Chapter 2 Reading Cin Duniya Book Compelet Hausa Novels By Chuchujay Arewa Novels

Cin Duniya Book Compelet Hausa Novels By Chuchujay

Author :  Chuchujay Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   2 / 16

3K to 6K   out of 45.5K words

na ɗaga na ɗaukesa da mari,take hawaye ya fara bi mun kunci ga wata karkarwa da ta kawo mun ziyara,hannu ya ɗora bisa kumatun yana mun wani irin ɗan iskan kallo yana lasar leɓensa kamar wani tsohon maye,ganin yana sake tunkaroni ya saka na wawuri ƙaramar wuƙar dake kan cart ɗin ina mai zazzaro idanuna ina nuna shi da ita.

Bakina na karkarwa na ce"kana matsowa sai na Chaka maka wallahi".hannunsa ya ɗaga alamun surrender har a lokacin yana mun wannan ɗan iskan kallon da nake jin kamar nayi ta marinsa har sai wannan marin ya ɗauke wannan yanayin nishaɗin dake kan fuskarsa.

"Zunairahhhhhh..."ya ja sunana cikin wata irin siga ta riƙaƙƙuna yan bariki.

Cigaba nayi da nuna wuƙar jikina na karkarwa hankalina kuwa idan ya yi dubu ya tashi.

Hanyar fita na nufa ,bai hanani ba bai kuma biyoni ba,burina kawai naga na fita a ɗakin dan bana tunanin Anisa ma,ina jin tana kiran sunana lokacin da na buɗe ƙofar na fita,biyoni tayi amma gudu kawai nake iya ƙarfina har na bar cikin gidan,Allah ya saka jakata na bayana ban sauke ba kuma ina da kuɗi a ciki duk da na san ba isa ta zai ba,hakanan na fara trekking ,sai da na rage tafiya sosai kafin na samu wani mai adaidaita sahu ya ɗaukeni akan Naira ɗari biyu da hamsin ya aje ni tsamiyar boka.

Na jima a bakin layin mu ina saita kaina gudun kada kowa gidan mu ya fahimci halin da nake ciki sanin cewa a yanzu suna nan suna jirana.

Da sallama bakina na shiga gida ,banga kowa tsakar gida ba kai tsaye na shiga Falo ina sake jaddada Sallamata,cracker ɗin da aka saki ya razanani kafin suka fara fitowa daga ɗaki da cake madaidaici hannun Baba suna masu mun waƙar happy birthday.take na fashe da kukan da nake jiran nayi,cikin tashin hankali Mama ta ƙaraso ta kamani jin yadda na fashe da kuka.

"Seduwe suné? "(mai yasa ki ke kuka?)Mai ya faru?,mama ta tambaye ni cike da damuwa.

"Ayamo hine"(ina farin cikine)Mama,na kasa riƙe kukana.

Rungumeni mama tayi,tana mai kissing kaina kafin su Baba suka ƙaraso suka bani runguma baki ɗayansu,take naji dukkan wata damuwata ta yaye,haka nan na sake ina mai jin kamar babu abin da ya sameni.

Mama ta bani ƙyautar wata azurfa da nake ta maitar ta bani amma tace Maman baba ta bata baza ta bani ba,Baba kuma ya bani set ɗin Eweh(beads)wanda aka kawo daga kogi ashe yana ta ajiyar su yana jiran birthday na yazo ya bani,sarka ne da ɗanƙunne da abun hannu masu kyau.

Hauwa'u ta bani sabon journal mai pen a jiki wanda ta tara kuɗin break ɗinta ta siya mun .

Muhammad kuma ya bani set na pens ɗin barbie doll masu kyau wanda Hauwa'u ta shiga sahad da kuɗinta da nasa suka siya mun.

Al'adar gidan mu ce sharing gifts ranar birthday kowa yana san Faranta ma ɗan uwansa ,ba san kai ba yan gidan mu muna da san junan mu da tausayin juna.

Haka ranar ta ƙare mun cikin farin ciki,duk yadda zan yi na yi ganin na manta da wani Adam da abin da ya yi mun,abu ɗaya na sani wanda shine ban yafe mishi ba ,Allah ya isa na,sa'arsa ɗaya ɗan uwan Anisa ne da saina mishi wulaƙancin da bai taɓa tunanin zan mishi ba,amma kash duk wani abu da ya danganta da Anisa mai daraja ne a gurina.

Washegari muka yi shirin makaranta kamar kullum ,Muhammad muka fara ajewa kafin muka wuce namu gurin,na riga Anisa zuwa kasancewar babu assembly ranar ya saka direct aji na wuce ina mai jin kunyar haɗuwa da Anisa haka nan kawai dan Ban san mene zan faɗa mata ba.

Latti tayi na zuwa dan lokacin da ta shigo har an fara first class,a chan sit ɗin baya ta zauna kasancewar namu an zauna ,naji daɗin hakan dan ko kallonta ban bari nayi ba.malamin na fita daga class ɗin Economics teacher na tsaye yana jiran sa ,ba ƙaramin daɗi naji ba duk da na san dole muyi magana amma atleast na samu break.

Ille kuwa ana fita break ta dawo gurina ta zauna,ina ƙokarin tashi ta kamo hannuna ta ce "kamar muna da pending magana,mene ya saka ki ka gudu ina ta kiran ki baki ko juyi kin kalleni ba?,wani abu Yaya Adam ɗin ya yi Miki?".

Ajiyar zuciya na sauke kafin na zauna ina mai kallanta"Ni nace miki ya yi mun wani abu?,kawai ina tsoran kada nayi dare ne".

"Zunairah kenan,i thought na faɗa Miki har gida zan sauke ki and na yi imani da Allah idan Mama ta ji tare muka fita babu abin da zata ce,ban ji daɗi ba,he told me ai daga ya ya hugging ɗin ki ne,he was wrong for doing that duk da ba wani aibu bane shi yake gani a gurin sa amma ai da kin tsaya,har magana nayi mishi ya ce na baki haƙuri,ki yi haƙuri".ta faɗa tana mai bina da kallon da ta san bana iya ce mata a'a idan har ta marairace mun, although bai faɗa mata part ɗin kiss ɗin ba nima sai na zaɓi da na ɓoye mata.

"Dan Allah kinji ki yi haƙuri ba zai ƙara ba na Miki alƙawari"ta sake faɗa tana mai marairacewa fiye da farko.

"Naji na haƙura but gaskiya ba zan iya cigaba da kula Yaya Adam ba ,yanayin rayuwarsa da tawa ba iri ɗaya bace Anisa kema kin sani,da ace wani ne ma da wallahi sai na masa wulaƙanci but ɗan Uwanki ne ,ni kuma duk abu indai ya dangance ki ba zan iya mishi wulaƙanci ba".

"Baki haƙura ba kawai zakice mun besty,nace Miki ya ce fa ki yi haƙuri ba zai sake ba, besides har kyautar da ya tanadar Miki ya bani na baki zai baki haƙuri da kan sa".hannu ta saka ta ciro ƙwalin waya na Tecno ƙirar pop 10.

Dariya kawai nayi taƙaitacciya,yo ko giyar wake na sha ita kanta ta san ba zan taɓa karɓar wayar yaya Adam ba,koda kuwa ita ta bani ba shi ba zan ƙarɓa ba,sai nace da iyayena mene?

"Bafa zan karɓi wayar nan ba Anisa ba da wasa nake ba,So ki ke na shiga uku hannun Baba da Mama su ce dan basu bani bane and Baba ya yi mun alƙawari ina gama secondary school zai bani waya so i want to give him that chance bana san sage masa gwiwa, understand me please".

Mayar da wayar tayi haka without further nagging kafin ta ce"its okay,so Daddy ke tambayana wani course zanyi idan naje BUK,like duh I told this man fa Journalism muka zaɓa but this man is trying to push me to public relation ni ba zan iya ba muna tare a Buk,idan ban samu ba ko ke baki samu ba i will stick to wanda kika samu ke koda Kazaure ne,so suke su turani Canada ba zan iya ba"

Ɗan shiru nayi ina nazarinta,ina mamakin Anisa ,wai ka samu damar tafiya Canada ka samu karatu mai inganci amma kace kai a'a ba za ka je ba, Journalism shine burina ,naji ance a bangarensu ana rubutu,burina naga ina rubuta Jarida na shirya dukkan wani content ɗinta abun haka kawai yana bani ƙawa,lokacin da zamu yi jamb Anisa bata cike ba sai da na cike kafin ta cike duk wani abu dana saka a nawa kama daga management school,second choice,Kazpoly ,da makarantun Fashion and design,ko da nayi mata Magana akan kada ta biyeni sai cewa tayi idan babu ni babu ita,abun yana burgeni sosai Wallahi amma bana san ace ta cutar da kanta dan kawai tana san alaƙarmu ta ɗaure,Bature yace out of sight is never out of mind,ni dai na san duk inda Anisa zata shiga a faɗin duniya ba zan taɓa cireta a Zuciyata ba haka nan ita.

"Idan har yana san naje Canada ɗin ya biya mana tare".

Murmushi nayi lokacin da maganarta ta jawo ni daga duniyar tunanin,Baba ne zai barni naje Canada da kuɗin wasu?tab har yanzu Anisa bata san su wane iyayena ba,bamu raina namu bamu hangen na wani.

Tashi nayi na ɗauki jakata ina cewa"well Journalism is my purpose,I found my purpose a chan ban san mene ke ki ka samu a gurin ba,don't rush babes".

"I found you"ta faɗa itama tana mai tashi,fara takawa nayi dan barin ajin tana gefena,dawowa tayi ta gabana tana takawa da baya tana cewa"idan ya zama na ɓata i want you to be there for me,na fi sabawa da ke ,Sabone da bana san wani daban ,i choose you babe,so your royal majesty Ohunene I want you to hold my hands and guide me in bayero University ".
Ɗukawa tayi kamar yadda ake yi a gidan sarauta,ban san lokacin da na saka dariya ba sosai musamman da ta kusa kaiwa bakin kofa,kin faɗa mata nayi na cigaba da dariya sai ji tayi ta bige.
Dafa gurin tayi tana faɗin"occh you're wicked wallah Zunairah ".muna dariya a tare muka fita domin zuwa yin break.
𝘊𝘩𝘶𝘤𝘩𝘶 𝘫𝘢𝘺✍️
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔

𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎

Na

𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay

EPISODE 3:viper in her bosom.

*𝙰𝙽𝙸𝚂𝙰*

Tunda ta rabu da zunairah bayan tashi makaranta take jin ranta ya mata wani irin nauyi,babu abin da ke ɓata mata rai kamar yadda a kullum zunairah ke nuna ita mutuniyar kirkice,yana ci mata tuwo a ƙwarya musamman da ya zama babu yadda za tayi sai dai ta ɓoye muddin tana so ta cigaba da naɗewa a sheƙarta,bata da wani buri da ya wuce a rayuwa a ce yau ta wuce zunairah,ta san cewa rayuwa ba gasa bace amma a nata fagen ta shata layin tsere tsakaninsu,dole ne duk yadda za ayi at the end of the day ta cinye wannan tafiya ta tsakaninta da Zunairah.

Idan za'ayi jarabawa hana kanta sakat take burinta guda ɗaya wanda bai wuce taga ta fi Zunairah cinyewa ba sanin idan ba haka ɗin ya kasance ba ta gamu da kumfar baki a gida dan basu da aiki sai faɗin ta kalli dai Zunairah,basu taɓa nuna mata nata ya yi sai dai a ce da Zunairah ce da ya fi haka,kada ma mahaifinta ya ji labari,he like comparing them wanda hakan yana mutuƙar ɓata mata rai.

Exam na ƙarshe ta wuce Zunairah wanda ta saka hakan a ranta matsayin farin wasan dan baza ta ɗaga mata ƙafa ba idan sukaje jami'a,yana ɗaya daga cikin dalilin da ya saka ta nace sai course ɗaya za suyi amma bayan haka ko burgeta aikin jarida bayayi,this is a war that she must win,kamar yadda zunairah tace Journalism is her purpose,ta yarda ita ba nata bane dalilin hakan ya saka take ƙara ƙaimi wajen ganin ta daketa a nata so called purpose ɗin da ta ke ikirari.koda ƙasar da tafi kowacce ƙasa tsadar da jin daɗi za a kaita tayi karatu baza ta je ba,tana nan Buk da zunairah taga tsakaninsu wane zai winning.

Ɗabiun Zunairah na munafurci suna ɗaya daga cikin abin da ke ɓata mata rai,dan a nata yardar duk wani sumi sumi da zunairah take yi munafurci ne,ta bata waya tana wani faɗin bata so bayan ta san ko babanta zai siya mata waya ba zai iya affording wadda Adam ya bata ba,tana jin haushin dabi'unta na nuna bata san abin duniya,ko kayi mata Abu ta mayar dashi wani babban abu kamar wadda ka bama duniya,that particular attitude yana kaita maƙurar da take ji kamar ta shaƙeta sau tari.

Ƙawance su ya fara lafiya ƙalau kafin ta san kanta tayi wayau dan a gida ko chocolate aka bata da suna nursery sai an bata na Zunairah take tafiya,ba zata ce ga yadda aka yi ba amma makarantar bata dace da tsarin arziƙin mahaifin Zunairah ba but haka nan ya saka ta ,haɗuwarsu ya fara da gurin zama da aka haɗa musu kafin term ya ƙare sai shaƙuwa ta ƙullo tsakaninsu tun kafin su san ma menene shaƙuwar,haka nan Anisa bata da aiki sai maganar Zunairah Buhari wanda hakan ya saka iyayenta suka santa sai suka ƙaunaceta kamar yadda suka ga ɗiyarsu nayi.

Duk da cewa zunairah ta fi Anisa ƙokari bata damu ba ,idan tazo gida tana cewa an koya musu kaza zunairah ta cinye sai babanta ya dinga mata mitan zunairah zai koma siya ma abun daɗi da teddies Banda ita,har ga Allah a lokacin ko a jikinta dan takan ɗauki nata na gida ma ta kaimata,hassadar bata fara ba sai da suka shiga primary 5,haka kawai sai tana jin bata so ta fita,da suka zana Junior WAEC lokaci guda Zunairah ta zaɓi Art.

Anisa was not expecting that dan tunaninta ƙokarin zunairah science zata kaishi,burinta bai wuce ta zama Doctor ba domin a tunaninta itama Zunairah haka ne dan har ta fara tunanin yadda za su fafata a Wannan fagen amma wai aikin jarida,haka nan ba dan tana so ba itama ta zaɓi Art ,abun da ke ƙona mata rai shine idan Zunairah ta ce mata wai ba purpose ɗinta bane,yo ai ta daɗe da aje wani purpose da kowa ke tunanin, purpose guda ta riƙe wanda shine wuce Zunairah a rayuwa.

A ƙofar gidan su Adam driver ɗinta ya faka ta fito,kai tsaye ta shiga tana mai share gateman ɗin dake gaida ta ,shi kuma kamar masifa Indai zai ganta sai ya gaisheta.

Kai tsaye tana shiga ta murɗa handle ɗin kofar falon ta shiga tana ƙwala mishi kira,jin bai amsa ba kuma tana jin motsi a sama ya saka ta haura ,duk takunta nishin da take ji yana kusanto ta,daga ɗakin yaya Adam ne,kai tsaye ta isa ƙofar ta murɗa,ba tayi mamaki ba ganinsa tayi kan mace yana ta aiki ita kuma tana ta faman surutai,basu ma san ta buɗe ƙofa ba dan haka ta koma dan jiransa dan ta san last abun da za tayi shine katsesa,iyayen Yaya Adam sun tafi vacation dan haka gidan ya zamana a hannunsa shi kaɗai yake sheƙa ayarsa.

Bayan wasu lokuta taji suna saukowa suna ƙananun dariya,macen ta fara ganinta ,cike da tsoro ta dafe ƙirjinta dan bata yi tunanin ganinta ba dalilin hakan ya saka ta tsorata.

Tsaki Anisa tayi tana mai bin su da kallo,yaya Adam ne ya sauko yana faɗin"sis Ani yaushe ki ka zo,You should have call me".

Wani kallon ta masa kafin ta saka hannu cikin jakarta ta ciro wayar ta miƙa mishi ta ce"Zunairah taƙi karɓan wayarka Sannan ta ce dan Allah ka rabu da ita and Nima da nazo gidan nan na goyi bayan ta domin da ace na san kana fucking Yaya Hibba ba zan bada gudunmawa ta ba".

Da sauri Hibba ta matso inda take tana cewa"innallahi cousin sis ta yaya zan fucking Yaya Adam?he's my cousin for God sake,Allah ya kiyaye, besides ni ba mazinaciya bace kada ki sake dangantani da wannan harkar ".

Dariya Anisa ta saka sosai kafin ta sake miƙa masa wayar da yaƙi karɓa yana kallon ta"yaya Adam ka karɓa na wuce dan Allah,dan naga alamun yarinya ake san mayar Dani,for your information Yaya Hibba kina wannan Surutan na shigo baku ma san na shigo ba and ni a samanki naga Yaya Adam and it doesn't seem like yana koya Miki assignment ne".

Shiru duka suka yi ,ganin ya ƙi ƙaraɓar wayar ya saka ta aje mishi kan kujerar ta juya ta fita ,biyo bayanta Hibba tayi tana mata Magana amma tayi mata banza.

Hibba yarinyar ƙanwar Mahaifiyar Adam ce,bangaren Anisa kuma yarinyar ƙanwar mahaifintan ce, tunda mamanta ta rasu ta baro Nassarawa ta dawo gidan su Anisa ,duk yadda mutanen ƙauyen Aila na ciki Benue suke mitar ta dawo ta zauna da yan uwan mahaifinta abun bai iyu ba dan a cewar Mahaifin Anisa Hibba baza ta iya zaman ƙyauye ba tunda ko iyayenta ɗin cikin Lafiya na Nassarawa suke da zama,tun lokacin ya dawo da ita gidansa.

Anisa ta ji daɗin zuwanta dan dama bata da yar uwa Yaya Halil kuma ba mazauni bane ,idan ma ya zauna ba hirar da take sakewa ba suke, its always about school da abin da take so a siya mata ,babu zaman wannan gossip ɗin na mata,amma Hibba kuwa zasu zauna su ɗan tattauna abin su duk da cewa Hibba ɗin ta bawa Anisa kusa shekaru huɗu.

Abin da ya ɓata mata rai da abin da ta Kama suna yi da Adam shine ɓata mata Rayuwa da yake,ta san Yaya Adam baya ji amma bata taɓa tunanin zai bi ta gida ba ,a hakan ko Zunairah a wannan gaɓar dai bata fatan mata ya lalata mata rayuwar,Hassadar da ke tsakaninsu bata tunanin a Zuciyarta ta kai wannan stage ɗin,wani lokacin idan tana irin wannan tunanin sai tama rasa ina ne ta dosa a tafiyar,shin har yanzu tana san Zunairah ɗinne kamar farko ko kuwa competition,idan competition ne mutane kan bin ko wane irin logic domin gannin sun cinye amma a Wannan gejin ta fi son Free and fair competition,bai kai deep ɗin da zata so Adam ya lalata ta ba dan haka dole Ya manta da Batun Zunairah.

Tana shiga gida a falo ta tarar da mahaifiyarta tana kallo,abun da ta tsana ta tambayeta shine abin da ya fara fita bakinta bayan sun gaisa,wai ina Zunairah.

"Tana lafiya"ta bata amsa a taƙaice kafin ta yi ƙokarin shiga ciki domin Cire kaya.

"Ya kamata dai ta kawo mana ziyara ".

Tana jin Muryar Enen na mata maganar tayi mata banza ta wuce ciki, enough Zunairah drama for the day,sai a jira na gobe (Enen da Idoma shine sunan da Anisa take kiran mamanta,ma'ana Mama).

Bata jima da dawowa ba Hibba ma ta dawo a tsarge domin duk a tunaninta Anisa ta faɗa abin da ta kamata tana yi,idan kuwa ta tona mata Asiri ta shiga uku dan ta san ƙarshen zancen sai ta koma Benue ,ganin sun gaisa da Enen faran faran ya saka ta doshi ɗakin Anisa,kwance ta tarar da ita kan cikinta tana danna waya,zama tayi gefenta,ko kallonta Anisa ba tayi ba ta cigaba da taɓa wayar cike da tsoro ta fara magana .

"Nisa I'm sorry Mana,it's not like Ina bin maza ne,Ni da Yaya Adam muna soyayya ne and bana tunanin big deal ne dan mun ƙarama soyayyarmu ɗanko ,i just want you to understand Aurena zai yi".

Da Mamaki Anisa ke kallonta kafin ta ce"shi Yaya Adam ɗin

2 / 16