jaddada ma Asshe lallai lallai kar a samu wani matsala.

Asshe Tai sakare tana duban wayar. Zama Tai gijif cikin gado zuciyarta naci gaba da tsinkewa. Shikenan.. Ta faru ta k are wai anyiwa mai dami d aya sata yanzu mi zatayi..? Ba tada ikon canza komai a halin yanzu. A dole ta nad e Ummulkhairy ta kaita ma Yayarta Kwaise. Yanzu ita meye abinyi. Anisa ce ta fad o zuciyarta. A fili ta furta  Anisa.. Anisa zata taimaka min na aiwatar da komai ba tareda Haidar Ya cutu ba sann ba tareda  Yaruwata ta fahimci komai ba. Lallai zaman Anisa a can shine kawai rufin asirina. Toh amma idan Anisa taje ta tafka wani shashancin fah.? Kuma kenan zaki sanar da Anisa komai.? Ta soma girgiza kai a hankali  A a Anisa doesn t need to know about everything. Kawai umarni zan dinga bata daga nan. A hankali ta shiga jinjina kai kafin ta nufo k asa.

Nan Asshe ta tadda Inna Dije ta titsiye Umma sai ta fito mata da Ummulkhairy ta tafi da ita. Umma sai kuka take tana rok on Mama Dije ta rufa mata asiri kar ta tona mata Auren Ummul ya mutu tun a daren aurenta kafin tafiyarta. Cikin gunjin kuka Umma taci gaba  Dije ki dubi girman Allah ki rufa mun asiri.. Wanda kika tona min ma Ya isheni wllhi.. Yanzu idan auren Ummul Ya Mutu Tun a daren yau da wani idanun zan kalli mutanen unguwarmu da dangi baki d aya& Dije idan kina ma Allah kar ki d auki Ummul.. Kar ki tafi da Ummul..

Kaman daga sama muryar Asshe ya katse su  Babu yanda za a tafi da Ummul domin kuwa a halin yanzu mutum d aya keda iko da Ummul shine mijinta..!

Gaba d aya suka juyo suna dubanta, daga Umman Har Mama Dije.

Asshe taci gaba da sauk owa daga bene cikeda k asaita. Ta k araso gaban Inna Dije dake tsaye gaban Umma wacce ke duk e kaman mabaraciya tana Koke Koke.

Dije ta zuba ma Asshe idanu. Su duka biyun suna duban juna. kowacce tana sak awa cikin zuciyarta.

Murmusawa Dije Tai tana kuma duban Asshe da kyau  Da gaske..? Bayan duk abubuwan da kika ji& Kin amince a kaima D anki ajalinsa..? Oh! D an  yaruwarki..? Haka ne..?!

Asshe ta murmusa tana ma Dije irin duban da biri yake ma Ayaba  Ko mai zai faru a halin yanzu.. Ummul tana k ark ashin ikon mu ne.. Sadaki D anmu Ya biya Wanda Ya tabbatar da wanzuwan igiyoyi Har guda uku da suka mallaka masa cikakken dama da iko akan Ummul. Duk wani abinda zai biyo baya, hukunci zai zamana yana wajenmu.!

Sosai Mama Dije ta tsareta da idanu tana ji akwai wata a k asa. Dan ta tabbata wann aure ba auren Allah da Annabi bane.. Duk yanda akai akwai wata shiryayya. Idan auren tsakani da Allah ne bayan duk abinda ta sanar ma Asshe a gaban Suwaiba wacce take mahaifiya ga Ummul ba yanda za ai Asshe ta amince akaima D ansu mace irin Ummul.

Umma harda sujudusshukur tayi dan farin ciki. Ta shiga d aga hannaye sama tana mik a ma Allah godiya  Alhamdulillah..! Alhamdulillah Allah abin godiya.. Allah gatan bawansa.. Kai amma dai annamimi baiji dadi ba.. Zakaran da Allah ya nufa da cara ko fah ana Muzuru ko ana shaho sai yayi.. Kuma wllhi idan rana ta fito tafin hannunki bata isa ta rufesa ba Dije..! Tani ma ta buga Dani ta barni balle ke..! Ta k arashe tana mik ewa tsaye harda rangad a gud a.

 Bada garaje ba Suwaiba..! Muryar Asshe ya dakatar da ita.

Umma ta waro idanu waje dafe da k irji tana duban Asshe. Sai kuma ta soma girgiza Kai  A a dan Allah.. Ki rufa mun asiri Hajja Asshe.. Ki dubi girman Allah kar ki bari mak iya suyi dariya.. Wllhi duk abinda kikaji daga bakin Dije ba komai bane face sharrin mak iya..

Asshe ta dafa Umma tana murmushi  Kin yarda cewa aure rai ne dashi..?!

Umma ta jinjina kai tana duban Asshe.

Asshe taci gaba  Bazai Mutu ba sai kwanakin Sa ya k are.. Haka ne..?

Nan ma a sanyaye Umma ta jinina Kai.

Asshe ta juya ta basu baya daga Umma har mama Dije lokaci guda tana taka parlorn nata a hankali take ci gaba da fad in  Bari muce auren Ummul zai rayu ne na wani d an lokaci..!

Dummm! Haka k irjin Umma ya buga. Jiri ne taji na neman aikata k asa. Ta dafe garu tana furta  Ban ban.. Ban fahimceki ba Hajja Asshe.. Mai Kike nufi da cewa auren Ummul zai rayu ne na wani d an lokaci..?

Assshe ta juyo tana dubansu  Ina nufin zai rayu ne na tsawon watanni uku kacal.!

Dije ta gyara tsayuwarta sosai tana duban Asshe makirin murmushi kwance saman fuskarta. Cikin zuciyarta take furtawa  Eh Lallai.. Da alama yanzu ne wasan zai d au zafi.. Bari dai mu gani..!

Muryar Umma ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi.

 Ban.. Ban gane tsawon watanni uku kacal ba.. Me kike nufi Hajiya Asshe..? Me kike nufi da auren Ummul zai rayu ne na tsawon watanni uku kacal..? Ki min magana dan Allah.. Ki sanar Dani mai kike nufi..?!

 AUREN WATA UKU..! Ina nufin AUREN WATA UKU kawai mukayi ma D anmu da  yarki.. Bayan wata uku..  Yarki zata dawo gareki.. Sai ki shirya mata wajen zama bayan wata uku..!

Duniyar Umma ya shiga juyawa sama na koma mata k asa& Ta girgiza kai tana jin hankalinta na neman gushewa da gaske. Cikin rawar murya Umma ke furta  Amma.. Amma meyasa haka Hajiya Asshe.. Shin wani irin aure kukai ma D anku da  Yata& Meyasa na wata uku kawai..?

 D an  Yar uwata yana aiki ne k ark ashin Kampanin Mahaifinsa. Mahaifinsa zai basa wani k wangila ne na tsawon watanni uku kawai idan yayi aure.. Bayan wata uku zai gama wann kwangilar.. Daga nan kuma bamuda buk atar  yarki dan kwangilar ta k are.. Kin fahimta..? Ta k arashe tana duban Umma sosai.

Umma na girgiza kai cikeda rashin yarda take duban Asshe  Amm.. Amma.. Amma.. Bamu yi haka dake ba.. Wann zalunci ne..  Yata ta jima, ta d auki lokaci batayi aure ba.. meyasa kuka zab i cutar mun da  ya.. Ummul.. Ta wahala a rayuwa, ta fuskanci k alubale na gujewan manema.. Ta fuskanci k alubale da dama.. Bata cancanci irin wann auren ba..  Yata ta cancanci aure na gaske.. Aure mai d orewa ba mai rabewa ba.. Shin Auren Kwangila kukaima D anku da  yata..? Hajiya Asshe kin cuceni.!

 Ban cuceki ba hasalima taimakon ki nayi.. Idan baki mance ba sadakin  yarki shine kud in jinyar mijinki.!

 Wani irin taimako ne wann..? Wane irin taimako ne haka.. Wann zalunci ne ba taimako ba..

A zuciye Asshe ta katseta  Kar ki sake cewa na cuceki.. Ke kika cuci kanki.. Magana akan cuta.. Shin tsakanin ni da Ke waye ya cuci wani..? Ni da naima D ana auren cikan

23 / 52