ABINDA KE FARUWA HAUSA NOVELS BY YAR JINGAU

Author :  Yar Jingau Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   15 / 31

42K to 45K   out of 92.1K words

wannan tarin wankin yanzu ba wasu ne zasu taru,gara kabayar asiyo muyi su yanzu.


Ya ce to ke kinsan babu sabulun kika lodo wannan wankin kika to waja dasu,akwashe amayar dasu ayi wani lokacin.


Tsabar haushin danaji namanta da hajiya agun, na ce ,Aiko wallahi inzasu shekara ba wanki bazan siya ba ,kaga fa nama daina siyan sabulun wanki a gidannan, baka dubawa tsakanin sabulun wanka da na wanki na nawa nake siya,amma duk sanda zance kasiyo banidashi sai kaki aiba akaina take ba ,na cillar da tsintsiyar nashige na bashshi anan tsaye.


Dana rasa abinyi saboda takaici sai na hau gyaran wardrobe.


Kai Kai kai,ikon Allah baya karewa ,tare da abin mamaki, lallai rashin kunyar da namiji yawa gareta,kutsaya kuji wani abin mamaki ko ince rainin wayo.


Akwai kayan danafi shekara ma bandaga suba balle insa,yafuskanci hakanne kome oho shiyasa ni,Ina dagasu zangyara musu zama ,sai ga abin mamaki,kidine burjik yan dari biyu, dari biyar ,dubu dubu ,wallahi bansan adadin suba ,nidai nasan bana ajiyarsu ,balle ince nawane,tashi nayi na leka tsakar gida ,hangoshi nayi da hajiya suna magana,komawa nayi baya tare da mayar dasu inda nagansu nacigaba da aikina,sai kiyasi nake araina,to me mutumin yake nufi yarasa ma inda zayyi ajiyarsa sai a kayana,to bara dai zanbi ba,asi,haka nagama aikina har namike zanfuta wata zuciyar tacemin ga kudin sabulu nasamu ,nakoma nazaro dari biyar nafuta, ba,alamar bacin rai atare dani,saddiku dake gefe yana wasa nayi kira ,nace jeka ka siyomin sabulu da omo,ko kallonsa banyi ba nacigaba da sabgata.


Gefe daya kuma baba sai fada take mar amma ba fahimtar abinda take cewa nakeyiba.



Ba kunya yasa hannu mukayi wankin dashi kuma yadebo kayansa muka hadu muka wanke tass.


Haka na kyaleshi yana abinda yakeso, inya bani kudin in sun isa shikenan, inkuma basu isaba inbude ma,ajiyarsa in diba mucika aci abinci, Niko nawa kudin ai har sun fara zuwa inda nakeso suje domin duk runtsi yanzu duk wata nakansan abinda zan rage domin nima in ajiye,iya matsi na matse,amma fa Ina fuskantar abubuwa kala kala gurinsa.



Dana gaji daganin kudin ,nake tambayarsa kudin waye cikin kayana,

uhm uhm namiji sai yafara mita to meye a ciki Dan nayi ajiya akayanki shine me,to kudin rigima be nashiga tsakani ,wasune suke rigima akan kudin fili shine nashiga tsakani akebani kullum dari biyar Ina ajiyewa,


Dafarko har cikina yadan kada,sai kuma nafuskanci kamar zancan narashin gaskiya ne sai na maze na nuna Masa nayarda ,ammafa gaskiya nasan tabasu bansan banaka bane.


Wayyo Allah Ina wuta yasakani, ta inda yake shiga batanan yake futaba Kai naga tijara har Saida takaishi ga cewa intafi gidanmu.

Aiko bansan na iya Bala,i ba sai ayau,

Tsalle nayi na dire na ce wallahi sai dai Kai katafi gidanku, danni basaki bakuma yaji nariga na auru ehe, yo Kai kana tinanin wannan gidan nakane ,to kabude kunnanka da kyau duk Randa kayi kuskuren sakina wallahi ko soro bakada rabo anan daga sai hajiya sai yayana,inzaka gyara kagyara inkuma kaki abinci a gidannan sai ya gagareka ci , yo ma kasan abinda akecewa inda darinka ka daro inkuma Babu ka dara, to nice nan ,inzaka iya ciyar damu to inkuma bazaka iyaba kamar sauran magidanci ba to ni kaje nasake ka.


Zai kuma magana yaji maganar hajiya atsakar gida.



Sorry nku fans banida caji wannan ma dannace zaku jini ne kuyi manage.

*INA BUKATAR COMMENT DINKU INHAR KUNA SO INCI GABA NA ROKEKU*




🀝 *DAGA ALKALAMIN YAR MUTANAN JINGAUπŸ™‹*
[21/01 Γ  12:09] +234 703 197 3585: πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€



😳😳😳😳😳😳




πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™

*_PART 2_*


*LABARI DA RUBUTAWA*


*BY*

🀝 *FAUZIYYA AUWALU ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹.





*πŸ…Ώ45(S FOR* *SCHEDULE)*





🌈 *KAINUWA WRITERS✍🏾 ASSOCIATION* 🀝






Cikin rashin kuzari nakarasa shiryawa, sannan na tattara kan yayana muka fito, inacikin kulle kofa ne sai ga su khalil aguje, dama kince inzaki kuma zuwa unguwa Zaki damu, shikenan sai mu biki .


Shafa kan usaini nayi Wanda ya damare hannunsa a kirji Yana kallona, nace kuyi hakuri sai wani lokacin sai inje daku.

Hassan ne yace nidai zan biki ,uhm kuyi hakuri yanzu nasan ummanku baza ta bari kubini ba , nanny ce dauke da goyo a bayanta ta karaso ,ta ce nima Dan Allah anti zan biki nagaji da zaman gidan.


Uhm Kuna dai so kujazamin magana ne amma kunsan ba za,a bari kubini ba ,kubani hanya na wuce Kuna batan lokaci, amma kugayamin mezan taho muku dashi '.



"Alhaji sabo" ne ya taho gurinmu ,tin daga nesa nafuskanci dukkanin nutsuwarsa ya tare ta a kaina,har sai da nadauke kaina gefe,domin yara ma naga sun fara yima na kallon kallo.



Yace sai Ina kenan?


Ba tare da na bashi amsa ba naja yara domin mubar gurin,ya ce au tare zaku tafi, waigo wa nayi na kalli yaran da duk sun biyo bayana ,na ce cikin fada ku koma na ce Kar ku jaza min masifa yanzu yanzu ba ita na fito yiba.


Ya ce kitafi dasu mana ,afusace na kuma juyowa ,na ce e Mana kace in tafi dasu mana kodan ka tsokano min jarabar duniya ku hadu kuci mutuncin.


Wace ce jarabar duniyar,zakiyimin rashin kunyarne futsarau da har yau baki risina ba,kodan banyi maganinki ba,kukuma kushige mu je ciki kan incicci....uhm haka ki ka ce ko Tom shikenan,ya ran na kalla na ce Khalil kuzo muje zani daku muje kunji Yan albarka.


Tsalle suka kamayi gaba dayansu suna murna ,shikansa baban nasu tayasu yakeyi, dubu uku yadakko ya bamu da sunan mu shiga mota.

Aiko ta dire ta ce bazan tafar mata da ya ra ba ,Dan batasan Ina zan Kai mata su ba,shine ya kalle ni tare da lumshemin ido daya , ya ce. Wai ameera Ina zakuje ne nima ban San inda zaku jeba;


Na ce da ai baka taba tambaya ta Ina nake zuwa ba, bare yau kafi uwa ta sa ka tambaye ni ,Dan haka ki shige mutafi ,hannun nanny nakama muka fuce .


In kika tafi da nanny dinnan ta futa kenan Dan ba gidan uban ta bane,

Yo ko takanta ma nabi tini mun dau hanya,kowa yana cikin farin ciki domin wannan ita ce ranar farko dana fara zuwa unguwa dasu, nanny ce taja gudaya taki tafiya,ta ce anti komawa zanyi nasan Inna biki korata zatayi daga gidan ni kuma aikin shine taimakona kiyi hakuri kitafi.


Ke kyaleta ki shige mutafi inma ta koreki Niki dawo gurina, kicigaba da aikin ba inda Zaki kinji rabu da ita maganinta zanyi.


Sanda mukayi sallama muka shiga gidan su biyu ne a zaune ,sai hira suke cikin kwanciyar hankali Kai kace ba wata damuwa a tare da umma,ni gani ma nayi kamar kuruciyarta ta dada futowa ga wata kiba da tayi ta kwanciyar hankali.


Lale marhabun da mijin Daba cefane ,a,a kuce yau Baku kadai bane da Baki kike tafe ,to ku karaso,zubewa sukayi dukansu suna gaishesu, baba iya ce ta ce wasu mazan nasamu kenan,bance komai ba sai gaishesu nima danayi.



Bayan gama yin barkwancin da yaran da sukayi umma take tambayata yaran waye?



Bance komai ba sai sun kuyar da kaina da nayi , baba iya ce ta maimaita tambayar,ido nane ya kawo ruwa ,na ce yayan Yaya sabo ne.


Da azama ta dago kanta ta watsa idonta akansu, daya bayan daya take binsu da kallo,na ce Khalil tashi kaida su Hassan kukarasa gun umma ku Kara gaisheta ,sunan ta umma kakarku ce ita ce babar daddy dinku ,tashi kuje kuzauna kusa da ita,


Hannu ta miko musu dukkanin su suka wada jikinta, rungumesu tayi ido na me zubar da hawaye,shafa kansu takeyi batare da tayi magana ba, baba iya ma hawayen takeyi , sannan ta ce na gaya miki komai yayi farko zayyi karshe ,yanzu mun hau mataki na farko kenan , sannu kan hankali za a kai inda muke son zuwa.


Umma ce ta nuna nanny ta ce ita kuma wannan fa?


Ita dinma acikin gidan take, ita ce take kula da su khalil,tare da Taya sadiya hidimar gida,nace sakko dashi Shima wannan na sadiyar ne sunansa bashir.

Allah sarki sannu yarinya.

Na ce ita ce wadda ta taimake ni a shekarun baya, sanda sadiya ta karbo maganin da zata zubamin acikin abinci, ita ta dakko min sannan na bata maganin basir ta mayar a madadin wancan, Dan wani lokacin ma in taga ta zuba magani a abincin yaya takanyi dabarar da bazaici ba ,misali ko tafaki ido ta Kara gishiri a ciki ko maggi yadda bazai ciyu ba dai, a takaice dai tana taimakamin.


Baba iya ta ce ikon Allah , Allah yasaka Miki da mafificin alheri, yanzunma zuwan da akayi dake yayimin dai dai ,domin a kwai wani taimako dazakiyi mana acikin dakin alhaji sabon,nayi murna da zuwanki.


Na ce to Allah yasa ya yiwu domin da Kar zata sake Kar barta domin yanzun ma ba ta Dadi muka fito ba.


Shikenan dai koma meye dai Allah zai taimaka.


Haka muka wuni cikin farin ciki , musamman ma umma data wuni tare da jikokinta,nidai rabon dana ganta cikin walwala haka nama manta.


Sanda zamu tafi dakyar tasake su muka tafi, harda kukanta, haka ma Hassan yasa kuka sai na barshi gurin kaka, yo ba sai usaini ma yasa kukaba ,ta ce kibar min su Kya dawo ki dauke su,na ce umma kinsan ko da kwarban da na futo dasu ,yanzu haka nasan tana can tayimin tanadin da bansan karshensa ba,to shikenan ta share hawaye tare da shafar kan Khalil dake gefenta , ta ce me gidana na gode muku kunji Allah yayi muku albarka, kuce Ina gaida babanku kunji , Kai ya daga ya ce sunanki kaka ko, murmushi ta yi ,ta ce haka ne amma kuce ummansa tana gaisheshi ,kuma na yafe Masa duk abinda yayimin albarkacin zuwan da kukayi kuka ganni.


Haka muka tafi badon rai Yaso ba nikaina haka nadinga ji kamar kar mu tafi.



Sanda muka dawo bata gidan sai kofofinne a kulle dukkanin mu falo na muka yada zango.

Nanny ce ta ce inama da mukulli inje inyi abinda baba iya tasa ni kinga Koda ta dawo ma ta ce inbar Mata gida an dai yi aikin .

Na ce ,aiko amma bara na duba ko za,a samu acikin wadansu mukulla ye da yaya sabo ya taba barinsu a nan.


Bata nayi na ce Yi sauri kije ki gwada ko za,a dace,ni kuma zan dauke hankalin yaran Kar sufito ammafa kiyi da jiki ,Kar ta dawo ta tarar kin bude Mata daki,ki nutsu ki duba ko za,a dace.

Karba tayi tana gyada kanta tare da yin waje,ita kuma ameerar ta Kira wo yaran domin dauke hankalinsu ga futa ,bare suga me zai faru.


Yau tashi nayi bana jin dadin jikina ,ga wani kunci danakeji araina,aikine dani sosai, amma na kasa tashi na futa bare innemawa mutan gidan abinda zasu ci,nasan yau akwai tashin hankali ballanta na matar so tana laulayi, ankafa min dokar gama abinci da wuri domin Wai Bata iya Zama da yunwa, ga asiya ma ankusa tasowa daga school, kuma nasan muddin ta dawo Babu abinci sai na fuskanci bacin rai, gashi kuma ni kaina yanzun nayi yaushi sosai dukkanin wani hope dina ya gudu ,ni ba da ba jika agu amma dukkanin bacin rai ya hakke min.


Jina yi raina ya kuma baci da na tina irin bautar da nake musu amma banida kima a idonsu,tin Ina kokarin ramawa ma insunyi min har na dena,yanzu Banda uban rashin mutuncin da take Mata Bata gani sai nawa ,hadiza Bata ganin mutuncin ta ko kadan shikansa habibun ba mutun tashi takeyi ba bare ni Dan har gara ma ni tinda Muna can carewa da ita.


Kira nake jiyo wa Sama sama, Dakar nadaga kaina domin kokarin Mike wa.




Hadiza ce rike da labule ta rike kwankwaso baba kuma sai ruwan masifa take akanme zan shiga daki inkwanta ,sai kace nima cikin ne dani to kifuto ki nema Mana abinda zamu ci ,ke ba haihuwa ba sai iko na masu yaya .

Kai na dago nakai idona gareta ,na ce wallahi banajin Dadi ne bazan iya yin komai ba ,na kalli hadiza na ce kozaki tai maka ki dora bazan iya yin komai ba,


E ai dake ni din baiwar ki ce inzaki Dora ki bamu muci to in kuma bazaki dafa ba mujira me gidan shi sai ya dafa muci.

Aima dole ta futo meye amfaninta inbanda taci ta kwanta,ko kinga ta taba ko Bari ne agidannan, shekarar ta goma sha uku amma ko batan wata ,to inbata dafa munci ba mezatayi,ke ko yanzu yayanki nawa, nace yayanki nawa zuwanki gidannan .


Yo baba Kya hadani da juya nida tin awaje akai gwaji akasan lafiya ta....to burgewa kikayi ,ko burgewa ce gwajin da akayi ,ajiye shegiyar da kukayi ,kuka kafa mummunan tarihi ,da dai ace sai nayi shege kafin na haihu gara ace ban haihunba gaba daya,meza ayi da Dan kafin fatiha ,Dan Jan magana ,na nunata da yatsa ,na ce kibar baban tayimin ita kadai,itama takusa ta Bari,takusa denawa,domin duk Randa Allah ya yankemin zamana daku bazata sake ba,nakyaleta domin fur furar dake kanta, amma da ko kallon banza aka ce tayimin bazata yiba.


Mayafi na dake kan kofa najanyo nayi waje, inajinsu tana ta masifa ita kuma khadija sai zugata takeyi.


Ba gidanmu nayi ba domin konaje ma bazan Sami yadda nake so ba, shiyasa ma nadena zuwa duk abinda za,ayimin,wani layi nabi domin indan zaga kozan Sami yar sa ,ida anan naga an taso Yan makaranta ,rabe musu nayi domin wuce warsu, Ina tsaye Ina kallonsu har suka gama wucewa, kallo nake musu na Sha,awa domin zancan gaskiya Ina bukatar yara Dan bansamu bane,ido nane ya zubar da hawaye guri nasamu nadan Kade nazauna,tinanine yayimin nisa banma San sun bar gurinba sai Jin magana nayi a gefena,malaman makarantar ne sukusan takwas tsaye akaina,wata daga cikinsu ce take tambayata lafiya ,banida amsa sai dai wani kukan takura ne naji yatahomin domin dai nikaina nasan Ina neman dauki tare da abokanan shawara.


Ganin banyi magana bane daya daga cikinsu ta dafani ,ta ce karki damu Yar uwa munsan matsalarki bazata wuce *ABINDA KE FARUWA* acikin gidanku ba domin duk wata mace dazaki gani yanzu cikin kaso dari ta matsalar dake tare da ita tofa casa,in *ABINDA KE FARUWA* a cikin gidanta ne ,Dan haka Yi hakuri kitaso muje ko meye ma akwai Allah zakuma asami mafuta insha Allah.





*INA BUKATAR COMMENT DINKU INHAR KUNA SO INCI GABA NA ROKEKU*


🀝 *DAGA ALKALAMIN YAR MUTANAN JINGAUπŸ™‹*
[21/01 Γ  12:09] +234 703 197 3585: πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€



😳😳😳😳😳😳




πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™

*_PART 2_*


*LABARI DA RUBUTAWA*


*BY*

🀝 *FAUZIYYA AUWALU ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹.





*πŸ…Ώ44(R FOR* *ROBAR CRAB)*





🌈 *KAINUWA WRITERS✍🏾 ASSOCIATION* 🀝




"shu,aibu" meke faruwa ne nakejin hayaniya,?


Shiru ba amsa ,shi baice komai ba ,nima ban magana domin neman fashewa nakeyi,


To kuzo inasan gaminku, tajuya tayi tafiyarta.


Dafe Kai yayi ,nikuma najuya zanbita, kamoni yayi ya hadani da jikinsa ,funcikewa nayi naja baya,domin jinake kamar na hadiyeshi sabida bacin rai,na ce ko kamance meya faru ne, me kace yanzu ,ni ma me na ce ,ai kayi da Yar halak zaka kwashi sakamakon daka bani da hannunka, domin nibazan kwashe shiba sai dai ka kwashi kayanka.



Tsugune suke gaban umma tana tambayar su *ABINDA KE FARUWA* .



Ta ce kunyi min shiru Ina yimuku magana,Koda yake dakai zan fara wannan hayaniya da nakeji tame ce ce?


Dago Kai yayi yakai dubansa gareta,ya ce bakomai hajiya kawai dai Dan sabani muka samu amma komai ya wuce.


Murmushi manya tayi ta ce shu,aibu kenan ,ke karimatu Zaki iya gayamin *ABINDA KE* *FARUWA* ko kema kundedeta din bazaki gayanba,


Dan kallonta nayi naga ta bada hankalinta kaina,Baki na bude zanyi magana amma nakasa sai hawaye dasuka zubomin.


Shu,aibu kataka ahankali, domin Ina hankalce da komai da yake faruwa acikin gidannan, baka dai yin alkalanci sai ka tabbatar ,tofa randa nagama bincikena zakasha mamakin irin hukuncin dazanyi maka.



Yarinyar Nan yar halak ce ,ko bataci arzikin daraja mahaifiyarka datake ba taci na mutun taka datake ballanta akwai darajar datake da ita nikaina a idona balle Kai tofa ka kiyayeni banson tijara ,inta tafi gidan ubanka zata ,da kake cewa ta tafi gidansu, ai inhar mace ta futa daga gidansu Koda nayi gudane da sunan aure ta wuce zaman gaban iyayanta ballantana ita me shekara kusan Sha tara agidan aure,to ahir dinka ,duk randa tsautsayi ya kaika da rabuwa da ita wallahi ban yafe maka ba inkuma kayin tofa sai dai kabar gidan kaima katafi gidan ubanka ,domin nan gidan yayan tane Dan haka ka kula, tashi kabani guri mutumin banza butulu ,ai haka kuke sai kuncinye kuruciyar mutum sai wulakanci ya biyo baya,da kayi Maya mana sanda kake yawo wujiga wujiga sai yanzu daka fara samun na hawa adai daita sahu to Ina ga kasamu abin duniya.



Ke kuma kiyi hakuri duk abinda yayi Miki kizo kiga yamin ,ya kusa barin gidanma mu huta gaba daya ,Ina sane da kai tinda nazo gidannan kake Bata mata rai ,kizama name baka sone,sai intattara inbar maka gidan.


Ai ya gigice da zancanta ,haba hajiya yaza,ayi ince banason zamanki ,kiyi hakuri zan kiyaye insha Allah kiyi hakuri,sabani dama muka samu amma komai ya wuce kiyi hakuri hajiya.


Bayan komawarmu daki ne ya ke ta kame kame ,Niko ko takansa banbiba ,dagaske yafuta akaina domin rashin adalcinsa nema take yayimin yawa, juyowa nayi nakalleshi na ce ,tinatarwa a irin bashin danake binka kabani abinda yasamu domin nima Ina bukatar kudina.



Hana karimata ba hajiya takashe maganarba ,ko sokike mitayin hayaniya Ina Bata Miki rai ,bakisan innaganki kina fushiba banajin dadiba kiyi hakuri kome ake ciki zan tintibeki daga baya.


Ai ni bani da matsala ammafa kasani wallahi sai ka biyani irin kudina Dana dinga ranta maka wadanda nasami Wanda ko bansani ba dama dama basaninsu nayiba.


Shikenan zan biyaki, shikenan ko.


Yo ko kallonsa ma nayi bare inbashi amsa.



In bazaka sake taba, ni zan tattara inbar gidan sai kazauna da ita.


Ameera kije na sa....karka sakeni katuna

15 / 31