Author : Chuchujay Category : Romantic Hausa Novels
ina tare da wani ba bayan shi,"so all this while zargin da ka ke mun kenan?".
"No Baby ba haka bane kawai na fara feeling insecure ne"hannu na ɗaga mishi kafin na ce"yaisa Nagode "buɗe motar nayi na fita ,yana ƙokarin buɗewa ya fito domin biyoni Anisa ta bayyana a gurin,ganina ya saka da Mamaki ta sake kallon motar,kafin ta ce wani abu ya yi ma motar key ya bar gurin,bin motar tayi da ido kafin ta dawo da kallonta gareni ta ce"wannan ba motar Yaya Halil bane?naga kuma kin fito a ciki yana ganina kuma ya juya kamar bai sanni ba ya wuce".
"Mun haɗu a hanya ne ina tahowa shine ya rage mun hanya,amma tafiya da ya yi kam kilan bai kula da ke ba"na bata amsa ina mai kamo hannunta da zummar mu tafi,ƙwacewa ta yi ta ce"he saw me now,sai da na roƙeshi akan ya kawoni makaranta yau driver na baya nan ni kuma bana da license tukunna ya ƙi,yanzu kuma sai na ganku tare?".
Ganin irin kallon da take munne ya saka nayi dariya ina mai gudun kada ta gano ni kafin na ce "babe calm down yanzu taho dani da ya yi ma ai kamar ya yi miki alfarma ne ,na ce miki a hanya na ganshi ya rage mun hanya".
"Wacce hanyar,tunda dai na san daga gida abun hawa zaki hau ta ya akayi ya ganki a hanya ya ɗauko ki bayan ba guri ɗaya muke ba, ku haɗu a hanya kuma abu guda ne,either kin san zai zo ko kuma kun yi communicating"ta sake firing tana zuba mun ido.
Kafin ma bata Amsa mutumin da na tsana fiye da kowa a dangin Anisa ya cece ni,kiran sunanta yake amma yana gani na ya washe baki yana dawowa inda nake yana na faɗin"baby!!".
Yaƙe nayi ina mai cewa"ina kwana ya Adam "kafin na matsar da jikina daga inda yake .lasar leɓe yake yana kallona yana faɗin "Masha Allah, watanni kawai kin sake kyau Zunairah ,nayi missing abubuwa da dama gaskiya ".
Sosai Anisa ta haɗe rai ta kamo hannuna tana mai cewa "bana so Ya Adam mun yi maganar nan da kai ba sau ɗaya ba, ba biyu"da haka ta ja hannuna muka nufa inda na fi tunanin nan ne class ɗin mu,ban mamakin yadda ta samu seat ɗin gaba ba,Anisa ake faɗa muku,a lokacin da nayi tunanin ta bar maganar Yaya Halil a gibar ta kamo maganar munje Sallah inda take cewa "Zunairah kina san Yaya Halil?".
Sarƙewa nayi da yawon bakina dan ban taɓa tunanin zata mun wannan tambayar ba,tambayar ta nayi da wane irin tambayane wannan?.
Ƴar dariya ta saka tana mai san kawar da tambayar kafin ta ce"I'm sorry abun da na san zai wahala ya faru after all na san cewa Yaya Halil ba irin mazan da ki ke so bane ,how dumb of me".
Nima dariyar nayi yadda tayi amma deep down fargaba ta ziyarceni,cikin rashin Sanin nauyin furucina na ce"idan nace ina san shi fa?".
Kamar an ɗauke mata wuta haka komai nata ya tsaya inda na kasa karantar yanayin da furucin nawa ya jefa ta ,dariya na saka kamar wata taɓaɓɓiya ina mai mata dukan wasa ina cewa "babe im kidding ji yadda ki ka saka serious face,kin manta ina da boyfriend"ƙarasa maganar nayi ina mai nuna mata zoben dake hannuna,sai a Wannan lokacinne ta saki jikinta ta ce"well har na so na manta hakan,but mind you duk lokacin da ki ka fara san Yaya Halil ki ka ji kina san dumping waccan boyayyen gayen akan sa,na zama ta farko da zan sani domin nice kaɗai zan iya baki taimakon da ki ke buƙata,dan nafi kowa sanin wanene yaya Halil,duk da macen da yake so baki cikin tsarinta amma zan ƙoƙari nayi 1 or 2 a san ya za a yi".
Sosai maganar ta yi mun nauyi a ƙirji,sai naji raina ya ɓacci da Yaya Halil, maganar na fara haɗawa guri ɗaya da wadda ya yi mun,ko so yake ya rabu dani dan ya gano ban kai yadda yake so mace ta kai ba?to mene ma yake so ɗin?ban sani ba wadda zan tambaya kuma a yanzu dai a moment ɗin da muke ciki last wadda zan tambaya ita ce.
Kada kuga laifina ina so idan ina soyayya ko ina na cike gurbi gurin wanda nake so,yaya Halil yana nuna mun soyayya sosai,amma fitar maganar nan bakin Anisa sai sheɗan yake ƙara zugani kan maganar da ya faɗa mun ɗazu na kai karshen batun a kan yana san rabuwa dani ne dan ya samu wadda ta fini,baki ɗaya na kasa yarda maganar san kowa ya san muna tare ta kawo faɗan,ya san bana so a sani shine yake amfani da hakan dan nayi fushi nace a rabu.
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔
𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎
Na
𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchu jay)
E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟˚:8.:first fight
*𝘡𝘶𝘯𝘢𝘪𝘳𝘢𝘩*pov.
Baki ɗaya na kasa cire Maganar Anisa a raina,har na koma gida abun na damuna musamman da ya ƙi kirana,na duba wayata ya fi sau adadi ko zai kira ni,lokacin da Baba ya kira na haɗa shi da Mama baya samun wayarta jikina na ɓari na ɗauki wayar tunanina shine, atleast ina san na saurari haƙurin da zai bani dangane da ƙazafin da ya yi mun na ina tare da wani daga nan sai na kawo wancan maganar,amma har magrib bai kirani ba,haka na cire rai ina mai jin Zuciyata na mun wani irin zafi,na tambayi kaina ya fi a irga mene yake damuna ?.
Bayan sallar magrib ina yi ma Adavize tilawar hadda wani yaro ya shigo wai ana sallama da ni,wata irin faɗuwar gaba naji ta ziyarceni,cigaba nayi ban tsaya ba inda Mama ta ce yaje yace ina zuwa,har yaron ya fita ban dakata ba,ganin haka ya sa mama ta ce"Hafiza sai ki sauke karatun nan haka Ometere ta cigaba mishi,kinji ai ana Sallama da ke a waje na san kuma kina san zuwa ɗin". kunya ce ta kamani sosai, tashi nayi na shiga ɗaki,ina jin Hauwa'u ta karɓi karatun sai dai tun kafin aje ko ina sun fara faɗa.
Sallama nayi ma Mama kan zan fita tace na kula,na san fitar nan ko mu shirya ko mu sake wani faɗan,abun mamaki wannan shine faɗan mu na farko tunda muka fara soyayya.
Yana cikin mota bai fito ba ga motar duk tint Sannan ban san shi da ita ba,chogewa nayi na tsaya,horn ya yi amma na yi mishi banza,ai ya san bana zance a mota ba kuma zan fara a motar da take duk duhu ba gefe da gefe ,gaba da baya ganin bana da alamun takawa ya saka shi buɗe motar zai fito,ganin hakan ya saka na haɗe rai sosai ina mai kashe inda zai fito da ido.
Saurin ja da baya nayi ganin wanda ya fito daga motar yana kaɗa key ɗin sa ,idona na sauka cikin nasa ya kashe mun ido guda ɗaya,ya akayi wannan ɗan iska ya san gidan mu?. tambayar na mayar masa zuwa fili "Ya Adam mene kake a ƙofar gidan mu?"
Yar dariya ya yi yana mai takowa yana cewa"mai san tsuntsu ai shi yake bin sa ya jifeshi".
"Kada ka sake kirana tsuntsu"na faɗa cikin rashin zato da tsammani,dariya ya saka sosai jin abun da nace kafin ya ce "kin yadda ina sanki kenan tunda har kin amince ke tsuntsu ce,to forget about that,rashin iya Hausanki bai dameni ba,a haka nake san ki nake san kasancewa da ke matsayin matata,akan abin da ya faru tsakanin mu yanzu nake san gyarawa,dan Allah Zunairah ki kalleni ki manta da wani Halil bai dace dake ba".
Wani irin faɗuwa gaba ce ta kawo mun ziyara,ganin reaction ɗin da nayi da ido ya saka shi kecewa da wata shaƙiyyiyar dariya yana mai ɗaga mun gira ya ce"You heard me,kina tunanin ban san kina Soyayya da Halil ba?I'm not his little Naive sister Anisa ,Adam nake duk yadda ki ke tunani kuma na wuce Nan,ina da kaifin basira,a kallo ɗaya ba sai an faɗa mun soyayya ku ke ba ,ballanta kuma na ji daga bakin da soyayya ake yi da shi',Halil ya faɗa mun so which koda bai faɗa mun ba na san ke dashi kuna soyayya'".
Wani irin duka ƙirjina yake ,haɗe rai nayi sosai kafin na ce"to sai mene idan ka san muna soyayya ni da shi?,after all soyayya kace Muna yi ba iskanci ba,and Ina so ka sani ta ko ina ya fika tunda shi ɗin ba ɗan iska bane kamar ka mai neman duk hanyar da zai bi ganin ya keta haddin mace,kaga information ɗin nan da kake da shi idan kaga dama ka kaishi duk inda ya yi maka bai dameni ba, abu guda ɗaya nake san ka sani,kada ka kuskura ko da wasa ka sake taƙo ƙafar ka ƙofar gidan nan da sunan ka zo gurina,ina roƙonka kafin na sigar da police report kan harassment ".
Na juya zan shiga gida ya danƙo hannuna ,yin hakan da ya yi yazo mun a bazata,kalle kalle na fara gudun kada wani ya ganni hannu guda kuma ina kiciniyar hannun da ya damƙe da ƙarfi ya ƙi saki,kamar haɗin baki sai ga dannowar Motar Halil,sake kallon hannuna cikin na Adam nayi kafin na mayar da hankalina kan motarsa ina faɗin"ka sake ni dan girman Allah".maimakon ya sakeni ɗin sai ya mayar da dubansa direction ɗin da nake kallo,wata irin dariya ya saka yana cewa "ki ce Romeo ne ya zo well Kinga ya tarar da majnun ya riga da zuwa".
Riƙon da ya mun akwai azaba amma azabar bata dameni ba ,damuwata guda ɗaya kada Yaya Halil ya tadda mu cikin wannan situation ɗin dan ko da wasa ban taɓa faɗa mishi na san Adam ba,duk roƙon da nake ma mitsiyacin nan bai sake ni ba har sai da abin da nake gudu ya faru,tsaye yaya Halil ya yi a kan mu yana kallon ikon Allah yana mai faɗin"mene yake faruwa anan?kai Adam mene hakan ka riƙe mata hannu besides me ka ke yi a nan?"yana maganar ya saka hannunsa ya fincike riƙon da Ya Adam ya yi mun.
Dariya ya Adam ya yi irin mai shaƙar da wanda ake yi wa ya ce"kaji mun wata tambaya da Halil,i mean ka kalli Wannan yarinyar da kyau,ka kalli haɗuwarta fa,Nima ka dubani,ka ganni bakin gidansu ,sai ka tambayeni me nake yi?ni Adamu?,well it's understandable tunda kana tunanin kai kaɗai ake bawa ka ci,to Nima ina ƙwasar abin da ka ke samu ne".
"Innallahi waina illahir rajiun Ya Adam ka ji tsoron Allah "na furta hawaye na bi mun kunci kamar suna jira musamman ganin Ya Halil ya zuba mun ido,dariyar da Adam yake ce ke shigar mun ƙwaƙwalwa kamar zata Haukatani ga kallon da nake ƙarba daga gurin wanda nake so fiye da komai domin da ace kallo na kisa da tuni a wannan gurin na mutu,hannu na ɗaga na zabge algungumin da mari kafin na ce"duk Ku bar ƙofar gidan nan idan babu wanda yake da gadonsa".ina kai karshen maganata na juya na koma gida har ina haɗa hanya,ina jin Ya Adam yana dariya sosai ya wuce motarsa ya bar Yaya Halil A gurin wanda Allah kaɗai ya san abin da ke cikin zuciyarsa domin ni banace ba musamman da irin kallon da yake bani wanda na kasa fassara abin da yake nufi.
Da na shiga gida Mama bata nan su Hauwa'u ne inda na barsu,ina ji tana tambayata abin da ke faruwa nake kuka, banza na mata na shiga cikin ɗakin mu ina bakin ƙoƙarina wajen ganin na shanye kukan amma ina shiga ya ƙwace mun,mene na yiwa Adam a duk faɗin duniyar nan da ya nemi ya ɓata mun Alaƙata da Ya Halil a Wannan gejin da muke kan saɓani?.Tambayar da nake ta yiwa kaina kenan ,I'm sure akwai mata da yawa da zasu bashi kan su waje ba sai ya sha wannan wahalar ba ,mene ya saka ya zaɓi da ya ɓata tawa rayuwar bayan ya san ba zai taɓa samun abin da yake so daga gareni ba,1 minute ya ce yana sona,1 minute ya nemi ya maidani mutuniyar banza gurin mutumin da ke ganin kimata da mutunci na,tunanin hakan kawai ya saka kuka na ya kasa tsayawa baki ɗaya.
Ina jin motsin Mama nayi saurin goge hawayena,tambayata ta fara lafiya? Hauwa'u na bayanta wanda ita taje ta kira Mama ta ce mata wai ina ɗaki ina kuka dana shigo daga waje,kasa magana nayi sai kukan da nake ta yi wanda duk yadda na so na riƙe na kasa,Mama na ƙokarin zama kusa dani Muhammad Ya shigo da gudu ɗakin yana cewa "Mama Brother ɗin nan dake zuwa Gurin Aunty Zunairah ya shigo wai yana san ganin ki".
Kallona Mama tayi nima ita ɗin nake kallo,"me kuma zan mishi?"na faɗa ina ƙokarin tashi ina ƙarawa da "Mama bari naje na sallameshi".mayar dani tayi ta zaunar ta ce"Ni yake san gani ba ke ba,idan kuma gaskiyane baki dashi to wannan is another story,if not ki zauna a nan naje na ganshi, Hauwa'u je shiga dashi falo ina zuwa" .
Kuka na sake fashewa dashi musamman da ban san abin da zai faɗawa Mama ba,bata bi ta kaina ba ta fita a ɗakin tana mai sake jaddada mun kada na kuskura na fito a ɗakin nan idan ba so nake raina ya ɓaci ba.
*******************************************
*𝘏𝘈𝘓𝘐𝘓*
Tunda ya shawo ƙwana ya ga Zunairah da Adam hankalinsa ya yi mugun tashi Musamman ganin hannunsa riƙe da nata,tambayar da yake ma kansa abin da Adam yake a gidan su Zunairah,dama sun san Juna?sanin sai ya fita zai samu amsa ya saka ya buɗe Motarsa ya fita amma ga mamakinsa sai yaga riƙon da ya yi mata da bawai riƙone da ta yi na'am da shi ba,bai wani tunanin ba ya ƙarasa ya kwace hannunta yana mai tambayar dalilin da ya saka ya riƙe mata hannu da kuma abin da yake a ƙofar gidansu,Amsar da ya bashi ba ƙaramun kaɗa mishi hanji ya yi ba duk da ya yarda da Zunairah ɗari bisa ɗari sannan ya san ƙaryar Adam fiye da tunaninsa dan zai iya cewa babu maƙaryacin da yafi Adam a danginsu,idan ya zula maka ƙarya sai ka fara tunanin baya da ƙwakwalwa ko yana fama da larurar Hauka dan kai mai ji kana sauraro ka san ƙarya yake amma haka zai dage ya yi ta Zillo ta.
Kallon Zunairah yake Bama ya sauraron abin da Adam ke faɗa burinsa guda ya gama ya tafi ya gana da ita dan tun maganar da ya faɗa mata ya kasa nutsuwa dalilin da ya saka ya biyo baya kenan .
Jin tace su bar ƙofar gidan ta juya da gudu ya saka yaji wani irin nauyi,yana jin dariyar Adam har ya bar ƙofar gidan ,kamar ya tafi amma sai yaji ƙafafunsa sun ƙin amince mai da yin hakan ,baki ɗaya tunaninsa abin da yake bashi ya bita ciki,tsintar kansa ya yi da bin umarnin Ƙafafunsa wajen bin Zunairah cikin gidan,sai da ya shiga tukunna ya farga,Muhammad ne kawai a tsakar gidan wanda yana jin shigowar mutum ya ɗago ya zuba Mishi ido.
Ganin hakan ya saka yace ya yi mashi magana da Mama Wanda shi kansa bai san abin da zai ce mata ba,sai a Wannan lokacin Muhammad Ya gaishe dashi kafin ya tashi ya shiga dan kira mishi Mama
Tunda Hauwa'u ta shiga dashi Falo yake neman abin da zai faɗawa Maman,zuciyarsa ta riga ta faɗa mishi idan har bai shigo ɗin ba Zunairah ta ƙwace mishi har Abada inda shi kuma bai shirya hakan ba,Mama na Sallama ya sauko daga kujerar da yake ya zauna ƙasa,da fara'arta ta shigo ciki tana cewa"Malam Halil ka zauna mana ka sakko ƙasa".
"A'a Mama nan ɗin ma ya yi,ina wuni Mama?".
"Lafiya lau Álhamdulilah, ya mutanen gidan?"ta amsa tana mai zama kujerar dake kallonsa .
"Álhamdulilah Mama,dama nace bari na shigo mu gaisa idan da hali kuma na ga Zunairah yadda ta shigo ɗinne na kasa jurewa nace bari na shigo mu yi magana".
Cikin san sanin Abin da Yake faruwa Mama ta ce"fatan dai lafiya?don har yanzu kuka take bana tunanin kuma Good time ne da zaka ganta da kun daidaita ɗin,ku ɗinga haƙuri da juna ita alaƙa irin wannan idan Ubangiji ya haɗa dole ne mu koyi haƙuri,ba zan nace sai naji abin da ke tsakanin ku ba ,amma ku ɗinga haƙuri dan Allah".
Kamar jira yake ya fara Rero mata abin da ke faruwa inda ya sake jaddada mata ko a yanzu ba shine ya ɓatawa Zunairah rai ba dan uwansa ne Adam ,musabbabi ma bai san mene ya haɗasu ba,ƙarawa ya yi da cewa"Mama wallahi ina san Zunairah sosai dan Allah ki bata haƙuri ta saurareni ,kuma ina so iyaye su san da hakan, insecurities ɗin da take dashi a kaina insha Allahu zan ƙoƙari wajen bata tsaro idan shine ya saka bata san yan gidan mu su san muna Soyayya,maybe tana tsoron banbancin Yaren mu,ita Ebira ni Idoma,Mama mazan Yaren mu Muna riƙe mata sannan gidan mu babu ƙabilanci,insha Allahu ba za ku yi kuka dani ba ,itama kuma ba zata yi dana sanin Aurena ba".
Kunyar maganar nasa Mama ke ji sosai duk da ta gamsu da yana san Zunairah tunda har zai cire kunya ya zo gabanta ya furta mata wai yana san Zunairah,bayan ya gama ya tashi ya masu Sallama ya wuce gida zuciyarsa kamar an cire masa wata damuwa duk da bai samu ya ga Zunairah ba.
𝗖𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔
𝙲𝚊𝚞𝚝𝚒𝚘𝚗𝚊𝚛𝚢 𝚝𝚊𝚕𝚎
Na
𝗔𝗠𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗔𝗠𝗜𝗟 𝗔𝗗𝗔𝗠(chuchujay
E˟˚P˟˚I˟˚S˟˚O˟˚D˟˚E˟˚:9:Cat out of Bag
*𝘡𝘶𝘯𝘢𝘪𝘳𝘢𝘩*pov.
Ina jin Mama na mishi Sallama tana mai sake jaddada mishi kada ya manta ya sanar da Enen tana gaisheta sosai,yana tafiya ta shigo ɗakina,ina ƙoƙarin tashi ta ce mun "yáàtùû(zauna)ina zaki je?we need to talk.
Zama nayi kamar munafuka ina aikin sinnar da kai,itama kusa dani ta dawo ta zauna tana Nazarina kafin ta ce"Zunairah kina san Halil kuwa?i mean idan ba san shi ki ke ba ya kamata ace kin faɗa mishi sai ya daina wahalar da kan sa ya samu