Author : Chuchujay Category : Romantic Hausa Novels
dani ba,Yaya Halil dai danake kira ,Baby Habibi,Ina san Sanin mene nayi mishi ya yi mun wannan ɗanyan hukuncin mai firgici,sanin koda na tambayi Anisa ba sani tayi ba ya saka ban tada zancen ba nayi shiru ina auna yadda zanyi dakon wannan cin amanar da ya ziyarceni.
Haka muka wuni tare ba ita ta tafi ba sai da Mama suka dawo da Magrib,shima sai da Mama tayi da gaske dan a cewar ta kwana za tayi dani,da ace zata kwana ɗin dana so duk da nasan buƙatata zatayi yawa,bai kamata na kasance mai san kaina ba,tun fari ma bai kamata ace tazo ta bar bikin gidansu ba tunda dai kafin na zama ƙawarta Yaya Halil ne ya fara zama ɗanuwanta dole kuma ya zamo gaba dani.
Da dare kowa ya zauna cin abinci nima na fito daga ɗaki,babu wanda ya yi mun wata tambaya ,zama nayi gefen Hauwa'u dake aiki washe baki,Shinkafe ce da miyar Alayyahu Mama tayi mana,tare dukka muka haɗu a babban tray ɗin da muka saba cin abinci,Mama na saka Mana Nama Hauwa'u tayi saurin ɗaukar nata ta ƙara a nawa Muhammad ma ganin abin da tayi ya saka shima ya ɗora nasa a kan nawa,murmishi nayi nace"to idan na cinye namanku sai kuci mene ?".
"Dukkan satin da ya wuce mu muke cinye naki ,yau ki ci namu"Adavize ya faɗa,kafin na sake magana Baba da Mama sun basu nasu ,murmishi nayi ina mai danne hawayen dake san ƙwace mun kafin na ɗauki naman na ci,kafun na ƙwanta Anisa ta kirani tana mai sake tambayata anya ba sai tazo ba domin ta kasa cire tunanina da halin da nake ciki.
Dariya kawai nayi ina mai cewa"I'm not suicidal Besty,ba zan kashe kaina ba ,na yarda da ƙaddarar da ke tare dani a yanzu ". hira ta ɗanyi mun wadda ta sakani nishaɗi dan labaran da ta bani sun sani dariya,yan gidanmu ma sun shaida dan saida Mama ta shigo taga da ita nake waya,ikon Allah kenan Yayan ya dasan ciwo ƙanwar ta zamar mun Magani
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔
𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎
Na
𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay
E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟ 13: newlyweds
*𝘏𝘈𝘓𝘐𝘓*
Shi ɗaya zaune ya nutsu yana kallon zoben Zunairah kamar yana karatun wani abu a jiki, jin an fizge ya saka shi ɗagowa yana kallon wadda ta raina shi cikin gidan da ita kaɗai zata iya fizge wannan zoben.
Washe baki tayi ganin Z a cikin zoben ,cike da zumuɗi ta zura a hannunta tana ma cewa"Tuntuni Halil ka bani zoben na mene ka ke jira?".
Daga zaunen da yake ya taso ya kama hannunta da ƙarfin tsiya ya cire yace"ai kinfi kowa sanin ba naki bane,bana san irin abin da ki ke mun Zainab".
"Aw ashe baza ka cire wannan shegiyar yarinyar a zuciyarka ba ko Halil?,to wallahi ko ni ko kai a gidan nan,dan Ubanka idan kana ganin za kayi Auren Zaɓi biyu dani kayi tunanin zaka ƙuntata mun bayan nan wallahi sai dai mu ƙuntatawa juna"
Juyowa ya yi ya daskare a gurin yana kallonta"dan Ubana?"ya maimaita cike da mamaki,juyawa tayi ta bar gurin tana gunguni,saboda tsabagen Mamakin da ta shayar dashi bai iya yin komai ba illa bin ta da ya yi da ido har ta shige ɗaki,wai dan Ubansa,kalmar nan ta samu gurin ta toƙare mishi wuya,shin mene ya jefa kan sa shi kam?
Tunda yau Auri Zainab yau sati biyu kenan ya kasa gane gabanta balle bayanta,zai iya cewa sun yi zaman ƙwana goma lafiya although suma ƙwanakin tana ta aikin yaɓa masa magana dan kawai lokacin da suke tarawa ta Auratayya a daren farko su ya kirata da Zunairah,babu irin lallashin da bai mata ba sanin shine baya da gaskiya kuma ya ɗauka amma ta ɗauki abin ta riƙe a zuciya take ta tafka rashin mutuncinta yadda take so,koda yan uwansa na ƙyauye suka zo halin ko in kula tayi dasu amma basu ɗauki abin komai ba a cewarsu baƙunta ne amma shikam sarai ya san iskanci ne.
Yayi soyayya da Zainab sosai kuma ya sota abin da ya raba su shine kule kulen samari da kuma rashin iya magana,da fari ya zata zata bari amma ganin abun gaba gaba yake ya saka suka samu nesantuwa da juna,ranar da ya rabu da ita baki ɗaya shine ranar da yaje zance gurinta wani Alhaji yazo tace dashi wai ya jirata,kamar a mafarki ta nufa gurin Alhajin ta shiga motarsa yana tsaye yana mamaki.
Cikin son ya ga ƙarshen ƙarya ya jirata,sai da tayi wajen awa guda yana wajen yana jira kafin Alhajin ya tafi Sannan ta dawo gurinsa ,"kayi haƙuri kawuna ne"shine abun da kawai ta ce mishi ta cigaba da juya rafa na kuɗi daya bata,
"To"yace mata ya shiga motarsa ya tafi bai kuma waiwayenta ba itama kuma bata damu ba sanin soyayyar ta da Halil kamar Tururuwa da gida ne duk inda taje zata dawo ta shiga ta ƙwana,ta sani zai dawo dan dama haka faɗansu yake ,zai daɗe kamar ba zai dawo ba daga bisani kuma sai ya dawo ɗin.
A wannan zagayen ganin ya daɗe bai dawo ba ya saka ta fara bibiyarsa ,nan take tsintar soayyarsa da Zunairah,ta damu dan har ta fara yanke tsammani,kwatsam sai ga kiransa wai zai zo gidan su,bata wani ja mishi Aji ba musamman a lokacin da take neman miji gashi kowa da take kulawa babu na Aure babu ma wanda zata kira tace ya zo su yi Aure ya amince,Zainab yarinya ce da ake kira da Yar malam taƙi halin Malam,Ƙaddarar za suyi Aure ya haɗasu a wurin dinner na abokinsa.
Bai wani ja mata rai ba ya kawo maganar Aure inda babu ɓata lokaci tayi na'am da hakan,basu wani yi bincike mai kyau ba,binciken da sukayi ɗaya ya nuna musu Babanta Malamine ,kuma Malami a irin Matsayinsu dan shine babban Malamin Sanata Hadi madugu,babban Sanata a wannan yankin,sannan yana harka da manya yan siyasa,baya da wani abu da zai ɓatashi,hasalima yana cikin mutane mafi kima a unguwar ,a nasu tunanin indai ƴa tashice ai kamar an tsinci dami a akala ne.
Duk da shi ya kawo maganar Zainab amma dai Daddy ya fishi zumuɗi Ganin haka ya saka ya basu wuƙa da nama,Yana san Zunairah ba zai ƙaryata ba,yana mutuƙar santa fiye da yadda bai taɓa tunanin yana yi ba amma abin da Anisa ta nuna mishi ya danne dukkan wannan son ya rufe mishi idanu,babban abin da ya fi komai ɓata mishi rai shine yadda take kallonsa take mishi karyar ita ta Allah ce,ya riga ya saka ma ranshi ta yaudaresa tayi mishi ƙarya dalilin da ya saka ya yanke hukuncin da a yanzu yake ganin bai bi a hankali ba,ace Amaryar sati biyu har ta fara kallon Ango ta zagi ubansa?
Yanayin duk yadda ya kamata ganin ya cire Zunairah a zuciyarsa duk da ta kama kamar danƙo amma a koda yaushe tunaninta shine ke hana mishi sukuni,yana san ya yi rayuwa da Zainab ya bata dukkan kulawarsa ko hakan zai rage mishi wani abun amma ya kula ga dukkan alamu bata san su zauna lafiya.
Juyawa ya yi ya fita a gidan,bai ankara ba sai tsintar kansa ya yi a bakin layinsu Zunairah,daga Chan ya faka motarsa yana mai tuhumar kansa kan mene yazo yi nan ɗin?.Yana ƙokarin yiwa motarsa key yaga ta fito daga gida da wata mata,duk da daga nesa kaɗan yake hakan bai hanasa ganin yadda ta faɗa ba,murmishi take tayi matar nayi mata magana ,saurin ƙasa ya yi da kansa ganin sun nufo gurin da yake inda take kallon cikin motar,yama manta Tint ne glasses ɗinsa,duƙawa tayi bakin mirror ɗin motar tana mai gyara fuskarta Inda take faɗin"Aunty Muna ko ƙwalli ban saka Bafa kalli idona kamar Nama".
Kamo hannunta Aunty Muna tayi tana mai cewa"muje haka dai yau ai sai kin rakani bikin nan,kin zauna a gida kamar wadda ke takaba,ai kuwa yau sai na karya Wannan sirri sai munje, kizo mu wuce kafin mai motar ya fito daga inda ya shiga yaciki tarar kallan masa mudubi bada izininsa ba"
Dariya tayi ta ɗaga tana mai cewa"aikuwa duk wanda zai aje motarsa a nan gurin nisa yayi"da haka bai sake jin abin da suke faɗa ba Aunty Muna ta ja hannunta suka wuce,juyawa yayi yana kallonsu har suka sha ƙwana,rumtse idanunsa ya yi yana mai jin ƙwalla na fito masa,da ƙar ya iya kama kansa bai fito ba,dan ji yake kamar ya fito ya ɗauketa su bar nahiyar baki ɗaya su manta da wani abu ya faru tsakaninsu,su manta da komai sai soyayyarsu ita kaɗai ta zama abun da suka sani.
Bai san ya yi ƙewarta ba sai da ya sake ganinta,Anya abin da ya yi mata ya kyauta?ya kamata ace ya tunkareta ,amma a yanzu ya sani hakan baya da amfani,ya san da ace ta san shine cikin motar ba zata taɓa koda bin inda yake ba, babban dalilin da ya saka ya sake mota kenan dan ya sani a yanzu shine zai zama number 1 stalker ɗinta .
A haka ya tsaya yana tunanin da baya da amfani kafin daga bisani ya tashi motarsa ya nufi gida,gashi dai ya ɗauki hutun wata amma hutun baya da amfani kamar yadda ya zata zai mishi.A falo ya tarar da Enen da Hibba suna kallon TV show,Sallama ya yi musu kafin ya shiga ya zauna ya gaida Enen,da mamaki ta ce"Halil lafiya dai ka fito gida da wuri haka?".
"Mu da muketa saurin mu iskeka gida ni da Anisa"Hibba ta ƙara tana mai kallonsa.
"Well yanzu ma ai sai na aje ku,dama na fito ne na gaishe da su Enen,Daddy fa?".
"Daddy kam ai ka san ba zaka sameshi gida a wannan lokacin ba ya fita, fatan Zainab ɗin tana lafiya".cewar Enen.
", Álhamdulilah tana gaisheku kafin na kawota".
"Yayi bari su gama ɗin sai ka aje su".
Tashi Hibba tayi tana faɗin zata je ta kira Anisa itama ta ɗauko jaka da Mayafi,kallonsa kawai Enen take ,ta sani akwai wani abu dake damunsa duk da bai faɗa ba ,duk da bata tunanin matsalar ta gidansa ce tunda dai ai baza ka haɗa Angon sati biyu da matsala ba.
Sallama ya yi mata suka wuce ,tun a mota yake san magana da Anisa ,sai da suka isa Hibba ta fita, Anisa na ƙokarin fita ya ce"Anisa kin haɗu da Zunairah kuwa?".
Juyowa tayi tana kallonsa"Yaya ba dai tunanin Zunairah ka ke ba?Yaya zunairah ba sanka take ba, hasalima cewa Mamanta tayi kamar yadda na ɗaukeka Yaya haka ta ɗaukeka kuma wallahi na yarda da abin da tace ɗin yaudara kawai take maka,ka Auri Aunty Zainab and na tabbata kayi dacen macen da zata goge maka duk wani tabo da Zunairah ta ji maka,Forget about her and move on"tana Kai ƙarshen maganarta ta buɗe motar ta fita tana Allah Allah kada ya sake biyota ya dameta da maganar wata Zunairah.
Koda suka shiga a falo ta tarar da Hibba zaune ,da Sallama Anisa ta shiga ,ganin Hibba ya saka tace "Yaya Hibba ina Auntyn namu?".
"To nima dai nayi Sallama amma bata amsa min ba shine na zauna na jira Yaya Halil ya shigo sai ya shiga ya yi mata magana".
Baice musu komai ba ya nufin ɗakinta,ƙwance ya tarar da itana danna waya tana dariya,da mamaki yace"wai zainab bakiji ana sallama a Falo ba?".
Bata kallesa ba ta ce"naji so kake duk wanda yake sallama na tashi da gudu ina rawa ina guɗa na ɗauka na goya?kaga nifa Halil duk wannan abin da kake ban bika da gudu ina ihu ina cewa ka Aureni ba fa,kada ka tada mun hankali,ai wallahi ka taro Bala'i tunda ka kira sunan karuwa kana kaina,a danginku ka ware mun Wanda ba algungumi ba".
Wani irin abu ya ji ya zo ya tukare mishi wuya,wai shi Halil Zainab ke ciwa mutunci haka,tabbas idan ya biyewa zuciya sai ya mata shegen duka wanda abu ne da baya fata.
Gyara tsayuwarsa ya yi yana mai kallonta kana ya ce "kinji na rantse idan baki tashi kin je falon nan kin tarbi baƙi ba zan Miki shegen duka,wallahi sai dai a yar da abin kunya,zan Miki matsiyacin duka wanda baki tunani,dama ai ina ciki dake na zagina da ki ka yi,yanzu ba sai anjima ba ki tashi ki fita ko kisha Mamaki".
Sheƙeƙe ta kallesa kafin ta tashi tana mai gatsine baki,"dama ai ance mun mazan Edoma na dukan mata kamar jakai,to wallahi baza ka fara a kaina ba,kwalelen kare da roman Jaka".
Fita tayi tana wani kaɗa masa jiki,ya rasa mene yake damun Zainab,idan da za'a tambayesa mene hakan wallahi bai san mene zaice ba,yarinya sai rashin kunya kamar yar ƙwaya.
Bin bayanta ya yi,tana isa falon ta ruga da gudu gurin da Hibba ke zaune dan har sai da ta tsorata Hibba,hannu ta saka ta janye ta da ƙarfi ta ɗauki throw pillow ɗin da Hibba ta jingina dashi tana karkaɗewa kamar kashi ya taɓa "what sort of madness is this,baku san idan kunzo gidan mutum ba ku nemi izinin kafin ku fara taɓa masa abu,and who even asked you guys ku zauna mun bisa kujeru?"
Sheƙeƙe suka yi duka suna kallonta domin ba haka suka yi tsammani ba,Anisa ce ta waske tace"ina Kwana Aunty".
"Da ban kwana ba zaki ganni?bana san munafurci irin na dangin miji fa,mene? meye ya faru?,idan abinci ne ku ka zo ci yana kitchen kuje ku dafa kada yarinyar da tayi tunanin zata zo nan baligun da ita nayi mata girki ".
Duk yadda ya so ya ɗauka ,duk yadda ya so ya cije sai da ya tsinci hannunsa bisa fuskarta, wani irin zazzafan Mari ya zuba mata mai ratsa ƙwaƙwalwa,lokaci guda dukkan gurin ya ɗauke wuta,bai iya cewa komai ba haka su Anisa duk sun mutu a zaune,dafe gurin tayi sai da Marin ya kai mata iya kaiwa kafin ta fasa wani uban ihu mai ratsa kai kafin ta zube a gurin ta fara buge buge,kafin suce kwabo ta banƙare kamar yadda halittar kwaɗo yake da yadda yake jan ciki ,a tare suka haɗe guri guda cike da Mamaki,jan ciki ta fara ta nufosu tana wani irin kururuwa tana cewa "kun taɓa mana goɗiya,yau kowa sai ya mutu,yau za ayi gawa Uku, wayyo Bala'i ".
Ganin da gaske gurinsu take zuwa ya saka suka ɗiba a wani na kare baki ɗayansu suna masu gogar juna suka fita a falon, window ɗin motarsa Anisa ta fara ɗaga ƙafa kamar zata haura tana faɗin lailahaillahanta subhanaka inni kuntu minnazzalumin.
Ganin ta gigice da yawa ga Zainab har tazo bakin kofar Falo ya saka Halil fincikota kamar baby ya mara bayan Hibba wadda har ta kai bakin gate.
Datso kofar ya yi,Allah ya saka a Aljihu ya saka mukullensa,key yama gidan ya duƙa yana ajiyar zuciya.
Dan suna da yadda da abubuwa da yawa ,irin su Ojuju,spirits duk da ba garinsu suka tashi ba amma labari yana tsoratasu dasu dan kawunsu har yanzu yana ƙauye yana fama da sharrin evil spirits, although sun san Aljanu da zasu gani jikin mutum da sauƙi amma basu taɓa ganin wani ya yi gabansu ba sai Zainab.
"Yaya ƙwado fa ta zama"Hibba ta faɗa da mamaki har a lokacin tana haki.
Anisa kuwa ba baki burinta guda ɗaya ta ganta gida amma gashi ta manta Jakarta da takalminta, wayarta kuma na ciki da babu abin da zai hanata tafiya,ita da gidan Yaya Halil kuwa sai ta Allah amma ba da ita ba dan har Zuciyarta ba wasu Aljanu suka faɗo mata ba ,kawai Matar yaya Halil tana cult ne,idan ba haka ba ta ina mutum zai iya banƙarewa ya koma kamar ƙwado?ajiyar Zuciyar da ta sauke ya saka suka kalleta a tare kafin suka ƙwashe da dariya.
Cike da rashin fahimtar inda dariyar tasu ta dosa ta ce"mene kuma abin dariya?".
"Kece mana Anisa ,da ki ke bin window ina zaki shiga?"Hibba ta faɗa tana sake ƙwashewa da dariya.
"Yaya Hibba bafa abin dariya bane wannan,matar nan is possessed,kina ji tana zata kashe mutum amma ki ke dariya?ko nace ku ke dariya?thank God ba gidan zan ƙwana ba Yaya Halil ka cigaba da biyeta kai zaka ƙwana ciki".
Dariyar suka cigaba dayi wadda ke mutuƙar bawa Anisa Mamaki,kamar yadda ta faɗa ita fa bata ga abin dariya ba.
Mintuna mara sa yawa sai ga Yayar Zainab da Babban yayanta da ya kira sun zo,Halil ya fara ganinsu,Nadiya Yayar Zainab ta fara kula da ƙafar Halil babu takalmi,kafin kace mene ta kece da dariya,yayan da ya fito ne yaga ta sheƙa dariya.
"Ke lafiya ki ke dariya?".
Nuna ƙafar Halil tayi ta ƙara fasa dariya da ta kula Hibba ce kawai mai Takalmi,abin mamaki shima yayan goɗaigoɗai dashi wai sai ya fasa dariya har da riƙe ciki,sai su abin ya daina basu dariya kar ma ace Halil da yake wa Yaya Yunusa kallan mutumin kirki.
Ita kuwa Anisa ai burinta bai wuce ta bar gurinba dan ta fahimci gidan mahaukata Yaya Halil yaje ya samo mata,atleast if not Zunairah ya samu wadda ta fita Mana.
Basu iya gaishesu ba Yaya Yunusa yace ya buɗe gidan,buɗe musu ya yi suna shiga ,yana ƙokarin bin su Anisa ta ce"Yaya ka miƙo mun kayana ni gida zani".
"Ni zan aje ku,if not ki shigo ki ɗauka da kan ki"da haka ya shiga gidan Hibba na binsa a baya ,ita kuwa Anisa guri ta samu ta tsaya tana jiran su fito dan baza ta shiga ba,da suka shiga zaune suka tarar da ita bisa kujera tana danna waya,Yaya Nadiya na ganinta ta ƙwashe da dariya, ɗagowa Zainab tayi tana kallonta kafin da murna ta tashi ta rungumeta ta ce"Aunty Nadiya Oyoyo,Yaya harda kai? Har na fara tunanin fushi daku wallahi".
Abun sai ya zama kamar a Film,one minute tana nan tana musu ƙwaɗo tana faɗin zasu mutu,one minute yan uwanta sun zo ta tashi kamar ba ita ba, bai kuma cewa wani abu ba ya ɗauko tarkacen Anisa ya kama hannun hibba da ta ɗauki jakarta itama suka fita,yana jin Nadiya na mishi magana ya musu banza ya fita yana jin ɓacin rai.
𝘊𝘩𝘶𝘤𝘩𝘶 𝘫𝘢𝘺✍️
08130229878.
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔
𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎
Na
𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay
E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟ 14:Moving on
*𝘏𝘈𝘓𝘐𝘓*
Bai tashi motar ba baice komai