Author : Chuchujay Category : Romantic Hausa Novels
mafita,saboda wannan yaron na gani a idanunsa yana san ki ,na kasa gane wane dalili ne zai saka ki ce wai baki so kowa ya sani a gidan su,shin wasa ya zo ku yi ?I'm very sure ba Ten ten ya yazo yace yana so ku yi ba ke dashi ,banga dalilin da zai saka ki ce wai baki so kowa ya san cewa kuna soyayya' ba,dan haka yanzu ina so ki faɗa mun menene a zuciyarki dangane da shi,idan baki san shi ne tell me,sai mu san ya ya zamuyi".
Shiru nayi ina mai jin wani irin Nauyi,sai da ta sake maimaita mun tambayar kafin na iya cewa"Mama ina san shi "ina ƙokari wajen sake ƙasa da kaina dan bana so mu haɗa ido,hankali ta mayar kaina sosai kafin ta ce",to let me understand boye boyen na menene?".
"Mama kawai ina tunanin Yadda Anisa zata ɗauki abunne ,Kinga ni da ita tare muka tashi ,mu aminai ne,rana ɗaya Mama sai taji ina soyayya mata da Yaya?"amsar da na bawa Mama dariya ta sakata,sai da tayi yar daƙiƙiya kafin ta ce"ban san wane musuluncin ne ya baku wannan ruwayar ba na cewa idan kina ƙwance da ƙawarki kada ki yi soyayya da yayanta,look here my darling,kina wasa da damar ki,akwai damar da idan ta wuce ba ta dawo maka,i trust this guy sannan na san yana sanki ,kada ki bari wani nonsense belief naku ya rinjayi farin cikin ki,I'm sure ita kanta Anisa yadda take ƙaunarki farin ciki za tayi ba wai ta miki baƙin ciki ba,ki yi tunani mai zurfi ki zama mace ki riƙe abin da ki ke dashi a gabanki".
Shawarwarin da Mama ta bani sun ratsani sosai,sai a wannan lokacin nake ganin wautata na ɓoyewa Anisa , Message ɗin ya Adam ne ya katse ni daga dialing number ɗin da nake niyar yi na Anisa."Babe I will let the cat out of the bag,xx Adam ".
Tsaki nayi ina ignoring ɗin shi da inda ya samu number ɗina,blocking ɗinshi nayi baki ɗaya kafin na kira Anisa ,ina mata kira ɗaya ta ɗauka na sanar mata idan mun haɗu a school gobe akwai labari,zan faɗa mata wanda nake dating,duk yadda ta ƙagu akan na faɗa mata a lokacin ƙi nayi dan maganar ba ta waya bace,magana ce da ya kamata ace gani gata muna kallon juna sai a yi ta ,haka nan nayi ta duba wayata ko Yaya Halil zai kirani amma bai kira ba,tun ina saka rai har na cire,mayar da hankalina nayi wajen fuskantar Anisa a makaranta,na aminta da zan freeing kaina daga ƙejin da na yiwa soyayyata babu gaira babu dalili.
Washe gari na riga kowa tashi na fara kamawa Mama aiki,sai da na gama komai kana na shiga wanka sanin Lecture ɗin ƙarfe tara ne dani,baki ɗaya sukuku nake jina ,na saba Ya Halil zai kirani first thing in the morning ya san yadda na tashi ,sai nake jina kamar wadda bana da lafiya,sallama na yima Mama,har na kai bakin ƙofa ta kirani,kallona tayi kana ta ce"Zunairah ba dole sai Halil ya nemekine zaki nemesa ba,girman kai ba naki bane,kun samu misunderstanding sai a san yadda za a yi a gyara ba wai kice sai shine zai nemeki ba domin a yadda nake gani nutsuwarki bata nan".Kunya ta kamani sosai na kasa cewa komai,ganin nayi shiru kuma ni ban iya tashi ba ya saka ta cewa"kije makaranta kada kiyi latti,Allah ya yi maki albarka ya bada karatu mai amfani ".
Haka na wuce ina ta tunanin maganar da Mama ta faɗa,idan na kira ni ban san mene zance mishi ba,ina tafiya ina nazari naji horn ɗin mota a bayana,saurin matsawa nayi ba tare da na juya ba amma na tabbatar da na matsa a kan hanya,jin motar bata sauri ne ya saka na juya raina a ɓace musamman da na fahimci bina ake,wani faɗuwa gabana ya yi ganin motar sa,so nake na juya amma ƙafafuna sun ƙi barina nayi hakan , tsaye nayi ina kallonsa inda shi ma yake cikin motar yake kallona,shi bai fito ba bai kashe motar ba shi kuma bai tafi ba,wayata da ta ɗauki ruri a jakana ya sakani dawowa duniyar kallonsa dana tafi,juyawa nayi da sauri kafin na saka hannu cikin jakar na ɗauko wayar ina tafiya cikin hanzari,faɗuwa tayi yadda na cirota a ruɗe,hawayen babu gaira babu dalili naji suna bin kuncina na rasa na mene,faɗuwar wayarce ko mene ba nace ba,ni dai kawai naji hawaye na sauka,duƙawa nayi hannuna na karkarwa zan ɗauka amma kafin na ɗauka ya rigani,ɗauka ya yi yace mun"ina zaki je ki ke gudu kamar kin ga dodo".
Kasa kallon idanunsa nayi,ganin yadda muke a tsugunne tare ya saka nayi saurin tashi na juya mishi baya ina raba idanu ina mai yin wasa da hannuna,Zuciyata kuwa wani bugu take mun kamar nayi ma sarki ƙarya,dawowa inda nake ya yi ya miƙo mun wayar kafin ya ce"we need to talk babe ,ki zo muje na aje ki makaranta sai muyi magana a hanya dan Allah ".
"Ni zanyi latti sauri nake "na faɗa ina mai gudun haɗa ido da shi,murmushinsa mai burgeni ya yi kafin ya mayar da wayar aljihunsa ya juya ya nufi motarsa,bana da zaɓin da ya wuce na bisa ,kafin na ƙarasa ya buɗe mun ƙofa,bance komai ba na shiga ya rufe ya zaga ya mata key,tunda muka fara tafiya babu wanda ya ce komai ,ganin baya da niyar magana ya saka nima nayi mishi shiru ai shi ya kamata ya fara magana ba ni ba,Har muka kai makaranta bai ce mun komai ba sai da muka shiga harabar makaranta ya faka motan dai dai inda ya saba ,ganin baya da niyar magana ya saka na fara kokarin buɗewa zan fita amma sai naji ya yi locking door ɗin,kallona na mayar gareshi .
"Ka buɗe mun na fita".
Marairaicewa ya yi da ido kafin ya furta abin da ban tsammanin shine zai fara fitowa a bakinsa ba "ina sanki ZUNAIRAH,wallahi sosai da sosai,kinji".Kallon cikin idanunsa nayi na rasa abin da zance,hawaye suka tarar mun kafin na farga sun fara zuba,"ka buɗe mun na fita kada nayi late muna da lecture".
"Na sani amma dan Allah kada ki bari wani abu ya samu soyayyarmu,i understand idan kince kada mu faɗawa kowa amma zamu dawwama cikin ɓuyane,Mama sun san dani amma Enen bata san dake ba and ina so na nunawa duniya baki ɗaya ina sanki ina san na Aureki,dan Allah ki bani chance na tabbatar Miki da hakan".
Ganin yadda ya marairaice ya saka ni cewa "Ya Halil babu abin da ke tsakanina da Adam".
Ɗan murmushi ya yi ya ce"na sani ,Adam!! Is a bad story but ganinsa tare da ke bai saka naji wani abu ba dan na yadda babu abin da zai haɗa ki da mutum kamar Adam....".
Katse shi nayi."Cewa ya yi yana sona amma ban amince mishi ba ,shine ranar ya zo,har ya ce mun wai ka faɗa mishi muna tare abun da ya faɗa maka kuma wallahi ƙarya ne".
"Forget about kowa da duk abin da ya faru,I'm sorry abun da na faɗa Miki wai ko kina tare da wani ne i just said it,saboda I was frustrated and.... "
"Ya wuce Habibi mu kalli abun da yake gaba mu daina kallan baya and insha Allahu steps ɗin da na ɗauka da farko zan gyara ,You can tell Enen about us ni kuma zan faɗawa Anisa ".
Ɗan dariya ya yi yace"ke da Anisa dai Sai Allah,kada ki damu Anisa zata sake sanki fiye da baya ,kije kada na saka ki yi latti zan zo anjima".
Buɗe mun ya yi kafin na buɗe ya dakatar dani,fita ya yi ya buɗe mun ƙofar ya duƙa kafin ya ce"i love you".sunkuyar da kaina nayi ina murmushi kafin na ce"i love you ".matsawa ya yi na fito ,yana ƙokarin taka mun na dakatar dashi nace ya tafi kada ya damu,kafin ya bani Amsa Aminiyata ta bayyana ,da mamaki take bin mun da kallo Nima ita ɗin nake kallo musamman jin ta ambaci sunana.
"Amma wannan ba wani coincidence bane ,care to explain?"..
"Anisa !!"na kira sunanta ina mai jin wani Nervousness.
"Wane zai Miki explanation ina wasa dake ko?"ya Halil ya faɗa yana mai tsareta da ido,ganin zai ɓata mun abin da na shirya ya saka nayi saurin matsawa gareta na Kama hannunta ina cewa "muje zan Miki explanation ɗin ni da kaina"muna barin gurin da yake ta ƙwace hannunta tana mai cewa "Zunairah ina ji,mene yake haɗaki da ya Halil wanda ba ki faɗa mun ba,na tabbata yau ba a hanya ku ka haɗu ba,abin da nake gani tsakanin ku kuma kaina ya kasa fassara menene care to explain?".
"Anisa calm down zan faɗa miki".wayarta da ta fara ƙara ne ta katseni,ɗauka tayi tana mai cewa"wai ya Adam mene kake ta damuna dan Allah zan kiraka ina abu mai amfani"kashewa tayi tana kallona ta ce"Uhum ina ji".
"Ashe dai ke ce".
Tare muka kalleshi jin muryarsa ,cikin ƙaguwa Anisa ta ce"wai dama ya Adam bina ka ke,mene ka ke san faɗa mun wanda sai ka yi ta damuna,I'm in the middle of something ni yanzun".
Kafin ya yi magana na yi hanzari wajen cewa"ina dating YAYA HALIL Anisa "a wani irin 360 ta juyo tana kallona ta ce "pardon?"rumtse Idanuna nayi na sake maimaita mata,dariya ɗan iskan nan ya kwashe dashi ya na mai cewa"damn it da kin bari na yi wannan Alfarman na faɗa mata mai ya sa za ki mun haka".
"So kaima ka sani?"ta mayar da tambayarta da kallonta gareshi,ɗaga gira guda ya yi ya ce"Uhum ina ta binki na fesa miki best breakfast kina mun ihu so that's it,your brother and best friend are having illicit affair".
Kalmar illicit ɗin da ya faɗa ta mun zafi amma ba ta ita nake ba ina san karantar yanayin da na jefa Anisa,murmushi tayi tana mai gyara zaman jakarta kafin ta ce "first period Computer application ne kizo mu tafi kada ta shiga ta hana mu,Ya Adam thank you zaka iya wucewa".gaba tayi ina mai bin ta a baya ,atleast koda bata yi magana ba ni dai na sauke nauyin dake kafaɗata ,guri ɗaya muka zauna a class Mrs Jenna na mana dictation ma a cikin nawa take kwafa,idan bata gane mene na rubuta ba zata ce mene Wannan,ni dai baki ɗaya a tsarge nake har aka gama lecture ɗin nan,tana fita Communication in English ya shigo muka ɗora,har lokacin ban fahimci ina ta dosa ba dan ko a ido bata nuna mun wani abu ba,bayan mun fita har abinci mukaje ci tare ,ɗanwake muka siya kamar yadda muka saba ita ta ɗauke kwanon tana faɗin ladana ya ƙare,kullum haka muke Indai muka siya ɗanwake ita ke ɗauke ƙwanan ta lashe mai da yajin wai ya fi daɗi,duk yadda naso kawo maganar Yaya Halil sai ta kauce ta kawo wani zancen ,ganin yadda ta saki jiki ya saka na saki nawa ina tunanin na karɓu,sai naji banji daɗi da na ɓoye mata ba ,mai ma nake tunani da ɗin.
Bayan mun gama dukkan wani activities na school muka fita don tafiya gida,muna tsaye muna jiran keke ta ce mun"Daddy zai siya mun mota Kinga mun huta na aje ki gida nima na wuce,bana san driver yana kawoni makaranta ,I need my space ".
Murmushi nayi nace"Allah ya tabbatar da Alheri"wayarta ta ciro ta fara nuna mun hotunan motoci,wata Prado mai kyau ta nuna mun ta ce irinta take so a siya mata,sai na tsinci kaina cikin mutuƙar farin ciki har inda tsokanarta wa ya ganta gaban mota.
Haka muka sha hirar mu ,ni aka fara saukewa ina ƙokarin bashi kuɗi ta hanani ta hanyar cewa "ki bari zan bashi"cike da naci nace gaskiya ta bari na biya amma ta ƙiya har mai adaidaita sahun ya kunna ta leƙo da kanta tana kallona kafin tace "Besty i will appreciate it idan ki ka kawo ƙarshen Puppy love ɗin dake tsakaninki da Yaya Halil dan bana goyan baya bazan bada goyan baya ba kuma,sai dai idan zaki zaɓi soyayya sama da ƙawance da muka daɗe muna ginawa ni dake,Code ɗin basa da yawa,Don't date my brother and don't date my ex ".
Kafin na fita daga sukar da maganarta ta yi mun ta umarci mai Adaidaita sahun da ya ja su wuce,kamar wata bebin roba haka na tsaya ina bin hanyar da kallo har suka ɓacewa ganina,ban taɓa tunanin wai Anisa zata ce na zaɓi ita ko Halil ba, shin mene ma ya haɗa ƙawance da kuma abin da nake dashi tare da Ya Halil?shi kuma wannan sababbin abin da ba zai saɓu ba da take kira code daga ina aka samo su?.
"Aikuwa Wallahi Aunty bata isa ba, wai ki zaɓa ko ita ko Yaya Halil, wannan ɗin wane irin banzan Code ne?"
Juyawa nayi jin Muryar Hauwa'u,cikin ɓacin rai nace"laɓe ki ke mun ko?".
Ɗaga hannunta tayi sama ta ce"wallahi A'a Auntymu Fitowa kawai nayi fa zani shagon dan Fulani na siyo siga na tsinkayi maganar ta ki yi haƙuri".
Raɓawa nayi ta gefenta ina cewa "saura ki faɗawa Mama dan Allah zaki ga ya zamu ƙare ni dake "da haka na shiga ciki ita kuma ta fita,Mama na tarar tana hira da Aunty Muna wata yar Yaren mu da suka tare bayan layinmu,tunda taji ana kiran mu gidan Ebira ta shiga jikinmu ,take kuma sai ta samu shiga ,abunka da anga yan yare guda sai ya zama kamar yar uwarmu,dan wasu ma cewa suke muna da alaƙa dama,gaishe su nayi Mama ta mun sannu da zuwa inda take cewa akwai Kunun gyaɗa a kitchen naje na ɗauka na sha ta saka mun siga tuntuni ta aje mun,su kuma su Hauwa'u ta basu suje su siyo.
Tasan wani lokacin ina shigowa gida ina kukan yunwa shi yasa takan fara aje mun Abu mai ruwa ruwa,kunun na ɗauko na shiga ɗaki ,duk yadda nake san kunun gyaɗa sai naji na kasa sha,Anisa ta Shammaceni,ashe duk share zancen da take tana jirane mu zo rabuwa kenan ta faɗa mun bata yadda ba,to amma dole sai ta yarda zan soyayya i Zunairah?bansan yaushe wannan dokar ta shiga tsakaninmu ba,gaskiya zan amince da komai banda barazana da abin da na gama sawa rai,bana wasa da soyayya musamman a yanzu da na samu wanda nake so yake sona,dole ne idan Anisa na sona da gaske kamar yadda ta faɗa tayi Farin ciki da farin cikina,ban taɓa kin abu idan tace ba sanin ba zata cutar dani ba,amma a wannan karan kuwa dole ne Anisa tayi haƙuri ta Barni da abin da nake so dan bana tunanin zan iya ɗaukar wani heartbreak ɗin a karo na biyu,nayi nisan da idan aka mun haka zan samu matsala ainun.
Sakin jikina nayi na cigaba da hidimomina inda har kirana Yaya Halil ya yi ya shaida mun zai zo,ban saka komai a raina ba ban kuma faɗa mishi ya muka yi da Anisa ba muka sha soyayyar mu ya tafi,kamar ba muyi faɗa ba sai komai ya dawo kamar ranar da muka fara musayar kalmar soyayya,har na ƙwanta ina sake tabbatarwa da kaina ba zan bari wannan damar ta ƙwace mun ba musamman yadda na ga murnar da yake jin nace ya sanar da su Enen abin dake tsakanina dashi,har yana tsokanata da kawai gobe zasu zo. introduction.
𝘊𝘩𝘶𝘤𝘩𝘶 𝘫𝘢𝘺✍️
08130229878
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔
𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎
Na
𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay
E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟10.Love or Friendship
*𝘈𝘕𝘐𝘚𝘈*
Tana jin tashin hankali tana shiga tashin hankali amma wanda take ciki a yau ba ƙarami bane,jin kalmar Yaya Halil na soyayya da Zunairah kawai sai da ya so ya tsayar mata da dukkan wani tunani da take dashi,ina ma hakan zai iyu?ai wallahi ko ana muzuru ana shawo babu uban da ya isa ya haɗa wannan alaƙa ta zuba mishi ido,Yayanta fa wanda take ƙauna,taya za ace ta zuba ido tana kallo Zunairah ta ƙwace mata kashin soyayyarta,ba zai iyu ba ba zai faru ba.
Haka wunin ranar ta yi tana ƙunci duk da ta rasa ta inda zata fara ta kuma rasa wanda zata tunkara da maganar,tana zaune falo tana tunani Muryar Mahaifiyarta ta datseta inda take cewa"Aikuwa Halil kayi kyan kai da ya zamana Zunairah itace wadda ka ke so ,Anisa kinji wani labari mai daɗi kuwa,ko da yake ai wannan labari ma ke ya kamata ki bani karin haske".
Turo baki tayi gaba ta tashi tana mai cewa "aikuwa "cikin ɗaki tayi zuciyarta na mata ɗaci musamman da ta lura da yadda Yaya Halil ke washe baki,aikam zai yi ya gama dan wallahi dole ne a watse,daga ɗaki tana jin yadda Enen ke murna kamar wadda aka bawa duniya ,tayi tsaki yafi a irga ,kwanciya tayi tana ta juye juye kan gado ,ji take ƙirjinta na mata wani irin zafi kamar zuciyarta zata fasa mata ƙirjinta.
Haka ta wuni ranar kafin ta samu kwarin gwiwa da dare wuraren tara ta nufi ɗakin Halil,tsaye tayi tana tunanin ta inda zata fara,kafin ta ƙwanƙwasa ya fito,kallonsa tayi cike da fargaba ta ce"fita za kayi yaya Halil?".
Kallon kansa ya yi kafin ya kalleta ya ce"da daren nan ni kam Nisa ina zanje , besides singlet fa ki ka gani jikina".
Turo baki tayi ta ce"na sani ko gurin Zunairah zaka and ai ba zan mamaki ba idan kaje da singlet ɗin maybe ta koya maka abin da bai kamata ba".hannu ya saka ya yi folding yana mai kallonta kafin ya ce"mene maganarki ke nufi Anisa?".
Juyawa tayi tana cewa"shikenan ai yanzu ina magana sai a fassarani,amma ni ka sani brother babu wanda ya damu da damuwarka sama dani".
Cikin rashin sanin inda ta dosa ya kamota ta kwalar rigarta,sai da ta dawo tana kallosa kafin ya ce"me ki ke nufi?wani abu ki ke ɓoye mun?".
Dan kalle kalle ta fara kafin ta rage murya kamar tana tsoran kada wani ya jita kafin ta ce"muyi magana a ciki yaya bana san wani ya ji".bai mata musu ba ya juya ya koma ciki ta bi shi,zama tayi bakin gadonsa kafin ta tattara dukkan kwarin gwaiwarta ta ce"Yaya Zunairah aminiyatace ,babu wanda ya santa fiye dani,and na yi imani