Author : Chuchujay Category : Romantic Hausa Novels
ma bai taso ba Mama kawai zan fara faɗawa,da haka na yanke shawara da Zuciyata na kai kayan ɗaki na aje.
Na gama ƙwashe tuwo na saka a leda kenan wayana ta hau ruri,number ce wadda truecaller ɗin ke Bayyana Halil Ibrahim, murmushi na tsinci kaina da yi kafin na ɗauki wayar bakina ɗauke da sallama,ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ce"har na fara jin tsoron baza ki ɗauka ba".
"Saboda mene ni kam zan ƙi ɗauka?na buɗe kaya nagode duk da sun yi yawa Yaya Halil".
Ƙaramun murmushi yayi wanda ina jin sautinsa kafin yace"I guess kinga rubutun ciki mene amsa ta?".
Wani irin kunya naji ina ji kamar wanda yake tambayata a gabana,tsintar kaina nayi da cewa "Allah ya sa ba tsaddaden zobe bane dan bana san in fita dashi a hannuna a sace ni".
Cike da murna da san fahimta ta ya ce"kenan na samu ƙarɓuwa?, look Zunairah I've been having crush on you,tunda na ganki na farko naji kin burgeni,that's of course lokacin da ki ka fara girma,amma a ranar da na sake saka ki a ido a makarantarku,kin tafi da komai nawa da zan iya sauke wuyana ki hau,da gaske ina sanki Zunairah kuma Aurenki nake so nayi,amma ba zan miki dole ba idan ban Miki ba ki faɗa mun kin ji?"..
Idan ance na kwatanta kaina a kan sikeli na ɗari a wannan lokacin ban ma san a nawa nake ba amma fa Yaya Halil ya ƙwamishi zuciyata duk da irin abun nan na mata zai hanani bada kaina da wuri dan haka na nemi da ya bari nayi tunani.
Murmushin ya yi yana mai cewa "na samu karɓuwa kenan,ki ce na gyara zamana ,kin san idan mace tace za tayi tunani yana ɗaya daga cikin alamun nasara,yanzu dai ki ce naje na fara tara sadaki?".
Kunya ta saka na kashe wayar ina mai jin Zuciyata na bugawa da sauri da sauri,na kasa yarda wai na samu soyayya a gurin da bana tsammani,wai ni da Yaya Halil?abun kamar almara,wayata na kunna na shiga last call ɗina da nayi da Anisa,na daɗe da number ɗinta a rubuce dan ta saka na mata alƙawarin ina samun waya number ɗinta zan fara kira,ana siya mun Sim kuwa ita ɗin na fara kira inda ta nuna mun murnarta kamar ma ta fini har tana faɗin itama ƙawarta ta fito fili,Sai da ta gama ringing ba a ɗauka ba,har wani tsuma nake burina na ji na fesa mata soyayyar da na samu daga yayanta,na san ba ƙaramun farin ciki za tayi ba ,ina ƙokarin sake kira kiranta na shigowa,cike da zaƙuwa ta ce"Besty guess what?Ina ta san kiranki ki ka kirani ya I've found love,baki ganshi ba ya haɗu iya haɗuwa,yaran ƙawar mummy ne Khalifa wannan immigration da na faɗa Miki ina having crush a kansa,kin gane sa?".
Da murnar da na kasa ɓoyewa na kaɗa kai kafin na ce "Finally babe crush ɗin da ki ke bai tashi a banza ba,i can't believe this,tell me more".
Cigaba tayi"ina faɗa Miki Walimar da Aka haɗa mun a gida suka zo to cut the story short bai tafi ba sai da ya faɗa mun yana sona and of course na amince,ki fara tanadar duk wani abu da ki ka san Aure ya ƙunsa,we have a wedding to plan".
"To hajiyata ,yaushe aka fara soyayya da har kin fara maganar Aure?"..
"Hmm Ohunene,you see that guy?he's mine and Idan ina kallansa ji nake kamar har mun yi Aure,muna nan da ke Aurena dana Yaya Halil za a haɗa dan daga samun budurwa jiya jiya har ya fara maganar Aure,ke ki ji zaƙewa da Daddy ya tambayesa sun daidaita wai sai cewa ya yi tukunna dai"dariya ta saka sosai a ƙarshen maganar ta kafin ta ƙara da cewa"Allah ya sa ba gaja bace ko wata ƴar talakawan yaje ya ƙwaso dan Wallahi idan bata mun ba ubanta zataci".
Wani irin faɗuwar gaba naji ya sauka min, Chanza shawarar faɗa mata ɗin nayi na ja bakina nayi shiru har muka gama wayar duk da yadda zuciya ke ce mun na faɗa mata ɗan Wannan karan shine farko da na fara ɓoyewa Anisa abu,haka nan sai na tsinci kaina da tsoron faɗa mata nice duk da na san zata ji daɗi atleast ni ɗin aminiyarta ce dan haka na sake ɓalle maɓallin Zuciyata dan adana soyayyar Yaya Halil ta yi yaɗuwa,na san wannan karan ba zan samu karayar zuciya ba.
Da mama ta dawo kamar munafuka haka na shiga ɗakinta,doguwar rigar da ta fita da ita take cirewa tana faɗin"bari na zo na ɗora miya Allah ya sa baki ɗora mun ba".
"Ban ɗora ba amma Mama na kusa fara ɗorawa idan bana ɗorawa ɗin yaya zan iya?"na faɗa ina mai zama kan carpet da ledar a hannuna kamar wadda ta ƙwaso ganimar yaƙi.
"Shi ya saka ai nake yi tare dake ,tunda komai tare muke yi,so ki ke ki lalatani idan kin fara makaranta ko kin yi Aure na shiga ta kaina,ki dai biyoni kitchen mu yi tare".
Ƙarasa saka hannun rigar ta tayi kafin Idanunta suka sauka akan ledar da nake ta chikukuyewa baki.
"shi wannan ɗin mene a ciki?"
"Mama dan Allah kada ki yi mun faɗa ban roƙesa ba haka nan ya kawo mun and sai da na ce mishi ya yi yawa amma ya dage sai na karɓa wallahi ban roƙeshi ba".
Hular dake hannunta ta saka ta ƙaraso inda nake ta zauna tana mai faɗin "taƙaita mun zance?wane shi wane ya baki let me understand "saurin tashi nayi ta kamo hannuna ta zaunar tana mai faɗin "Izewano?(Ina zaki?) Mene a cikin ledar wane kuma ya baki?".
Na san tsakanina da Mama bamu ɓoye ɓoye,har soyayyata da nayi ta baya da Ma'aruf ta sani duk da ta kan kashede ni kan har a lokacin ban kai soyayya ba amma na kula,chance wanda zan experience menene ma soyayyar,da ya karya mun zuciya na faɗa mata ta sake jaddada mun dama irin wannan soyayyar ta gaji haka shima na saka shi cikin sanin wacece ni , menene zan ji idan soyayya ta bar ni Sannan ta yaya zan shawo kan matsalata,duk yana cikin karatun rayuwa,.a wannan bangaren na Yaya Halil sai na tsinci kaina da jin nauyi da kuma fargaba,ban sani ba ko dan ya ce Aurena zaiyyi?wanna idea ce da bata taɓa kawo mun cikin rai ba ban kuma taɓa tunanin samun soyayya ba ƙwana Kaɗan da gama secondary ɗina.
Ledar Mama ta buɗe tana mai Ganin kayan ciki,sai da ta gama ta mayar kafin ta miƙo mun hannunta,kamawa nayi ina mai yin ƙasa da idona.
"Kalleni nan"ta faɗa Idanunta cikin nawa,cike da nauyi na kalleta,tambayata ta farko itace"wane ya fara koya miki Sex education?".
"Ke ce "
"To ina so ki sani babu wani abu da zaki yi discussing da wani wanda ya shafi rayuwarki da ya wuce ni,ni Mahaifiyarki ce kuma abokiyar shawararki,mu kashe mu binne babu wanda ya ji which I'm very sure ba zan taɓa ɗora ki a kan hanyar da zaki cutu ba,haka nake da Mama na ina so kuma nima ace ina da wannan shaƙuwar da yarana,so now tell me kina san Halil ne?"
Cike da nauyi na kaɗa mata kai inda ta umarci da na faɗa da bakina ba wai ɗaga kai ba dan tana so ta ji na ambata da bakina.
"Ina san shi Mama"na bata amsa.
Murmushi tayi kafin ta ce"that's very Good na san yaran kirki ne although ba wani sanin sa nayi sosai ba tunda ba zama nake da shi ba,but iyayensa mutanen ƙwarai ne wanda na tabbata ba daga gidan banza ya fito ba,bana da right na faɗa Miki wane zaki so da wane baza ki so ba,.
"Kinga a time ɗin mu Mamana kance ba zan Auri bahaushe ba kada ma na fara kawo mata maganar bahaushe,to Nima lokacin bana ra'ayin su,amma yanzu kam rayuwa ta waye it doesn't matter yarene ko a'a Indai Musulmi ne kuma ɗan gidan tarbiyya babu amfanin banbance bambancen aƙida,it doesn't matter wai Halil yaron idomawa ne ,idan yana sanki yana girmamaki just go for it ki yi Addu'a muma muyi ta taya ku dashi,but one thing ki faɗa mishi babu unnecessary siyaya,i mean wannan kayan sun yi yawa,Allah ya yi muku Albarka ya rufa Asiri,but ki kula".
Gaɗa kai nayi ina mai yin murmushi,har ta tashi ta nufi hanyar fita na tsinci kai da cewa"Mama zan iya saka zoben".
Dariya tayi tana mai kallona kafin ta ce"ki Bama Hauwa'u ita zata saka ko ni ki bani sai mu yi ta yawo da symbol ɗin soyayyarki a hannu".
Wata irin kunya naji ta kamani da ta saka na sunkuyar da kaina,.bata ɓoyewa Baba haka magana bata wuce kunnen ƙannena ba haka Hauwa'u ta yi ta rawar jiki wai sun yi siriki ɗan gayu.
Kullum sai ya kirani duk da ban faɗa masa na amince ba sai da muka ɗauki sati guda a haka kafin na ɗauki hoton zoben dake hannuna na tura masa ta WhatsApp na aika mishi saƙon na amince,.Murna kamar zai maida ni ciki ta wayar , condition guda na bashi wanda shine siyayya mara amfani kamar yadda Mama ta Umarceni,ya amince amma ya ce ba haka ke nufin ba zai mun ƙyauta ba tunda ai ƙyauta na ƙara dangon ƙauna.
Kafin na farga soyayya mai ƙarfi da Tsafta ta shiga tsakanina da Yaya Halil,har a wannan lokacin na Gagara faɗawa Anisa,haka zata Kirani ta bani labarin Khalifa idan ya zo gurinta da irin kyautukan da yake mata,neman lokaci nake da rana yadda zan sanar mata da soyayyar da nake da ɗan uwanta,dalilin hakan ya saka na hana ya faɗa a gida nice duk da ya so sanar dasu ɗin tunda a maganar da yake mun so yake ina shiga shekara ta biyu haka a jami'a ayi Auren mu dan na samu damar adjusting a makaranta tunda first year shine tushen gina karatunka.
Shin yaya Anisa zata ɗauki soyayyar mu?tambayar da nakan yiwa kaina da yake sani fargaba,na san tana sona ba zata zamar min ƙanwar miji ba kamar yadda take faɗa,nasan alaƙar mu ƙarfi zata ƙara ,i can't wait naga irin farin cikin da zata nuna mun lokacin da ta ji nawa labarin farin cikin.
𝘊𝘩𝘶𝘤𝘩𝘶 𝘫𝘢𝘺✍️
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔
𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎
Na
𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay)
E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟˚:6: curiosity
*𝘡𝘶𝘯𝘢𝘪𝘳𝘢𝘩*pov
Tunda na shirya zuwa duba Anisa nake jin gabana yana faɗuwa , tsoro nake ji kada wani daga cikin yan gidan su ya gano wani abu,ji nake kamar wadda nake wani abun mara kyau ko wata ɓarauniya da tayi sata take tsoron kada a kamata ,tace mun dai bata da lafiya,duk da ban san taƙamaimai abin da yake damunta ba amma yadda take son nazo na san bayan ciwan Labari zan sha ,duk da Mama bata san ina fita amma idan abu ya shafi Anisa bata saka Question mark saboda yadda da tayi da ita .
Wayata ta hau ruri, ringtone ɗin da nasaka mishi na daban shi ya tabbatar mun da Wanda ke kira kafin idanunna suka sauka ƙan Sunan da nayi masa Saving da *Babyluv* wani irin faɗuwa naji gabana ya yi kafin na iya ɗauka bakina ɗauke da sallama ,ina jin sautin murmushin sa a lokacin da ya amsa ni ya ce"nayi ƙewar muryarki da fuskar ki Abar ƙauna".
Daga tsayen da nake na zauna ina mai wasa da ƙafafuna ina murmushin ƙauna,ni kaina bana gane irin halin da soyayyarsa ke jefa ni,wallahi ina san Yaya Halil da yawa ."Nima nayi ƙewarka Babyluv,ba dai ka ƙi zuwa hutu ba kana can kana kallon yan matan Abuja,aikuwa video call ɗin ma na kusa daina ɗauka"na faɗa ina mai pouting baki kamar ina gabansa.
Murmushi mai sauti ya yi kana ya ce"ki daina ɗaukar Video call ɗina fa ki ka ce,kina so ayi yaƙi a Kano,and yan matan Abuja babu wadda ke gabana ,besides da eyes mask ma nake yawo a bayan rigata kuma an saka Halil na Zunairah".
Dariya na saka ,yaya Halil yana da barkwanci sosai,suna cikin ɗabiunsa dake burgeni,gashi baya da girman kai,ɗabiunsa na ƙwantar da kai ke sakani sake faɗawa soyayyarsa
Koda na fito Mama da su Hauwa'u suna zaune suna kallon sharrin girkin Gabon,yau ranar hutun makaranta ne,kallona Hauwa'u tayi nima na kalleta nace"yanzu Hauwa'u bazaki rakani ba?".
"Allah Antynmu ta kan mu baƙi zan yi ,ga Adavize ki ja ku tafi".
Kafin na kira sunansa ma ya katseni ta hanyar faɗin"home work da rubutun hadda zan yi".
Ganin yadda na ɓata rai ya saka mama yin dariya tana mai cewa"i thought baki so ana bin ki gidansu Anisa gashi nan yau kina so sun ƙi zuwa,sai ki yi tafiyanki su yau ne ranar su".
"Ai wallahi babu wanda zan sake kai wa wani guri mama ki zama shaida"Sallama nayi mata na wuce inda take cewa na gaida Anisa da jikin na kuma gaida mata Enen ɗin ta sosai ,ban wani sha wahalar samun abin hawa ba kai tsaye ya saukeni unguwarsu Anisa ,na jima bakin ƙofar kafin na shiga dan ji nake ina shiga Anisa zata gane ina soyayya da Yaya Halil ,cire komai nayi a zuciyata lokacin da na gargaɗi kaina da "Zunairah ba sata ki ka yi ba ,Soyayyace babu kuma wanda zai ce Miki dan mene"a haka na shiga gidan bayan na gaida mai gadin gidansu.
Babu kowa a falon nasu,sallama na fara ina hangen ta inda zan ga mutum,duk da na san hanyar ɗakin Anisa kuma Enen ta sha faɗa mun idan na zo ban ga kowa ba na nufi ɗakin ta,amma a yanayin tawa tarbiyyar baza ta barni na ƙutsa kaina kai tsaye ba kamar wadda ba Musulma ba,maimakon na zauna sai na fara kiran layinta ina kalle kalle.
"Surprise!!!"
Da sauri na juya jin muryarsa,Hannu na saka bisa bakina ina kallonsa da Mamaki dan ban taɓa kawo zan iske shi ba duba da mintuna mara sa yawa nayi waya da shi yana Abuja,takowa ya yi yana kallona yana murmushi kafin ya sake faɗin"I told you na aje Miki surprise amma kamar baki farin ciki da gani na".
Kallonsa nake cikin ido ina mai jin shauƙi kafin na ce"amma mai ya sa kace mun kana Abuja?".
"Well kamar yadda nace zan baki surprise gashi nan na baki,jiya da dare na dawo jin kin ce zaki zo duba Anisa ya saka na yi amfani da wannan damar ki zo na gabatar dake ga Enen taga wadda ke neman zautar mata da ɗa".ya ƙara maganar yana mai kashe mun ido.
Wani irin faɗuwar gaba ne ya ziyarceni,ƙasa nayi da murya ina mai kallonsa kafin na matso daf dashi idanuna cike da fargaba nace"babe ba munyi magana a kan haka ba fa, wallahi ban shirya ba".
"Aikuwa ni na faɗa musu,abun da ba wani sharri muke aikatawa ba,Aure fa muke san mu yi ba wani abu ba mene ne ɓoyewa?".
Jin amsar da ya bani da kuma yanayin da gaske yake maganar ya saka na juya ina mai cewa"idan na tafi sai ka faɗa ɗin amma kuma ba zan sake maka magana ba daga yau".
Dariya ya saka sosai yana mai shan gabana yana faɗin"daga wasa,I'm just joking fa,idan ki ka daina mun magana sai nayi ya ya da rayuwata,ni wasa nake miki".
"Wane irin wasa?". Muryar Anisa ta Iske mu,a tare muka juya wani irin fargaba na ji ina ji,ni kaina ban san mene yake damuna ba,ko mene abun ɓoyewa oho.
"Wai yace baki nan ne har na juya zan wuce yake cewa wasa yake"na faɗa ina ƙarasawa gurinta,kallon yaya Halil take har na Kama hannunta inda shi kuma ya juya yana mai ɗauke idanunsa daga kanta ya yi bangaren da nake tunanin nasa ne.
Sai a wannan karan ta kalleni kafin ta ce"idan ban sani ba sai nace Soyayya ku ke, dan yadda yaya yake kallanki wallahi sai wani ya rantse soyayya kuke ke da shi"dariya ta sake fashewa da shi tana mai faɗin baza ta iya misaltawa ba kafin ta ja hannuna muka shiga ciki bayan ta shaida mun Ene bata nan.Kallan ɗakin nata nayi ganin yadda aka canza komai,kamar ta fahimci kallon da nake ta zauna gefen gadonta tana mai cewa:
"Kina kallon sabon design ɗin ɗakina hala?wallahi Yaya Halil ya canza mun komai,zo muje ki ga cikin wardrobe ɗin har da kaya".
Fito da kayayyakin ta fara tana mai nuna mun,sunyi kyau sosai haka nan sai na jini cikin farin ciki kamar ni aka sauyawa kaya,ɗayan wardrobe ɗin ta buɗe tana mai cewa "ga nan waɗancan har da wanda sawa ɗaya nayi mishi,kin sanni bana da yawan maimaita kaya,har Enen ta ce za a fita dasu a kai gidan Marayu na ce ta aje Zunairah ta zo sai ta zaɓa".
Wani irin zafi na ji a ƙirjina lokacin da ta faɗi maganar amma na danne ɓaccin raina na yi faɗa da shaiɗan ɗin da yake san hassalani na gwasile Alherinta,cikin mutunci na ce"aikuwa da kin bar Enen ta kai kayan nan gidan Marayu dan ba zan ɗiba ba , besides ai kin san cewa jikina da naki ba iri ɗaya bane".
Kallo na tayi na daƙika kana ta ce"hope ba ɓata Miki rai nayi ba,I'm sorry ni wallahi ba da wani abu na ce ba,zo ki zaɓa cikin sabon ma dama inda da niyyar ɗiba miki wasu".ta ƙarasa zancen tana mai aje doguwar rigar da ta ɗauko tana buɗa mun ta nufi sashen sababbin,dariya reaction ɗinta ya bani, kafaɗarta na kama na juyo da ita ina mai faɗin"Ani I mean it ba zan karɓi kayan ki ba,and ba wai na ɗauki maganar da wani abu ba,kyauta ce fa ki ka mun ta hanyar san Faranta mun, it's just that kada ki manta kin fini jiki na fiki tsayi,Kinga kuwa kayan ki ba za su mun ba,yanzu bama wannan ba ya jikin ki mene yake damunki?kin san yadda ki ka tada mun hankali kuwa?mama na ta mun faɗa wai ban tsaya na ji mene yake damunki ba tun a waya".
"Okay fine kin yi winning,jiki na da sauƙi,dama ƙoda ne ta sani gaba but I'm okay, although abun ba daɗi kwana biyu ɗin chan but yanzu ba Matsala,bari ki ga gifts ɗin da Khalifa ya kawo mun"ta ƙarasa maganar tana mai kwace hannunta daga nawa ta nufi ɗaya gefen wardrobe.
Shan gabanta nayi cike da tashin hankali"ciwan ƙoda Anisa har ki