Author : Chuchujay Category : Romantic Hausa Novels
kwanta asibiti amma ki kasa faɗa mun?rabu dani da wasu gifts abeg ya ki ke yanzu,ya jikin ?".
"Stop being a drama Queen best friend,I'm okay and ni na hana Enen faɗa Muku,kin san na fi so a ganni a best halittana."kamo hannuna tayi wanda Idanunta suka sauka akai,cike da tsantsan Mamakin da bata yi yunƙuri wajen ɓoyewa ba ta ce"wane ya baki wannan zoben mai shegen tsada da aka yi engraving sunanki ciki piece of diamond?".
"Diamond kuma?ba dai diamond ba".na faɗa ina mai mayar da hannun baya,kamo hannun tayi tana mai sake kalla lokaci guda kuma tana san cirewa daga hannuna wanda ban ƙasa a gwiwa ba wajen ganin ban bari ta cire ba,amma fa jikina ya yi sanyi,wai diamond menene haɗin Zunairah da diamond?""
"Wallahi diamond Zunairah,zan kasa gane diamond ne ko zan Miki ƙarya?Wane ya baki?ina ki ka samu? Mu gani dan Allah".
Gyaran murya nayi ƙarama kana na ce"zoben Alƙawari ne ,saurayina da nayi ya bani although da na san diamond ne ba zan karɓa ba"take ta rikice tana mai sake tambayata cikin ƙaguwa,wanene wannan guy ɗin?aikin mene yake,?,a ina ku ka haɗu da shi?,mene sunansa?,Dariya ta bani jin lokaci guda tana san sanin baki ɗaya Waɗannan informations ɗin a bakina,how wish zan iya faɗa mata,amma maganar zoben da ta tashi sai na ji ina san magana da shi kafin na sanar mata da yayanta ne dan haka na ce da ita zan sanar mata cikin ƙwanankin nan.
Duk yadda ta yi nacin san sanin wanene ban iya faɗa mata ba ,a haka ta haƙura tayi respecting decision ɗina kan idan na shirya na faɗa mata wannan saurayi da nake ta ɓoyewa ,fatanta ɗaya Allah yasa ba ɗan yankan kai bane , murmushi kawai na ɗinga yi,har na hango fuskarta lokacin da ta san Gaskiyar,duk da rashin sanin wanene ɗin bata ɓoye irin farincin da take tayani ba har tana tsokanata na fito daga kogin san Ma'aruf zuwa ga mysterious guy,cikin hirar da muke ne na ce"yauwa Anisa,so nake na ƙarɓi Draft na littafaina especially Love Scenery ɗin nan".
"Mene za ki yi da shi"ta tambaya tana mai nuna interest ɗin ta ,gyara zama nayi ina mai sake yashe baki "Kinga yanzu mun gama makaranta and ina da smartphone ina da laptop so nake na cigaba da rubutu a matsayin Career and Kinga Wannan Love Scenery ɗin?I was told zai karɓu sosai ".
"Inji wane ya ce Miki hakan,i mean beside me wane ya san da shi?".ido ta zuba mun tana neman jin amsata wanda ban ƙasa a gwiwa ba na bata Amsa"wata marubuciya na haɗu da ita mai kirki,ina yawan karanta books ɗin ta kwana biyu da na yi waya so sai na tambayeta shawara because sananniyace and litattafan ta na fita sosai a Ebooks tana samun kuɗi,so na bata labarin idea ɗin da nake da shi especially na Love Scenery and she told me idan na sake shi duniya zata so shi,and she will be there to Guide me,ba ki ji yadda na ji daɗi ba, Although da farko i was beyond Nervous amma yanzu kam ji nake kamar ban taɓa shiryawa ma Rubutu ba yadda na shirya karɓarsa yanzun,i want the world to hear me shi ya sa na zaɓi harshen Turanci duk da zan rubuta Hausan idan tafiya ta yi tafiya but yadda Hausa na bai goge ba ina san na ƙara gogewa duk da masu jin Hausa kawai ne zasu karanta ,but it will worth it dan akwai issue da nake san addressing wanda society ɗin mu yanzu ke fama da shi a hannu ɗaya muma Kinga mun zama Hausawan tunda muna cikin su".
"Kin zama dai amma ni Anisa har ƙwanan gobe Idoma na ke Ba abin da ya haɗani da Hausawa da issues ɗin su"ta yi saurin bani amsa.
Dariya na saka dan amsar nata ya bani dariya,"idan banda abin ki Anisa ai Hausawa sun mana rana tunda muka zo garin su muka Zauna,ki cire cewa Khalifa Yaren Margi ne either ways dukka Muna da matsalolinmu, idan kuma ki ka zauna ki ka duba sai ki ga abun kusan iri ɗaya ne,duk yarukan da ke akwai idan mun yadda abu guda ne sai dai banbanci na Al'ada amma abubuwan da ke faruwa in circle guda ɗaya ne a matsayin mu na mutane".
Taɓe baki tayi ta ce"ke dai ki ka jiyo,ni yanzu bama wannan ba drafts ɗin ki na littafi babu ko ɗaya da na san inda suke,but since kece ki ka rubuta I'm sure zaki sake har ma ki yi wanda ya fi wancan,i trust you,ko kuma ki sake labari because ba zan ɓoye Miki ba ba wani daɗi ya yi ba,don't take me wrong ita da tace ki rubutu ba karantawa ta yi ba,amma ni as a Bookworm na san irin littafan da ke ɗaukar hankalin masu karatu,Kinga Love Scenery ba zai taɓa ɗauka ba, besides yarinta ya yi yawa ciki which I can understand ya danganta da lokacin da ki ka rubuta shi,"
Shiru nayi ina nazarin maganarta,duk da ina san gamsuwa da batun nata amma sai na yanke shawara kawai zan rubuta shi ta wani salon na daban ba kamar new version ɗinsa tunda na riƙe labarin akai na,a haka ta bani ƙwarin gwiwa da tabbatar mun tana tare dani ɗari bisa ɗari.
Har nayi Haramar wucewa Enen bata dawo ba,na so na sameta mu gaisa ,riƙe jakana Anisa tayi tana mai shagwaɓe mun fuska kan na ƙwana bata gaji da ganina ba, dariya nayi na miƙa hannuna ina mai cewa"bani jakata tukunna"maƙe kafaɗa tayi kamar wata yarinya wanda yin hakan ya saka na ƙara darawa ina mai jinjina ƙarfin halinta,horn ɗin da aka yi daga Chan ya saka a tare muka kalli gurin kafin ta ce"Kinga mu je ya Sauke ki,yadda yake ta haɗe ran nan ba san kai ki ɗin yake ba,na fi tunanin ƙwarjini ki ka mishi wallahi".
Dariyata na ɓoye kafin muka taka ta rakani har bakin motar tana mai sake faɗin"yaya Halil kayi haƙuri dan Allah"ta bashi haƙurin nan ya fi irga, murmushi kawai nake ina mai hango abin da ni kaɗai nake gani a idanunsa.
Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da muka fita daga cikin gidan,dariya na saka wanda ya rasa abin da zai ce mun illa tayani da ya shiga yi mun dariya.
"Wallahi za ka dace da actor irin wannan haɗe rai kamar mugembu ya ga Amitha,kai wai a dole an dameka kana hutawarka zaka ma ƙawar ƙanwa alfarma,okay oo in munje last bus stop sai ka aje ni kamar yadda ka ce da fari"na faɗa abin na sake bani Dariya.
"Baby you caused all this,ni kuma bana so a ce na Miki abin da baki so,i will respect your decision,idan da ace zan bi abin da nake so,da zan nunawa kowa ke tawa ce ,idan na fara rawar kai kam,hmm sai kin ce mun ya isa haka,yanzu dai bari na fara kai ki shopping ina san na fake da hakan nayi ta ganin fuskar ki".
Dubansa na yi kafin na ce "aikuwa baza ka kaini shopping ba plus dama ina san nayi da kai,mene ya saka ka siya mun expensive zobe, diamond for that matter?".
Dariya ya sa wanda na kasa gane ta menene kafin ya ce"baby is just a piece of diamond,after all Bama pure bane duka,ki yi addu'a na yi kuɗi sosai zan siya Miki abin da ya fi na hannunki don kin yi Worthing more than duk wani abun da ki ke tunani,dan Allah ki daina magana idan na yi Miki kyauta sai ina ji kamar ban iya ba".
"Aikuwa baka iya ba,dan baka iya siyan Abu kaɗan ba ko mai madaidaicin kuɗi,ba komai bane about spending unnecessary money,bance kada ka mun kyauta ba,ina dai so ka na kintatawa ka daina ɓarna da kuɗi,and ni ka sauke Ni gida Babu wani shopping da zanyi"na ƙara maganar ina mai ɗan haɗe rai.
Ganin da gaske na haɗe rai ya saka ya samu gefe ya faka motar ya juyo yana kallona inda Ni kuma na sake haɗe rai na juyar da kaina ina mai kallon window,waƙar Auta waziri ya fara rera mun wanda yake faɗin sanki kamar ƙanƙara a ƙwalba,dariya sosai na saka ina mai toshe kunnuwana dan shi kan sa ba sai na faɗa masa ba, he's a terrible singer .
"Thank God Kana da aiki baza ka fara tunanin ci da waƙa ba cos babu inda za ta je".jin abin da na faɗa ya tabbatar mishi da na haƙura dan haka ya cigaba da zolayana da waƙoƙin da na tsinci kaina a nishaɗi domin su ,baza ka ce mun da wani Age gap ba dan aƙalla zai bani shekaru goma sha amma yadda yake zama yaro gabana sai abin ya sakani cikin jin daɗin.i found duk abin da nake nema ga Yaya Halil,ƙwanciyar hankali, soyayya,Farin ciki,shaƙuwa,babu abin da ya barni ina lalube domin samu,bai bar wata kafa ba ,dalilin haka ya saka bana jin akwai wani ɗa namiji da zai kawo mun tangarɗa dan kuwa soyayyar Yaya Halil ta shiga ko ina na jikina,kamar dai yadda dabi'ata take haka nan na zura dukkan jikina sanin babu wani matsala da zata ɓullo mana da yardar Allah.
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔
𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎
Na
𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchu jay)
E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟˚:7: Love ,treat,threats.
*𝘡𝘶𝘯𝘢𝘪𝘳𝘢𝘩*pov
Cikin Aminci rayuwarmu ta cigaba da tafiya inda komai yake tafiya mun dai dai Álhamdulilah,kamar yadda na ayyana a raina zan fara rubutun Love Scenery littafina da draft ɗin sa ya ɓata haka ya kasance,komai na cikin littafin a yadda na rubuta shi a baya sai na gyara shi na sake tsarinsa ta wata fuska daban amma dai Story line ɗin da Characters ɗina duk sune,sai da na kamalla rubuta shi kafin na fara saukesa a kan manhajar Wattpad da inkit da Dreame amma abun mamaki yadda nake expecting ƙarɓuwarsa ba haka abun yake ba,domin da nayi ƙoƙari shiga paid program ɗin su lokaci guda aka yi rejecting ɗina bayan sun gama reviewing littafin,da nake faɗawa Adda Ramlat marubuciyar da ta ɗora ni a kan hanya sai take ce mun kada na sare ,ba lokaci guda nasara ke zuwa ba sai anyi faɗi tashi tukunna ,a hankali lokacin da baka tsammani sai kaga abun ya zo maka kamar saukar ruwa ,da ƙwarin gwiwar da ta bani na cigaba da updating a wattpad ina mai sakawa a raina yanzu tafiyar ta fara sa'ar kuwa bata ga mutum Ubangiji ke badawa.
Ina ƙwance ɗakinmu ina typing a system ɗina Hauwa'u ta shigo da gudunta hannunta riƙe da wayana da na bata tana game,tashi nayi daga ƙwancen da nake ina mai matsawa da sauri kada ta takani kafin na ce mata "Ometere Are You okay? Mene hakan?".
Zama tayi tana mai nuna mun wayar dake hannunta"Auntyna Kalli ki gani comments ɗin dake cikin littafinki na Wattpad yana cewa wai kin saci littafin wata writer ,kalli nan handle ɗinta midnight Authoress".tashi nayi ina mai karɓar wayar ba tare da na damu da Hauwa'u ta kunna mun data ba ta shiga mun wattpad much more har ta san ina rubutu,abin da ban taɓa tunanin wani a gidan mu ya sani ba,shiga handle ɗin dake ɗauke da sunan midnight Authoress ɗin nayi, idanuna kan Followers ɗinta guda miliyan biyar suka sauka,kafin Wannan verifying button ɗin wanda ke nuna Wattpad ma sun san da ita,a hankali na yi scrolling zuwa ga littafanta wanda sunan da yan comment ke ta ambata na littafin nata na fara nema "BLUE",kafin na fara ganin wajen Guda shida baya,Bio ɗinta na duba,mutuniyar Najeriya ce yar garin Abuja baya ga wannan bata da wani information nata da ta ɗora , wannan littafi Mai suna BLUE har watty program ya shiga ,gashi nan ɗauke da tambarin wattpad,fita na yi da zumar zan duba daga baya inda na cigaba da karanta hate comment ɗin da na samu ƙarƙashin Littafin,harda masu ce mun daga fara Career ta ta rubutu na ɓata ta hanyar satar rubutun wasu,na rasa kuma na wa zan sata sai popular writer kamar midnight Authoress.
Ganin Hauwa'u nata zura kai ya saka na kashe wayar ina mai kallon ta kafin na ce "wane yace ki shigar mun wattpad?".
"I'm sorry Aunty Zunairah ban tambayeki ba,amma bana tunanin abun ƙi ne dan an san a gida kina rubutu,kyauta ne Allah ya baki why hide it?kin fi kowa sanin Mama da Baba baza su taɓa ƙin baki goyan baya ba, you're not doing anything Bad,kin san dalilin da Baba ya siya mika laptop kenan,ya sani tun baya ,har Mama duk mun sani mun bi ki ne a yadda ki ke so".
Shiru nayi ina mai kallon ta kafin na rumtse Idanuna na ce "yanzu it's all over ,babu wani amfani because na haƙura,I mean just look inda abun ya kaini ,i cant even face people tun kafin aje wani gurin,".
Kafin na sake magana muka tsinkayi Muryar Mama tana mai cewa"yarinyana We fall ,we raise and we move on,babu wani Nasara da zaki gani a rayuwa wadda bata zo da faɗuwa ba,mu Danginki ne,duk abin da zai faru dake mune dai zaki juyo garemu ki bamu damuwarki mu nemi Solution,rubutu is not a bad thing na kasa fahimtar dalilin da ya saka ki ke ɓoye mana,but Either ways we respect and do as you wish,but Kinga Wannan ƙaramun tangarɗa da ki ka samu,kada ta dameki kada Kuma ki bari ta zama sanadin barin abin da ki ke so,we are here for you as a family and we will support you".
I was emotional,ban san lokacin da na fashe da kuka ba na rungume Mama wadda ta fara lallashina tana mai shafa mun kai tana mai sake tabbatar mun komai zai zamar mun dai dai,one thing I love about my parent is that,a kullum suna koya mun how to Win ba wai na zauna na miƙe ƙafafuna ba and I love that,wannan lallashin shine ya ƙara mun ƙarfin gwiwa da ya saka na ƙi cire pages ɗin dana ɗora illa ma sai na saka ma raina ba zan daina rubuta Love Scenery ba ,sai dai at the end of the day zan Bama makaranta abun da Babu a BLUE dan haka na yunƙura domin karanta Abin da Wannan littafi ya ƙunsa,na sha Mamaki lokacin da na gama karatunsa dan Wallahi da ace zan ma marubuciyar nan rashin adalci zance littafina ne kawai ta sace,Amma tayaya ina Kano tana Abuja,na tabbata kawai saɓani ne.
Idea daban na sake na cigaba da rubutu na ina mai ignoring comments ɗin jama'a,I'm sure I will be there ,koda Adda Ramlat ta kirani a waya itama ƙarfin gwiwar ta bani,ba zan manta da Alherinta ba.
Admission ɗin mu ya fita cikin Aminci,inda ya zamana mun gama komai lecture kawai ya rage za mu fara attending,koda Monday ta zagayo idan ka kalleni za kasan ina cikin nishaɗi,Hijaban da Baba ya ɗinka min guda Shida na ciro ina tunanin wanne ma zan saka,haka na gama ruwan idona daga ƙarshe na ɗauƙi Farin ciki na saka,ina san Abu fari,yau da yake ranar Farko na ina san na zama mai Sa'a dan haka na zaɓi farin,na riga na chamfa Farin abu Sa'a ne a gurina,bayan mun gama Kari Baba ya fita da su Hauwa'u, kasancewar ba hanyar mu ɗaya ba ƙwataƙwata ya saka na ce mishi suje kawai Ni zan hau daidaita sahu,kuɗi Baba ya bani ya mun addu'a ya min Nasiha,daga bisani Mama ma ta sake jaddada nata a kan na kiyaye domin jami'a ba kamar Secondary bace,gurine da zan haɗu da mutane iri iri,da masu tarbiyya da akasinta,wasu idan suka ganka a suturce burinsu su girmamaka su tayaka riƙe mutuncinka,yayin da wasu burinsu Su bankaɗa kan su lalata maka tarbiyyar da kazo da ita.
Har Mama ta rakoni ƙofar gida sake faɗi take"Ohunene ki kiyaye babu ruwanki da Malaman jami'a,wasu su basu da amana dan Allah".
"Mama insha Allahu zan kiyaye"na bata amsa kafin nayi addu'ar fita daga gida na fita,a hankali nake tafiya domin fita titi duba da yanzu abin hawa yana ƙaranci cikin layin mu dole sai ka fita wajen titin,motar da ke biye a bayana na kaucewa jin motsin ta na koma gefe,horn aka fara mun ,kamar ba zan juya ba amma jin dani ake ya saka na juya ,Motar Habibi ce gabana murmushi nayi ina mai tsayawa ina kallon ƙofar da zai bayyana,fitowa ya yi yana ƙada key ɗin hannunsa,jakar da ke rataye a kafaɗata na sake riƙewa ina mai sake faɗaɗa murmushina, takowa ya yi ya ce"Babyn Habibi ,first day a university I hope baki tunanin zan barki ki tafi ke ɗaya?".
"Wait kana nufin ka ce mun ka zo ne kawai dan ka yi dropping ɗina school?ba zan tambaya yadda ka sani ba Since Anisa ma yau zata fara shiga ,but ya ka san yanzu zan fito a makaranta,7:15 am "na faɗa ina bin sa da ido.
Jakar hannuna ya mun alama da na bashi kafin ya buɗe mun mota yana mai mun alamun na shiga ,ba musu na tako na shiga, kafin ya rufe ya duƙo yana kallona kafin ya ce"kada ki manta i was once a JJC,Nima na je makaranta 7:00 farkon zuwa na".
Hannu na saka na rufe ido ina dariya inda shima ya sa dariya kafin ya zaga ya shiga motar,haka ya dinga tsokanata ina biye sa ,koda muka isa makaranta na so ya ajeni bakin Gate gudun haɗuwa da Anisa amma ya ƙi,haka nan ƙirjina na dukan huɗu huɗu ya shiga da ni,sai da ya je bakin department ɗin mu kafin ya yi parking, kallona ya yi ganin yadda nayi tsuru tsuru yar dariya ya yi kafin ya ce"why are you behaving kamar ni da ke muna aikata abu mara kyau?na kasa yarda kina wannan abun ne saboda Anisa,for God sake ƙanwata ce bata da hurumin zaɓar wadda zanyi soyayya da ,ina sanki babu abin da Anisa ta isa ta yi dangane da hakan,besides za taji daɗine ace yau matar da ƴaƴanta zai Aura ƙawartace sun saba ba sai sun fara sabon shaƙuwa ba, at this point na fara tunanin ba Anisa ki ke ɓoyewa ba,maybe baki san na ɗauki step forward saboda kina tare da wani".
Saurin juyowa nayi ina kallonsa dan ban taɓa tunanin zai zargi