Auren Wata Uku Book Complete By Sameena Aliyu.doc

Author :  Sameena Aliyu Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   44 / 52

129K to 132K   out of 153.1K words

you& This is your fault you know. Da ace kinyi abinda nace it wouldn t have to be this way. Wait let me see.. Ya soma k ok arin janye rigarta ai sai ta zaro ido da gaske ganin zai dage mata riga. Ta soma turasa cikin tsananin k idimewa tana fad in  Ai Ya.. Ya ya daina.. k alau nake yanzu ka gani..! Ta mik e tsaye kan k afafunta kaman wacce aka razaneta cikin k ok arin nuna masa lafiya take ba ciwon dake damunta.

Ya tsareta sosai da ido. Wato kukan da take acting ne kawai ba ciwon da take ji. Da taga da gaske zai d age rigarta ta daina acting d in. Women are so good in acting kaman dai mahaifiyarsa.

Sai shima ya mik e tsaye yana binta da kallo daga sama Har k asa. Ya kula har lokacin kaman rawa jikinta yake. Ai kuwa idan Har haka ne Ya gano lagonta. Zaisa tai signing papers din cikin sauk i. Ya soma takowa gareta tana k ok arin jada baya.

 Kodai ki saka hannu a takardun nan a dad in rai& Ko kuma&  Yana maganar yana k ok arin balle botiran rigarsa. Bai kuma fasa nufota ba.

Ta soma girgiza kai hawayen gaske na zubo mata  A a dan Allah..! Cikin rawar murya take maganar har saida Haidar Ya cimmata.

Zuciyarta bai daina tsinkewa ba ganin ya mata rumfa  Zaki saka ne ko na sakaki kisa da k arfi..! Ya fad i fuskarsa dab nata.

Dukda zuciyarta dake tsananin bugu bata fasa girgiza masa kai tana fad in  K ima da darajan mahaifiya Ya wuce ai fad a da ita balle a kaita kurkuku duk girman laifinta.!

Bakinta dake fitar da kalaman yaketa kalla zuciyarsa na kuma masa zafi da kiran Mommy mahaifiya da take dan shi a idonsa Mommy bata canci a kirata mahaifiya ba.

Jinjina kai yake yana huci  You think I m playing here right.?! Batai aune ba taji ya rufe bakinsa da nata.

Hankalin Ummul yakai k ololuwa wajen tashi. Al amarin da ko a mafarki bata tab a hasasho kanta ciki ba sai gashi na k ok arin faruwa da ita.

Numfashinta ne Ya soma fita sama sama& Take taja wani irin numfashi ta zube masa a wajen.

Ya duk a yana jijjigata yana fad in ta tashi ta daina wann wasan kwaikwayon.

Shiru bata tashi ba har dai Haidar Ya soma tunanin ko sumar gaske ne tai.

Ya tashi ya fice cikin k ok arin kawo ruwa ya yayyafa mata aiko yana ficewa Ummul ta mik e a guje dikda rawa da jikinta keyi ta isa ta rufe k ofan dan dama ya bar key d in jiki.

Da mamaki ya juyo yana duban k ofan. Ta dai k ara shashantar dashi a karo na biyu. Ya girgiza Kansa k adan yana mamakin yanda Ya fad a tarkon yarinyar Har sau biyu dikda matsalan saurin yarda da yake dashi gashi har sau biyu ya yarda da acting da Ummul tayi. Lallai da alama wann yarinyar zata basa matuk ar wahala kafin ya samu ya cimma burinsa na tura Mommy prison. Sai kuma yaji gaba d aya jikinsa ya sake kaman baida sauran kuazari. Ya isa saman kujera ya zauna gijif had ida kishingid a. Ya lumshe idanunsa bugun zuciyarsa na k ok arin daidaita.

**
Police headquarters.


Barr ya dubi Daddy da Mommy ya dan girgiza Kai  Zamu iya making abun Ya zama kaman illegal detention tinda Haidar ya b oye matarsa babu Wanda yasan yanda take.

Daddy yace  So does that mean they would let her off the hook.?

Kafin Barr yakai ga bada amsa Mommy ta katsesu  No.. I don t want money or power to speak for me.. Iyakacin abinda nake so shine D a na ya dawo gareni.. I ll plead guilty, if that s what it takes& Zan amsa laifin gaban Alk alai zan tafi prison for Haidar to forgive me.

Daddy ya dubi Barr yace ya dan basu waje.

Bayan Barr ya fice ya tsare Mommy sosai da ido kafin ya soma girgiza kai cikin rashin yarda  You don t know what you are talking about Kwaise. Do you really want to get convicted.? That ungrateful Son of yours doesn t even care about you..!


Mommy na hawaye take jinjina kai  Yes.. Zanyi idan hakan zai kawo maslaha cikin rayuwar Haidar. Na rasa shi a farko.. I can t lose him again.

Daddy yaci gaba da girgiza kai  You know you can t appear in court da aurena akanki, bearing my name& Mai kike tunanin sunana zai zama a duniyar Kasuwanci.?!

Mommy na kallon Daddy take girgiza kai  Then end it Engr.!

Da tsananin mamaki Daddy ke kallonta. Duk juran zaman da tai a gidansa dukda rikon ko inkula da yake masu daga ita Har Dan nata bata tab a zab an rabuwa dashi ba daidai da rana guda sai gashi yau tana fad in haka kai tsaye.

 It has always been& an empty marriage that s hanging by threads& Watak ila sabida Haidar ka barni na zauna. Saidai a bangarena na zama lost between zama Mata ko Uwa.. Watak ila na zab i na zauna ne Thinking one day komai zai wuce ahalin Ya daidaita& Na Had iye komai sabida D ah na da mijina. I even named him after you& I turned myself into a monster a k wayar idonsa ba tareda nayi la akari ba. Na tilasta masa ya zamo abinda nake so thinking watarana zaka k aunacesa zakai alfahari dashi kaman yanda ko wani uba yake& Ya kai matsayin da Har na mance cewa ni Uwa ce dik cikin k ok arin ganin burina na had e kan ahalin Ya cika. But then I realise wann burin nawa bazai tab a cika ba& Dik abinda naso ma nawa D an na hana ma D an wata ya samu.. Na rabaka da D anka da matarka& Ta Ya zanyi zaton zan samu wann farin cikin da nake fad i tashi akai tsawon rayuwata..? I am so selfish. Kuka ya hanata ci gaba da magana yayinda jikin Daddy yai matuk ar yin sanyi.

Mommy ta share hawayen da suka zubo mata kafin taci gaba  Na gode da hakurin da kai Dani tsawon shekarun nan. For letting me stay koda sabida D anmu. Na gode da ahalin da ka bamu koda bai zamto kaman ko wani ahali ba. Koda cike yake da tarin k alubali. Taci gaba da jinjina Kai  I give up Engr.. I m tired.. Na gaji.. Iyakacin abinda nake so a yanzu shine D ana Ya dawo gareni. The wealth, the name.. Duka na hakura dasu. Na zab i D ah na.. Na rasashi daga farko bazan kuma sake rasashi a karo na biyu ba.! Ta k arashe cikin tsananin rawar murya hawaye na gangaro mata.

Daddy ya kauda fuskarsa gefe yana k ok arin maida hawayen dake yunk urin ciko idonsa. Bai kuma cewa komai ba sai mik ewa da yai ta fice cikin sauri.

Mommy ta kuma rintse idonta wasu hawayen na gangaro mata. A halin yanzu ta gama aminta bokan da suka je wajensa itada Asshe mashahurin makaryaci ne. Tinda gashi turaren da Ya bata ta bama Ummul yasa ta fad a uku. Dama ita bata tab a yarda da aikin boka ba ko can baya Asshe ce ta ingizata sukaje. Sann she was desperate ta dawo da D anta gareta. Bazata gushe ba zataci gaba da rok on Allah Ya yafe mata kaucewa da tayi dan Tabbas taga aya. Zuciyarta na cikin natsuwa da aminci matuk a Haidar d inta na tareda Ummul. Ta aminta da hankali da natsuwar Ummul. Tanada yak inin D anta bazai tab e ba cikin ikon Allah matuk a na tareda Ummul. Da wann tunani Zuciyar Mommy ya dan samu natsuwa.



SameenaAleeyou=???
*AUREN WATA UKU..!*



*37*





*??Sameena Aleeyou&
'



Bayan shud ewan awanni ta mik e da kyar dan a tunaninta ya tafi musamman da taji sam babu d uriyarsa. Window ta lek a a hankali kaman mai tsoron kar a ganta. Ga mamakinta shi ta hango zaune k asar wata bishiya Ya bada baya ma yanda take tsaye daga cikin d akin. Tsuntsayi ta gani kaman dangin tattabarai Sun taru gabansa sai watsa masu abinci yake suna ci. Wasu Har kaman zasu d ale saman hannunsa. Kai da gani zaka fahimci yana cikin annashuwa da jin dad in abinda yake. Juyowa yai yana watsa ma sauran abincin nan ta hango kyakkyawan murmushi saman fuskarsa. Abinda bata tab a gani ba. Zuciyarta yai wani irin yankewa tai sauri ta koma da baya had ida jingina jikin gini.

Ta d auki lokaci a haka. Kafin ta kuma rintse idonta sakamakon tunowa da tai da yanayin da suka kasance ciki bada jimawa ba. Bata San dalili ba amma sai taji hawaye Sun ziraro mata. Ta jima nan a haka kafin ta bud e lumsassun idonta da suka jike da hawaye. Ta kuma leka window amma sai taga bata gansa ba wann karon. Babu tsintsayen shima baya nan. Babu ko alamunsa. Ta sauk e ajiyan zuciya a hankali kafin tai k ok arin saita kanta. Bata San ya za ai tai escaping kurkukun da Haidar ya boyeta ciki ba. Bata san hanya ba bata kuma san idan zata iya isaga Mommy ba. Saidai abinda take da tabbaci akai shine zata fice tinda tai saa makulin na tareda ita. Zata fice kodan taje ta ceci Mommy. Har abada bazata bari Mommy ta tafi prison saboda ita ba.

Sauri sauri ta isa k ofa ta murda makullin ta soma k ok arin fitowa a hankali cikin sand a. Tana tafe tana waige waige ga tsoro da Ya cikata. Saidai tana zuwa k ofan da zai fitar da ita waje taji gam an rik e hannunta. K iris Ya rage bata saki k ara ba amma sai taji an toshe bakinta. Ta d ago idonta masu cikeda tsoro tana duban Haidar dake huci yana dubanta.

A matuk ar tsare yace  Are you trying to escape.? Where do you think you are going.? Answer me.! Guduwa kike so kiyi..?

Girgiza kai take hawaye naci gaba da gangaro mata. Haidar yaci gaba da janyota yana fad in bazata bar wann gidan ba Har sai tayi abinda ya umarceta. Da k arfin gaske Ya tura k ofan d akin Ya jefata ciki.

Cikin rawar jiki Ummul ra soma k ok arin rarrafowa tana fad in  Dan Allah kar ka sake rufeni.. Dan Allah Kaji tausayi na ka kyaleni na tafi.. Na maka alk awari bazan zauna cikin rayuwarka ba.. Dan..!


 Shiiii..! Ya mata alama da yatsarsa saman labb ansa. Ya duk a gabanta yanda take nan duke tana hawaye cikin rawar jiki. Sai ta soma k ok arin matsawa baya ganin Ya duk o gabanta suna fuskantar juna. Ga zuciyarta da bai daina tsinkewa ba.

Haidar ya dan d auki lokaci yana dubanta kafin ya kauda kansa gefe. Hannu yasa ya kamo hannunta cikin k ok arin hanata ci gaba da matsawa. Tsoro Ya hango sosai saman fuskarta. Sai ya soma sassauta rikon da yai mata a hankali. D ankwalinta da ya fad i gefe ya d auko. Ummul taga Ya kuma nufota taci gaba da k ok arin matsawa Har saida ta isa jikin gado. Ga mamakinta bai mata komai ba sai rufa mata D ankwalin da yai. Ya kuma duk awa gabanta suna fuskantar juna.

Ta sadda kanta kasa tsoron dake fuskarta bai gushe ba.

A hankali ya soma fad in  Look, you can call me a monster, but I don t hate you& And..that doesn t mean I like you either.. Kuma idan har kikayi abinda na sakaki.. Believe me, I ll let you go..

Ta dago raunannun idanunta tana dubansa. Sai Ya jinjina mata kai a hankali alamun tabbatarwa.

Dubansa take shima ita yake duba. Sai ta sadda nata idon a hankali tana mai girgiza masa kai alamun a a. Cikin sanyin murya mai gauraye da rauni take furta  Ubangijina Ya bani umarni da nai maka biyayya cikin abinda bai sab a masa ba. An shar anta wa mace neman al jannah a k ark ashin mijinta. Kaman yanda shima namiji nashi aljannar yana k ark ashin mahaifiyarsa. Ka sani Mommy da kake k ok arin turawa kurkuku naka aljannan ta wajenta aka ce ka nema.? Shiru baice komai ba. Ummul ta goge hawayen da suka gangaro mata kafin taci gaba  Shin akwai D an Adam din da zai wasa da aljannarsa.? Cikin k arfin hali Tai maganar dukda zuciyarta dake bugawa.

Katseta Haidar yai da fad in  Shut up.! Ya katseta yana mai nunata da yatsa kafin yaci gaba  Who do you think you are.? Ya kuma girgiza Kai yana rage muryarsa cikeda gargad i  You don t have the right to speak to me that way.?

Sai ta tsinci zuciyarta da ba ma Haidar amsa da fad in  Ni matarka ce.!

Kaman Wanda yaji amsar da Zuciyar nata ta bayar sai yaci gaba da jinjina Kai had ida furta  Kiyi gaggawan yin abinda na umarceki for your own freedom. You don t want to live with a monster as a husband.! Ya k arashe yana tsareta da ido.

Girgiza masa kai tai  Kai ba mugu bane. Kana kuma da zuciya mai kyau.. Wanda har zaiji tausayin dabba Ya bata abinci bana jin zaik i jin tausayin mahaifiyarsa wacce tai sanadiyar zuwansa wann duniyar, ta rainesa har kawo girma..

Katseta yai da fad in  Enough.! Ya isheki haka.. You don t know anything..! Ke baki san komai ba gameda wann matar.!

Sosai Ummul ta razana da yanayinsa.

Haidar yaci gaba cikin tsananin huci  Yes you might be right.! Watak ila tayi sanadiyan zuwana wann duniyar. Amma naso ace ta barni na Mutu ina yaro da rayuwar k unci da ta bani.! Yes. Watak ila ta raine ni kaman yanda kikace. But I was sacred the whole time! Yaci gaba da jinina Kai yana duban Ummul da idanunsa da suka kad a sukai jazir  She raised me while degrading me.. While insulting me.. She raised me locking me up in a dark room. Forcing me to eat papers. She raised me punishing me for her sins.! Yaci gaba  Because of her.. I grew up feeling low self esteem, feeling insignificant& I had a hard time living in myself..! Yaci gaba da huci yana jinjina akai  And for years& It took me years to overcome the fear and the trauma..! Ya matso da fuskarsa kusan nata  Did you know na girma ina shakku da kokonto if she s really my real mother.? Do you know how it feels ka girma cikin shakku da kokonton sanin wanene kai.?!

Suka dauki lokaci a haka suna duban juna hawaye na gangaro ma Ummul. Haidar ya matso kusanta had ida sassauta murya  So don t act like you know everything.! Yana ida fad in haka yasa kai ya fice ba tareda ya kuma yunk urin rufeta ba.

Tana jin sautin tashin motarsa. Tai saurin Lek awa nan taga Ya fuzgi motar ya bar wajen a guje. Tabi bayan motar da kallo Har ya b ace ma ganinta. Sai ta tsinci kanta da masa addu an kasancewa cikin aminci.

Jiki a sanyaye ta dawo da baya ta zauna saman gado had ida rapka tagumi. Ta rasa mai zuciyarta ke ji gameda al amarin Haidar. Idan ta fahimcesa kaman dai ya amo da abinda ke masa ciwo a zuciya ne. Har k asan zuciyarta bata jin shid in mugu ne. Sai ta stinci zuciyarta da tausaya ma rayuwar Haidar d in. Dan bayan abinda ya gama amo mata ta fahimci alak arsa da mahaifyarsa ya samo nakasu ne tun yarintarsa. Sosai taji tana son sanin asalin wanene Haidar. A wata fuskar sai tana ganin kaman shida ita sunada k addara mai kamanceceniya musamman a b angaren abinda ya shafi alak arsu da iyayensu. Tunanin Umma da irin rabuwar da sukai ya fad o mata.. A hankali ta lumshe idonta hawaye na gangaro mata.

Ranan har dare bata kuma saka shi a idonta ba.

**

Hisham yai tsaki a karo na ba adadi. Da alama amfanin Dareen ya k are cikin rayuwar Haidar. Da alama Anisa ce kawai yanzu zatai masa amfani wajen cimma burinsa. Idan kuwa har amfanin Dareen ya k are baiga amfanin zamanta da Haidar ba. Watak ila idan asirin da Dareen tai masa ya karye Haidar zai fito da Ummul daga yanda ya b oye ta. Bazai iya jure rashin sanin ina Haidar yakai Ummul ya b oye ba. He knows Haidar so well. Idan zai Mutu bazai tab a sanar da kowa ga yanda ya b oye Ummul ba. Shi mutum ne da ke aiwatar da abubuwansa ba tareda shawarin kowa ba. Shi mutum ne da baida kusanci da kowa face zuciyarsa da abinda ta raya masa. Idan kuwa har haka ne Dareen batada wani amfani. Da ita da dodon nata k arya suke. Tinda asiri baiyi wani aiki ba ya kamata ya gwada tactics d in Anisa. Watak ila ta haka zai samu ya mallaki Ummul. Shi Akan ya rasa Ummul ya yarda zai iya abandoning mission d insa na ganin bayan mahaifinsa wato Engr Aliyu Maitama da ahalinsa. Da wann tunanin ya mik e yana huci yana ayyana a cikin zuciyarsa bazai tab a bari ma Haidar Ummul ba. Soyayyarsa ga Ummul ne last abu da ya kamata ya tabba bai bari Haidar ya rigasa samu ba. Hajja ta saka masu albarka dashi da ita. Ummul bata cancanci miji irin Haidar ba. Bata cancanci zama cikin ahali irin na Maitama ba. Akan ya mallaketa ya yarda ya rasa komai.

44 / 52