Author : Chuchujay Category : Romantic Hausa Novels
ba,zaman shiru suka yi na wani lokaci cikin motar kafin Anisa katse shirun"wai Yaya baza mu wuce ba?".
Juyowa ya yi ya kalleta ita dake baya ya ce"Anisa bana san Enen taji maganar nan,magana ta tsaya tsakaninmu".
"Kai Yaya,duk Abinda matar nan tayi amma kace kada mu faɗawa Enen? someone need to step in o dan waɗannan da ka kira ba mutanen kirki bane banga alamaba baki ɗayansu yan iskane".
Sauke ajiyar zuciya ya yi ya rumtse idanunsa yana san ya yi reasoning da ita kafin ya ce"Hibba ki mata magana, wannan maganar bai kamata ace Enen taji ba saboda girman Allah fa,Satina biyu da Zainab da Aure sai kawai ace mata wai Mun fara samun matsala?come on".
Hibba ta saka baki har Anisa ta amince bazata faɗa ba duk da abun bai wani kwanta mata ba,idan ba Hauka ba bayan ta gama musu wannan iskancin yan uwanta kuma su zo su yi musu dariya?.haka tayi ta jaljala abun a ranta har ya kaisu gida ya aje,bai shiga ba ya juya,koda ya koma gidan abin haushin da ya tarar ya fi wanda ya bari ,Yaya Yunusa ya wani baraje mishi a falo sai kai lomar abinci yake gefe ya yi kaca kaca da ladar fast-food wanda ga dukkan alamu ya ci ne kafin a gama Taliyar da ko a ido bata burgesa ba.
"Har ka dawo kenan"Nadiya ta faɗa tana mai fitowa daga kitchen ita kuma hannunta ɗauke da plate ɗin shinkafa bayanta Zainab tana yin waƙa itama hannunta da plate ɗin indomie.
"Kan ubancan,wato abinci daban daban suka dafa dan tsabar rainin wayau ,dama ace gararsuce sai yace tasu ce amma good stuffs ne wanda ya siya da kuɗinsa tsabar isknci,ya yarda da Anisa ta ce dangin mahaukata ne su,amma dole a nemo mai hankali fa"guri ya samu ya zauna yana mai sake jin takaicin Yaya Yunusa wanda tunda ya yi sallama ya amsa bai kuma ce mishi wani abu ba,cike da baƙin ciki yace"ko dai sai na kira Malam ne,naga kamar maganar sai hannunsa".
"Malam kuma Halilu,mene ya kawo maganar Malam?".
"To fisabillilahi Yaya Nadiya na kiraku kan maganar da na san kune za ku faɗa mata taji amma sai naga kamar ma goyan bayanta kuke, Wannan yarinyar bata da kirki fa,ga wulaƙanci gaskiya bazan iya ba,idan baza kuyi mata magana ba zan kira shi Malam,nasan shi dattijo ne zai tsawatar".
Kamar haɗin baki sauka fashe da dariya dukansu wanda yin hakan ba ƙaramun saka harzuƙa Halil ya yi ba,saƙeƙe ya saki baki yana kallon ikon Allah,jikinsa ya fara kallo kafin ya mayar da kallonsa garesu ya ce"akwai kashi a jikina ko kuwa maganar da nayi ce tayi kama da kashi ya gitta?wane irin abu ne wannan,wai har da kai yaya Yunusa,to gaskiya A'a ku tashi ku tafi,dama ai nayi tunanin manyan arziƙine amma tunda abin har da rashin mutunci kawai ku zo ku wuce idan ma da abincin ne zaku tafi da ku ka dafa kashi kashi ta baku kula,amma gaskiya kuzo ku wuce kafin na harzuƙa ace nayi ma dangin matata wulaƙanci ".
Da zafi Zainab ta taso."Ni zaka cima mutunci gaban yan uwana?"
"Kina zuwan nan wallahi sai na burma Miki hannu a baki wallahi,sai na fasa Miki baki ya yi jini kin rasa Waɗannan ƙazaman haƙoran naki da sukayi wutsiyar kare,Ni zaki cewa ina ma yan uwanki wulaƙanci,wanda suke min fa? "Ganin ya dunƙule hannu ya saka Yaya Yunusa ya jawota baya yana faɗin"Calm down Halil ba wai wulaƙanci bane kayi haƙuri iskokan Zainab ne sun iya iskanci shi yasa kaga munyi dariya mun saba da halinsu na banza".
A wannan moment ɗin ji yake kamar yayi mishi mugun duka,"wato iskanta sun iya iskanci to ai nima Yaya Yunusa wallahi na iya,kada ku damu zan yiwa tufkar hanci kuje kawai Nagode ba damuwa ai iskanci ne yazo gidan ɗan iska ku gaida gida,zan maganin abun "bai bi ta kan Nadiya dake kiran sunansa ba ya wuce ya shiga ciki,yadda ya buga ƙofar kamar zai ɓalla ya saka Zainab ɗan firgita.
"Wow this is amazing Zainab shi mijinki bai san wasa bane?"Nadiya ta faɗa inda Yaya Yunusa ya aje spoon ɗin da yake cikin abincin ya ce"Dallah Nadiya zo mu bar mishi gidansa ,mene a ciki idan ba tsiya abincin kuma ɗan ubansa sai mun tafi dashi,ke zuba mana a kula ai ya san ba tsiyarsa muke ba".
"Bari kaga na zuba da kaina ubanwa muke tsoro,na fahimci idan muka biyema yaron nan ƙarshe iyaka zai mana da gidan yar uwarmu"cewar Nadiya wadda ta nufi kitchen dan juyin sauran abincin da suka dafa, Food pack Zainab ta ɗauko musu aka jera komai kafin suka kama gabansu,Nadiya na faɗa mata duk wanda bai raga mata ba kar ta raga mishi.
"Wallahi kada ki ɗagama kowane shege ƙafa dan na kula mijin nan naki dan iskane"Yaya Yunusa ya faɗa cikin siga ta gaɓunta,haka suka gama suka wuce kafin ta koma cikin gidan tana mai juya huɗubar yan uwanta,wanda bai raga mata ba bazata taɓa raga mishi ba daga Halil har danginsa.
*******************************************
*𝘡𝘜𝘕𝘈𝘐𝘙𝘈𝘏*
Kula da nayi rayuwa baza ta tsaya ba domin wani abu guda ɗaya na rashin jin daɗi ya saka na tattara dukkan lamurana na miƙawa Allah kamar yadda iyayena kan bani shawara,Mama zata ce mun"Ohunene duk abin da ki ka ga ya faru da bawa to tabbas baya da hanyar guje masa dole kuma sai ya faru Indai yana cikin zane na ƙaddarasa,dole ki yi haƙuri da Halil,duk wani abu da ya faru Alherina,yana nuna Miki tsakaninki dashi babu Alheri,idan kuwa da Alherin sai kiga daga baya kamar ba'a samu ɓacin rai ba".
Kalmar watarana mu na sake komawa da Yaya Halil kawai da Mama ta faɗa sai da naji wani ɗacin a bakina,tunda na duƙufa da roƙon Allah kuwa sai nake jin koda yanzu aka bani dama na Aure shi ba zan amince ba, mutumin da ya yi mun haka kafin Aure ina ga idan ya Aureni ɗin?.Yaya Halil ba mutumin da ya dace nayi sha'awa bane matsayin wanda zanyi rayuwa dashi, forever is too long to joke with,bana ganin Forever ɗina dashi.
A hankali sai nake jina sakayau kamar wadda aka saukewa nauyi,cikin yan satikan na fara jin sauƙi duk da nasan ba zan warke ba,amma mene sai na nemi abin da zai ɗebe mun ƙewar komai na ƙunci,duƙufa nayi wajen cigaba da rubutuna na littafin Love Scenery wanda Álhamdulilah sai nake ganin nasara tattare da hakan musamman a Arewapen da aka mun recommending ,a matsayina na Yar Arewa sai abin ya sake burgeni musamman ganin yadda aka karɓeni a manhajar duk da a sabuwa nake,sai nake jin tuntuni ina na tafi nake kokawar samun guri a inda wata ta bigeni har ake tunanin na sace mata fasaha,amma fa ban bar sauran Apps ɗin ba wanda suma a hankali aka fara karɓata musamman da suka kula Labarina ya sha banban da na 𝘔𝘪𝘥𝘯𝘪𝘨𝘩𝘵 𝘈𝘶𝘵𝘩𝘰𝘳𝘦𝘴𝘴 ga waɗanda suka bani dama kenan fa.
Na gama sakankancewa akan baƙin ciki da fargaba zai barni sai kwatsam wata ranar Lahadi Muna zaune a tsakar gida,ni ina assignment ɗin makaranta da zamu koma Hauwa'u ma nayi na makaranta Mama kuma na ragewa Adavize gashi da clipper ɗinsa ,Sallama Aunty Muna tayi da sassarfa tana kuka tana mai ambatar "Mama Zunairah akwai tashin hankali"
Sakin kan Adavize Mama tayi ta je gurin Aunty Muna tana tambayarta "Lafiya?.Uncle Abdulbaƙi ne ya shigo yana kiran sunanta yana cewa"wai kam Muna ba nace Miki kada ki zo ki tada musu hankali ba?"aikuwa take tashin hankali ya ƙwanƙwasa mana ƙofa dukkanmu lokacin da ya ce wai Baba yana state CID a kan case ɗin Satar Waya.
Ruɗewa sosai Mama tayi ta fashe da kuka ta doshi ƙofar gida wai zata gurin Baba,Uncle Abdulbaƙi ne ya dawo da ita yana bata haƙuri yana cewa"Maman Zunairah abin zamu bi a hankali yanzu chan zamuje ni da maƙocin ku Malam Bello,dan Allah kiyi haƙuri ba wai ance ya yi sata bane".
Ɗaga hannu Mama tayi sama tana kiran Allah tana mai gyara Zaninta ta ce"Abdulbaƙi Allah da nake bautawa ya fi Allahn wanda mugaye ke bautawa,Baban Zunairah ba ɓarawo bane ba kuma zai fara sata a yanzu ba da girmansa da yayansa da mutuncinsa,ka barni naje na samu yan sandan sai na faɗa musu hakan su ma".
Mu kuka Mama kuka babu wanda zai ce da wani ya yi shiru ,gidanmu sai ya zama kamar gidan yaran da akewa allurar rigakafi,da ƙyar suka lallashi Mama shima sai da Malam Bello ya tabbatar mata zasu dawo da Baba cikin aminci,idan sunje basu dawo ba da shi ɗin ba sai a koma da ita gobe.
Ai tana jin wannan Magana ta sake rushewa da kuka tana maimaita"aw yanzu sai ya ƙwana?"jin haka ya saka muma yaransa muka cigaba da rusa namu.
Munsha kuka iya kuka,daga bisani Mama tace ai wannan kuka ba zai mana ba kowa yaje ya yi alwala ya yi Sallan Nafila ya faɗawa Ubangiji Mai kowa mai komai halin da muka faɗa duk da yana kallo kuma yanaji.
Da su Uncle Abdulbaƙi suka je duk yadda suka so basu dawo da Baba ba saboda yadda case ɗin ya yi girma dan ko ganinshi ba'a bari sunyi ba amma an faɗa musu abin da ya faru,lokacin da suka kama Baba sai ya bada number ɗin maƙocinsa Malam Bello wanda shi ya sanar da Uncle Abdulbaƙi abin da ke faruwa.
Dayake ƙwana biyu baya fita da mota ta samu Matsala sai yake hawa motar haya,to yana dawowa ranar sai ya ke dan rage ta daga gidan Gwamna duba da kuɗin dake jikinsa basu da yawa kafin ya hau abin hawa,kwasam sai yaga motar yan sanda har guda biyu sun kamo wasu a ciki suna bin wani dake ta tirƙar gudu kamar dai ƙwace musu ya yi,yana zuwa daidai saitin Baba suka cimmasa,Baba ya gama ruɗewa sai ya kasa gudu ya tsaya,ganin hakan ya saka wannan yaro da suke bi ya riƙe Baba Tsam yana faɗin "Oga ba haka muka yi da kai ba,kace duk rintsi baza ka bari a kamamu ba".
Still Baba ya yi a gurun yana kallon yaran da ke kallansa cikin ido yana faɗa mishi maganar da bai ma san ina ta dosa ba,kafin Baba ya farga sai gani ya yi shima an daɓa mishi anƙwa tare da wannan yaro,.wai sai da suka je CID yake jin wai barayin wayane da suka damu yankin Tarauni aka kama sannan a cewar barayin Babane shugaban su,idan sun saci wayar shi suke kaiwa ,shine yake saka su yana biyansu wani abun,kuma wai Baba ke basu Layar ɓata.
Abin Mamakin shine yadda duka yaran shida suka amsa sharrin na farkon akan abinda ya faɗa gaskiyane Baba ne ogansu,duka suka bada shaida guda ɗaya,ba a fara tuhumar Baba da ya mutu a zaune sai da aka ciro abubuwan dake jikinsu na tsubu,wai sai cewa sukayi Baba duk ya basu.
Ɗaukar Baba akayi aka kai ɗakin DPO wanda yake san magana dashi ta san fahimta,suna so kada ya basu wahala suma kada su basu wahala a kaisu kuto a yanke musu hukunci,cike da rashin jin daɗin al'amarin DPO ɗin ya kalli Baba ya ce"Malam Buhari Muhammad daga kallonka dai kayi zubin mutane masu kamala na yi mamaki da ka saka kanka cikin irin wannan ƙazamar harkar,gaka dai aikin gwamnati ka ke yi gidan Gwamna ma amma kuma kana bada gudunmawa wajen ɓata mana tarbiyyan yara,saboda Allah yaran nan duk zaka haifesu amma ace kai kake goya musu baya wajen ganin ɓarna ta yaɗu?ka san yaran nan har kisa sunayi?ko da yake ai ba sai na tambayeka ba tunda kaine Uban gidansu,yanzu dai Bama wannan ba ka faɗa mun dalilin da ya saka kake goya musu baya ka ke saka su, bana san ta kaimu da sai an taɓa maka lafiya".
Kuka kawai Baba ya fashe dashi Yana sake jaddada musu Wallahi ƙarya suke mishi hasalima shi bai san waɗannan yaran ba".
Duk yadda suka bi da Baba maganarsa guda ɗaya ce,hakan ya saka DPO sawa a ɗauke Baba aje a bashi kashin tsiya,Allah sarki Babana,duk wannan Azabar bata saka ya amsa laifin da bashine ya yi ba,bayan sun masa matsiyacin duka har da karaya aka watsosa ɗakin da aka kulle yaran cikin Azaba,yanaji ɗaya daga cikinsu na cewa"Amma kamalu baka kyautawa tsohon nan ba,kalli yadda kwalawan nan suka mishi ragaraga fa".
"To Habu dan Allah idan kwalawan sun shigo kace sharri nayi mishi kagani,ka dai san Oga bamaiyi zai kuɓutar damu ko? to idan muka ambaci sunansa aka zo aka kamashi mu wanene zai cecemu?shi wannan tsoho Eh mai sunan Daraja Allah yayi zai ɓara gyaɗar da bai soya ba ya kuma fige kazar wahala,kaddarasa,idan za ka ja eh banƙareren bakinka ka ja ka yi shiru".
"Sai da kai mataimakin Oga,wanda ya bi wani bayanka Uwassa,Hubule na Atikar farm Centre mai shikafa da waken yan gata Allah wallahi "ɗaya daga cikin yaran ya faɗa.
Ɗan sanda guda ɗayane ya leƙo ya ce"baza kuyi mana shiru ba ko ai mun saka ku?".
"Sai Oga,ka huce haka nan"cewar Habu,Baba yana jin su bai ma iya faɗin komai Azabar dake ratsa tsohon jikinsa kawai ta ishe sa.
Da safe Labari ke iske mu inda Malam Bello yace Mama tazo suje,suna maganar ne naji yana cewa Uncle Abdulbaƙi da ace wani babban zai shiga da abun yazo da sauƙi,da Mama suka wuce duk da Muna cikin tashin hankali haka nayi ta lallaɓa Su Hauwa'u suka wuce islamiyya duk yadda Hauwa'u ke nacin dan Allah kada na musu dole amma ganin rashin amfanin zaman da zamuyi mu haɗa kai muyi ta kuka gwara suje ɗin.
Bayan wucewarsu abin duniya ya isheni,wane muka sani mai kuɗi mukam?duk inda tunanina ya kai na rasa wane zan kamo,ina wannan tunanin Anisa ta faɗon mun,ko wanka banyi ba na doshi gidansu na san idan naje daddynta zai taimakawa Baba.
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔
𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎
Na
𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay
E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟ 15:
*𝘡𝘜𝘕𝘈𝘐𝘙𝘈𝘏*
Ganin nake kamar mai adaidaita sahun da na hau baya sauri,tsaki nayi har yafi a irga,tun yana tambayata lafiya ina ce mishi ƙalau har ya mun banza shima,daga gani na kaishi maƙura tsakin da nake ta bugawa,ban ji baƙin ciki ba sai da na sauka wai babu chanji.
Da mugun takaici nace "amma mai keke sai da na faɗa maka ɗari biyar ce a hannuna kafin na hau ko?".
"To Hajiya ki yi haƙuri a samu mana haba dan Allah,mutum ya yi ta tsaki kamar bashi da lafiya,Allah ya sa ba dani ki ke ba,yauwa abokina ɗan raba mun mana"ya maida zancensa kan ɗan uwansa mai adaidaita sahu,ni dai bance Mishi komai ba dan idan na biyesa ba ƙaramun faɗa za muyi ba a yanayin yadda nake jina,miƙomun chanji na ya yi yana mai cewa"Ƴar wahala".
Na gefen dana sauka ne ya ce "dan Allah bawan Allah mu wuce ke kuma kiyi haƙuri kada ki biyesa".
"Zaka samu daidai kai ne a gaba, wallahi"daga haka ban sake cewa wani abu ba na shiga layin su Anisa ,ni nake tafiya amma ji nake kamar ƙafafuna basu sauri duk irin saurin danake,sai da naje bakin gate ɗin gidansu sai ƙafafuna suka tsaya ,idan na shiga mene zan ce musu?after abin da Yaya Halil ya yi mun ya kamata ace nazo neman taimako su?take naji wasu hawaye sun fara zubar mun a kunci lokaci guda kuma maganar da mai Napep ɗin ya faɗa mun na ƴar wahala ya fara dawo mun,sai kawai naji maganar tayi mun wani ciwo da ta bada gudunmawa wajen sake fashewa da kuka na mara sauti,Aikuwa Ƴar wahalar ce ba komai ba,idan ba haka mene zai kawoni ƙofar gidansu Anisa neman taimako,ina self respect ɗin?
"Mene ake da self respect bayan wanda yake riƙe mun respect ɗin danake taƙama dashi yana chan a kulle akan tuhuma mafi muni da ƙasƙanci"ina tsayen nan ina so na ƙwanƙwasa aka buɗe,Yaya Halil ne ya fito bayansa biye da Wata mata da ba sai an faɗa mun matarsa bace,
Saurin matsawa nayi a kiɗime na ɗauke kaina ina jiran su wuce,tsaye yayi yana kallona,ganin yaƙi fita ya saka ta fito tana cewa"kaga malaika ne da ka Maƙale a gurin nan ko.."ɗaukewa maganar da take niyar yi tayi tana mai kallona kafin ta kallesa ganin ya yi mun ƙuri ya saka ta gano wacece ni,cike da sigar tambaya ta ce"Zunairah??"kallonta nayi a karo na farko ban dai amsa mata ba,Kama hannunta ya yi kamar wadda za tayi mun wani abu yana mai cewa"No Zainab bana san fitina".
"Aw fitina Halil?fitina?da wannan yarinyar ka ke cin amanata ko ?shegiya ki ke yawo da wani tsayi kamar daren mutuwa,to wallahi karya ki ke,yanzu ubanki ki ka zo yi gidan nan dan Uwar babanki,Shegu matsiyata masu bin maza har gidan iyayensu"
Rasa abin yi ya saka na fashe da kuka,na juya zan bar gurin ya rugo ya riƙe hannuna yana mai faɗin"mene yake damunki Zunairah?i can see it a idanunki wani abu na faruwa,menene ya faru? ".
Ƙokarin ƙwacewa nake ganin Zainab na faman huci,cikin rasa wani abu da Zanyi nace Mishi gurin Daddy nazo ni ba gurin ka nazo ba".
"Ka barni ni sai na tambayeta matsiyaciya yar iska".
Ganin ta sake tunkaroni ya saka ya mayar dani bayansa ,ban ƙokarin Matsawa ba kula da nayi kamar bata da hankali,hannuna ya kama yayi gidan dani yana mai ƙokarin tare Zainab daga tunkarata,gyalen jikinta ta cire ta ɗaura a ƙugu ,tana mai yin wani shewa,ganin haka ya saka muna zuwa ƙofar na shiga da gudu inda tayi wani kukan kura ta yo ƙofar gidan itama amma sai ya tareta cikin zafin Nama,da gudu na shiga gidan ko sallama banyi musu ba na banka cikin falon ina zazzare ido".
A tare suka taso suna tambayar Lafiya?,kuka kawai na fashe dashi,Anisa ta taso tazo inda nake ta rungumeni tana tambayar menene cike da damuwa,kafin na bada Amsa Yaya Halil ya shigo yana tare Zainab da ke rugowa da gudu tana faɗin wai sai ta kasheni.
Enen ce ta tareta"menene hakan Zainab?".
"Enen ki barni nayi maganin damuwata,wai yarinyar nan ashe har yanzu cin amanata suke da Halil,Kinga yadda suke magana da ido tsabar shaiɗanci?".
Cike da jin haushinta Yaya Hibba ta ce"Wai ke kam mene damuwarki Aunty Zainab? Shi ya faɗa Miki wani abu ke tsakanin su".
"Kada