Author : Chuchujay Category : Romantic Hausa Novels
ki raina mun hankali Hibba,wa zaku mayar ɗan iska?ku dai da ku ke danne abin da yake zahiri saboda munafurci ku cigaba da yaudarar kan ku amma ni babu wanda zai Hainceni na yafe".ta faɗa cike da masifa tana mai tunkarar Zunairah da ke gefen Anisa tana ta kuka,ita ba wannan ma yake damunta ba,damuwar dake Zuciyarta tafi wannan haukan da Zainab ke gwadawa.
Daddy da ya ji hayaniyarsu ya fito dan dama gama sallama da su Zainab kenan ya koma ciki kasancewar weekend,cike da mamakin faɗan da ake ya ce"mene ke faruwa ne ?".
"Daddy Zina Halil yake ".Zainab ta tarwatsawa kowa kunne.
A tare suka maimaita kalmar ZINA,?
"mene ku ke maimaitawa kamar anyi mishi ƙarya,idan ba haka mene tsakaninsu shi da Zunairah,Daddy sigina suke ga juna ".
"Kin wuce mu tafi wallahi kafin na saɓa miki"Yaya Halil ya faɗa ganin zata masa haukan da ta saba gaban iyayensa,a wannan point ɗin ya yarda idan aka kai Zainab asibitin mahaukata babu ɓata lokaci zasu bata gado.
"Ja matarka Halil ku wuce gida "Enen ta faɗa tana mai mamakin ɗabi'ar Zainab,babu musu ya fincikota suka fita tana ta ihu tana zage zage har suka bar cikin falon baki ɗaya.
"What madness "Daddy ya faɗa,yana ƙoƙarin juyawa Zunairah ta ce "Daddy gurinka nazo".
Juyowa ya yi "Ni?"
"Eh Daddy taimako Nazo kayi min dan Allah ,idan kayi min ba zan taɓa mantawa ba,and wannan abin da Matar Yaya Halil ke faɗa babu gaskiya ciki,babu abin da ya haɗani da Yaya Halil bayan mutunci ".
"Kada ki damu da wancan abin tukunna dai taimakon menene ki ke so,wani ne baya da lafiya ko mene?".
"Daddy Baba ne,yana state CID sun kullesa akan case ɗin satar waya tun jiya sunƙi bari kowa ya gansa?".
Zama daddy ya dawo ya yi yana mai cewa"to mene ya faru garin yaya?".Labarin abin da ya faru na bashi cike da mamaki yake mayar da abin,kowa a falon na bashi tausayi daga kallonsu, tausayin nake so na basu a taimakawa Babana,dan naji ance idan aka kaika bompai sai Allah zaka dawo daga nan idan ba kayi wasa ba Abuja za a wuce da kai,idan kuwa aka kai Baba Abuja mun shiga uku mun lalace.
"To su haka kawai sai su ambaci sunansa babu wani ƙamshin gaskiya kuma?"
"Daddy!!!! Please kafi kowa sanin Baban Zunairah mutumin kirki ne just help him na san zaka iya daddy"Anisa ta faɗa tana mai zuwa inda yake jin abin da yace,duk da naji Haushi sai na danne tunda naima nake .
"Wallahi Baba baya sata Daddy ,abu na karshe da Baba zaiyyi shine sata kawai dai tsautsayine da ƙaddarar da bawa baya iya tsallake mata".
Shiru Daddy ya yi kamar yana nazari kafin daga bisani yace"ki je gidan zanje chan ɗin,zan kira commissioner of police".ban masa musu ba na tashi na tafi gida,lallashina Enen ta ringa yi har ta haɗa ni da driver muka wuce tare a Anisa wadda Idanunta ya kaɗa saboda Kuka da ta sha.
Da mukaje gida a ƙofar gida muka tarar da Yaya Halil,ji nake kamar na mishi shegen duka ko uban me yazo ya yi mun oho,ina fitowa kai tsaye na shiga gida Anisa ta tsaya dashi inda take faɗa mishi abin da ya faru,wucewa ya yi shima station ɗin cike da damuwa mutuƙa,da ta shigo take faɗa mun yaje station ɗin.
Mun gama saka rai haka Mama ta dawo wai har yanzu ba'a sake su ba,kana kallonta ba sai an faɗa maka gwiwowinta sun sage ba,cike da sarewa take faɗa mana wai kuto za a tura su washegari,Anisa ta fara kiran Daddy wanda ya shaida mata kada ta damu case ɗin ba zai kai har aje kotu ba,mu dai shiru kawai mukayi dan a wannan gejin kukan ma yaƙi zuwa.ɗaki Mama ta shiga ba dai tace komai ba.
Da kulawa Anisa ke faɗa mun"Zunairah komai zai zama dai dai babu abin da zai faru da Baba".
"Allah ya sa domin idan wani abu ya faru da Baba ina mai tabbatar Miki Anisa Mama zata samu damuwa idan Mama ta faɗa wani hali kuwa Kinga Asirin mu ya gama tonuwa".
"Insha Allahu babu abin da zai faru,baki yarda da Daddy bane?komai idan aka haɗa da siyasa za'a dace,Daddy fa influenced ɗan siyasa ne kada ma ki yi tantama akan abin da zai iya"
"To Allah ya zaɓa abin da ya fi zama Alheri "na faɗa ina mai tausayawa rayuwarmu tun kafin ta zama abin tausayi domin da Akwai tausayi
Ita ta dafa mana shinkafa tunda dama gidanmu ba'a rasa miya,Aunty Muna kuma ta kawo tuwo,Anisa ce kawai ta iya ci sai Adavize da Hauwa'u dana titsiye su ci shikafan ko kaɗanne.Tuwon na kai ma Mama duk da na sani zai wahala ta iya cin abinci ni kaina ba dan Anisa ta saka mana tare tana mitar muci ba da babu abin da zan iya ci,. Tunani zata wuce ganin har munyi sallar isha'i ya tabbatar mun kwana ne za tayi,ban dai tambaya ba amma tunanin zata ƙwana ɗin kawai ya saka naji wani irin farin ciki,ina jin daɗi dana Samu ƙyautar Anisa,ita ɗin ƙwace da kowa zai so ya yi Alfahari da ita.
Wuraren ƙarfe sha biyu na dare bacci har ya ɗauke mu naji Knocking kamar a mafarki,ni kaɗai na iya farkawa Anisa kam bacci take sosai ba damar na tasheta,dama su Hauwa'u ɗakin Mama suka ƙwana,wayata ce ta hau ruri,layin Yaya Halil da na mayar da Sunansa zuwa LESSON LEARNED ne ya Kirani,kamar bazan ɗauka ba dan sai da ta katse ya sake kira kafin na ɗauka.
"Muna kofar gida da Baba ki zo ki buɗe".
Wuntsilowa nayi daga kan gado,banyi tunanin ko saceni zai yi ba ko ya yi mun wani mugun abin,Babban abu mai muhimmanci shine Babana da ya ambata.
A tsakar gida naga Mama da ƙatuwar fitilar ta tana tambayar wanene,kafin a amsa mata nace Mata "Baba ne ".
Rige Rige mukayi wajen buɗewa,there Comes Baba an Mishi tara tara an kamo shi kamar kayan wanki,ban san ya akayi na fáshe da wani irin Kuka ba.
"Ya mutu ko Halil?"Mama ta tambaya cikin wani irin yanayi da baza ka iya fassara abin da ya ƙunsa ba.
"a'a Mama ya samu karaya ne a ƙafarsa guda ɗaya da hannunsa"ya faɗa yana mai kamo Baba abokin tafiyar nasa yana bin bayansa,sai a lokacin baki ɗayan mu muka kula da ɗaurin da ya sha,ɗaki aka shiga dashi,gado aka ajesa kafin Mama ta Mishi shinfiɗa Sanin jinyar karaya kan gado ba zai iyuba,wani bulo dake kitchen ɗin mu aka ɗauko dan ɗora masa ƙafa,abin haushi duk abin nan da ake Hauwa'u baccinta take shaƙa har gwanda adavize ace yarone.
Godiya Mama ta yi ta musu,ni dai ban iya cewa komai duk da naji daɗin abin da suka mun har cikin Zuciyata.
Itafa ƙasar nan tamu ta gado sai Kana da wanda ka sani,bafa wai baza a iya bane lalacine kawai irin namu,yaran da suka wa Baba Sharri babu wanda ya tuhumesu ko ya yi tunanin karya suke,an magana sunce ai rai shida baza suyima mutum guda ƙarya ba,amma menene hikimar bincike?.Baba fa duk Wannan baƙar Azabar bai amsa laifinsa ba amma har ake ƙokarin tura su kuto,mu dai ba bincike aka zo akayi gidanmu ba amma sai cewa sukayi an tara hujjojin da zasu kai su Baba kotu,da Daddy ya shiga a wunin Ranar aka fito da Ogansu Bamaiyyi inda suka ƙaryata kansu suka tabbatar da sharri sukayi wa Baba, bincikene wanda da ace anyi tun farko da ba'a taɓa wanda baiji bai gani ba,sai gashi da sanannen ya shiga anyi abin daya kamata ace anyi,wata shari'ar sai a lahira domin duk inda Baba ya juya ya ji azaba sai ya tsinewa masu hannu da tsaki da suka jefa shi cikin jidali.
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔
𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎
Na
𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay
E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟ 16:call it a day
Jinya Baba ya fara cikin samun kulawa daga iyalansa, Álhamdulilah ana samun sauƙi dan bakinsa da ya kumbura ya sauka,muna dai shan yan dubiya,kama daga gurin Aikinsu har zuwa maƙota, ranar gidan su Anisa baki ɗaya suka zo sake duba shi,a nan ne Mama ta samu tayi musu isasshiyar godiya , kayan marmari da abubuwan taɓawa suka kawo mishi,fruits kam baya yankewa dan ko bamu siya ba Anisa zata zo takanas tace Daddy da Enen sun aikota ta kawo,sun bamu kulawa yadda ya kamata domin a wannan stage ɗin kallon yan uwa na fara musu ba iyayen ƙawa ba.
Yaya Halil ya kan Kirani mu gaisa Sama sama ,na kasa samun ƙarfun gwiwar ƙin ɗauka mishi Wayarsa sai nake jin wannan Alheri da ya mun ya sanyaya mun Zuciya duk da ban manta yaudarar da ya mun ba,amma kamar yadda ya faɗa sai na ɗauki matsayin Yaya na bashi,akwai ranar da ina tare da Anisa ya Kirani kamar ba zan ɗauka ba amma sai na ɗauka,jin na ambaci Sunansa ya saka ta juyo a ɗari tana kallona.
"Yaya Halil kuma?"
Ban kulata ba sai da muka gama kafin ta sake dawowa kusa dani tana mai faɗin"kada ki ce mun ruwa ki ka koma".
"Ruwa kuma?".
"Eh mana,kada ki ce mun Yaya Halil ya samu nasara wajen yaudararki da daɗin baki ku dawo Soyayya da shi after duk abin da ya yi miki".
Dariya nayi ganin yadda ta zazzare ido tana san jin amsata,"calm down babe babu abin da ke tsakanina da Yaya Halil bayan mutunci,after duk abin da ya yi mun kina tunanin shawara ce mai kyau na ƙi gaisawa dashi?Anisa wani lokacin ya kamata muna kallon Alheri kafin mu duba sharri,Yaya Halil bai Aureni ba haka Allah ya ƙaddara,duk abin da Ubangiji ya yi shine dai dai, Kingani komai ya zauna a gurinsa mai zai hana a cigaba da rayuwa kamar ba'ayi ba a manta abin da Ubangiji bai nufa ba?".
"Amma Zunairah wannan abin fa akwai haɗari,da kike faɗin ya taimakeki ince Daddy ne kan gaba,mene ya yi Bayan zuwa ya tsaya har abin ya ƙare sai Umarni da Daddy ya bashi ya kawo Baba gida,kada ki bari ki koma baya kan namijin da bai cancanta ba, wallahi idan ki ka ce zaki Auri Yaya Halil Babu abin da zai hana matarsa banka miki wuta ki mutu dan bata da hankali".
Ganin yadda tayi maganar da gasken gasken ya saka nima na saka tawa gasken waje bata tabbaci,"Anisa ba zan auri Yaya Halil ba koda zai rabu da matarsa ,na san you're looking out for me amma ki ƙwantar da hankalinki,irin wannan alaƙar ta yanke tsakanina a Yaya Halil ".
"Da gaske?".
"Insha Allah,yanzu dai ki cigaba da duba mun Draft ɗin page ɗin nan da zan ɗora anjima kada ki damu idan aka fara bani contract a Dreame zaki dara ".
A haka muka shashantar da maganar Yaya dan dama babu amfanin tada ta.washgari Monday muka yi resuming makaranta abin da nayi missing shine baccin safe,first week of resumption muka koma ni da Anisa, idan kaga dama kira mu Mayun boko,maitar ta saka mu zuwa idan ance yau za a koma ai akwai dalilin komawar koda kuwa revision ne an ɗan tada mana ƙwaƙwalwa ,bayan gama Lecture Anisa ta kira Khalipha ya zo ya ɗauketa,jin hakan ya saka na ce"guess ba tare za mu wuce ba".
"Aikuwa baki isa ba,tare zamu wuce zai fara dropping ɗinki gida in yaso mu sai mu wuce"
Sanin koda nayi mata musu ba yarda za tayi ba ya saka nace to kawai,bayan wani lokaci ya kirata akan yazo ,dama muna bakin department ɗin Computer science nan muka gama cin Awara,powder ta ɗauko a jakarta ta ɗan shafa bisa fuska kafin ta shafa lip balm ,ni dai kallonta kawai nake,Anisa na san Khalipha da yawa ina mai mata fatan Ubangiji ya saka su ɗin Alherin juna ne dan da ace Khalipha zai ma Anisa abin da Yaya Halil ya yi mun ina ji ita sai mutuwa,.Tunanin hakan kawai da nayi sai da na nemi tsari da shaiɗan dake nema ya ɗarsa mun haddasa a zuciyata .
"Ya ki ka ga fuskata? All set ko?".
"Kin haɗu kilan idan Khalipha ya ganki yau straight waliyansa zai kira yace a ɗaura kawai daga nan sai gidansa".
Dariya ta saka sosai tana mai tashi kana ta ce"ana zuwa wannan gurin,soon zamu zo nan i can't wait to have you as my chief bride maid ke nifa kafin na gama Buk nake san kama Khalifa a hannu dan ba zan bari a ƙwace mun shi ba,so nake na samu lokaci na mishi maganar Aure idan zai turo kawai ya turo".
Ni dai murmushi kawai nake ina tsoron bada amsar da zata fito kamar ina baƙin ciki a haka har muka isa inda motar Khalifa take ,yana ganin mu ya fito yana murmishi,cike da shagwaɓa ta ce"Babyna Allah yasa baka jira da yawa ba".
"Ban jira ba idan ma na jira ai gimbiyata abin a jirata ne,ƙawarmu ina wuni"ya mayar da idanunsa kaina.
Kafin na kai ga amsa mishi Anisa ta karɓa"nifa bana gane ƙawarmu ɗin nan da kake yi fa,Zunairah ƙawatace ni kaɗai bana so wannan ai salon ƙwace ne".
"Naji Allah ya baki haƙuri,babu wanda zai ƙwacewa Anisa Zunairah,ƙawar Baby ina wuni".
Nima ina wuni ɗin nace Mishi,hannu Anisa ta saka dan buɗe gidan gaba ,Khalifa ne ya katse ta,"babe Farouk yana gaba ne tare muke".
"And so,sai ya fito ya dawo baya kasan gaban mota nawa ne".
Buɗe motar wanda aka kira da Farouk ya yi ya ce"ran ki shi daɗe yau sai dai a koma baya ,ai muna zaman lafiya ki ka taso mu dole yau ki zauna a baya".
Haɗe rai tayi sosai tana mai cewa"to Allah yau sai na nuna maka motar Saurayina ce ba taka ba".
A yadda suke yi Khalifa na musu dariya na fahimci Farouk da Anisa basa shiri,kowa na ganin Hanjin juna,ni dai gefe na koma na tsaya Khalifa na musu dariya,ni kaina ba so nake Farouk ɗin ya shiga bayan ba,idan ma ba iskanci irin na Anisa ba mene laifi idan ta shiga bayan mun zauna tare?.
Juyawa tayi akan tafiya za tayi idan har Farouk bai bar mata gaba ba, Khalifa ya ci mata yana bata haƙuri inda Farouk ya fito gidan gaban yana mai cewa"ai sai ki zo ki zauna ɗin mara zuciya".
Yana ƙokarin buɗe bayan ya kula dani dan ina jin sai a lokacin ya san tare muke,murmishi ya faɗaɗa da ya dora idanunsa a kaina,ganin ya zuba mun ido yasa nima na zuba mishi,buɗe mun ƙofar ya yi ya ce"Bismillah mai kyau da ace na san da ke waccan ɗara wada ɗin take ai bazan tsaya biyeta ta ba,cikin bugun zuciya guda zan dawo baya na zauna kusa da macen da tunda garin Allah ya waye banga mai kyawunta ba,infact na daɗe banga mai kyawunta ba".
Wani dogon tsaki Anisa ta ja tana mai kiransa da Fuck boy kafin ta buɗe gaban motar ta shiga ,nima shiga nayi bangaren da Farouk ya buɗe mun kafin ya zaga shima ya shiga,Khalifa ne ya ce"ran gimbiya ya huce"kafin ya tada motar ni dai baki ɗaya na kasa samun nutsuwa musamman ganin yadda Farouk ya zuba mun ido,
"Dan Allah ki faɗawa bawan Allah nam sunanki ko zan ƙara a cikin Zuciyata na ƙara kaimun bege ki,kinga idan na haɗa da sunanki mai kyau mai daɗi sai abin ya fi armashi".
"Ummm kaji mayaudari,idan ka tashi sai ka faɗa mata yan mata nawa ka yaudara"
"Khalifa hold your babe oo,ita ta samu gurin fakewa ni shine zata bata mun rawata da tsalle,kalli nan ƙawarta ki manta da wannan dan kawai naƙi santa kafin ta koma ga abokina shine take baƙin ciki".
Ai kamar jira take ta juyo ta fara masifa tana faɗin"wallahi tallahi kai ka san nafi ƙarfinka,sannan baby ya fika ta ko wace irin siga,i will never choose you over him".hannu ta saka tana mai ɗorawa bisa gemun Khalifa wanda murmishi kawai yake yana tuƙi ,ni dai Allah Allah nake a saukeni na Kama gabana ba wannan nazo yi ba,koda ace Farouk da gaske yake dangane dani sai dai ya yi haƙuri na rufe babin saurayi,ko zanyi ba yanzu ba ,a yanzu karatuna shine Soyayyata dan na kula soyayya bata karɓeni ba.
A haka Farouk da Anisa sukayi ta musayar zance har aka kaini ƙofar gidan mu,ina ƙokarin fitane Anisa ta dakatar dani ta hanyar faɗin"yauwa baby baka yi wa Besty jaje ba,Babane wallahi aka kulle a station akan case ɗin satar waya wai yaran sunce shine Ogansu ,kasan yanzu kuma al'amarin basu tsaya wani bincike ba suka karkarya Baba,har za aje kotu ma Daddy ya yi stepping in abun babu daɗi yanzu haka Baba jinya yake ,Allah ya sa ba akai ga kuto ba da yanzu yana gidan maza babu hakkinsa".
Wani abune yazo ya tokare yawon da nake niyar haɗiya,kallona Khalifa ya yi cike da tausayin halin da ta zayyana masa da Baba ya faɗa yace"Ya Salam,Allah ya sake kiyaye gaba,Allah ya bashi lafiya ai ban sani ba da nazo na dubashi,kuma laifinkine Anisa da baki faɗa mun ba".
"Yanzu ma ai bai ɓacci ba zaka iya zuwa ka duba sa"ta faɗa.
Murmushin yaƙe kawai nake da ya buƙaci shiga duba Baba,fita nayi da zummar zan sanar da Mama kafin su shiga ɗin,kamar wadda laka ta karyewa a ciki haka na shiga gidanmu,ina mayar da Kofar na jingina da gate ɗin ,rumtse Idanuna nayi sai jin hawaye nayi,shin mene ya ɓata mun rai?.
Mutunci Anisa tayi mun saurayinta yayiwa Babana jaje ya duba lafiyarsa Amma dole sai ta zayyana dukkan abin da ya faru da Baba,ba domin Anisa bace sai nace da biyu tayi min,na kasa haɗa abun ,sai nake jin zafin da ya kasance gaban abokin Khalifa ne,idan wani ya fahimta wani ba zai fahimta ba,cewa za ayi kilan ma dan Daddy dinta ya shiga ne aka yi siyasa aka fitar da Baba amma da saka hannunsa.
"Auntynmu lafiya?".
Buɗe idona nayi na saka su cikin na Hauwa'u dake sanye cikin uniform ɗin islamiyya,saurin goge hawayen da ya zuba kan kumatuna nayi ina cewa"lafiya mana,baku wuce ba uku saura ina Muhammad ɗin,Mama fa".
Wucewa nayi ina kiran sunan Mama gudun kada Hauwa'u ta gane kuka nake,bina tayi da kallo har na shiga falo ,Mama ke Niyar fita tana kiran Hauwa'u.
Kaina na saka nace"inya ki zo mana kina ji ana kiranki" takowa tayi daga inda na barta a tsaye ta shigo falon,Naira ɗari biyu Mama ta