Author : Chuchujay Category : Romantic Hausa Novels
mun kwanta nace mata "Hauwa'u mene ya saka ki ke ma Anisa irin abin a ki ke mata?".
"Auntyna nifa tun abin da ta faɗa Miki kan Yaya Halil sai nake jin haushinta,har yanzu kuma sai nake jin kamar ita tayi silar rabuwar ku,nifa Aunty tsakani da Allah ba zan iya ƙawancen da kuke ke da Aunty Anisa ba,kin bata yadda da yawa,baki tunanin komai idan zakiyi mata wani abun,kullum kina nuna mata kina yinta,I'm just scared ita ɗin red flag ce because friendship ɗinku kamar ke kaɗai ki ke yi Allah yasa nan gaba kada ta yaudareki".
"Da zata yaudareni Hauwa'u da tuni tayi,kada ki manta mun daɗe tare,maganar Yaya Halil kuma ina so ki cire wannan a zuciyarki,dama ni dashi ba rabon juna bane, tsakanina da Anisa kuma insha Allahu sai Alheri,i might be overbearing amma ai ba wai bana da wayau bane,muna faɗa mu shirya wanda haka alaƙar gaskiya ta gada a ɓata a shirya".
Jin amsata tayi kafin tace"Allah ya saka to hasashe kawai nake yi,dama ina ta san faɗa Miki,kin san yanzu Midnight Authoress ashe tana da hardcopy na littattafanta?ɗazu mun shiga wani bookshop ni da ƙwayena naga littafan ta".
Wani abu naji a ƙirjina wanda ya yi mun kama da hassada,ɗan adam kam baya rabo da ita once in a while sai dai ya fi karfinta,saurin kawar da jin dama nice nayi kafin nace"Allah ya ƙara mata ɗaukaka muma Muna fatan Allah ya kaimu inda suke ".
"Amin Auntyna ai ke kam sai kin fita ma insha Allahu,rubutu ma wallahi kin fita iyawa kawai dai ta fiki Fans ne da daɗewa tana rubutu amma kema kina hanya insha Allahu".
Naji daɗin addu'anta cike da farin ciki na amsa da Allah yasa,ita ta rigani yin Bacci ni sai da na tsaya nayi ɗan rubutun da ba zan rasa ba.
*******************************************
*𝘏𝘈𝘓𝘐𝘓*
Baki ɗaya tunda al'amari Zainab da Zunairah ya faru sai yake jin baki ɗaya baya da nutsuwa,ya rasa mene yake damun zainab,watarana tayi ƙalau watarana kuma ta fi tsohon Babur fitina,a wannan gejin ya yarda da cewa Auren garaje ba shine ba,Anisa ta nuna mishi video ɗin Zunairah da Adam suna kiss ranar da ya haɗa mata birthday,ya kasa yadda wai duk wannan lokacin Zunairah fuska biyu take nuna mishi,abu ɗaya ya yi la'akari dashi wanda shine taje gidansa wani abu yana faruwa tsakanin su,a lokacin ya ɗau zafin da bai auna komai ba sai kawai tunanin ganin Adam da yayi a gidansu da kuma yadda ta ruɗe da hannunta dake cikin nashi.
Mene ya saka waɗannan abubuwan kawai ya duba?, baiyyi tunanin maybe one-time mistake ne da bai kamata ace ya yanke mata hukunci ya rabu da ita ba sai a yanzu da yake ganin abune na yafewa tunda ba turmi da taɓarya ya gansu ba,but still kiss fa abin ya kasa bari masa ido da zuciya da tunani,Zunairah ɗinsa da yake so kamar rai da ɗan uwansa Adam,duk da ba wani shiri suke ba amma ai ɗan uwansa ne.
Abu na kamata da yake ganin dama shi ya yi shine fuskantarta ,kamata ya yi ya mata magana amma ya gaza ya yanke hukunci ya Auri Zainab da a yanzu yake dana sani.
Bayan gajiya daga gurin aiki da yayi ya kamata ace an tarbesa tun a falo amma abin baƙin cikin sai ganin falon ya yi kamar anyi sukuwa, tsaki ya yi ya shiga cikin ɗaki bai damu da nemanta ba,kwance ya tarar da ita kan gado tayi baje baje a sigar kwanciyar rubda ciki tana ta jan minshari,tun safe da ya fita ya barta haka nan take ko wanka batayi ba indai ba wai tayi ta mayar da kayan baccin da ta cire jiya ba,tsaki ya yi ya shiga bayi,yana shiga ya dawo a sittin sakamakon bayan gidanta da ya gani cikin seater batayi flushing ba,haba ya ji wari amma duk tunaninsa warin bayin da bata san wankewa ne,duk masifar da zaiyyi ta ƙi aminta da zaman ɗakinta sai nashi,a cewar ta idan ya keɓe karuwai yake kira.
Hannu ya ɗaga ya samu mazaunen da ta ɗaga sama ya ɗaɗa mata duka da ƙarfinsa,a zabure ta tashi tana ƙokarin haye fuskar gado tana faɗin"wane ?su wane?".
"Shine your eyes sai kiga wane ƙazama kawai,ki tashi kije ko kora kashin chan da ki ka yi wallahi ko na Miki rashin mutunci,idan ba ma ɗabi'ar mahaukata ba ina ka taɓa barin kashi a masai har ka zauna a ɗakin ka iya bacci?".
Tsaki tayi tace"dama shine ya saka ka tasheni daga bacci?kada ka sake kirana ƙazama ai na aje ne idan na tashi na kora bacci ne yaci ƙarfina,kai ka rantse da Allah baka taɓa ajiyar kashi ba?".
Wani maƙoƙon bakin ciki ya tokare mishi zuciya, tunanin wane irin hauka zai mata ya fara,belt ɗinsa dake gefen gado ya nufa ya naɗeta bisa hannu ya ce"dan Allah Zainab kada ki tashi ki kora ƙazantar chan".
Tashi tayi tana ɗaga mishi hannu tana cewa"wallahi kada ka fara,naji zan kora shima dan kawai ni nayi,amma wallahi idan ka bari wannan abar ta taɓani zamu samu gagarumar matsala da kai".
Banɗakin ta shiga ta danna abun flushing ɗin tana mai doɗe hanci da baki kamar wani ya yi mata,fita tayi a ɗakin tana sosa kai tana cewa"ba dan halinka ba wallahi".
Scanning dakin yayi da ido,babu abin da yake face wari ga ko ina kacakaca.
"Ni kam na shiga uku,mata ga iskanci ga rashin tarbiyya ga ƙazanta da wanne zanji ni Halilu?".
Ƙofar ya nufa ya kulle kafin ya rage kayan jikinsa ya fara gyara ɗakin,zanin gadon ya fara cirewa kafin ya sake wani ya gyara ɗakin ,bayan ya gama ya shiga bathroom,wankewa yayi kamar baya san jikinsa yana lissafa ta gama shiga mishi daki taje chan nata tayi duk wata ƙazanta da za tayi amma banda ɗakinsa,buƙata wannan ba dan ta zamar mishi dole ba babu abin da zai saka ya kusanci Zainab,ya yi ta tsaki kenan idan ya gama ita kuwa ko a jikinta,gashi wani lokacin sai ya biyata kudi .
Shin a duniya ma kam ina zai fara kai ƙarar Zainab,ta zamar mishi fitinar da bai san ta inda zai shawo kanta ba.
Bayan ya gama dakin ya ɗauki sassanyan ƙamshin room freshener ,cikinsa da ya fara kukan yunwa ya sashi ya fita domin newa kansa abinci, sai da ya tabbata ya saka key dan yanzu ɗakinsa a nan ne kawai zai samu ƙamshin Rahma.
Baje ya tarar da ita a falo tana cin gugguru tana kallo,riƙe ƙugunsa ya yi ya ce"wai ni kam Zainab mene hakan?ki kalli fa falon nan dan Allah.".
"Aw aw kana so kace mun kawai aiki nazo yi sai na fahimta ,to wallahi bari kaji ni ba boyi boyi bace ba zan Shara ba idan ban niyya ba,duk lokacin da naji ina san yi babu mai jina amma yau kuwa ƙazanta day ce shi yasa ko wanka banyi ba,kasa da hastag ƙazanta day,ka Barni na sarara idan na isheka da wari ka rufe hancinka ni da wanka sai dare "
"Aw ashe ma za kiyi ai ni duk tunanina baki ɗaya baza kiyi ba,to ina san ki sani ɗaki mun raba ki koma naki ba zai iyu ki mayar mun ɗaki kamar na yan iska ba,Kinga falon nan haka wallahi ko shi ba zan ɗauka ba ki san yadda za kiyi na dai faɗa Miki".
Kitchen ya nufa yana ji tana cewa wallahi bai isa ba,shi dai bai kula ta ba ya shiga kai tsaye,window ɗin kitchen ɗin ya gani a buɗe kudaje nata waƙe bisa ƙwanikan da tayi amfani dashi,daga gani ta shiga tsaminsu ya isheta ta buɗe window ɗin,kai wannan mata akwai annakiyar ƙazama.
Fita yayi ya tarar da ita tana tsince falon, tsaki yayi yace idan kin gama Wallahi ki gyara kitchen ɗin chan aikin banza kawai,ta saka karfi da yaji ya koyi tsaki kamar wani tsaka,kullum wannan matar tashi da sabon salon dabi'u take,kamar wasa ta fara ƙazanta gashi yanzu tana san zama mata dabi'a ko ma yace ta zama.
Car key ya ɗauko,ya juya baya ta biyosa kamar zata dakesa,yana juyowa tayi saurin duƙawa kamar zata ɗauki abu,kaɗa kai yayi yace "Allah ya mun tsari da shaiɗancinki Zainab"da haka ya fita yana jin tana ta dariya kamar ta zare,at this point ya fara tunanin ta zare ɗin ba kaɗan ba shine shima take san ya haukace bayan Allah ya fita.
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔
𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎
Na
𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay)
E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟20:
*𝘡𝘜𝘕𝘈𝘐𝘙𝘈𝘏*
Tafiya nake kamar wadda laka ta fashewa a ciki,yau da kasala na tashi , na san idan na zauna a gidan babu abin da zanyi,ina ƙoƙarin tsallaka titin Adaidaita sahu ya tsaya,daɗi kasheni ,da saurina na ƙarasa nace"BUK".
Ganin Adaidaita sahun Khubayb ce sai nayi mamaki, Khubayb?na faɗa da mamaki dan ban taɓa tunanin nan ɗin hanyarsa bace.
"Barka da safiya Hajiya Zunairah muje ko?".
"Idan har ba za ka ɗauka passenger ba zan hau ba".
Dariya yayi wadda ta bayyana haƙoran da ban ƙasa a gwiwa ba wajen hango teeth gap ɗinsa "kada ki damu ai aiki na fito Allah zan ɗauki passenger ".Murmishi nayi kafin na hau Adaidaita ina mai fadi mishi ina kwana.
"Kin tashi lafiya ya kwanan Mutanen gidan?".
"Álhamdulilah ".
"Masha Allah"da haka ya tashi Adaidaita sahun muka ɗauki hanya,muna tafiyane yake ce mun ,"mai zai hana ki bani number ɗinki idan nazo unguwarku da safe sai na ɗaukeki mu wuce makarantar,Kinga kin huta kuma nima gashi daga nan nake lodin passangers,in case kinyi Mamaki kince wannan mene ya zai na kawo shi nan da safe ko kuma ki yi gudun zan latti sha kuruminki a nan tsamiyar boka na samu gurin zama kwanan nan".
Ban ce komai ba illa murmishi da nayi na ƙarbi wayarsa na rubuta mishi numberta,godiya ya yi mun ya kira layina number ɗinsa ta shigo nayi saving da Khubayb.
Bai sake mun wata dogowar hirar ba har muka cika Adaidaita sahun da yan makarantarmu ,da na haɗu da Anisa haka nan na ganta kamar wata mara lafiya baki ɗaya tayi pale da ita kamar wadda bata da jini,cike da damuwa nace da ita"Anisa baki da lafiya ne?".
Cikinta da ta riƙe take nuna mun tana cije baki wanda ba sai an faɗa maka tana cikin ciwo ba,bata da lafiya idan ba abun Anisa ba mene ya kawo ta makaranta?
Kama mata kafaɗa nayi ina mata sannu duk da ban san takamaimai mene ba amma ganin cikin da take nunawa ya saka na barshi a kan cikinta ke ciwo,duk yadda ta so mu gama lecture abin sai ya ci tura,excuse muka ɗauka muka bar hall ɗin ,rasa abin yi nayi musamman ganin ta rike gefen cikinta ta kasa cigaba da tafiya tana kuka,Nima kukan nake dan kaina ya kulle na rasa tunanin mene zanyi, Khubayb ne ya faɗo mun,babu ɓata lokaci na kirasa ,lokaci mara yawa ya ɗaukesa ya zo,tare muka taimaka aka sakata cikin Napep ɗin a wannan point ɗin she's unconscious,pass ya basu a bakin gate kafin muka ɗauki hanya,kuka kawai nake ina kiran sunanta akai akai cike da tsantsan tashin hankali,tunda nake da ita ban taɓa ganinta cikin yanayi irin wannan ba,Yaya Halil na kira na sanar mishi,nan ne yake cewa mu wuce da ita asibitin da suke zuwa na Garkuwa zasu same mu chan,a haka muka ɗauki hanya dan zuwa Asibitin Garkuwa,ban mamakin ganin Yaya Halil a chan ba,kai tsaye aka shiga da ita emergency domin bata taimakon gaggawa.
"Mene ya faru?".yaya Halil ya tambayeni.
"Dama na shigo makaranta naganta wani iri na tambayeta shine take ce mun cikinta,to muna Lectures abun sai yaci tura muka ɗauki excuse to muna fitowa kuma shine sai hakan".
Baice komai ba amma damuwace fal ransa,zuwan Enen ce take faɗin "Halil kidney ɗin ne ko?".
"Wallahi Enen ina gudun abin da muke tsoro shine zai faru,shi yasa nace ayi aikin nan tuntuni ta tsaya gardama ke da Daddy ku ka biyeta".
Ni dai da ba fahimtar inda zancen nasu ya dosa ba addu'ata guda ɗayace Allah ya bata lafiya ya kawo mata wannan al'amarin da sauƙi,bayan wasu lokuta likita ya fito yake mai shaida musu sun samo kanta amma tana bacci,neman yaya Halil ya yi da yana san magana dashi,jin hakan ya saka Enen shiga ɗakin.
Bayan wasu lokuta ni duk lokacin ina waje gudun kada na shiga tunda babu wanda ya mun tayi,Yaya Halil ne ya dosuni,da damuwa na tashi daga zaunen da nake ,da ya ƙaraso gurina ne nake tambayarsa jikin nata shine yake faɗa mun"kidney failure ne,tana fama da ESKD,end stage kidney disease dalilin kidney cancer wanda dole sai an mata transplant,last time na faɗa musu doctors ɗin sunce tana buƙatar wani amma yarinyar nan ta kafe kan a ɗorata a kan maganai".
Rasa abin faɗa nayi sai hawaye dake bin kuncina ɗaya Bayan ɗaya, bakina na karkarwa nace"amma Yaya Halil will she survive it?".
"Abun da muke fata kenan,insha Allahu she will survive it,cikin ni Ko daddy ko Enen I'm sure duk wanda tissue ɗinsu ya zama compatible zamu bata, she's going to be okay"ya bani amsa kamar bai yadda da kansa ba.
"Zamu iya shiga ciki"ya sake faɗa.
"Taje ina munafukan Allah?"
Muryar Zainab Pagal ta Mana sallama, sunan da Hauwa'u ke kiranta dashi kenan,da zafinta ta ƙaraso tana mai cewa"Hala tayi ciki kun zo ku zubar?".
"Ya subhanallah Menene hakan wai Zainab mene yake damunki da a rayuwa baki da aiki sai jawa mutane Bala'i? tukunna ma da kika fito wa ki ka tambaya?".
"Aw sai na tambaya?kai ka ɗako daɗironka kuka zo nan ka tambayeni?'A'a dan haka ka rufe mun baki ba wannan nake san ji ba,uban mene ya kawoku asibiti tare?ai tunda ka taho nake binka a baya ina mamakin abin da kazo yi ashe ga amsata".
Wani irin kaɗa jiki take,ni dai babu abin da nake sai kallon ikon Allah,ace mace kamar yar daba,bata da aiki sai faɗa, Wannan idan aka ce maka tayi shure shure na masifa cikin mamanta ba zaka Musa ba,juyawa nayi na shiga ɗakin da aka mayar da Anisa na barsu su ƙare lafiya,ina ji tana ihun na dawo ko na kasa gane kaina,ban kula ta ba sanin babu amfani biye wadda bata tsoran iyayenta ko kaɗan,da ace tana tsoronsu babu abin da zai saka ta sake kulani,ina ƙoƙarin shiga ɗakin naji an turani cike da faɗa yaya Halil ya ce"wai mane haka Zainab baki ji ko?da ciwon Anisa za muji ko da tijararki?".
Sai a wannan lokacin ta kula da Anisa dake kwance baki ɗaya ta sauya kama lokaci guda,mayar da kallonta tayi kan Enen wadda babu abin da take sai aikin hararar Zainab,cike da borin kunya tace"Enen ashe Anisa ce rai hannun Allah ai ban sani ba,ya jikin nata,na zata wallahi Halil tare yake da yar iskar nan duk da bana lamuncin hirar da na tarar sunayi".
"Álhamdulilah Zainab da ki ka san Anisa ranta a hannun Allah yake ba a naki ba,nayi imani da Allah da ace ranta a hannunki yake da tuni kuma wannan haukan ki ciresa,ace ke a rayuwa baki da aiki sai bala'i,kada fa ki saka kiyi abin da zai dameki dan Allah na gaji da Lamuni".
Haɗe rai tayi wanda ya nuna Maganar Enen tayi mata Zafi sai wani cije baki take, kai wannan da ace namiji ce ba ƙaramun shiryayye za ayi ba,wallahi duk tunanina ba zata kuma cewa wani abu ba ganin Enen ta mata kashedi,wai sai cewa tayi "mumze a huce amma gaskiya ni bana san kina mun magana a haka,babu wanda na taɓa idan nayi faɗa akan abuna a ɗaga mun ƙafa kada a danne mun hakkina".
"Aw Halil ɗinne abun ki?"Enen ta tambayeta baki buɗe,sake tsuke baki Zainab tayi kamar ka saka almakashi ka datse ɗan banza.
"To Enen mene ki ke so na faɗa".
Jin furucin da tayi ya saka Yaya Halil da Yake binta da kallon Mamakin kama hannunta ,sai da yaje bakin ƙofar ya ɗaɗa mata duka a baya kafin ya watsata waje ya saka key,duka ƙofar ta fara tana yan ihunta kafin lokaci ɗaya kuma muka ji shiru.
Tsaki ya yi ya ce"masu tsaron asibitin sunyi gaba da ita, wallahi Zainab sai da haka,idan tana wani abun kamar bata da hankali".
"Anya Halil yarinyar nan bata ƙwaya kuwa?"Enen ta faɗa cike da alhini.
"Babu wata ƙwaya baya ga iskanci wallahi,kamar a kanta aka saukar da dukkan wani iskancin duniya kullum kuma abun nata sake gaba yake".
"A dai bincika dan wannan yarinyar ban yarda babu sharrin ƙwaya ba, kana kallon cikin Idanunta kamar an tsaga rashin kunya?gaskiya da sakel ace duk duniya Zainab tayi maka matsayin mata?".
Ganin za su wuce suyi maganar da bai dace gabana ba ya saka na sauya zacen nace"yanzu Enen yaushe suka ce zata farfaɗo".
"Ƴata yi haƙuri ina nan ina mita ga Anisa da likita yace kada a cika ta da hayaniya, ya dai ce zata farfaɗo bai faɗi lokaci ba,Nagode sosai da ki kayi saurin kawota asibiti Allah ya yi Miki albarka ".
"Amin Enen ai yima kaine,bari dai na wuce in yaso ko da su Mama sai mu dawo tunda ban faɗa musu ina nan ba ".
"Ai kada ki damu,ki huta idan ta tashi na faɗa mata kin wuce amma kada kice zaki damu kanki wai ki dawo anjima,ai nayi admitting ɗin mu har ayi mata aiki idan yaso gobe idan da hali sai ku zo ɗin ,suma ai ba a tasosu ba zato ba".
Ba dan na so ba dai na ɗauki maganar Enen,Yaya Halil ya yi tayin kaini gida,ban ƙasa a gwiwa ba na ƙiya sanin mene sakamakon binsa a motarsa,ƙila dai ƙarshe so yake matarsa ta ƙoneni kowa ya huta,duk yadda naso aka kada ya mayar dani gida haka Enen ta saka baki dole muka jero a tare muka fito.
"Baki da wata tambaya da za kiyi mun?"muryarsa ta katsen saƙesaƙe zuci.
"Yaya Halil ya kamata nayi maka wata tambayar ne ban sani ba?I mean mene ya kamata na sani?".
Ɗan sosa kansa ya yi da yatsa ɗaya kafin yace"akan Zainab mana,baza ki tambayeni komai ba?".
"Yaya Halil mene ya saka zan tambayeka abin da ya shafi gidanka?ko wane gida da nasu kai shine na gidan ka ina maka fatan Allah ya sassaita maka,matarka ce kana santa tana sanka atleast zaka iya nuna mata daidai,ni Alfarmar Abu ɗayane dama shine ka faɗa mata babu abin da ya taɓa shiga tsakanina da kai dan Allah ta daina kawo mun hari".
Gani