Author : Chuchujay Category : Romantic Hausa Novels
Murmushi irin na dattaku Mama tayi kana tace "to Enennisa (maman Anisa )ni na kasa fahimtar inda tashin hankalin yake, Aurena fa za'ayi ba mutuwa akayi ba,shi kansa haƙurin na gaza gane ta inda muka cancanta,ai abun mu haɗune mu nuna farin cikinmu ga shi Halil mu yi mashi addu'a Allah yasa abokiyar Alherinsace" ..
Maganar mama ta mutuƙar bama Enen kunya,daurewa kawai tayi ganin tazo ɗin ya saka tace"Mama Zunairah,shi Halil ya yi leading Zunairah har ta ɗauka suna soyayya ne ,nima kuma da ya fara faɗa mun wallahi na yarda dan ce mun ya yi ita yake so,to da ya kawo maganar wannan Auren ne na damu nake tambayarsa Zunairah fa,sai yake faɗa mun ƙawance ke tsakaninsu dama, although da sun fara da soyayya abun kuma bai working out ba, still dai naji ya kamata nazo na baku haƙuri,Abu ne Allah bai ba".
Ko Mama bata faɗa ba ranta ya ɓacci tunda ai baki da baki Yaya Halil ya shigo har gidan nan har falonta ya kalli tsabar idanunta yace yana san Zunairah yanzu kuma sai yace wai abokantaka ce?
"Bakomai Enennisa ai ba laifinsa bane ,laifin ita Zunairah da ta bari har abokantaka ya shiga tsakaninsu duk da ta san babu abota tsakanin mace da namiji,muna dai Amfani ne da zamani amma babu komai ai Ubangiji ne baiyyi ba".ƙwala mun kira tayi, hannuna yana riƙe da gashin Hauwa'u dana kama ina kitsawa,ni ban kitsa ba ni ban saki ba,ba niyata na ji abin da suke faɗi ba dan bama kusa da gurin ma Amma maganar da suke ba wai ƙusƙus bace,itama Hauwa'u batace na saki ba duk yadda na damƙe mata gashi ,jin Mama ta kira sunana ya saka na saki gashin wanda ya saka Hauwa'u yin yar ƙara,sai a lokacin na kula i was hurting her ita kuma ba zata iya katseni ba sanin halin da na faɗa.
Riƙeni tayi ta ce"Auntyna kada kije bari na shiga"murmushin ƙarfin Hali nayi nace ta barshi zan shiga ai ni aka kira,daga kujerar da Mama take naje na zauna ina mai san sakin fuskata kamar babu abin da ke damuna,Mamace ta ce"so Ohunene ga nan invitation card ɗin Halil da sweet ɗin Aurensa I thought na faɗa Miki babu abota tsakanin mace da ɗa namiji?mene ya haɗaki dashi?".
Danne kukan dake san ƙwace mun nayi na bata amsar da na sani ita take san ji a bakina"Mama ai ba abota muke ba,kamar yadda Anisa ta ɗaukesa Yaya nima haka na ɗaukesa,babu komai tsakanina dashi".
"Masha Allah,to ki kalla IV ɗin nan nasa sunan matar da zai Aura Zainab dan haka Wannan zoben da ya baki na ajiya ki cire mishi ki Basu sai a wuce mishi dashi".
Tashi nayi na shiga ɗaki na ɗauko ƙaramin akwatin zoben da ya bani na cire daga hannuna ina mai jin zafin ƙirji kafin na rufe na koma falon na miƙawa Enen,ƙarba tayi ta buɗe kafin ta kalleni,nayi murmushi nace "ajiya ne dama ya bani".
Miƙama yaya Hibba tayi wadda ta saka cikin jaka ,ban tashi ba Mama ma batace na tashi ba tace "insha Allahu zamu shigo baki ɗayan mu tun safe,Allah ya sanya Alheri ya rufa asiri".
Sallama suka mana suka wuce Mama ta rakasu har Kofar gida ,suna fita na saka hannuna na riƙe ƙirjina dan ji nake kamar zai faɗi ,Mama na shigowa na miƙa mata hannuna ina kiran sunanta da kyar ,da gudu ta ƙaraso ta riƙe hannuna,wani irin kuka na fashe dashi ina faɗin"Innallahi waina illahir rajiun Mama ƙirjina,Zuciyata zata fashe Mama na shiga uku".
Shigowa Hauwa'u da Adavize sukayi suna masu tayani kuka ganin yadda baki ɗaya na rikice ina mai dafe da ƙirjina ina faɗin zan mutu,ba zan iya fassalta irin ciwan danake ji ba ji nake kamar an zuba mun wuta cikin ƙirjina,rungumeni Mama tayi tana faɗin Allah ya bani haƙuri,ji nake kamar tana ta wanka mun mari,ta ina zan fara haƙuri?ta ina zan fara?ta ina?wane irin cin mutuncine da wulaƙancine wannan,mene nayi mishi da zai mun haka?".
Ranar ji nake kamar alƙiyamata kawai ta tsaya ,koda Baba ya dawo shima haka ya yi ta aikin lallashi ,ransa sosai ya ɓaci amma sanin nuna fushin a fili baya da amfani ya saka ya ce nayi ta addu'a Allah ya bani wanda ya fishi,da zazzaɓi na ƙwana na tashi,ban taɓa tunanin a rayuwata zan iya cigaba da rayuwa bayan cin amanar da yaya Halil yayi mun ba,ta mun suka lokacin guda,baban ɓakin cikin guda wanda shine ban san abin da nayi mishi ba.
Haka nayi satin nan har ya zagayo bana da walwala sai dai na samu kulawa sosai gurin iyayena wanda dalilin hakan ya saka na fara sakewa duk da na san har abada wannan tabon ba zai taɓa barin Zuciyata ba,yana cikin Labarina.
Ranar da bakin yazo haka Mama ta shirya wurin sha biyu zata, Hauwa'u ce ta shirya rai a ɓace dan bata da niyyar zuwa mama ta saka sai ta bita,Ni kuwa dama duk wanda yace naje sai naji dalilin da ya saka yace naje,ƙarshe ma ina jin sai na yi gagarumar gaba da mutum dan maƙiyina ne kawai zai ce naje bikin Yaya Halil,abun da yake ɗaure mun kai shine yadda ya samu mata cikin wata uku,sai na barshi kan dama tun muna tare yana neman ta,idan har ni na cucesa ai Ubangiji yana ji kuma yana gani zai saka mishi,idan kuma shine ya mun haka da gangan yaje zai gani.
Suna fita na koma na kwanta ,ni kaɗaice a gidan Muhammad Adavize ya wuce hadda,bacci shine kawai abin da yake cire mun tunani a yanzu.
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔
𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎
Na
𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay
E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟ 12.Babysitting
*𝘈𝘕𝘐𝘚𝘈*
Ta rasa ina zata tsoma ranta saboda irin farin cikin da take ciki,zata iya cewa rabon da ta jita cikin farin ciki irin Wannan har ta manta,tana jin Enen na bawa Yaya Halil labarin abin da ya faru da sukaje gidansu Zunairah Sannan da zoben da ya bata wai na ajiya,a yadda Enen ta ce wai sun ɗauki abun da sauƙi ta san ƙarya suke ita ai ta san komai ta tabbata Zunairah na chan cikin halin tashin hankali,shine abin da take nema,idan tana tunanin zata mata soyayya da Yaya har a kai ga Aure to tayi ƙarya,sai dai idan har bata raye ne za ayi wannan ta'asar.
Cikin faɗa Enen ke cewa"nan haka kazo ina zaman zamana kace mun soyayya ku ke kai da ita ashe tsiyar da kake shiryawa kenan,wallahi naji kunya,dan kawai ka san ba zan maka dole bane shi yasa kayi mun haka"
"Yanzu dai ai ya wuce Enen tunda mu dasu muna kan yarjejeniya ɗaya,i told you kuma ina kan matsayata ni da Zunairah abota muke".
Ganin yadda ya ƙarbi zoben cikin karamar zuciya ya saka yana tashi ta bi bayansa ,yana ƙoƙarin shiga ɗakinsa tayi Saurin kiran sunansa,juyowa yayi ya kalleta ,idan bata yi ƙarya ba wallahi hawaye ta gani a fuskarsa,da Mamaki ta ce"Yaya Kuka kuma?Yaya Zunairah fa bata cancanci hawayenka ba,duk Halin da take ciki yanzu gwara ta shiga data jefaka a halin da gaba zaka zo kana danasani mara amfani,ga Aunty Zainab yarinya yar gidan mutunci beside babanta malami ne I'm sure ka samu matar da duk inda akaje aka dawo yaranka za suyi alfahari da kai ka sama musu uwa ta gari,Annabi ma yace....."
"Kin gama?"ya katse ta ,da ƙwalaƙwalan Idanunta ta ke binsa tana mai zazzaresu ganin ya zuba mata nashi,"idan kin gama ki wuce ki bani guri kada ki sake zuwa gurin nan ki ce zaki mun wani wa'azi bana san iskancin banza da munafurci".shiga ɗakin ya yi ya banko mata ƙofa,taɓe baki tayi ta bar gurin,ya yi ya gama ta san ƙarshe abun zai zama labarin tunda gashi nan ai babu wanda ya sama masa Zainab,shi da kansa ya nemota,duk yadda taƙi jinin haɗa Aure da Hausawa gwara su sau dubu da situation ɗin da yake nema jefata na Zunairah.
Kafin kace mene ta fara nuna damuwarta ainun dan kuka sosai ta zauna tana Yima Enen lokacin da taji an fara maganar Auren Halil,dama shi da Zainab sun taɓa soyayya shi yasa da ya koma bai wani sha wahala ba aka daidaita,cikin wata guda aka gama komai aka saka Auren,koda Enen ta tambayeta tsakanin Halil da zunairah ita da kanta ta faɗa mata soyayya suke wanda hakan ya saka Enen shiga damuwa amma da ta sake tambayarsa sai ce mata yayi shi abota suke ita ta ɗauka da wani abun,sarai Anisa ta san halinsa idan ya kafe a abu guda ɗaya musamman idan yaji kamar an yaudaresa baya juyawa yana da taurin kai ta wannan fannin ,ta san a yanzu ma kan batun Zunairah yadda ta bashi babban Blow babu yadda za'ayi ya Aureta ya sake yarda da ita ,makamin da tayi amfani dashi da shine zata cigaba da cin yaƙinta muddin ba na ƙasa da su sosai Zunairah ta kawo matsayin miji ba.
Lokacin da Khalipha yazo da biyu ta dinga manne mishi dan tana so Zunairah ta ji kwaɗayin soyayyar da ke neman ƙwace mata kafin ta ƙwace mata , Sannan wai dan raini ita take ma nasiha kan tana mannewa Khalipha, ta riƙe kanta ne bata kifa mata mari ba amma aje zuwa ,sai tayi mata raunin da bata taba tunanin zata mata ba,sai ta fita ta ko'ina a nan ne zata fito fili ta faɗa mata itama zata iya abun da yafi wanda ta iya.
Anisa ce har da zazzaɓi idan ta shiga ɗaki zata lafe tayi ta kuka Hibba kuma zata ruɗe ta kira Enen su zauna suna ta bata haƙuri a haka har ta kwana biyu kafin ta saki jiki.
Ranar da ta zagayo bikin Yaya Halil maimakon ta zauna a gida ayi da ita sai take jin babban bikinta yana gidansu Zunairah a matsayinta na Aminiyarta yaci ace ƙwana tayi gurinta tana dannar mata ƙirji,amma kuma idan taje ta ƙwana ya zama bata ji kunyar yaudarar da yayanta ya yi mata ba,ya kamata ace a zahiri taji kunya sai wasan ya tafi dai dai.
Koda ta faɗama Enen zataje ta dawo bata damu da sanin inda zataje ba musamman yadda gidan ya cika da yan uwansu da suka zo daga Benue chan ƙauye ,kai tsaye gidansu Zunairah ta nufa,koda taje su mama na ƙoƙarin fitowa tayi tsammanin ba zata samesu ba,da fari raɓeraɓe ta fara amma ganin yadda mama ta tarbeta sai abun ya bata Mamaki,ta fahimci inda zunairah ta tsotsi munafurci, Hauwa'u ce kawai bata sake mata fuska ba dan da tayi mata magana ciki ciki ta amsa mata ,dama tana cike a ita da ta tsinkayi tana faɗawa Zunairah ta rabu mata da Yaya,itafa dama tuntuni ba wani mugun san Anisa take yi ba Saboda Auntynta ya saka take dannewa amma ai ba sai anfaɗa mata Anisa nada zubin munafukai ba ko ƙwalaƙwalan Idanunta zasu faɗa maka ,tayi ta wani zuba su tana kallon mutane.
"Anisa dama baki damu kan ki ba kinyi zamanki gida biki fa ku ke yi, Zunairah kuma ƙalau take tana ɗan fama da ciwan kaine ƙwana biyu shi yasa ma baza ta je bikin ba"Mama ta faɗa lokacin da Anisa tace wai ta zo ta zauna da Zunairah.
Cike da makirci ta ce"Mama na san abin da Yaya Halil ya yi ba kyauta ba amma dan Allah mama kada laifinsa ya shafeni,ba zan iya cigaba da mu'amala mai kyau ba idan har ku ka nisantani da Zunairah,zafinta nawane ,daɗinta nawane,na san komai Mama koda su Enen basu sani ba,babu abin da muke ɓoyema juna ni da zunairah tabbas soyayya mai ƙarfi suke da Yaya ban san mene ya saka ya yi mata wannan yaudarar ba,shi yasa ba zan iya zama bikinsa ba sanin Zunairah ta fi buƙatata a yau fiye da kowace rana"ta ƙare zance tana mai sharce ƴar ƙaramar ƙwala wadda ta kashe jikin Mama,bata iya hanata ba tace mata ta shiga ɗaki ta sameta su zasu wuce.
Ita ta kulle ƙofar gidan kafin ta nufa ɗakinsu Zunairah ,ƙwance ta tarar da ita tana bacci,bata tasheta ba ta zuba mata ido tana kallon yadda ta rame,cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ta ji karayar zuciya tana mai jin dama bata san Zunairah ba a rayuwarta da bata mata abin da tayi mata ba,lokaci guda kuma wani bangare na Zuciyata ya sake tunatar da ita,tunda ta santa babu damar chanza baya ko yin nadama.
*𝘡𝘜𝘕𝘈𝘐𝘙𝘈𝘏 𝘗𝘖𝘝*
Cikin bacci naji kamar ana kallona,buɗe ido nayi na sauke kan Anisa,komai sai ya dawo mun sabo dan gani nayi kamar shine a gabana,zuba mata ido nayi sai kace wadda nake neman amsar wani abu a fuskarta,itama ɗin kallona take batace komai ba na ɗan wani lokaci Idanunta sun fara kawo ruwa,saurin kawar da kai nayi gefe ina mai rumtse Idanuna da hawaye suka gangaro daga cikinsu suka sauka bisa ƙuncina,daga ƙwancen da nake ta ƙwanta kan cikina ta rungumeni tana mai fashewa da kuka ,bana da zaɓin da ya wuce na tayata domin cikin satin da ya gabata bana da aikin da ya wuce kuka ,cikin kukan take faɗin"mene zan Miki na cire ciwon da yaya Halil ya ji miki a zuciya?".
Ban iya cewa komai ba sai kuka da nake tayi kamar raina zai fita,sai da nayi iya gajiyata kafin na iya yin shiru ,shima dan ana gajiyane amma fa ba zan gaji dana Zuciya ba,ruwa dana nema ya sa ta tashi taje ta ɗauko min sachet water ,koda ta dawo na tashi daga ƙwancen danake na zauna na jingina bayana da pillow,wani irin ciwo kaina yake yi, paracetamol da ta gani kan bedside ɗin mu ta ɗauko ta ɓalla mun tana mai cewa"na san kan ki yana Miki ciwo,amma tukuna kin ci abinci?".
"Bana jin yunwa"
Zama ta gyara tana mai aje ruwan kafun ta ce"Zunairah kan namiji ki ke san ki kashe kanki ko kuwa menene?ya nuna baya sanki bai damu dake ba ,ya ci amanarki ya yaudareki akan mene zaki zauna ke ki illata kanki?koda kin mutu fa ina so ki sani kece ki ka mutu shi tarewa zai da matarsa babu abin da ya damesa,dan Allah kada ki jama kan ki ciwan da Namiji bai cancanta ba".
"Yanzu shikenan Anisa sai kawai na rabu da yaya Halil?kin san yadda nake ɗaukan soyayya na ɗauki Yaya Halil da girma na bashi dukkan yardata,na bashi dukkan zuciya mene nayi mishi mai muni da zai saka mun da haka?wallahi babu abin da na yi mishi na yi tunani na duba ban gani ba"na ƙarasa ina mai jan majina ina share hawayena.
"Namiji kenan Besty sai ki bashi duniya idan ya tashi ya zuba Miki wuta ki ƙone ki mutu,idan baki damƙi kanki ba Mission ɗin Yaya Halil kenan ,ni dai fatana ɗaya Zunairah Allah yasa baki bashi jikinki ba".
A yadda na zabura ko ban bata amsa ba ta san maganar ta dakeni,wani irin kuka na sake fashewa dashi ina cewa"shikenan abin da wasu zasuna faɗa kenan,amma Anisa ke kin fi kowa sanin halina,duk zafin soyayyar da nake ma namiji ba zan taɓa iya bashi jikina ba mene ya saka wannan zai ɗarsu a zuciyarki?haka ake faɗa a gidanku ko? wallahi babu abin da muka taɓayi ko taɓa hannuna ban taɓa bari ya yi ba ki tambayesa Indai akwai saura imani a zuciyarsa ba zai mun sharri ba".
Ganin yadda na ruɗe lokaci guda ya saka ta rungumeni tana kuka tana bani haƙuri tana cewa ta yarda dani ta tambayane kawai saboda tsoron abin da zai je ya dawo.
Cornflakes ta ɗauko a kitchen ta haɗa mun , kaɗan nasha,shima sai da tayi ta mun magiya sannan,maganin da ta ɓalla mun nasha,tanata lallashina kamar karamar yarinya,Anisa na sona,Nima ina santa bazan bari abin da Yaya Halil ya yi mun ya ɓata tsakanina da ita ba,na saka hakan a raina,ga wani irin girmanta dana ƙara gani,ban tsammanin zata iya barin bikin yayanta tazo kula dani ba har ta goya mun baya.
"Mene ki ke ta kallona?I hope ba tunanin Yaya kike ba?"ta tambaya tana mai nufar mudubinmu ta ɗauko kibiya da mataji a gurin da muke ajewa.
"Kawai ina jin daɗi da Allah ya bani ke matsayin ƙawa,ina jin daɗin yadda ki ke nuna damuwarki kaina, Nagode Allah ya bar mu tare ya tsarkake alaƙarmu"na faɗa ina murmushi,tunda aka fara abun nan sai zuwanta na samu nutsuwar dana samu na amayar da abin da yake raina.
Murmishi tayi ta fara mun tsifa tana cewa "kada ki manta kafin Yaya Halil ya zama ɗan uwana Namiji aka fara haifarsa,dan haka zan zaɓeki a kowanne irin situation domin kafin na zama ƴar uwarsa mace aka fara haihuwata,Kinga kuwa babu yadda za'ayi kina mace ina mace na zaɓi ɗan uwana Namiji daya cutar dake dan kawai yana ɗan uwana,ba'ayin rayuwa a haka ko nace bana rayuwata haka because akwai masu zaɓan ɗan uwansu,amma ni i choose you,so chill kiyi kukanki yadda ki ke so kina da kafaɗar ɗora kai,I'm sorry lokacin Ma'aruf we were just minors ban iya baki kulawar da ya kamata ace na baki ba,but in tambayeki mana,da Yaya Halil da Ma'aruf wane yafi baki one blow seven die?".
Dariya na saka wadda na ɗauka ba zan ƙara ba,Anisa kenan a duk halin da ake sai ta samo abin da zatayi da zai sakani dariya.
Ban bata amsa ba itama ta tayani dariyar tana dawo da lokacin da nayi ta kuka Ma'aruf ɗin da zan Aura ya yaudareni,har cewa mukayi lokacin zamuje gidansu dan hauka,Anisa kuma na faɗin sai ta saka yan zaman banza sun karya mata shi ta basu kuɗi ,a wannan zagayen koda zuwan da tayi ta zauna da ni kawai ta barni dashi na gode mata it means alot to me .
Tana ƙarasa tsefe mun kitson karshen cikin huɗun dake kaina wayarta ya hau ruri,tana ɗagawa Muryar Yaya Hibba ya bayyana tana cewa"Anisa an ɗaura Auren gashi tun ɗazu Yaya Halil na nemanki ".
"Nayi Mishi mene?kice nace Allah ya sanya Alheri ni nayi nisa"amsar da ta basu kenan ta kashe wayar tana mai cigaba da mitar da ban taya ba,shiru kawai nayi amma a Zuciyata tunanine kala kala,na kasa yarda wai Yaya Halil ya yi Aure da wata ba