Author : Chuchujay Category : Romantic Hausa Novels
bata:"dan Allah Inya ki bawa Adavize kuɗinsa ya siya abin da yake so bani da chanji shi ya saka na haɗa muku"..
"Cewa yake bana bashi kenan,ni Mama ba sai kin faɗa mun Inya ba muna fita zan tsaya shagon Baban chakwai na bashi kuɗinsa".
"Naji dai Allah ya yi muku albarka ya bada ilimi mai amfani".
Kallonsu nake ina mai ayyana abubuwa da dama da yaso ya mantar dani abin da ya shigo dani gida sai ga Muryar Anisa tana Sallama.
"Wa nake ji kamar Anisa"Mama ta faɗa tana buɗe labule,shigowa Anisa tayi bayanta Khalifa da Farouk waɗanda suka tsaya nan ita kuma ta nufo falo tana cewa "wallahi Mama ina nan ina jiran Zunairah,wai Khalifa ne yazo duba Baba shine nace su shigo jinta shiru ".
"Allah sarki ina nan ina sallamar su Inya ne,maraba shigo dasu mana Bismillah malam Khalifa maraba".
Bance dai komai ba har ta kai mun dukan wasa a kafaɗa,daka bakin ƙofa suka duƙa suka gaida Baba wanda ya amsa musu duk da bai san su wane ba,Kuɗi Khalifa ya ciro a aljihunsa ya aje ma Baba,Mama ta ɗauka ta maida mishi,inda Baba ke cewa ai iya dubasa ma da sukayi ya isa ba sai sun bashi kudin ba,duk yadda ya yi Baba ƙin karɓa ya yi,gidan mu Muna da wadatar zuciya,idan har da kuɗi zaka siyemu zaka daɗe baka samu kasuwa ba.
Ban rakasu ba Mamace dai ta taka musu tana mai sake musu godiya,kafin ta dawo ta mun maganar su na shiga ɗaki,tunda nake wannan ne karo na farko da naji zafin Anisa fiye da tunanina.
Duk yadda na guji maganar sai da Mama ta tada mun tana mai faɗin wai suna da kirki na sake musu godiya,to kawai nace na cigaba da duba handout ɗina ,ganin kamar bana san maganar ya saka Mama rabuwa dani ta koma gurin Baba,da dare Anisa ta kirani, ina ganin kiran nata amma na kasa ɗagawa dan nayi fushi da gaske da ita.
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔
𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎
Na
𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay
E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟17: Negative Scene
*𝘈𝘕𝘐𝘚𝘈*
Tunda Farouk ya fara maganar Zunairah taji baki ɗaya bata da nutsuwa,Farouk yana samu dan har ya fi Khalifa samu yana cikin babban dalilin da baza ta iya barin wata alaƙa ta ƙullu tsakaninsu ba,duk da cewa abin da ya faru da Baban Zunairah sharri aka yi mishi amma sai ta tsinci nishaɗi cikin hakan,atleast sun fahimci su ɗin kaskantune da family ɗinta zasu iya yi mata alfarma.
Da biyu ta kawo maganar Baba ga Khalifa ganin Farouk yana neman tsaƙalewa iyakarsa shi ya saka ta saki bomb,tana kallon fuskar Zunairah ta san bata ji daɗiba amma daɗinne bata so ta ji dama,shi ya saka tayi suggesting su shiga gidan, although basa da kazanta,kullum gidansu tsaf yake amma tana so Farouk yaga cewa ita ɗin ba sa'arsa bace ba tsararsa bace ,sosai ta samu satisfaction lokacin da ta kalli idanun Zunairah,jin shiru bata fito ba ya saka ta ɗauki wayarta kamar tana magana da Zunairah sai cewa tayi gamu nan,babu musu suka bita cikin gidan kai tsaye tunanin an musu isone.
Ganin Khalifa ya ciro kuɗi abun sai ya ƙara mata armashi amma wai sai suka ce baza su karɓa,"shegu munafukai" ta ayyana a ranta,da suka fito suna Mota Farouk ya ce"mutumina family ɗin Zunairah sun burgeni,and ke kuma da kika hanani sunanta ai gashi nan naji a ƙyauta,yar baƙin cikina kawai,abeg see how humble they are".
Juyawa tayi tace mishi"na faɗa maka dai ka fita hanyarta,nayi maka baƙin cikin wallahi jelar raƙumi tayi nesa a ƙasa, Zunairah ta fi ƙarfinka sau babu adadi,ka saka kawai a ranka ƙwalelenka".
"Ashe?to dan Allah Anisa idan har na nemi soyayyarta ta bani ki kasheni saboda baƙin ciki yarinya sai kace na kashe mata wani,senior ma hold your babe o".
Ganin da gaske abun na san zaman musu faɗa ya saka Khalifa saka baki"ku yi haƙuri idan ba za kuyi ba nikam zan fita a motar nan ku yi dambe".
Kallon Khalifa tayi ranta na sake ɓacci tace"babe nayi dambe da Farouk fa kace?ni? ,tsaya kawai na fita ".ganin yadda ta ɓata rai sosai yasa Khalifa ya fahimci da gaske take,magana yayi ma Farouk akan ya bari,badan yaso ba ya yi shirun amma har ransa a kan zunairah ya fara jin haushin Anisa.
Bata bi ta kansu ba da suka isa gida suka aje ta,kai tsaye ta wuce gida,fitowa Farouk ya yi ya dawo gaba yana cewa "Man da gaske fa nake ina san Zunairah,i just see my future with her,but na kula babe ɗinka zata zamar mun matsala ".
Key ya yi ma motar ya yi reverse kafin ya ce"well bani da wani abu da zan iya faɗa maka bayan yi maka fatan nasara,amma bana jin Anisa zata zama matsala a Soyayyarka,i mean mene zai dameta ".
"Exactly abin da nake san sani,ban san mene zai dameta ba,idan babu ta bani space mana,she's getting on my nerves,amma kaga wannan Babe ɗin Zunairah na samu destination kawai".
"Amma ita Fatima sai kayi yaya da ita?".ya tambaya hankalinsa na kan tuƙin da yake.
Gyara zamansa ya yi yana mai rumtse ido "Khalifa ka san Fatima ba zaɓina bace ba kuma ba zan Aureta ba,Umma ce kawai ke kiɗanta take rawar ta ,ai na faɗa mata sannan tayi mun alƙawari duk lokacin da na kawo mata matar da nake so za'abar maganar Fatima,ni dai yanzu na kamu,ni bance Anisa ta bani number ɗintà ba da kaina zan nemawa kaina after all na san gidansu".
"Babu abin da zance maka sai fatan Nasara cos Zunairah ta fita daga heartbreak wanda nake tunani ya yi affecting ɗinta sosai and yadda na tsinta gun babe this is not the first time".
Juyowa yayi yana kallon Khalifa "shi kuwa wane mai asarar ne ya yi missing out wannan babe ɗin mai tsada".
Ƴar dariya Khalifa yayi yana mai cewa "kada ka kuma kiran brother in-law ɗina asararre ka godewa Allah gimbiyar arewa bata jika ba".
"Kana so kace mun Halil ya yaudareta,well asararsace ba nawa ba and kai ka sani duk wani heartbreak da take fama dashi i can mend it indai ta bani chance,kada ka manta Farouk fa ake Magana kai dai ka zuba ido kayi kallo".
"To ai shikenan mutumina all the best Allah ya sa ka dace "cewar Khalifa da yake jin har ransa yana fatan Farouk ya samu Zunairah.
Tunda Anisa ta shiga ɗakinta take safa da Marwa tana saƙa da warwara,ta rasa mene Matsalar Zunairah ,daga ta bata wannan ciwan kan sai ta nemi ta bata wani babu gaira babu dalili,bata gama ji da yaya Halil da ya dawo bibiyarta ba yanzu ga Farouk,big catch kamar Farouk wanda da ace babu Khalifa ita mai iya soyayya dashi ce dan ya haɗu aikuwa ko ana muzuru ana shawo babu yadda za ayi wannan alaƙar ta haɗu, wayarta ta ciro ta shiga number ɗin Zainab da ta samu wayar Enen,tunanin mene za tayi da zai Haukatata ta wulaƙanta Anisa cikin makaranta take.
Sim card ɗin da take Data dashi ta tura mata saƙo"𝘩𝘢𝘳 𝘺𝘢𝘯𝘻𝘶 𝘮𝘪𝘫𝘪𝘯𝘬𝘪 𝘺𝘢𝘯𝘢 𝘣𝘪𝘣𝘪𝘺𝘢𝘳 𝘡𝘶𝘯𝘢𝘪𝘳𝘢𝘩 𝘥𝘢𝘻𝘶 𝘮𝘢 𝘢 𝘏𝘪𝘭𝘵𝘰𝘯 𝘩𝘰𝘵𝘦𝘭 𝘯𝘢 𝘨𝘢𝘯𝘴𝘶,𝘨𝘢𝘯𝘴𝘶,𝘈𝘶𝘳𝘦𝘯𝘬𝘪 𝘯𝘢 𝘤𝘪𝘬𝘪𝘯 𝘩𝘢𝘥𝘢𝘳𝘪 𝘪𝘥𝘢𝘯 𝘣𝘢𝘬𝘪 𝘧𝘢𝘳𝘬𝘢 b𝘢,𝘻𝘢𝘬𝘪 𝘪𝘺𝘢 𝘮𝘢𝘨𝘢𝘯𝘪𝘯 𝘢𝘣𝘶 𝘪𝘥𝘢𝘯 𝘬𝘪𝘬𝘢 𝘻𝘰 𝘉𝘜𝘒 𝘮𝘢𝘴𝘴 𝘤𝘰𝘮𝘮𝘶𝘯𝘪𝘤𝘢𝘵𝘪𝘰𝘯 𝘥𝘦𝘱𝘵 𝘥𝘢 𝘴𝘢𝘧𝘦".
Sakon yana nuna mata yaje ta cire layin ta karya tana addu'ar Allah ya saka gobe zainab tayi mata tijarar da tunda take babu wanda ya taɓa mata irinta,Farouk kuwa ta san tana da wani babban gurbi a zuciyar Zunairah da zata saka mata dafinsa a Zuciyarta.
Tana zaune yaya Hibba ta shigo da sassarfa tana neman dan kunnen Anisa irin nata,tashi tayi ta ɗauko mata tana mai cewa"na san ya Adam za ki bi ku fita ,ki dai bi a hankali ".
Dafa mata kafaɗa tayi,"sis ki ƙwantar da hankalinki next 2 months za ayi mana introduction nan zaki gane duk abin da nake faɗa Miki babu ƙarya a ciki".
"Um"kawai Anisa ta faɗa ta bata ɗan kunnen ,duk wanda ya ja ruwa ai shi ruwa kan doka,lokacin da zai mata ciki ya yi denying ɗinta a nan ne zata zo ta ciki musu gidan da tashin hankali.
Da safe babu wanda ya tasheta dan zuwa makaranta dan yau farar Safiya take a gurinta,Driver dake ajeta shi kansa ya yi mamaki sanin wacece Anisa Indai wurin nawa ne,yau ita ta jira Zunairah a makaranta,da fara'a ta tareta amma ga mamakinta sai taga ta zauna bata ce mata komai ba ta fara fito da litattafai,sai abun ya zo mata a wani iri domin tunda take da Zunairah bata taɓa mata irin haka ba ko da wasa.
Matsowa kusa da ita tayi sosai ta ce"Besty wane yau ya ɓato Miki rai?".
Rumtse ido tayi ta juyo tana kallonta kafin ta ce"abin da ya faru jiya Anisa it shouldn't repeat it self,banji daɗi ba yadda ki ka kawo maganar Baba,bai kamata ba,kin san cewa magana ake ta Babana mene ya saka zaki faɗa ma Khalifa,har da baƙon fuska a gurin,idan wani ya fahimta kina tunanin kowane zai fahimta,wani ma cewa zaiyyi dan Daddy ya shiga aka saki Baba Amma da saka hannunsa,gaskiya banji daɗi ba".
Sakin baki Anisa tayi "aw yanzu Zunairah dan na faɗawa Khalifa abin da ya sameki mara daɗi ya yi Miki jaje ya zama matsala?".
"Ni ban ce Miki ya zama matsala ba,amma yadda ki ka faɗa mishi bai kamata ba ba dole sai kin faɗa Mishi duk abu da ya faru ba idan dole sai ya sani,a barshi ma Khalifa ne kaɗai,mene ya saka za kiyi magana irin wannan gaban Farouk wanda ban sani ba".
"Ko kice wanda ke ƙokarin toasting ɗinki ba, kina tunanin ni kuma na faɗi hakan dan ya janye,in one word Zunairah kawai ki ce na Miki baƙin ciki".
Kallonta Zunairah tayi na daƙikai tana mamakin abin da tace,daina kallonta tayi ta ce"duk abin a kika ɗauka haka ne,amma ni na faɗa Miki kada ki sake mun irin haka".cigaba tayi da ƙarasa assignment ɗinta wanda bata iya ƙarasawa ba jiya dare saboda baƙin cikin.
Kallonta kawai Anisa take tana sake sake a ranta,a hankali ajin nasu ya fara cika,class rep ne ya shigo inda yake shaida musu yau Lecturer ya ce ba zai samu zuwa ba,kafin kace mene aji ya ɗauki ihu inda wasu suka fara ɗaukar jakarsu dan tafiya, Zunairah ma assignment ɗin ta mayar jaka dan dama na malamin ne,kamar ance Anisa ta ɗaga ido ta hango Zainab bakin hall ɗin nasu tana kalle kalle,itama Zainab ɗin sai Idanunta ya sauka a direction ɗin su,ai a zabure ta ƙaraso ciki har tana haɗe kafa,ita kuwa Zunairah baki ɗaya bata ma kula da ita ba,kafin ta ankara sai taji saukar bulala a jikinta ta ko ina,a ruɗe ta tashi sai a lokacin ta kula da mai dukan nata,bata tsaya mamaki ba ta fara neman hanyar gudawa,kamota Zainab tayi ta cigaba da tsula mata bulala tana faɗin"mijina baza ki daina binsa kuna iskanci ba ko?,uban mene ya kai ku hotel ke dashi jiya".
Tasowa Anisa tayi tana kiran sunan Zainab kan ta bari amma bata karasa ba dan hanata sai hargagi dai take,yan ajin da suka rage ne suka riƙe Zainab dake aikin ɗura ashar akan Itafa sai ta kashe Zunairah,babban baƙin cikin Zunairah kuwa ba dukan bane ɓata mata suna da take a cikin aji,tashi tayi da gudu ta fita a ajin tana jin dama duniyarta ta tsaya a wannan lokacin.
Biyota Anisa tayi a baya da jakarta ta kamo hannunta wai su gudu,baƙin ciki takaici ya saka ta fizge jakarta tana mai cewa"ke sai ki yi ta gudun mana, kada ki biyoni"da haka ta bar gurin inda Anisa ta fashe da dariya ganin ta sha ƙwana,fitowa Zainab tayi,ganin Anisa ya saka ta ce"ina shegiyar tayi,ko da yake ai kema munafukace ba faɗa za kiyi ba".
"Ina cewa hanya guda ɗayace ta fita daga Nan,ta inda ki ka biyo nan ne hanyar komawarki itama nan ne zata bi amma duk abin da ya sameki ke ki ka jawa kan ki".
Tsaki Zainab tayi ta bi hanyar da Zunairah ta biyo,wayarta ta ciro ta kira yaya Halil ta ce masa ai ga nan Zainab ta zo Makaranta tana zane Zunairah,bin bayansu tayi bayan ta gama tada mishi hankali,so take tayi nawa da abin yadda har Yaya Halil zai zo dan ya ce mata yana kusa da makarantar nasu.
Zainab na barin gurin Allah ya ɗora Idanunta kan Zunairah dake jiran keke,kamota tayi ta baya kamar kayan wanki kafin ta ɗauketa da mari ta cigaba da zaginta tana faɗa maganganun ɓatanci a kanta,zafin hakan ya saka Zunairah ta biyeta ,kafin kace mene dambe ya kaure tsakaninsu,ƙoƙarin raba su ake dan masu daidaita sahun nan duka suka yo kan su,kafin securities dake bakin ƙofa,kafin Zunairah ta kula Zainab ta kamo mata hijabinta wanda ta sauke mata shi har ƙasa,tana aiming rigarta wani ɗan takifen dan Napep ya ɗauke ta da mari yana faɗin"dan uwarki tsirara zaki yi mata, shegiya mahaukaciya".
Wani irin ihu ta fasa tayi tsalle ta dira ta zube a ƙasa,ganin haka kowa ya dare a gurin,har da Zunairah,me Napep ɗin da ya mareta ne ya cire belt ɗin jikinsa yana cewa"ai mu abin nema ya samu Aljanu ?wallahi kin zo gun masu maganinsu".
Kafin ya kai ga dukanta ɗaya daga cikin security ɗin da yazo ya hanasa,ihu kawai take a ƙasa tana ta mirgine mirgine ,duk waɗanda tazo inda suke sai kaga sun dare,Anisa kuwa tana chan gefe tana video duk wani abu da ya faru,mai dan sahun nan ne ya bi bayan zunairah da yaga ta juya dan barin gurin tana mai riƙe gaban hijab ɗinta,"Hajiya ina zaki na aje ki".
"Tsamiyar boka"ta bashi amsa idanun nan sun kaɗa sunyi ja saboda kuka,tana kokarin shiga keken nashi sai ga Yaya Halil domin yana zuwa Anisa ta nuno mishi ita ,bai bi ta kan Zainab ba ya nufeta,riƙe keken dake niyar tashi ya yi ya ce"Zunairah ki tsaya muyi magana ".
Kallonsa tayi amma ta gaza faɗin komai illa ɗauke ido da tayi daga kan sa,ganin haka mai sahun ya ce"Malam ka sakar mun Keke ko na fizgeka Wallahi ".
Ganin zai fizge shi din ya saka ya saki suka bar gurin ,komawa yayi kan Zainab da ke ta hauka,sun daɗe a gurin ana abu ɗaya kafin iskanci da take ya lafa,da kanta ta tashi ta shiga motar Halil dan dama bada mota tazo ba,jikin nan nata biɗubiɗu,Anisa ma su tabi tana mai jin itafa an biyata,gida ya Kaita ƙin fita tayi sai da ya fita ya jawota waje ya yasar nan compound kafin ya koma motar ya fita a gidan Anisa na gefensa,sai da suka bar gidan ya faka motar ya kalli Anisa ya ce mene ya faru?
Matsar ƙwalla tayi ta ce"Yaya wallahi yau Aunty Zainab kam ta ɓatawa Zunairah suna a makaranta,wai ance an ganku tare a hotel jiya".
"Ita wane ya ce mata hakan?"ya tambaya ransa babu daɗi.
"Oho,nima Yaya wallahi ban sani ba,bari kagani har recording nayi maka sanin ba zan iya dakatar da ita ba amma ai ina da hujja akanta".Yana gama kalla ya tashi motar yana tunanin menene ma zaiyyi zuciyarsa tayi masa sanyi dangane da abin da Zainab ta aikata.
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔
𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎
Na
𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay)
E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟18:Behind all odds
*𝘡𝘜𝘕𝘈𝘐𝘙𝘈𝘏*
Kuka kawai nake a cikin Napep ɗin da na hau,duk da babu sauti amma hawaye fa ɗaya bisa ɗaya,bini bini mai keken nan yana juyowa yace mun nayi haƙuri,da muka shigo tsamiyar boka ne na nuna mishi layinmu dake jikin masu wankin Hula,da yake gidanmu ba can ciki yake ba a layin muna shiga na nuna mishi gidanmu,daidai ƙofar ya tsaya kuɗinsa na fara lalube zan bashi ya katseni ta hanya faɗin "Ita rayuwa dole bawa ya haɗu da jarabawa,idan mutum kuwa ya san kamala ba sai an nuna mishi mutum mai kamala ba,daga ganinki na san ke mai mutunci ce kuma duk abin da wancan mahaukacinyar ta faɗa a kanki na san karya take,kuma muna nan zata haɗu da daidai itane a gaba,kalle itane ke da asara musamman yadda ta wulaƙanta kanta waje wulaƙantaki,da zafi ki yi haƙuri".
Kuka ne mai ƙara yake san fito mun amma na danne sai hawaye,ɗauke idona nayi daga kallonsa na ce"nawa ne kuɗinka?".
"Ki ɗauka akan yau driver ɗinki ya ɗaukoki,idan mun haɗu gaba sai ki bani,ki saving sunana a ranki da Khubaybu mai keke "da haka ya ja adaidaita sahunsa ya yi gaba tsintar kaina nayi da yin murmushi ban bari yadda yake magana ba ya wuceni wajen gane mutumin Kaduna ne (itane,wancan kalle,),ban taɓa tunanin zan samu dan adaidaita sahu mai mutunci ba,tun haɗuwata da wanda ya kaini gidan su Anisa da damarmakinsu sai nake ganin kamar duk basu da kirki.
Gida na shiga ina mai sake riƙe hijabina,ina shiga gida ɗaki nayi niyar guduwa amma mama ta ganni,cike da tashin hankali da Mamaki ta ce"ke lafiyarki ki ka shigo kamar wadda tayi kokawa?".
Ɗauke kai nayi na ce"lafiya ƙalau Mama,"hannu ta saka ta jawo hijab ɗin da nake riƙewa ta ce"ba dai Lafiya ba Ohunene wane ya yaga miki hijabi?,faɗa ki ka yi a makaranta?,eh ye ye muga fuskanki wane ya yaƙusheki?"
At that point bana da halin ɓoye mata kawai sai na fashe da kuka ina ma faɗawa jikinta,bata hanani ba illa ma sake rungumeni da tayi tana mai ɗan buga mun bayana ,sai da nayi wanka naci abinci kafin Mama ta sake tambayata abin da ya faru,ban cire mata komai ba na faɗa mata,ita kanta abin ya yi mata ciwo dan haka nan tayi ta yagar faɗa Baba yana ɗaki sai dai kaji ya ce"Áhé(ayi haƙuri)"kamar ƙara tunzirata yake haka ta cigaba da faɗan,Mama bata iya fushi ba,gata da nacin faɗa da su Hauwa'u suka dawo ni ina ɗaki ma naji tana bawa Hauwa'u labarin abin da ya faru,ko kayan makaranta basu cire ba suka haɗu sunata ƙwashewa Zainab albarka ni dai ina jin su bance komai ba na koma na rufe ido na.
Wuraren la'asar muka ji Sallama a bakin gida,Mama ce ta leƙa,ina ji tana maraba Muryar Anisa dana tsinkaya ya sa na fahimci zuga aka mana,ƙaramin tsaki nayi na cigaba da danna wayata, can baya sun shiga ɗaki