Author : Chuchujay Category : Romantic Hausa Novels
nayi ya tsaya daga tafiyar da yake,juyawa nayi na kallesa,ganin kamar maganar ta masa ciwo a yanayin fuskantarsa ya saka na cigaba da tafiyata,ganin da gaske bana da lokacinsa ya sa ya tako sai da yazo inda nake yace"mai yasa ki ke san denying abun da muke dashi a baya?".
"Bakaji kace a baya ba,kai kana ma ɗaukarsa baya amma ni kam Yaya Halil na binne wannan,zaifi idan kaima ka binne tunda dama ai abu ne da ka ƙi.".
Kafin ya yi wata maganar na hangi Khubayb,wallahi baki ɗaya na manta tare muke dashi,yana tsaye jikin ɗan sahunsa yana kaɗa mukulli,kallon direction ɗin da nake kalla yayi kafin yace "wane wancan ɗin?".
"Wanda ya kawo mu Asibitin all thanks to him ƙilan da Bamu san mene zai faru ba".
Takawa nayi yana biye dani,sosai naji daɗin ganin Khubayb atleast ya sakar mun mara nayi fitsari,da muka isa gun Khubayb da damuwa yake tambaye lafiyar Anisa amma wai abin haushi Yaya Halil sai cewa yayi "maigida nawane kuɗinka?".
Kamar nayi ta kifa mishi mari haka baki,wai maigida nawa ne kuɗinka,murmishin yaƙe nayi nace mishi"Yaya Halil ɗan uwan mu ne banyi zaton yana jirana".
"Aw Sannu"shine Abin a ya iya faɗa,yan kallo muka bar gurin,muna fita cikin asibitin na sauke ajiyar zuciya,a nan ne nake faɗawa Khubayb jikin Anisa ,yaji tausayinta sosai inda yake mata addu'ar samun sassauci.
Da naje gida nake faɗawa Mama ,ta shiga damuwa sosai inda take cewa goben insha Allahu za suje,da tunanin Anisa na ƙwana baki ɗaya na rasa mene yake mun daɗi,ban taɓa tunani Anisa bata da lafiya har haka ba,sai nake jin kamar ban zamar mata ƙawa ta kirki ba tunda har ban iya gane bata da lafiya har haka ba.
**********
Da safe banje makaranta ba muka wuce tare da Mama,abinci mai kyau Mama ta mata muka wuce, har Daddy muka tarar a asibitin,sunji daɗin zuwan mu ,ina zuwa na rungume Anisa wadda tana ganina ta fashe da kuka tana faɗin"Kinga halin da na shiga ba".
"Sai ki faɗa mata rigimar da ki ka tada mana "cewar Daddy.
Kallona take cikin ido hawaye cike a Idanunta,hannuna da ta riƙe take rubbing a hankali Idanunta a ƙasa ta kasa ɗagowa ta kalleni.
Sai na fara tsoron abin da zanji daga bakin nata,ɗagowa nayi na kalli su Enen wanda suma sun kasa haɗa ido dani,a tsorace nake tambayar su mene ya faru ina kuka,Mama ma tayani tambaya tayi ganin baki ɗaya kamar mun zama surukai dasu.
"Anisa idan har kin ɗaukeni ƴar uwa wadda take ɗaukar damuwarka tata kiyi mun magana dan Allah , Wallahi gabana faɗuwa yake sosai tsoro nake ji".na faɗa ina sake riƙe hannunta.
"Zaki iya bani abu idan na tambayeki?"ya tambaya a yanzu tana kallon cikin idona.
Da sauri na kaɗa kaina ina mai cewa"indai bai saɓawa Shari'a ba bai kuma fi ƙarfina ba Anisa zan baki,abu koda shine ƙarshe a hannuna zan baki ni na haƙura,zan baki ko mene shi".
"ZUNAIRAH INA SO BANI ƘODARKI ƊAYA".
Hmmm to fa kunji dai abin da Anisa ta bukata daga Zunairah.
Shin zata iya yiwa Anisa wannan sadaukarwar ko kuwa zata gagara?
Ƙoda fa
Hmm Nima dai ban san mene zai ce ba.
Domin san cigaba da bin littafin Cin dunduniya kuyi maza kuyi payment ɗinku akan Naira 600 kacal domin cigaba da samunsa a telegram ko ku bibiyesa a Arewapen kan handle ɗina mai Suna Chuchujay.
8130229878
Opay
Amina Jamil Adam