Chapter 8 Reading Cin Duniya Book Compelet Hausa Novels By Chuchujay Arewa Novels

Cin Duniya Book Compelet Hausa Novels By Chuchujay

Author :  Chuchujay Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   8 / 16

21K to 24K   out of 45.5K words

da Allah ba matar da zaka Aura kayi alfahari da ita bane,na san abin zai baka mamaki kace daga bakina wannan maganar ke fita,amma ina so ka sani wallahi ba sharri nake mata ba,and ba wai ina cewa bata da hali mai kyau bane,dan har gobe bana da ƙawar da ta wuce ita amma dai Maganar Aure gaskiya bana goyan baya".

Daga zaune kan mudibin da yake ya kura mata ido bai ce komai ba,ganin yana mata irin wannan kallon ya saka tace"yaya baka ce komai ba".

"Uhum ina sauraranki dan baki faɗi maganar da ya kamata nace komai ba har yanzun,ita Zunairah ɗin mene tayi ,tana da mugun hali amma ki ke tare da ita,ina ƙoƙarin na saka maganarki kan sikeli ne na Auna dan ban san taƙamaimai ina ki ka dosa ba".

Ɗan cije leɓenta tayi ta ciro wayarta tana mai cewa"zan nuna maka wani abu amma dan Allah yaya ka rufe mata sirrinta bana san kowa ya sani,and ka san mene yafi damuna,da ace zata canza da tuni ta canza amma bata da tunani na sake ɗabiun banzanta".

"For God sake Anisa idan zaki nuna mun ki nuna min,idan ba haka ba ki bari nayi relationship ɗina in peace"ya faɗa cike da ƙosawa.

Bata tsaya further ɓata lokaci ba ta kunna masa abin da take kira well kept evidence.

*𝘡𝘜𝘕𝘈𝘐𝘙𝘈𝘏 𝘗𝘖𝘝*

Introduction to mass communication shine first period ɗin da muke dashi,yau ko da na shiga makaranta na ɗanyi latti amma sanin malamin baya da matsala sai abun bai dameni ba,ban mamaki ba ganin Anisa bata jire mun guri ba sannan bata kirani ba,idan ta rigani shiga aji takan kirani tace mun an shiga,zaune take tare da wata course mate ɗin mu da suka fara shiri kwana biyu Safina Bala,sai wani Saurayi da ban wayi sunansa ba danni bana da wannan shige shigen.

Class rep ɗin mu Imran ne ya mun guri na zauna har yana tsokanata yau akwai Quiz yana tare dani ya san zamu buge kowa,haka aka yi Quiz ɗin roll ɗin mu muka ci na farko,Use of English ne second period mai ɗaukar mu ya sanar da class rep ba zai samu damar zuwa ba dan haka sai ya zamana 10 mun zama free ,ina haɗa kayana dan tafiya gida Anisa tazo tana mai cewa"ƙawata yau mene ya saka ki latti?".

Dan murmushi nayi ina mai kallanta na amsa mata "ban samu abun hawa bane da wuri wallahi shi yasa nayi latti,and kin san Malam A Bello baya da matsala shi yasa ban damu ba ,da dai A A Garba ne na san Dama ba zan samu aji ba".

Jakata da nake ƙoƙarin ratayawa gefen Kafaɗata ta karɓa ta rataya ,kallonta nayi ,gira ɗaya ta ɗaga mun tana mai cewa"zaki iya amfani dani matsayin mai riƙe Miki jaka indai zaki rakani".

"Ina ɗin zan raka ki?".

"Kin san dai ai ba zan cutar dake ba,kizo muje dan Allah"ta faɗa tana mai kamo hannuna ,haka nan na bita ina tunanin yadda zata ɗauki hukuncin da na yanke ,sai da na bari mun fita daga class nace ",Besty baki tambayeni decision ɗin dana yanke kan yaya Halil ba".

Juyawa tayi tana kallona tayi murmushi kafin ta ce"well I'm all ears ,mene decision ɗinki?".

Ɗan shiru nayi kamar ba zan magana ba,zura mun ido tayi,cikin dan dakewa nace"Anisa look here babu inda addini ya haramta alaƙata da Yaya Halil,ni dake kamar yan uwa ne,kada ki bari wani code na Bature ya yi mun katangar ƙarfe da farin cikina,Wallahi a tare da Yaya Halil nake ganin Rayuwata nan gaba ,ina san sa ina san kasancewa dashi,bayan relationship ɗina na baya da Ma'aruf ke shaida ce yadda nayi ta fama,idan na rabu da Yaya Halil zan faɗa cikin hali mafi munin na baya ,ba zan zaɓa tsakanin Ƙawance ko Soyayyata ba,duka nake so koda za'a Kirani mai san zuciya,ki yi haƙuri".

Wani irin kallo take bina dashi ranta a mutuƙar ɓace,cikin yanayi na ɓacin rai tace"haka ki ka zaɓa Zunairah?".

"Im sorry"shine Abin da na furta ina mai jin babu yadda za'ayi ta sake mun tunanina ,zan iya bar mata komai nawa amma ba zan bari na cutar da kaina ta yadda zan illata kaina da kaina ba,bayan na gama sakankancewa da tayi fushi ta kwashe da wata irin dariya,sosai take dariyar kamar wadda ta zare inda ni kuma nake kallonta fuskata babu yabo babu fallasa,matsowa tayi kusa dani ta dafa kafaɗata kafin tace"saki ranki mana mene hakan?God Kinga yadda ki ka zama serious kamar wadda tayi wani babban laifi?well kin cinye jarabawar da nake san miki dama ina son gwadawa ne naga kin chanchan,Yayana,and kamar yadda nake expecting kin cinye, welcome to the house,ki saurareni da kyau,ni da ki ka gani well wisher ɗinki ce ,duk abin da ki ke so idan ban nema Miki ba ba zan ƙwace Miki ba, ballantana ma sai inda karfina ya ƙare wajen nema Miki farin ciki,ke nifa ko Khalifa ki ka ce kina so ni mai bar mikice".

Dariya na saka jin wai zata bar mun Khalifa ,as if"kece zaki bar mun Khalifa,da anyi ruwa da ƙanƙara,balle ma ba zan taɓa having interest kan Khalifa ba,shi naki ne nima kuma ina da mai bani Zazu".

"Sai dai abin da ya fi Zazu,ni dai ga yayana na baki amana kada ki ci amanarsa domin duk abin da Yaya Halil ke so nima ina so ina kuma taimaka mishi wajen ganin nima na so wannan abin fiye da tunanin mai tunani,yanzu dai muje kada mu makara".

Tsaye nayi bakin wata dallekiyar Mercedes ina mai jin Zuciyata bata bani goyan baya ba da na shiga ba,buɗe murfin baya Anisa tayi ta tura nii tana mai cewa ,nace miki za muyi latti,Khalifa dake zaune kujerar mai tuƙine ya mun murmushi yana mai cewa"Barka ƙawarmu,ina wuni?".

"Ina wuni ya gida,ya Aiki?"

"Álhamdulilah mun gode Allah".

Da wata irin siga ta shagwaɓa Anisa ta ɗora kanta bisa kafaɗarsa tana mai kamo hannunsa kana ta ce"i miss you Chocolate ",wani irin kunya abun ya bani musamman ganin yadda Khalifa ke ƙoƙarin ɗagata daga jikinsa idanunsa kuma na gareni ta mirror,saurin ɗauke ido nayi ina kallon gefe lokacin da idanunmu ya sarƙe a na juna,ji nake kamar na buɗe na fita dan ban san wane iskanci ke damun Anisa ba kuma.

Juyowa tayi ta kalleni tana mai yin murmushi kafin ta ce"da ace baki dating da na shaƙa miki,sai Allah ya saka kin fita sahun yan nema, Chocolaty ka san Zunairah da Yaya Halil soyayya suke,kasan har tazo gidanmu ya mayar da ita gida bata faɗa mun ba ashe ni suka maida bi ta chan suna pretending,Besty kin iya munafurci, tsakaniki da Allah lokacin baku tare?kada ki ji kunyar Baby"..

Yaƙe kawai nake na kasa cewa komai,kana kallo ka san a takure nake musamman jin maganar da ta ɗakko gaban Khalifa,shine ya katse ta hanyar cewa"Ayya Allah ya sanya Alheri,ki ce muna da biki nan kusa".ƙwace hannunsa ya yi da ya kai ƙarshen maganar cikin sigar dabara amma da yake ƙawata ta iya zubar da mu ta sake kamowa tana cewa"Who knows a fara yin namu,cos nan da wasu watanni ina jiyo ƙamshin Aure".

"Allah ya amsa Mana ,bari muje kada mu tsayar da Zunairah ko?"ya faɗa yana mai yi ma motar key,ni dai da ban san ina zamuje ba nawa ido,a Zuciyata kuwa ina ta saƙa da warwara,dan dole na yima Anisa maganar yadda take ta taɓa Khalifa wanda ba sai ya faɗa maka baya na'am da hakan ba , gidan babbar yayarsa muka je ,shima nan Anisa tayi ta zaƙewa,ban sani ba ko abin da take ne zai saka su san ta waye ko mene oho,amma nifa a nawa belief ɗin ba dai dai bane, zaƙewa ba shine zai saka a san kai ɗin a waye ka ke ba.

Koda muka tashi tafiya leda biyu ta mana tana ta mana godiya,har Kofar gida suka kaini,ina ƙoƙarin shiga gida ta fito da ledar hannunta tana cewa"wannan ɗin wa ki ka barwa?"

"Anisa mai yasa baki faɗa mun inda zamuje ba,ina kuma da magana dake".

Jiki na rawa ta saka mun ledar a hannuna tana cewa"naji muyi magana gobe ,kiyi haƙuri,yanzu Khalifa na jira ki gaida mun da su Mama ".

Bata jira abin da zan sake faɗa ba ta koma motar tana mai ɗaga mun hannu,haka nayi tsaye har suka wuce kafin na shiga gida,ban tarar da kowa ba sanin Mama na islamiyyar da har yanzu aka ƙi gamawa,sau tari nakan tambayeta yaushe zata yi sauka sai dai ta ce mun mene amfaninta ,kullum yi ake,karatun matan Aure kenan haka mukan tsokaneta,ledar na buɗe naga doguwar riga mai kamfala da gyale a ciki,ajewa nayi ina mai niyar bawa Hauwa'u ba dan Alheri bane dama ni ba zan karɓa ba.

Sallar Azabar da aka fara kira nayi kafin na dumduma Egusi dake fridge na dauko Saƙwara dan ban yadda na ci abinci gidan Auntyn Khalifa ba duk yadda tayi ta nacin mu ci ɗin,sai da na samu natsuwa na koma na ƙwanta sai kuma damuwar ƙin naimana da baiyyi ba ,na saba kullum shine ke fara kirana a waya,yau da bai Kirani ba sai na ɗauki hakan da ƙilan yana wani abune sai kuma ga Anisa ta ɗauke mun dukkan lokacina.

Kiran wayarsa nayi a karo na uku bai ɗauka ba, tunanin baya yanayi na ɗaukar wayar ya saka na tura masa saƙon idan ya gama ya ya Kirani ina kewar jin muryarsa,bai mayar mun da saƙon ba kamar yadda nayi tsammanin zai maido, idan har nayi masa dropping message baya ɗaukar lokaci zai dawo mun dashi ya faɗa mun ko yana aiki ko yana wani abun amma zai kirani,haka dai ban ɗauki abin wani abu ba na ƙwanta ko zan ɗan samu bacci bashin na asuba da ban yi ba.

Wajen yamma Mama ta dawo take faɗa mun ta tsaya meeting ne nasu na yan ajinsu tunda dama duk inda ƙarfe biyu yake ta dawo gida, kaya da Auntyn Khalifa ta bamu na nuna mata nake shaida mata munje tayi haƙuri ban faɗa mata ba,ko da nace Hauwa'u ta ɗauka mama tace ba zai iyu ba ai babu daɗi a maka ƙyauta ka ƙi sakawa,koda ita bata gani ba ai ita Anisa zata gani taji daɗi.

Naso na dai Bawa Hauwa'u na san kuma zata ji daɗi amma abin da Mama tace shima gaskiya ne,na mata ko sawa biyu ne na Bawa Hauwa'un.
Har daren ranar Yaya Halil bai nemini ba,abun da ya bani mamaki shine da na hau WhatsApp na ganshi online, message nayi mashi bai reply ba ,sai abin ya fara damuna a wannan stage ɗin na san dole akwai wani abun,to amma menene shi?
𝘊𝘩𝘶𝘤𝘩𝘶 𝘫𝘢𝘺✍️
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔

𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎

Na

𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay

E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟11.Fire breakout

*𝘡𝘜𝘕𝘈𝘐𝘙𝘈𝘏*

Tunani yana neman ya saka na zauce ,yau Friday ranar da nasan dama dole zai zo gurina da dare,duk da haka da wuri na shirya dan zuwa makaranta duk da period ɗaya garemu Report writing,ko abincin kirki ban ci ba,burina na samu Anisa na tambayata lafiyarsa,Sai da nayi awa ɗaya a makaranta kafin ta zo, straight gurina ta nufa ta zauna duba da class ɗin sai Sha biyu muke dashi ya saka da yawan ɗalibai da dama basu kai ga ƙarasowa ba.

Cikin damuwa na ce"Anisa Yaya Halil fa lafiya ƙalau yake?".

Cire jakarta tayi daga kafaɗarta tana mai ɗan zaro idon alamun tambaya tana cewa"Well last dana tuna ƙalau yake dan shine ya ajeni makaranta yanzu ya wuce and ai kya bari mu fara gaisawa atleast sai ki tambaya ,Anisa ya darenki ?ya ki ka kwana ya kuka rabu da masoyinki?but its okay yanzu bari na fara kiran Yaya Halil".

Kamar Nace kada ta kira amma sai na rabu da ita ɗin dan ƙasan Zuciyata ina san naji mene ne faruwa,muryarsa da nake kewace ta shiga cikin kunnuwana.

"Yayana kana ina ne?".

"Kamar ya ina ina?ke dai ba na aje ki makaranta ba,gida nake san na koma nayi bacci tunda kin katse mun". ya faɗa daga ɗayan bangaren da Alama yana tuƙine.

Matso da wayar tayi kusa dani ta sake cewa"well hala baka Kira Zunairah ba".

"WHO IS SHE? wacece wata Zunairah,dan Allah kada ki dameni kafin ki ɓata mun rai na ɓata miki"yana faɗin hakan ya kashe wayarsa,i was shocked,hawaye naji suna neman cika mun ido,saurin gogewa nayi ganin yadda Anisa ta zuba mun ido,ɗan murmushi nayi nace "well lets talk about you".

Cike da kula ta ce"mene ya faru tsakanin ku?wani abu ki ka mishi?no nama tabbata babu abin da zaki mishi wulaƙancine kawai irin na ɗa namiji,Allah bari naje gida na sameshi,lokacin da yake zuwa yana kalamiyeki da zancen ƙauna ai bai tambayi wace ke ba,lokacin kuma da zai je ya siya miki Zobe mai tsada duk bai san da wannan wacece ɗin ba,zan koma wallahi dole ya jini ko na jisa,wane irin abu ne wannan".

Murmushin yaƙe nayi ina ƙokarin danne abin da ya taso mun a ƙirji kafin na sake salon maganar "manta da wannan maganar yanzu dai dama ina san miki magana kan jiya,ba wai dan kiji haushi ba amma Anisa yadda ki ke taɓa Khalipha bai kamata ba,i mean he's not your Muharram ,Muna fakewa da soyayya muna kama hannun juna wallahi babu kyau, sannan ni gani nake ba sai kin zama loud bane zasu gane kin waye ba,ba wai kuma dan na ɓata Miki nake faɗa ba,kinsani ba zanga abin da zai cutar dake nayi shiru ba ".

Maganar ta ɓata mata rai dan ya nuna a fuskarta amma sai cewa tayi"naji nagode ,Allah ya saka da Alheri zan gyara".daga haka bata sake cewa komai ba dangane da abin da na faɗa ɗin,da muna tashi makaranta ganin yadda taƙi walwala yasa na ce mata "Ani I'm sorry akan abin da na faɗa Miki I mean no harm ,idan na ɓata Miki rai kiyi haƙuri dan Allah ,ko'ina ina so a ga mutuncinki fiye da kowa su kuma maza abu kaɗan kakeyi sai mutuncinka bar idanunsu".

Murmushi tayi "Zunairah wallahi ba haushi naji ba ,kawai naji kunya ne da kika faɗa sai kuma yanzu abin yake dawo mun amma insha Allahu zan kiyaye,Allah ya shirya tsakaninki da yaya Halil".

Bance komai ba ,ban san mene zance ɗinba dan haɗuwarmu dashi baza tayi kyauba,muddin kuma bai nemeni ba bazan sake nemansa ba duk da nasan zan sha wahala domin nayi sabo dashi ta yadda tunanin rabuwa dashi kawai yana sakani shiga mutuƙar tashin hankali, addu'ata Allah ya kawo mun duk wani abu da zai tunkaroni da sauƙi.

Duk haka na wuni bana da walwala a gida,da Mama ta tambayeni mene ke damuna ce mata nayi kawai kaina ke ciwo na gaji,na iddar da sallar isha'i aka aiko wai ana kirana inji Halil,sai da na gama adduo'ina kafin na tashi na fita ina mai sake danne ɓaccin raina,tsaye yake jikin motarsa yana danna waya ,sallama na mishi inda ya ɗago da idanunsa yana kallona kana yace"yan mata".

Kamar ya sake tunzurani,wai yan mata,cikin ɗacin rai nace "sannu ,ka aika a kirani Allah yasa lafiya".Bai amsani ba illa kallona da ya tsaya yanayi kamar wanda ya ga wani abu a jikina ko fuskata wanda bai taɓa gani ba.

"Kin Kirani ɗazu Allah yasa lafiya shi yasa nazo naji"ya faɗa yana mai mayar da hankalinsa kan wayarsa,tunda shekarar ta shiga ba'a taɓa raina mun hankali kamar yadda Yaya Halil ya raina mun ba yau,cikin tawa sigar ta rainin wayau ɗin nace"aikuwa ban san na kiraka ba ,kilan na kwanta bisa wayarne ta shiga contact ɗin tayi dialing,kasan waya na haka amma ni kam ban kira ka ba"misafar Who is she ɗin da nake san mishi ma sai na kasa illa tambayarsa da nayi idan da wani abu idan babu kuma zan koma gida ,abun mamaki sai cewa yayi babu zan iya wucewa,kafin ma na wuce ɗin ya rigani shiga motarsa ya mata key ya bar gurin bai sake ko kallona ba hawaye kawai naji suna zubar mun a kunci da haka na juya nima na shiga gida Amma fa abin duniya ya mutuƙar damuna.

Koda Mama ta tambayeni har ya wuce ɓoye mata nayi nace yazo ne dama kawai mu gaisa,har na shiga ɗaki ina jin tana yabansa.

A haka muka ɗauke watanni uku da Yaya Halil yana nuna mun halin ko in kula,zai kira sau ɗaya yace wai ya kira yace mun sannu, gidanmu kuwa ya daina zuwa,wata kalmar soyayya kam nama manta yaushe rabon da ya furta mun ,da ace zan iya da tuni na daina ɗaukar wayarsa,amma Zuciyata ta gaza yin mubaya'a dani atleast yana tare dani yana kirana a kullum koda sannu yace mun sai na ɗan samu peace of mind,koda mama ta tambayeni yanzu baya zuwa sai ce mata nayi an mishi transfer zuwa Lagos ne shiyasa,ban bari tayi zargin wani abuba na cigaba da dakon soyayya da ban san ina muka tsaya ba dan ina saman tekune bisa gadar sarƙa,a haka har muka zana jarabawa duk da banyi wasa ba ban bari abin da ke gabana ya hanani nuna ƙwazona ba,na dage nayi karatu na rubuta,ranar da muka gama jarabawar washegari ranar juma'a wadda zan iya kira da bakar rana gareni ,ina zaune ina yima Hauwa'u kitso Enen da Aunty Hibba suka yi sallama,rabon Enen da gidanmu har na manta,zuwanta yanzu kuwa na tabbata abu mai muhimmanci ya kawota,har nagama sawa a rai magana tace da Yaya Halil, farin cikin ganinsu naji sosai,cike da kunya na gaishesu ta amsa mini tana kirana yarinyarta tana mai saka mun albarka,tare suka shiga falon Mama tana mai musu maraba kafin ta kira Adavize ya ƙarbo musu minerals gidan Maman Baba maƙotanmu,hanawa Enen tayi ta ce ruwa ma ya isa a hanya suke ,sweet ta miƙawa Mama da invitation card tana mai cewa "sweet ne da invitation card ɗin bikin Halil juma'a mai zuwa ,dalilin zuwa da kaina kuwa ɗaya ne ba biyu ba,dan Allah Maman Zunairah kuyi haƙuri an rasa mai zuwa ya faɗa muku,ita Anisa wai kunya take ji can na barta gida tana kuka bakiji ba wallahi har zazzaɓi tace mun ya kamata ,ɗaki na barta kwance,ta saka abunne a ranta".

8 / 16