Chapter 3 Reading Cin Duniya Book Compelet Hausa Novels By Chuchujay Arewa Novels

Cin Duniya Book Compelet Hausa Novels By Chuchujay

Author :  Chuchujay Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   3 / 16

6K to 9K   out of 45.5K words

ya ce zai Aureki?".

"Eh".

Wani dariya tayi ƙarama kafin ta tashi ta zauna ta kamo hannun Hibba."yaya Hibba you deserve better than Yaya Adam, he's a user and definitely yana using ɗinki ne kawai dan ya biya ma kan sa buƙata amma there is no way on earth da Yaya Adam zai yarda ya Aureki bayan kin bashi jikinki,wallahi ƙarya yake,I'm not judging you tunda abin da ya faru ya riga ya faru amma gaskiya ki fita harkarsa If not zaki barni da rashin zaɓi na faɗawa Enen".
"Insha Allahu ba zai kai nan ba ma Neesa na rabu da shi I'm sorry".ta faɗa cikin zaƙuwa da san Anisa ta yarda da ita amma babu ma yadda zai iyu ace wai ta rabu da Adam zadai ta zama careful gaba kada a sake kama su."
𝘊𝘩𝘶𝘤𝘩𝘶 𝘫𝘢𝘺✍️
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔

𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎

Na

𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay)

EPISODE 4:when life gives you tangerine

*𝚉𝚄𝙽𝙰𝙸𝚁𝙰𝙷*

Kamar da wasa muka fara zana jarabawa har ya kai da muna kan rubuta tourism paper ɗin ƙarshe,dukkan yan set ɗin mu kowa uniform ya sha guga ga graduation gown da muka sha Sky blue jira kawai muke mu gama muje mu haɗu da iyayenmu dan ko ni tare muka zo da Baba da Mama,dama su Hauwa'u an basu hutu, Theater Hall ya sha decoration inda nan aka aje iyayen Yara inda mu kuma muke jarabawar ƙarshen mu cikin Rehearse Hall,baki ɗaya papers ɗin a Theater Hall muka yi kasancewar ya fi girma da ya zamana kuma za'ayi amfani da shi sai aka gyara mana Rehearse dan mu yi a ciki.

Zumuɗi kawai nake da murnar da ya saka ina gamawa ban tsaya wani Cross checking ba nayi submitting,dama Tourism ba wani wahala ne da shi ba,ina fita Anisa ma ta fito,cike da wani irin ihun murna muka rungume juna muna masu faɗin"we are graduates"

Sir Umar Ali ne ya leƙo yana mai faɗin"Mss Buhari and Ms Ibrahim I'm sure kun san wasu basu gama exam ba,so I will appreciate it idan ku ka samu guri ku ka zauna har yan uwanku su fito ku yi making entrance cikin Theater Hall as real graduates".

Ƴar dariya muka yi a tare kafin muka samu guri muka zauna hannunmu cikin na juna ,cike da zaƙuwa Anisa ta ce"best farin ciki nake wallahi na kasa yadda wai yau zamu bar bright scholars,and guess what yau har da Yaya Halil aka zo mun".

Ganin yadda take ta giggling ya tabbatar mun tana cikin farin ciki ɗin har zuci musamman batun zuwan Yaya Halil, he's always absent duba da yanayin aikinsa gashi Anisa na masifar ƙaunarsa kamar ranta.

"Gaskiya dai Yaya Halil ya kyauta da ya samu zuwa"na faɗa ina mai tayata murna.sake damƙe hannuna tayi tace"girl I'm beyond happy,ai ya sani na faɗa masa idan bai zo ba wallahi sai bikinsa zan tsiro zuwa ƙauye,matarsa kuma bani babu ita ta kuma haɗu da ƙanwar miji".

A tare muka saka dariya ina cewa"wa ya ga Anisa ƙanwar miji da kanta".

Muna nan zaune aka fara fitowa kowa da nashi salon nuna murnar,bayan duk mun gama fitowa Principal ɗin mu da taci gayu cikin kaya kalar graduation gown ɗin mu ta shigo tare da vice ɗinta da sauran malamai,cike da murna tayi addressing ɗin mu kafin muka haɗa layi guda,tana gaba crew na kiɗa na baya,a haka muka fita da parade har cikin Theater Hall,abun gwanin sha'awa haka appearance ɗin mu ya kasance ga iyayen mu,sai da muka shiga kafin kiɗan ya tsaya,tafi gurin ya ɗauka ganin yadda duka muka cire hulunan mu maka ɗora so a kafaɗa muna masu musu duƙan girmamawa da kai,kai kace a command muke,gurin muka samu muka zauna banda masu muƙami,dama Ni ba prefect bace,Anisa ce labor prefect ,layi sukayi su shida inda shadow prefect ma su shida,vice principal ne ya sanar da handing over da zasuyi na beret ɗin su,dama abun ka da aka daɗe ana practice kada aji kunya,band ne suka fara ƙida inda prefects ɗin suke parade a hankali suna masu bin ƙidan,umarni commander na parade ya basu da su cire hulunan su su ɗora bisa kafaɗa,suna cirewa suka taka da parade zuwa gaban shadows ɗinsu ko wacce ta ɗora beret bisa kan wadda zata maye gurbin ta,tafi gurin ya ɗauka inda iyaye da dama suka tashi suna ɗaukar hoto da bidiyo, bayan sun gama kowa ya koma ya samu guri ya zauna.

Sosai principal ta tsara komai dan kuɗin da muka bayar ba da wasa ba,ya ci sunansa kuɗi,bayan gudanar da bikin raba kyautuka inda naci har guda biyu,punctuality da kuma zama ciki head na top 5 ɗin aji,Anisa kuwa guda uku ta samu,na aikin da ta gudanar da tana prefect da na zama ta biyu cikin top 5,da kuma na gayu,bata wasa ba da aje karin guga a kaya,iyaye suka fara fita kafin mu,muna fita na rungume Anisa ina tayata murnar kyautukanta,da murnar itama ta tayani har tana tsokanata tana cewa"na kwace mata head of top five but ta bar mun".

A haka muka riske iyayenmu a wajen gurin,ban mamakin ganin su tare da yan gidan su Anisa ba,ina zuwa Hauwa'u ta ɗane ni tana faɗin"congratulations love,yayata ta zama graduate"kowa sai da abun ya bashi dariya wanda ya saka naji kunya musamman ganin Yaya Halil yana darawa sosai,

"Sauka a jikina ni ji yadda ki ke kunyatani kamar wadda na gama University , secondary dai nagama"na faɗa ina mai ƙin sake haɗa ido da Yaya Halil wanda rabona da shi har na manta,zan iya cewa tun Muna primary,shekarun kam da yawa,ya sake kyau da Haiba abin sa kamar ba yayan Anisa ba dan ya fita kyau sosai.

Gaishe da iyayen Anisa nayi inda ta gaida nawa wanda suka amsa mu cikin soyayya,Daddyn Anisa ne ya dafa mun kaina ya ce"my daughter head of best five cikin class of 25, you're blessed,Allah ya Miki albarka,naji daɗi sosai"godiya na mishi ina mai jin Yaya Halil na kirana da Brainy ,ƙanwata kuwa batayi ƙasa a gwiwa ba wajen cewa:"ai Guruwa ka ke ji Yaya Halil,tana bacci ma tana karatu".dariya mukayi.

"Daddy atleast ka ce congratulations tunda ba na ashirin da biyar ɗin naci ba".Anisa dake gefen Yaya Hibba ta faɗa.

ENEN ce ta yabeta ta hanyar cewa,"kin san muna alfahari dake ,shi yasa muna san kasancewar Zunairah a rayuwarki,Allah ya sake haɗa kan ku ya kawar da shaiɗan tsakanin ku".

"Amin"muka amsa a tare ,bouquet ɗin Naira ɗari ɗari Hauwa'u ta bani tana mai cewa"gashi nan na 10k Ni da Muhammad,and I made it with love "ganin ina mata kallon ban yarda ba ya saka ta rumtse Idanunta ta ce"naji Baba ya cika mana amma ai zamu biya sa na faɗa mishi bashine so don't give me that look,".

Dariya Anisa tayi wanda ya Saka Nima ɗin nayi kafin na ƙarɓa bouquet ɗin da chocolate a wani ƙaramin box, Hauwa'u kenan akwai sai ire iren waɗannan abubuwan, hotuna muka ɗan yi kafin muka yi haramar kama gaban mu,gayyatar mu taron walimar da za a yi ma Anisa iyayenta suka mana amma Baba ya basu haƙuri kan Nima walimar zasu haɗa mun,sun so a haɗa amma Baba ya ƙi,haka nan suka haƙura.

Bayan kowa ya ɗauki hanyar motar su na koma Hall dan nayi matuwa,ina jin Anisa na faɗa mun ita kam ta tafi mu haɗu wajen school.

Slum book ɗina na manta wanda dukkan wani detail na yan ajin mu yana ciki sun cike .

"Hope ƙanwata ta ga abin da take nema".

a tsorace na juyo dan ban yi tsammanin sa ba."Yaya Halil?"na faɗa cikin sigar tambaya,kan desk ɗaya ya zauna yana mai ɗaga mun gira ɗaya kana ya ce"hala ba kiyi maraba da ganina ba,dama na zo ne na tayaki neman abin da ki ke nema,Allah ya sa ban laifi ba".

Murmushi nayi ina mai girgiza mai kai kafin na ɗaga slum book ɗin ina mai nuna mishi,karɓa ya yi,kamar ya buɗe sai kuma ya nuna yana murmushi ,hannu ya saka ya ciro bandir na kuɗi ya miƙa mun,kallon kuɗin nayi kafin na kalleshi,zuba mun ido ya yi Nima na zuba mishi,ki ƙarɓa tunda ban siya miki komai ba kuma kun ƙi yadda da zuwa gidan mu so wannan ne kyauta ta.

Girgiza kai na fara ina faɗin"Nagode Yaya Halil amma ba zan karɓa ba Allah,dan Allah kada kace sai na karɓa"ganin da gaske nake duk na ruɗe ya saka ya mayar aljihunsa ya ce"na ji amma zan siyo Miki kyauta na kawo Miki har gida amma sai kin karɓa".

Murmushi nayi ina mai yin ƙasa da kaina ban iya faɗin komai,wayarsa ya miƙa mun,kallon wayar nayi na kalleshi,."ki karɓa ki saka mun number ɗin ki,I'm very sure kin san ba zan gane gidan ku ba sai na kira ki".

"Yaya Halil ai bana da waya"na faɗa mishi ina ɗan murmushi.

Da mamakin faɗin bana da waya ɗin da nayi ya buɗe baki kafin ya ce"ki ce dai baza ki bani number ɗinki ba saboda kada yayanki yace yana sanki".

Haka nan sai naji kunyar maganar sosai da ya saka na kasa haɗa ido dashi illa sake tabbatar mishi da nayi wallahi bani da waya,ya yi mamaki wanda ni ban ga abun mamaki ba ,haka nan muka jera a tare yana mai ce mun zai dai zo ko ya ya ne amma dole zai kawo min gift.

"I'm sure yanzu ina komawa gida zan tarar da waya Baba ya siya dan dama ya ce ba zai siya mun waya ba sai na gama makaranta".na tsinci kaina da faɗa Mishi gudun kada ma ya siya mun waya dan na san kaɗan daga aikin sa kenan ni kuma Allah ya san ba zan taɓa karɓa ba.

kawar da zancen ya yi ta hanyar nuna burgewar tsarin Baba,haka ya yi ta jana da wasa yana mai sake tabbatar mun ko da waya ko babu zai zo gida kuma muna da magana mai girma ,da haka muka yi sallama,already su Anisa sun wuce hakan ya saka ya wuce motarsa bayan ya sake sallama da su Mama.

Da muka koma gida ƙaramar walima suka haɗa mun ,mama Ta yi mun abinci mai daɗi da kaza Baba kuma ya bani kyautar waya ƙirar Infinix smart 10, Murna kamar zan yi mene,addu'a na ɗinga bin Baba da shi dan sosai naji daɗi wanda bana iya misaltawa,murnar da Hauwa'u da Muhammad ke tayani sai ka rantse su aka siyawa wayan,ina kan wannan murnar ban fita daga ita ba Baba ya sake kasheni da wata,hannunsa da ke miƙa mun Laptop nake kallo,nuna laptop ɗin nayi kafin na nuna kaina ina mai kallan Baba ,ƴar dariya ya yi ya kaɗa mun kai kafin ya ce"ga system nan saboda makaranta da assignment da ɗan abun da baza a rasa ba".ban san lokacin da na rungumesa ba ina kuka.

Haka ranar ta kasance mun ranar farin ciki da jaddada soyayyata da sake tabbatar da muddin na rasa dangina na shiga uku.

*******************************************

*𝙰𝙽𝙸𝚂𝙰*

Tunda ta shiga Mota wani tuƙuƙi ya tare mata maƙoshi Idanunta da tunaninta sunƙi fita daga bouquet ɗin da Hauwa'u ta bama Zunairah,ta san ba ƙaramun party za'a haɗa mata ba a gida amma ta so itama yadda aka kawowa zunairah money bouquet a kawo mata wanda yafi nata ,ga babban abin da ya sake shaƙa mata shine ganin yadda Daddy ke aikin koɗata dan ta ci na ɗaya,that was supposed to be her place amma ta sace Mata,tunda suka shiga motar take expecting mitar Daddy,ta so ta hau motar yaya Halil amma ya ce shi ba gida Zaije straight ba,har ta cire ran ba zai maganar ba ta tsinci Muryarsa yana mai faɗin.

"Yanzu Anisa baki ko da kunya ba,and baki jin cewa ya kamata ki Bama iyayenki masu sponsoring karatun ki haƙuri ba,i mean ina san sanin menene a upstairs ɗin Zunairah da ke naki upstairs ɗin babu".

"Amma Daddy da 1 mark ne kawai ta wuceni fa,atleast ka ce mun sannu da ƙokari after all babu wanda ya wuce ni bayan ita ".

Cike da spark ya Juyo yana mai cewa"shi 1 mark ɗin baza ki iya cinsa bane?".

"Daddyn Anisa dan Allah ka kalli Titi kana tuƙine idan munje gida sai ayi maganar nan"Enen ta faɗa ganin ya mayar da hankalinsa kan Anisa ga kuma tuƙi yana yi .

Zumɓura baki kawai Anisa tayi tana mai jin yadda yaya Hibba ke shafa mata hannu a hankali cikin siga ta lallashi.

Koda suka isa gida bai ƙasa a gwiwa ba ya cigaba,ƙin tsayawa tayi a gurin ta wuce ɗakinta dan idan zata tsaya sauraron Daddy at the end of the day faɗa za suyi,ta yaya ma za a yi tabar Zunairah ta cigaba da winning akan ta idan sun je University?the more suna nuna mata Zunairah ta fita the more tana san ta ga ta buge ta a komai,ba dai winning suke so tayi ba,to yanzu suka fara .

Shigowar Enen ya tsayar da ita daga wankan da ta yi niyyar shiga,wata gown ta kawo mata mai kyau,ajewa tayi kan gado kafin ta isa gareta,riƙe mata hannu tayi tana murmushi kafin ta ce"kinyi ƙokari yarinyana,cin na biyu ba abu bane mai sauƙi,".

Wani irin kuka ta fashe dashi tana mai rungume Enen kana ta ce"mene abin wahala idan daddy ya faɗa mun haka?Enen I'm trying ,Ina duk abin da zan yi ganin ban Bama Daddy kunya ba why this? kullum a rayuwarsa ban kai inda yake so ba,shin fault ɗina ne idan Zunairah ta ci Marks fiye dani?".

Kaɗa mata kai Enen ta fara tana mai cewa"you're doing your best kuma kina yi yadda ya kamata kada ki biye ma Daddy and na san yanayi ne saboda ke, Sweetheart duk abin da ki ka ga iyaye sun yi a rayuwar ɗan su dan samun cigabansa ne because mu namu ya wuce,kada ki saka maganar Daddy a zuciya,and baki sani ba idan baki nan yana yabon ki".
"To Enen ego ba zai barshi ya faɗa a gabana ba ko,I'm sick and tired ".
Lallashinta Enen ta dinga yi har ta samo kanta amma deep down abin yana cikin Zuciyarta,babu ma yadda za a yi Zunairah ta cigaba da wuceta,idan tana da wani tunanin na Chanza makaranta a yanzu ta sake tabbatar da inda Zunairah ta je nanne itama zata je.
𝘊𝘩𝘶𝘤𝘩𝘶 𝘫𝘢𝘺✍️
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔

𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎

Na

𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay)

EPISODE 5:unknown broken code.

*𝚉𝚄𝙽𝙰𝙸𝚁𝙰𝙷*

Bayan ƙwana huɗu da gama makarantar mu,ina zaune ina gyarawa Mama egusi seed kafin ta dawo daga Barka da taje unguwa uku gidan wata ƙawarta,so nake nayi na gama na ɗora mata tuwan dan na rage mata aiki,na san halin Mama bata so a sa mata hannu a egusi ɗinta shi ya sa ban ma yi attempting ba Illa gyarawa da nake,ina san Miyan Egusi ɗin Mama daɗi kamar kada ka daina sha.

Hauwa'u da Muhammad tare suka wuce islamiyya babu ɗan tayani hira sai sabuwar wayata da na ƙunna Haddar da zan bada ina ji lokaci guda kuma ina aiki,ƙofar aka ƙwanƙwasa kafin Kuma Muryar wani yaro ta bayyana inda yake cewa "wai ana sallama da Zunairah ".

Wani irin faɗuwa gabana yayi dan sabon abu ne,Ni dai na san bani da wanda zai zo gurina dan ni ba saurayi gareni ba saurayi kuma shine kawai zai tsaya ƙofar gida yace ana sallama

"Zunairah kuwa?"na tambaya jin yaron bai bar gurin ba.

"Eh wai inji Halil"ya bani amsa yana mai barin gurin,da Mamaki nake sake maimaita sunan,wane kuma Halil?kamar ba zan fita ba sai kuma dai na aje tray ɗin na shiga ɗaki na ɗauko ƙaton hijab ɗina na fita,Turus nayi lokacin da idanuna suka sauka kan nasa,jingine ya yi jikin mota hannayensa naɗe bisa ƙirjinsa,baƙin yadin da ke jikinsa ya saka haskensa ya bayyana, Murmushi yake watso mun wanda yake bayyana haƙoransa,gira guda ɗaya ya ɗaga mun gannin na tsaya ni ban koma ba ni ban ƙarasa ba.

"Ko ba a maraba dani na koma?"

"A'a Yaya Halil ina dai mamaki ne yadda ka san gidan"takowa nayi ina mai bashi amsa har na isa inda yake ina mai yin ƙasa da kaina na gaishe da shi cike da girmamawa.

"Lafiya lau yan mata sanin gida kuma ki daina mamaki ai mai san ɗaukar abu a guri baya bari ya yi ƙasa a gwiwa,well ranar graduation ɗin ku na bi ku a baya,I'm sorry idan nayi ba dai dai ba i just can't help it,like I promised na ce zan zo sai yau Allah ya bani iko".Buɗe gidan zaman baya ya yi ya ciro wata leda ya miƙa mun yana mai ƙarawa da cewa"ga kyautar ki,kamar yadda ki ka gargaɗeni a wayau ban sai waya ba,yanzu tunda ga waya a hannunki sai ki saka mun number ɗin ki".

Kallan wayar dake hannuna nayi kafin na kalli leɗar,kamar ya san zan kawo uzurin da zan ƙi karɓa ne ya ce"bana san a mayar mun da kyauta, dan ke na siya kuma zaki karɓa idan ba so ki ke na je na faɗawa Mama ba,dama ina so na shiga mu gaisa".

Hannu na saka na karɓa ina mishi godiya kafin na faɗa mishi Mama bata nan ni kaɗaice a gidan,ganin yadda nake ta jin kunya haka nan ya saka bai ja ni da surutu ba ya mun Sallama a kan za muyi waya,haka nan naji ni cikin wani irin nishaɗi da ni kaina ban san ya akayi na faɗa cikin ba,wani irin burgeni kawai na ji ya yi,idan za a tambayeni zaɓina dangane da namiji,zan iya cewa ina san mutum kamar Yaya Halil dan ya haɗu ta ko ina ,ɗan gayune sosai .

Leɗar na buɗe dana shiga gida ,kayan ƙwalliya ne da Turaruka sai kayan cimma na ƙwaɗayi,wani ɗan box ne a wrapping wanda ke ɗauke da note ɗin da ya saka gabana Faɗuwa sosai,I LOVE YOU ZUNAIRAH,na karanta ya fi a irga ,buɗewa nayi ina mai zaƙuwa da san ganin menene a ciki,wani zobe ne wanda aka saka kalmar Z a cikin glass ɗin sa,ni dai ba sanin zobe mai tsada nayi ba amma daga gani mai tsada ne yadda yake ta ƙyalli abin sa,to na dai karɓi kaya ban san ta yadda zan faɗa ga yan gidan mu ba,zance na ɓoye

3 / 16