Auren Wata Uku Book Complete By Sameena Aliyu.doc

Author :  Sameena Aliyu Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   18 / 52

51K to 54K   out of 153.1K words

waye zasu fidda.

Take Mama ta shiga masu nuni da Umma tana fad in  Ga Suwaiba ita zaku kama ita zaku fidda.. Yar shan jini ce..

Ai sai Mama taga securities sun isa gaban Umma suna duk awa suna kwasan gaisuwa lokaci guda suna tambayar ko da abinda kike so a miki Hajiya.

Mama sai ta saki baki tana duban ikon Allah. Suwaiba.? Suwaibar ne Hajiya..?

Umma ta murmusa tana gyara zaman mayafinta  A a babu komai Kar ku damu. Haukar wancan Matar ne Ya motsa inaga b allewa tayi daga b angaren masu jinyar hauka.

Mama jin an ambaceta da Mahaukaciya ya sanyata kuma hayyak owa. Jikinta Har rawa yake.

Sauran mutanen dake wajen Wanda dama fitinan Maman a ishesu sukace da gaske ne batada saiti kullum fama ake da ita.

Aiko nan take securities suka fidda Mama da k arfin gaske sai ihu take tana tsine ma Umma. Yaranta suka bi bayanta a guje suna ambato sunanta.

Umma ta zuba masu idanu har aka fice dasu kafin ta sauk e ajiyan zuciya ta juyo tana duban yaranta Khulsum da Ummul Wanda Har lokacin kallon mamaki ko muce kallon tsoro suke binta dashi musamman bayan da Mama ta gama fad e fad enta.

Umma ta kuma dubansu sai ta k arasa ta rungumesu. Basu iya maida mata martanin rungumar ba.

 Ummul, Khulsum.. Ni ce fah mahaifiyarku Ummanku.. Meyasa kuke dubana kaman bak uwar fuska. Shin ko baku shaida mahaifiyarku bace.?

Girgiza mata kai Ummul tai  Mun shaida kamanninki Umma amma yanayi ki yafi kama da bak uwar Fuska.. Umma mai ya canza ki cikin kwanaki k alilan..?

Murmushi Umma ta saki kafin ta dafa Ummul  K addararki itace ta canza ni cikin kwanaki k alilan Ummul.. K addaranki Wanda a baya naita Allah wadai dashi shine ya zamto mabud in Alherinmu..

Girgiza kai Ummul tai cikin tsananin sanyin jiki  Umma ban fahimceki ba..

Umma ta kuma murmusawa  Kar ki damu  Yata da sannu zaki fahimci komai.. Kuzo muje.. Ta shiga janyo hannuwansu suka nufo waje yanda suka hangi Mama har lokacin huci take bayan an tilasta mata yin shiru.

Mama ta zabura zata nufo Umma amma sai taga wata jibgegiyar jeep taja tayi parking gaban Umma. Mama taja wani wawan birki tana dafe k irji.

Mamaki da sanyin jiki Ya kuma sauk ar masu Ummul.

Umma ta dubesu  Toh yarana ni zan tafi, in sha Allah zan kuma dawowa nan bada jimawa ba.

Da tsananin mamaki suke duban mahaifiyarsu. Tasa kai kenan zata shige mota Ummul tai saurin kamo hannunta. Hawaye na gangaro mata take girgiza kai  Umma.. Ina zakije ki bar Abba cikin halinda yake ciki..? Umma ina kikaje kika barmu mu nata nemanki.. Shin Kinsan abubuwan dake faruwa a nan.. Umma wai meke faruwa.. Umma meke faruwa ne..?

Dafata Umma tai  Da sannu zaki fahimci abinda ke faruwa Ummul.. Zan rok i alfarmarku. Kar ku bar kusan mahaifinku.. Ku zauna ku kula dashi.. In sha Allah daga yanzu duk wani abinda za a kashe sabida jinyar mahaifinku bazai zama matsala ba. Na barku lafiya yarana..

Ummul na kuka ta kuma kamo hannunta  Umma shin kinsan kalan tashin hankalin da muka shiga na rashin ganinki.. dan Allah kar ki tafi ki barmu.. Umma.. saidai tuni Umma ta cire hannunta daga rik on da Khulsum tai mata ta shige mota. Ummul ta kuma yunk ura tana ambato Umma amma saiji tai Khulsum ta rik on hannunta had ida dakatar da ita  K yaleta Adda.. Wann ba Umman mu bace.. Idan ma itace banida haufi an canzata dare d aya.

Fad awa jikin Khulsum Ummul tai wani irin kuka na kufce mata.

Mama kaw zuba masu idanu tai tana mai kuma tabbatar da zarginta cewa Suwaiba dai K ungiyar asiri ta fad a.


Umma tana shigewa cikin motan ta dubi Asshe dake zaune gefe. Ta d an yi adjusting mayafin  Hajja Asshe Ya kikaga k warewata..? Kinga kaw yanda na razana Tani na haukata ta na gigitata.? Gaba d aya fah ta birkice..

Asshe ta murmusa tace  Ai ma fah bama ayi komai ba, wann ai sharan fage ne. Sai randa aka kai lefen Ummulkhairi, ranan ne zaki kashe kishiyar ki da k unci. Dan ina mai tabbatar miki sai ta had iyi ranta. Kaf abinda ta miki kan Ummulkhairi sai kin rama. Ranan biki kuma a fice da gawarta.

Umma ta zaro idanu  Na shiga uku, bazan so Yaya ta Mutu ba ai& 

Asshe ta d an murmusa kad an had ida dafe kafad ar Umma guda  Bazata Mutu ba ma sai taga Nasaranki da na Ummul. Kuma ko yanzu kin tauna tsakuwa aya kuma taji tsoro.. Ni so nake ki kece raini a kamfatanin layinku.. Duk masu aibata Ummul d inki sai Sun shaida auren gata da za a mata..

Nan fah Umma ta shiga wage baki zuciyarta na mata dad i. Karfa ku mance mijin Umma na kwance gadon asibiti tsakanin rayuwa da mutuwa. Amma Har yanzu burin Umma shine Ummul d inta tayi aure kota halin k ak a ko ba dan komai ba sai dan ta birge Mama da sauran jama an unga sabida abinda suka jima suna mata kan Ummul.

**

A b angaren su Ummul kuwa tinda Umma ta shige bak ar Jeep d in nan mai lullub e da tint suka kasa komawa cikin asibiti wajen Abbansu dan haka su Mama da Azeema sukai caa a haraban asibiti suna nunasu suna cewa ga  ya yan mayya. A dole suka fice daga asibitin suka dawo gida.

Ummul ta zuba tagumi Khulsum ma da kalan nata tagumin.

 Adda anya ba gaskiya Mama take fad i kan Umma ba.. Anya Umma ba wani k ungiyar asirin ta shiga ba..! Tai maganar kaman mai tsoron furtawa.

Ummul tai saurin d agowa tana dubanta  Haba Khulsum ta ya zakiyi irin wann tunanin..?

 Adda abinda idanun mu suka gane mana fah kenan& Ina Umma ta samo dukiya irin wann tsakanin kwanakin nan..? Sann meyasa ta tafi ta k yalemu..? Meyasa bata damu ta bar Abba cikin halinda yake ba.. Adda kifa duba kiga yanayin da Abba yake ciki amma Umma tana a matsayin matarsa ta saka k afa ta tsallake shi har da shigewa shirgegiyar Jeep d in nan. Ga ado da tayi irin wanda bata tab a yi ba. Wata matace zatayi wad ann abubuwan alhalin mijinta na kwance cikin tsananin jinya. Wllhi ko baki fad i ba Kema kanki nasan zuciyarki bai kwanta ba Adda kuma akwai irin tambayoyin da nakeyi kwance cikin zuciyarki.

Sauk e wani irin ajiyan zuciya Ummul tai sai kuma ta jinjina kai tace  Kinyi gaskiya& Akwai tarin tambayoyi k unshe cikin zuciyata Wanda zanso Umma ta amsa min su.. Amma ko ma menene kar muyi gaggawan yanke hukunci da abinda idanu mu ka iya gani.. So tari abubuwan da idanun mu ke iya gani a zahiri ba haka suke a bad ini ba.. Mu tsaya Har muga gudun ruwan Umma mu kuma ji abinda ke faruwa.

Khulsum taja wani irin gauron numfashi ba tareda ta kuma furta komai ba.

**

Abuja.

Laptop ne gabansa waya manne kunnensa yana duban wasu sketches na manyan bridges iri daban daban. Ko ba ace ba da Hisham yake wayan. Da alama shi ya turo masa sketches d in da suke tattanawa akai. Bayan Sun gama magana shiru yai yana nazarin abinda ke gabansa. Sai kuma ya rufe laptop d in ya k ura ma waje guda idanu.

Dareen da waya ke mak ale kunnenta ta kuma lek ensa kafin ta koma da baya tana rage murya had ida matse wayar jikin kunnenta sosai  How would I know.. He s been acting strange lately..

Daga d aya b angaren muryar mutumin ya katseta  What are you there for idan har bazaki iya karantar yanayin da yake ciki ba..?!

Ta d an rausayar da idanu had ida furzar da huci  Look, I see him everyday but I can t grasp his mood. Ba ko yaushe asiri yake tasiri ba. Kar ka mance Shi mutum ne Wanda tun kafin sihiri ya jefesa yakeda wahalan sha ani.

Mutumin yace cikin tsawatarwa  Kalla Dareen. Ban kawo ki cikin rayuwar Haidar dan kiyi holewarki dashi ba. Kinfi kowa sanin dalilin da yasa kike tare dashi. Idan Har bazaki min amfani ba. Zan tarwatsaki da kaina.. Kinsan inada makamin da zan tarwatsaki a hannuna tinda har yau baki san yanda na bisne sirrin da Ya rufe Aurenki da Haidar ba.

Lumshe idanunta tai had ida bud esu  Fine, zanyi iya k ok arina na fahimci mai yake shiryawa. Amma karkayi gangancin rabani da Haidar domin zan tashi wutan da kaima baka isa kashewa ba.!

Ya murmusa  Kar ki mance I m the one calling the shots here. Kibi umarnina ki zauna lafiya.! Yana ida fad in haka ya katse kiran.


Furzar da huci ta kumayi kafin tai k ok arin kintsa kanta ta fito parlor yanda Haidar ke zaune.

Murmushi saman fuskarta ta zauna gefensa  Love.. Ta fad i tana shigewa jikinsa. Sai kuma ta d ago fuskarta tana dubansa  Is something bothering you..? You seem preoccupied& Is it about work..? Ko kaje duba Mommy ne..?

Tambayan da ta masa na k arshe yasa ya dubeta sai kuma ya maida dubansa wani b angaren  I m fine.. Ya fad i a tak aice ba tareda ya kuma cewa komai ba. A  yan kwanakin ta kula magana ma sai ya zama dole yakeyi. Ya koma mata tamkar bak o cikin gidan dukda dama a iya zamansu bata isa tace ta sansa kaman yanda tasan tafin hannunta ba dukda kuwa Auren sihiri da tayi dashi. Mik ewa yai ya nufi sama ba tareda ya kuma ce mata komai ba. Hannayensa sakale cikin aljihun sweatpants d in dake jikinsa.

Tabi bayansa da kallo har ya haye sama kafin tai saurin janyo laptop d in ta bud e. Sannu a hankali take bin duk wasu abubuwan dake fuskan computer d in tana karantawa.
Aiki yake sosai kan project d in da takeda masaniya yanata fad i tashi akai. Toh kodai mahaifinsa ya basa go ahead ne.? Idan har mahaifinsa ya amince ya jagoranci aikin dole akwai wani abu a k asa. Ba yanda za ayi mahaifinsa ya amince masa cikin sauk i.. She needs to find out meke faruwa.

**
Yau kwanaki biyu kenan Umma bata kuma waiwayowa ba. Hankalin Mama kaw gaba d aya ya gaza kwanciya. Damuwarta kawai shine tasan yanda Suwaiba ta samo irin wann arziki da ta gani tareda ita. Gaba d aya ta ma mance da batun Tasi u da halinda kud ad en shagon Abba ke ciki.

Yau d in ko asibiti wajen Abba ta gaza komawa. Tare take da yaranta Badi a da Azeema yayinda suka baro Salima can wajen Abba. Tunanin Mama d aya idan ta fice Suwaiba na iya zuwa gidan wajen  ya yanta Shiyasa ko k ofa ta gaza fita.

Mama da yaranta Azeema da Badia Suna tsaka da aibata Suwaiba  yar k ungiyar asiri gaban su Ummul suka soma jiwo hayaniya daga waje. Wann Ya dubi wancan wancan ya dubi wann.

Azeema tai saurin tare wani yaron cikin gidan da ya shigo a guje rik eda gudan dubu a hannunsa yana ihun murna. Azeema ta rik esa tana tambayarsa meke faruwa waje.

Yaron yace  Umma ce.. Umman su Khulsum itace tazo da k atotuwar mota tanata rabon kud i a waje..

Mama dasu Azeema suka dubi juna. Babu shiri suka nufi waje a fujajan yayinda su Ummul ma duban junan sukai itada Khulsum. Take suma suka take ma su Mama baya.


Mama da yaranta suka wani irin birki Har saida ya rage saura k iris Mama bataci tuntub e da wani yaro da ya nufo gida a guje yana ihu yana d aga kud insa sama.

Daskarewa Ummul da Khulsum ma sukai suna duban kayan al ajabi. Ikon Allah. Da gaske Umma ce ta fito cikin wann bak ar shirgegiyar mota tana rabon kud i ma Al umman unguwar. Mutane kaw sai fitowa suke kusufa kusufa daga lungu da sak o suna amsan kud ad en da Umma ke rabawa.

A haka Umma ta k araso gaban Mama. Ta murmusa tana dubanta  Tani ya muka sameku..

Mama ta kuma bud e baki tana duban Umma jin irin gaisuwan rainin da tai mata. Wai Tani ya muka sameku.. Tani fah.. yau Suwaiba bata kirata da Yaya kaman yanda ta saba ba. Tani fah ta kirata dashi gatsau. Waima Yaushe Suwaiba ta sami  yanci cikin gidan. Dan lokacin da aka aurota daga rugarsu babu kalan uk uban da bata gallaza mata ba ga wauwauta ga shashashanci had ida mugun k auyanci da sukai mata dabaibayi.. Wai har Suwaiba ne ta waye yanzu.. Lallai ta yarda da hausar nan da ake cewa Shege na k auye.. Idan bak auye ya samu faraga yafi d an birni iya shege.. Eh Tabbas yanzu ta shaida wann da idanunta.. Dan barikin da Suwaiba take a yanzu ko goggan d an birni Wanda aka haifesa tsakiyar wayayyu bazai ba. Ko ita kanta bata tasa k afa ta tsallake mijinsu dake kwance yana jinya ta tafi ta barsa ba. Sai yanzu take ganin ashe ita jaririya ce a bariki tinda ita saida shagon Isubu kawai tayi, tanata kumfan baki tana fad i tashi ta raba gadon Isubu tun yana raye dan kar Suwaiba da yaranta su samu. Ashe Suwaiba kallon k aramar  yar iska take mata. Ita a daidai wann gab ar ma ta baje Rumfar barikinta.

Muryar Umma ne Ya kuma dawo da ita daga duniyar tunanin da yai nisa ciki  Yauwa Tani nace ba ga wann ki kula da Abban Ummul sosai.. Naga Salima wajensa. Bansan mai kike a nan ba da har yanzu baki tafi wajensa ba. Idan akwai abinda ake buk ata kina iya sanar Dani dukda dai duk wani abinda ya kamata a bayar an bayar. An canza masa d aki ma ya koma b angaren kud i. Kira Salima zata sanar dake komai tinda tareda ita akayi duk wasu sauye sauyen. Tai maganar tana mai Ciro kud ad en cikin hamshak in jakanta. Yacce kasan matar gida na bawa  yar aikinta sak o.

Mama tai sakare tana duban Suwaiba.

 Ungo amshi mana..! Umma tace tana mai kamo hannun Mama had ida damk a mata kud ad en ciki.

Lokaci guda Umma tasa kai tana taku d add aya sai juya ma Tani mazaunai take.

Kusan silalewa wajen Mama tai har saida Azeema ta tallafeta.

Kasa motsawa Khulsum tai har Umma ta shige ta nan gabanta rik eda hannun Ummulkhairi wacce ke biye da ita tamkar rak umi da akala. Bata iya dawowa hayyacinta ba saida ta sinkayo muryar Mama na fad ida Azeema ta rik eta sosai bata iya tsayuwa kan k afafunta.

Cikin sauri Khulsum ta nufi bayansu Umma k afafunta Har hard ewa suke.

Tana shigowa ta sinkayo muryar Umma dake rik eda hannun Ummulkhairi tana fad in  Ba sai Kin d auki komai ba.... Maza tashi muje direba yana jiranmu..

Katseta Khulsum tai da fad in  Ina zaki Kai  Yaruwata Umma..?



SameenaAleeyou=???

*AUREN WATA UKU..!*



*17*



*??Sameena Aleeyou&
'




Katseta Khulsum tai da fad in  Ina zaki kaita Umma..? Muryarta Ya soma rawa sosai sanda take ci gaba da furta  Umma shin abinda mutane ke fad i gaskiya ne..? Umma dan Allah wacece ke..? Ina asalin Ummanmu da muka sani..?

 Banida lokacin Miki bayanin komai a yanzu Khulsum.. A halin da ake ciki  yaruwarki nazo d auka.. Ta k arashe tana mai janyo hannun Ummulkhairi.

Cikin azama Khulsum ta rik e Ummulkhairi tana girgiza mata kai tana hawaye  A a Adda kar ki bi Umma.. Adda dan Allah kar kije..

Dubanta Umma tai a yatsine kafin direba ya bud e mata owners corner saida ta dubi yaranta na d an lokaci kafin taceda Ummul idan kin gama kya shigo muje. Daga haka ta fad a mota kayanta.

Khulsum ta kuma share hawayen da suka gangaro mata. Hannayenta cikin na Ummul take fad in  Adda dan Allah kar ki bi matar nan.. Bamu san Ina zata kaiki ba.. Watak ila rad erad in da mutane suke da gaske ne Adda.. Kinga Umma dai an canzata gaba d aya bamu San Wacece ita ba a halin yanzu.

Khulsum na hawaye take girgiza kai lokaci guda taci gaba  Adda Ummul, Mai zai faru idan da gaske wajen matsafa zata kaiki.. Mai zai faru idan wani abun ya sameki.?

Ummul ta zame hannunta daga cikin na Khulsum tabi bayan Umma aka bud e mata mota ta shige. Tana kallon Khulsum dake tsaye wajen hawaye na gangaro mata yayinda itama Ummul d in hawaye ne ke gangaro mata. Ta rintse idanunta cikin zuciyarta take furta  Kiyi hak uri  Yaruwata. Ya zama dole nayi wann. Babu abinda zai sameni face Allah ya k addari faruwan hakan.. Dani dake mun San yanayin Umma a d abi a da halayya. Munsan matsalan mahaifiyarmu, Abu ne mai sauk i a rud eta.. mahaifiyarmu ce, ya zama dole na bita na gano hak ik anin abinda ke faruwa da ita. Domin kaw bazamu bari ta auka ma halaka ba munaji muna gani. In sha Allah komai zai daidaita K anwata.. Ta k arashe tuanin nata wasu hawayen na kuma gangaro mata.

A daidai gate d in wani gida mai matuk ar kyau da tsari motar tai horn.

Khulsum da tuni ta d ale acab a tabisu a baya ba tareda saninsu ba. Tana ganin gidan da akai parking tace ma me mashin ya ajeta daga can nesa dan sai ta karanci gidan kafin ta danna kai ciki. Allah ya gani bazata bari mahaifiyarsu ta bada  yaruwarta ayi tsafi da ita ba.

Driver na Ida parking Ya fito ya bud e masu k ofofin. Zuciyar Ummul sai tsinkewa yake tana duban

18 / 52