Chapter 1 Reading Cin Duniya Book Compelet Hausa Novels By Chuchujay Arewa Novels

Cin Duniya Book Compelet Hausa Novels By Chuchujay

Author :  Chuchujay Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   1 / 16

1 to 3K   out of 45.5K words

 𝘓𝘪𝘵𝘵𝘢𝘧𝘪𝘯 𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔 𝘯𝘢 𝘬𝘶𝘥𝘪𝘯𝘦 𝘢𝘬𝘢𝘯 𝘧𝘢𝘳𝘢𝘴𝘩𝘪𝘯 𝘕600 𝘬𝘢𝘤𝘢𝘭 𝘷𝘪𝘢 𝘵𝘦𝘭𝘦𝘨𝘳𝘢𝘮.

08130229878

𝘈 𝘵𝘶𝘣𝘵𝘶𝘣𝘪 𝘸𝘢𝘯𝘯𝘢𝘯 𝘓𝘢𝘺𝘪𝘯 𝘥𝘰𝘮𝘪𝘯 𝘒𝘢𝘳𝘪𝘯 𝘣𝘢𝘺𝘢𝘯𝘪.

𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔

𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎

Na

𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay)

Sadaukarwa ga Marubuciya Azizat Hamza,Allah ya kula dake ya ƙara Miki ɗaukaka da nisan ƙwana mai amfani,Allah ya biya miki dukkan wasu buƙatunki na Alheri♥️

HALISH Sultan..a duk inda ki ke ina addu'ar Allah ya kula da ke.

Saƙon gaisuwa ga dukkanin members ɗin Women of words writers association (wow).

(COPYRIGHTS)

All Rights are reserved. ©

Ma'ana babu wani sashe na littafin nan da na yarje a kwafa ko a sake masa samfari ta ko wacce irin siga.

[DISCLAIMER ]

Ƙirƙirarren labari ne,suna, guri , Character dukka fictional ne,idan yayi dai dai da rayuwar wani ko wata coincidence ne,it's fictional.

[My Contacts info]

WhatsApp:08130229878 Instagram:Chuchu_jay_

TikTok:chuchujay4

Wattpad/Arewapen:chuchujay

Facebook:Ameenatuh Jameel.

[WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION ]wow.

Littafin Zunairah ya samun chanjin suna saboda suna yayi iri ɗaya dana wata marubuciya.ngd

EPISODE 1:my life

* 𝚉𝚄𝙽𝙰𝙸𝚁𝙰𝙷 *

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Tun kiran farko da Mama ta fara na ji ta amma nayi lamo a kan gado ina mai jin takaicin tashi ,duka duka ƙarfe shida fa na safe haka nan bana san tashin wurin nan, sai naje makaranta ya zamana ni ce ta farkon zuwa a ajin mu kamar wata mayya.

"Zunairah na san kina jina Allah kada ki bari na ɗauko bulala because zan zane Miki jiki".jin Muryar Mama da kuma alamun tana takowa cikin ɗakin ya saka nayi Saurin tashi zaune wanda hakan ya yi dai dai da shigowarta,miƙa nayi ina mai saka murmushi a fuskata kafin na ce"NYene Mama"(ina kwana Mama).

"Da ban kwana ba zaki ganni na tashi har na haɗa muku abin kari,Abeg my friend ki tashi ki shirya makaranta,kin san ba section ɗin ku ɗaya da Adavize ba amma ke da Ometere ku je chan ku ƙarata amma kada ku bari a daki mun Auta saboda Latti,maza ki tashi mu je mu haɗu mu ci"ta faɗa tana mai juyawa dan barin ɗakin.

"Mama ni fa ba sunana Ometere ba,haka jiya na zo da abokaina ki ka kirani da Ometere suka ɗinga yi mun dariya ,I'm sure yanzu kowa a makaranta Ometere zai na kirana, Sunana Hauwa'u Please ko ki ce mun jiddoh,ita Aunty Zunairah da take san Ohunene ɗin ai baki faɗa mata sai dai Baba ya faɗa".ƙanwata Hauwa dake sanye da uniform bakin ƙofar ɗakin ta faɗa.

Towel ɗina na jawo ina mai cewa"an dai ji haushi,yarinya duk inda mutum yake tushensa Yaren sa,ni kam ina alfahari da yarena,da za a daina kirana Zunairah ma ana ce mun Ohunene so nake amma either ways suna nan mai daɗi ne".

"Aw wai dama Zunairah ba kiyi wanka ba?"Mama ta tambaya tana mai ignoring Hauwa'u .

Kafin ta sake wani maganar na faɗa bathroom ina mai cewa"Mama wanka na da babu daɗewa".

"To dai wallahi Veyanarisa ko mu cinye"(ki zo mu ci abinci).Hauwa'u ta faɗa .

Ina jin fitarsu na fara wanka,kullum haka daily routine ɗin gidan mu yake da safe in dai maganar makaranta ce.

Cikin kayan makarantana Green finafore da farin long sleeve,sai ƙaramun farin hijabina na shirya, Hauwa'u da Muhammad Adavize suna zaune suna jirana dan mu ci abinci,bakin nan na Hauwa'u ya yi tsini kamar zai taɓo sama saboda takaicin Mama ta hana su cin abinci kan sai na fito za mu haɗu mu ci ,haka gidan mu ya ke ,duk abu sai an jira kowa ake fara cin abinci,mu duka muke haɗuwa har Baba da Mama mu ci mun riga da mun saba dan idan ɗaya Baya nan sai muna ji babu daɗi.

Zama nayi kan tambarman da suke ina mai taɓa Hauwa'u a cinya ina mai faɗin"Ometere ƙanwata ta kaina".

Cikin jin haushi ta ce"Mama kina jinta ba,ki faɗa mata bana so".

"To Inya dama kana ƙin identity ɗin ka".Baba dake fitowa daga cikin ɗakinsu ya faɗa yana mai zama gefen Mama.

"Ni ban ce ba Baba ai babu wanda ya ji na ƙi Hauwa'u tunda babu yadda zanyi ga Hauwa'u ga Ometere ni kam na shiga uku ".

Babu wanda ya sake kulata mu kayi Bismillah muka fara cin jallof ɗin taliyar Mama mai ɗan Banzan daɗi gefe guda kuma kowa da ruwan lipton ɗin sa da ya ji kayan ƙamshi.

Bayan mun gama ne duka muka tashi domin tafiya makaranta gudun Lattin da Mama bata so,kallon Baba nayi :"wai Baba Har yanzu ba a gama gyara maka motar nan naka ba?Allah keke napep ba kowa ke shiga lungun makarantar mu ba".

"Yace sai gobe Ohunene haka nan za ku yi ta haƙuri kafin na ƙarɓo ,nima dole sai a daidaita sahun nake bi ga tsada daga nan zuwa cikin gari ya isheni na sha mai ya yi min kwana biyu"ya faɗa yana mai saka hannu a aljihu ya ciro kuɗi ya bamu,tun kafin mu fita na ɗauki nawa na bama Hauwa'u da Muhammad na su sanin halin Hauwa'u yanzu sai ta ce an bani abin da ya fi haka na boye dan rigima duk da a gabanta fa aka bada kuɗin.

Sallama muka musu suna masu saka mana albarka kafin muka fita dan zuwa bright scholars School.

Sunana Zunairah Buhari ,Asalin mu Yaren Ebira ne daga garin kogi karƙashin Ovehira amma mu mazauna Garin Kano ne cikin Unguwar Hotoro tsamiyar boka,sau tari idan na tambayi Baba mai ya kawo mu Kano daga kogi sai ya ce Karatu ya kawosa BUK da ya gama kuma sai ya samu aiki a gidan gwanmati,jin daɗin garin ya saka shi miƙe ƙafa ya zauna har ya Auro Mama Fatima wadda suke yan yare guda gari guda,mu ba masu kuɗi bane amma baza mu kira kan mu da talakawa ba tunda Álhamdulilah muna ci sau uku a rana ,Gidan Ebira shine mutanen layi ke kiran gidan mu .

Duk yadda Baba zaiyyi ya yi ƙokari wajen ganin ya bamu ilimi mai kyau da kuma rayuwa mai kyau ,makaranta bai bari mun yi ta gwamnati ba,Duk yadda iyayen mu za suyi,sun yi ganin sun nuna mana yadda za mu so juna a tsakanin mu,Mu uku Allah ya basu amma Mama haihuwarta huɗu,ta haifi babban Yayanmu Abdullahi da mijinta na farko a kogi kafin ta Auri Baba,a yanzu yana zaune a okene da yan uwan mahaifinsa,bayan ta Auri Baba aka haifeni inda naci suna Zunairah,Baba ya ce mun ma'anar sa sunan wani Fure ne da ke gidan Aljanna,a sunan yare na ci Ohunene wanda ba sai an faɗa mun na dace da sunan ba saboda sanyina da haƙurina ya yi yawa da yake saka mutane ke tunanin bana da wayau ko za suci kashi a kaina ban tanka ba,abu guda da basu sani ba ,Ni haka Allah ya yi ne bana san damuwa.

Hauwa mai shekaru sha biyar ita ke bina ,Ometere kenan rigimammiyar gidan mu,Tsakanina da ita shekaru Huɗu ne dan har Mama ta fara tunanin ba zata sake haihuwa ba sai ga cikin Ometere,bayan haihuwarta taci sunan Maman Baba Hauwa'u,dalilin da ya saka Baba ke kiranta da Inya kenan ma'ana Mamana.

Mama ta bata sunan Yare Ometere ma'ana kyautar da aka daɗe ba'a samu ba,bayan shekaru Biyu kuma aka haifi Muhammad Adavize wanda ke da shekaru sha uku.

Ni ina Ss3 inda a yanzu muke shirye shiryen rubuta WAEC Hauwa'u kuma yanzu ta shiga Ss1 Muhammad kuma zai shiga Js1,Bana da wani buri a rayuwa da ya wuce naga ina rubutun littafan Turanci duk da turancin ba yarena bane na farko,idan aka bamu Littafin makaranta na amfani ciki nake ɗaukar guda ɗaya nayi rubutu a ɓoye ba tare da kowa a gida ya sani ba,sai na aje Bayan Mutum ɗaya ta karanta,Aminiya ta kenan Anisah Ibrahim,tun muna primary school muke tare ,Ni da ita irin ƙawayen nan ne da ake kira inseparable idan ka ganni dole za ka ganta,ita ɗin Yaren Idoma ce na garin Benue ,Agatu local Government amma mazauna garin Kano ne kamar mu,

Ni da ita secret keepers ɗin juna ne dan sau tari a makaranta har malamai kan tsokane mu da yan biyu.

Abun da ya fara jana rubutu shine soyayya,ni ɗin mayyar soyayyace idan na faɗa ban iya ba,gani da shegen yarda kamar duk duniya Babu na banza,kana raɓata ka nuna mun soyayya shikenan kamar wawuya sai na baka dukkan yardata,Mama ta ce ba wawanci bane dabi'a ce,Ni tawa ɗabi'ar kenan ,idan na zaune da biro na bisa takarda wani irin shauƙi ke kamani ,ni kaɗai nayi ta murmushi ,kuma fa a hakan bana da wani saurayin da nake kulawa although akwai masu bina,tun wani saurayina ma'aruf da nayi ma san mutuwa ya gudu ya barni ban sake sakewa ba dan na sha wahala dalilin rashin sa,a matsayin amateur writer abin da na ƙware kenan ban sani ba gaba idan na san inda na dosa na fara Cautionary tales yanzu akan abun da zan nusar ba nace ba dan na ga mostly marubuta sukan nusar akan abubuwan da suka shafi Zaman Aure ,zamantakewa ta mutane ,abubuwan zahiri da sauran su amma nikam Zunairah na rubuta soyayya kawai mai ƙalubale karshe kuma ya zama happy ending .menene daɗin idan babu happy ending?I just hope Nima rayuwa ta yi mun happy ending yadda bana da aiki sai rubutun Happy ending wanda at the end of the day aminiyata kawai take karantawa ta yi appreciating ɗina ta ƙara mun ƙarfin gwiwa kan zan iya amma na bari sai mun gama secondary kafin na nuna ma duniya talent ɗina.

Tunda na shiga cikin makaranta Anisa kawai nake nema,sakata cikin idanuna first thing a makaranta shi ɗaya yana faranta mun rai ,jin ihunta a bayana ba ƙaramun razanani ya yi ba,ɗane ni tayi ta baya tana dariya,nima dariyar na saka dan baza mu taɓa girma ba idan muna tare da juna,ganin Baba discipline master yana nufar mu da ƙatuwar bulalarsa ya saka muka ruga da gudu muna dariya,dukan sa Babu daɗi gashin mun tsaya a inda in har ya shigo ɗin sai ya zane mu.

Bayan assembly dukkan ɗalibai suka wuce aji, Mathematics ne da mu first period,Ina mamakin masu cewa suna san Maths domin ni Zunairah a wannan bangaren kaina fanko ne ,a barni dai bangare Literature in English,duk ajin mu babu Guru a wannan fannin Kamar ni.

Bayan mun gama classes ɗin kafin lokacin break aka fita break,ina ƙokarin tashi Anisa ta riƙe mun hannu, kallonta nayi kafin na ce"break time baby".

"I've got something for you".

Zama nayi ina mai facing ɗin ta jin abin da ta ce,hannu ta saka cikin jakarta ta ciro wani box da aka yi wrapping da ledan wrap mai kyalli, miƙa mun tayi tana murmushi,cikin rashin fahimta na karba ina juya box ɗin ina kallonta ina san sanin na mene ,dariya ta saka sosai kafin ta nuna ni tana mai faɗin"kada ki ce mun na last year za muyi,Zunairah wace irin mutum ce ke?for God sake today is your fucking birthday ".

Hannu na saka bisa bakina dan wallahi da gaske na manta,bana da wannan tsari na birthday or something wanda dalilin hakan ya kan saka nama manta cewa wai ranar murnar Haihuwarta ta zagayo, rungumeta nayi ina mai jin hawaye na san zubo mun,haka nan last year ita ta tuna mun birthday na dan gida dama sun saba bani surprise bayan makaranta,amma bayin Allah nan suna da wani abu,suna fa sane amma a yadda na fito gida ma babu wanda ya ce mun koda Barka sai zane ni ma da Mama ke faɗin za tayi.

"I love You best friend,thank you very much kina ɓata ni da yawa".Shafa bayana tayi a hankali kafin ta furta "happy fully nineteen bitch I love You ".

Bana da wata ƙawa da ta wuce Anisa wallahi har cikin jinina nake jin ta,.Buɗe box ɗin na fara,wani mayen agogon Amiri designer na gani,da mamaki na kalleta na ce"babe Amiri?this is much".

Ƴar dariya tayi kana ta ce "kin chanchanci fiye da haka gurina Zunairah so chill and Rock your Amiri and after school akwai more surprise,but I don't know yadda za muyi da Hauwa'u da Muhammad".

Ɗan shiru nayi dan babu ma yadda za a yi Hauwa da Muhammad su tafi gida su kaɗai ni ina wani gurin daban,kama hannunta nayi "babe it's okay,wannan ma kaɗai ya isa cos men nawa ya yi worthing agogon nan ma kansa".

"250 thausand"ta bani amsa,ban san lokacin da na aje mata kan cinyarta ba ina mai zaro ido.
"Dubu ɗari biyu da hamsin fa Anisa ina ki ka samu kuɗi haka and ki ka yi wasting a kaina?bama zan iya kai agogon nan gida ba tambayar Mama da Baba kawai ya ishe Ni,what?250? No now".
Dariyar da ta saka ta dakatar dani, kallonta kawai nake dan banga abin dariya ba,sai da tayi mai isarta kana ta ce"hala kin manta Babana ɗan Siyasane Mama head ɗin NGO,Yayana Halil Custom,ni kuma only female child ko?baby we are loaded so dan na cutting miki agogon dubu ɗari biyu da hamsin chicken change ne so dan haka i wont take baza ki bini ba after school driver na waje ya kaimu ni kuma har gida zan aje ki".
Mantawa nake Anisa ɗiyar masu kuɗi ce ganin yadda ta sake sosai dani,duk wani fancy abu mai kyau itace,wani fancy sneakers, sandals,bags,hatta pen ɗin da take amfani da shi fancy ne,dukkan littanta kuwa tayi wrapping ɗin su da Wrapping set na Strawberry short cake nima har nawa sun samu wannan arziƙin although abun hannunta baki ɗaya bai dameni ba domin shi kuɗi yana cikin manyan abubuwa dake gurɓata Alaƙa.
"Ina za muje to"na tambaye ta.
"Idan na faɗa Miki ai ya tashi a surprise kuma "ta bani amsa tana dariya.
Yanke shawarar driver ɗin nata ya aje su Hauwa'u gida nayi idan ya so mu sai mu hau adaidaita sahu.a Haka muka tsayar da maganar muna jiran lokacin tashi ya yi,haka kawai na ƙagu naga Wannan surprise na best friend ɗina kafin naje gida na tarar da na dangina na san suma sun shirya mun.
𝘊𝘩𝘶𝘤𝘩𝘶 𝘫𝘢𝘺✍️
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔

𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎

Na

𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay

EPISODE 2: unexpected sin

*𝚉𝚄𝙽𝙰𝙸𝚁𝙰𝙷*

Tunda muka hau keke ni da Anisa tunanina yana gida duk da na cewa Hauwa'u ta faɗa ma Mama mun je duba wata ƴar ajin mu ne bata da lafiya,duk irin bin diddigi na Hauwa'u bata bi ba sai to da ta ce mun kasancewar ina tare da Anisa Sannan na san idan ta faɗama Mama haka zata amince tunda kowa ya sanni da Anisa,saboda yadda muke kowa a gidan mu santa yake har Baba.

Kuntau muka nufa,dama ni bana da kuɗin motar zuwa kuntau ,kuɗin motana daga CBN Quarters ne inda makarantar mu take zuwa Tsamiyar boka Naira Ɗari ,sai wata ɗari da hamsin da nake da a jaka,haka nan ta bada 2000 mu biyu ko tayi bata yi ba.

Koda muka isa Kuntau a ƙofar wani haɗaɗen gida Mai keken ya aje mu bisa jagorancin Anisa,kuɗinsa ta bashi ta kamo hannuna ganin yadda nake bin gidan da kallo,"gidan wane Wannan ɗin?"na tambaya ina bin ta.

"Idan na faɗa Miki ai surprise ya tashi surprise kuma ,ke dai ki biyo ni,kin san ba zan kai ki inda za a siyar da ke ba ko?".

Shiru nayi na bita,Knocking gate ɗin tayi,wani matashin Saurayi ne ya zo ya buɗe wanda kana kallansa ka san mai gadin gidan ne,gaishe mu ya yi nima na gaida shi amma Anisa kam gaba ta ci har a lokacin hannuna cikin nata,wayarta ta ciro daga side purse ɗinta ta kira ta ce "mun zo"kana ta kashe.

Ni dai baki ɗaya na ƙosa naga Wannan surprise ɗin da za a yi mun ,Allah ya sani dan dai kawai Anisa ce ,ƙofar na buɗewa bata yi wata wata ba ta ja hannuna muka shiga ,Falo ne madaidaci mai kyau wanda ya tsaru da kayan ƙawa,"zauna ina zuwa".ta faɗa kafin ta Haura madaidaicin saman da a ƙalla zai ɗauki ɗakuna biyu,juye juye na fara ina san ganin wanda ya buɗe mana ƙofar, ƙarar waƙa mai sanyi da ya fara tashi ya saka na ƙurawa gurin da waƙar ke fitowa ido,cart ne ya fara fitowa ɗauke da wani ƙaton cake kafin mutumin da bana expecting ya bayyana yana mai murmushi ,tashi nayi tsaye cikin yanayi na kiɗima ,ƙarasowa ya yi inda nake yana mai murmushi bakin nan ɗauke da chewgum yana tauna kamar wata tsohuwar karuwa.

Ƙokarin saita kaina nake gudun kada ya fuskanci halin da bayyanar sa ta jefani.

"Yaya Adam"na ambaci sunansa,.ɗaga mun gira ya yi yana mai sakin cart ɗin mai ɗauke da cake ɗin da sunana ke rubuce gwanin sha'awa wanda da ace a gidan mu ne aka mun irin sa tsalle kawai zan fara ina murna saboda haɗuwa da ya yi,amma ina ta wani murna ina gaban ɗan iskan nan gashi Anisa ta wani haura ta barni,wallahi da na san shi zan tarar babu abin da zai saka na biyo ta.

Yaya Adam cousin ɗin Anisa ne wanda ya daɗe yana nuna yana sona tun ina minor,akwai ranar da muka taɓa haɗuwa a gidansu Anisa har yake ce mun nazo mu je mu huta a hotel sai ya kai ni gida,tun daga ranar na tsorata dashi musamman da yake ta aikin bijiro da yana sona ita kuma Anisa baiwar Allah bata da masaniya sai tura mun shi take ,na tabbata da ta san ya taɓa mun zancen banza baza ta taɓa ƙokarin haɗani da shi ba,ni kuma gashi ina jin nauyin faɗa mata ɗan iska ne dan duk cikin cousins ɗinta Adam yana cikin waɗanda take shiri da su.

Matsowa kusa dani ya yi ,kafin nayi aune ya rungumeni ƙam a jikinsa yana faɗin happy birthday love,ƙokarin ƙwacewa nake amma ya yi mun abin da ban taɓa tsammani ba,idanuna na zazzaro jin leɓensa bisa nawa yana ƙokarin sada bakinsa da nawa ,ban san lokacin da nayi masa wata irin mahaukaciyar hankaɗa ba,hannu

1 / 16