ABINDA KE FARUWA HAUSA NOVELS BY YAR JINGAU

Author :  Yar Jingau Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   24 / 31

69K to 72K   out of 92.1K words

sukeyi.


"Alhaji sabo" ne ya amsa ma sa da cewa Ina ko lafiya matso ciki kagani baba,kalli abinda zasu sake yimin a cikin gida ,Dan haka daga yau karka kara barin wani bako ya shigo cikin gidannan da sunan gurin sadiya yazo, ita kanta karka kara barinta ta futa sai dai inni na bada umarni, nuna aminiya yayi wacce fuskarta ta Yi luhu luhu ya ce ke kuma tashi kibarmin gida, Kar in Kara ganinki ko a kofar gidannan ne bare a cikinsa,da sauri ta mike ta na laluben mayafinta ,ya ce zo Nan kikwashe tarka cenki ki tafi dasu, tsugunawa ta Yi tana tattaresu ,baba me gadi ya ce, badan kar in maka karambani ba da sai ince karta tafi dasu, ta warwaresu da hannunta sannan ta sa ashana ta ko nesu In Yaso sai ta tafi da tokar.


Ya ce ai kagama magana ,warware su da hannunki,jikinta ne ya fara rawa ta na me cewa Dan Allah"alhaji" ka yi hakuri kuskure ne na riga na yi ,ku Yi min hakuri na tuba na bi Allah.



Ko ta kanta Bai bi ba ya barta da baba me gadi wanda ya kasa ya tsare sai ta warware dukkanin tarkacen da tazo dasu.

Ta daya bangaren sadiya ya mikawa hannu ya ce bani wayoyinki Dan bada ga gidan ubanki kika zo dasu ba ,kuma ki bani a,t,m dinki da dukkanin abinda kika San kin cuceni Wanda ya ke gunki ,in ba haka ba wallahi da hukuma Zan hadaki barganin na saurara miki, hannu ta dora akanta ta rushe da ihu Dan tasan inhar yaraba ta da wadannan abubuwan tofa ta ga banu,.


Har ya juya zai futa wani Abu ya wado masa arai, da saurinsa ya dawo ya ce Ina takardun da kika sakani na siyawa iyayanki gida ,mucuciya muje ki dakkomin Allah ya isa tsakani na dake.


Karar da aminiya ta saki ne yaja hankalinsu zuwa gefen da suke ita da me gadi, wani irin feshi maganin hannunta ya Yi mata a fuska da hanna yanta, garin kwance bakin kwalbar maganin ne ya subuce ya tallatso waje, Aiko sai a jikinta, Nan danan ta hau sosa gurin ga wani uban radadi da ya ziyar ceta, umma ko da ameera Baki sake suke kallo,ita ko sadiya inda kukasan ance lahirar ta ta tsaya saboda furgici.


Mika ta ke ta na karawa, gun da zainab din ta ke ta dosa ta ce me zangani ,indomie da tsakar rana wallahi sai dai kici ke kadai ,ko muci ki tashi ki dora mana abinda zai rike mana ciki , amma wannan ma ai salon mugunta ne,arasa abinda za,a dafa mana Dan cuta sai abincin yara,magan ganunta ne suka tada baba daga bacci, tafito tana murza ido,ta ce meke faruwa ne nakejin hayaniya;

Yo ai abinda yafi Haka ma zakiji ,Wai indomie da tsakar ranar nan ko me zanyi da wata indomie da wannan tsohon cikin.

Ai bake ba ni ta ke nema da magana, tin jiya yarinyar nan ta ke wahalar Dani da yunwa, shine yau ta dafa mana tsutsar yara ,to ko sai dai muci ki dafa mana wani abin.


Ita ko zainab duk wannan surutun da sukeyi batabi ta kansu ba,har ta gama zurkuma lomar tsutsar yaranta, sannan ta nannade tabarmar ta ta shige daki.

Ganin ba ta sauraresu ba ,sai baba ta shige kitchen din domin dakko tsutsar yaran dasuke fadan an dafa musu ,aiko babu alamar anyi girki, dan tin dattin safe da ta gama abun kari ne a gurin ,ba,a kawar dashi ba bare a dafa musu wani abun.




*INA BUKATAR COMMENT DINKU INHAR KUNA SO INCI GABA*



🀝 *DAGA ALKALAMIN YAR MUTANAN JINGAUπŸ™‹*
[21/01 Γ  12:10] +234 703 197 3585: *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€__



😳😳😳😳😳😳



πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™


*_PART 2_*

*LABARI DA RUBUTAWA*


*BY*



🀝 *FAUZIYYA AUWALU ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹





*πŸ…Ώ63(K FOR KIDS)*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*



turus ta yi Dan ba ta da bakin magana ,kawar da kayan gun ta fara yi kafin ta hada bakunan itatuwa,

Shirun da khadija taji ne yasa ta daga kafarta da kar ,ta karasa dakin girkin,Baki bude ta ke kallon abinda baban ke kokarin yi, wani tsohon Bala,inta ne yamotsa ,


ta ce kanbuuuu na rantse an kusayin yakin da ba Mai iya kasheshi a gidan ,

keeee zainab ta kwala mata kira cikin haushi,ta ce ai bansan kedin bakida mutunci ba sai yau ,ko baki dafawa mutan gidanba ai ni kya dafa ki dibarmin ko Dan cikin da na ke dauke dashi, na rantse munsa kafar wando daya da ke, banza Mara mammora ta ko ina, baga mu mutan gida ba, bare miji da bayayi da mutum ,mtsss mara zuciya Babu abinda ta iya sai ci,sai jiran ayo sallama a ce abani manja ko man kuli.


Baba ce ta ce ke dai barta tukun ingama dafa mana mu ci mukoshi ,yanzu in kika kulata sai tazo ta na wahalar damu ga yunwa ga babatu.



Zainab ko redio ta dakko ta ware ta ,dan karma su dame ta Dan so ta ke ta dansa hakar karinta ta huta.


Ramla ce ta fito daga bayi ,dakar ta ke daga kafarta,yau din jinta ta ke jikinta ba dadi ,kwana ta yi kanta na ciwo ga wata gajiya ta ba gaira ba dalili da ta saukar mata.


Amina ce ta kawo Kai hannunta dauke da tukunya za ta ajiye gurin wanke wanke,ta ce anti lafiya na ga ki na daga kafa Dakar?

Dan karamin tsaki ta saki,ta ce kedai bari banajin dadi sosai wallahi,

Turus ta yi tare da nuna alhininta ,ta ce sannu anti to ki koma ki kwanta ko Zaki Sami bacci in Allah yasa sai ki farka jikin da sauki.


Dama kwanciyar zanyi , amma zanso in Dan watsa ruwan dumi ko zanfi Jin dadi,ga shi ina son futa taron kungiya in anjima,amma dai to ko Zan iya zuwa gashinan dai;


Ai Ina ga Babu ruwan zafi kuwa dazu na juye na Yi wa yara wanka dashi,sai dai in dora miki wani sannu anti Allah ya baki lafiya, yawwa amina temaka min ki Dan tafasa ko zansa mi Dan karfin jikin,

Tom anti.



Har ta juya zata shiga kitchen din cikin sauri ,sai Kuma ta juyo ta ce niko anti na ce sai kuma ta Yi shiru , kallonta ta Yi ta ce kinada magana ne;

dama cewa zanyi Dan Allah kije dani gurin taron dazaki ,sabida inason in kuma ganin wannan kawar taki wallahi ta burgeni sosai,


Murmushi ramlar ta yi ta ce bake kadai ta burge ba , rayuwar karimatu abar kwaikwayo ce hundred percent ,ta ko ina zakiso ki kwaikwaye ta cikin dukkanin Al,amuranta, musamman Kuma in kika mu,amalan ceta,zanso kije din ,ballan tana in kika ji labarin rayuwarta, Zaki kadu kiji lallai Mata suna suka tara, kiji yadda ake rayuwar aure da miji ,kiji yadda ake kwatar yanci da hikima ba tare da hargagiba,ki doramin ruwan inyi wanka ,innaji dadin jikina Zan Baki labarinta ko Zaki karu, ammafa wanda nasani sauran kuma sai mubarshi har zuwa sanda zata bamu tarihin ragowar rayuwarta, maybe yau din in akwai enough time tabamu labarin nikaina so nake naji karashen *ABINDA KE* *FARUWA*.


aiko zanso na ji wallahi kodan natsinci wani abun da zai kuma taimakamin cikin Al,amurana, amma to anti har yanzu bakice zakije daniba hhh.


To shikenan ki shirya sai muje, ammafa kinsan Baki tambayi mijinki ba ko;nasani anti ai bazaice komiba tinda tare muka fita.


Kar ki Yi consider dani ,nidin nariga na auru, Kuma duwawuce Dole a zauna da ni,Dan haka Zan dayyi kokarin kiransa a waya in shaida masa,ni sai infuta ban tambaya ba in zauna lafiya,kedin ki futa ta kwabe miki.


Jiki a mace tabar gurin ta shiga kitchen domin ba ta gane wannan zaurancen antin nataba,ita ko ramla butar hannunta ta ajiye tashige daki.


Cikin mintinan da basu gaza a Shirin ba har ta hada mata ruwan wankan,lekowa ta yi ta na gaya mata ta fito gashi,sanda ramlan ta fito ne ta ke tambayarta yau me gidan me yabar mana;(dama girkin aminan ne yau) yaken dole ta Yi ta ce yadai ce zai dawo kan azahar sai ya kawo,kebe baki ta yi ta ce sabida mukuma dashi muka dogara ai sai mujira shi ,kinga shiga dakin can ki dakko cuscus ki tafasa Mana shi ko zamu futa da sauri,in yaso in ya kawo sai ki karba ki boye ma hadu gaba.


Allah sarki dama yunwar ce ta ke sasukarta, Dan ruwan bunu Tasha ita da yaranta sai dankalin hausan da ramla ta Bata da safe ,wanda yaji suya da kwai ,cikin sauri kafin ma ramlan ta gama shiryawa har ta kammala dafawa,har tayi jajjagen kayan miyar data futo mata dashi,kafin kace meye abinci ya kammala.


Itama ruwan ta dafa tayi wanka, bayan taci ta koshi har ta dibarwa diyoyinta , ta na cikin shirya wane me gidan ya shigo,da ramla ya farayin Karo a tsakar gida ta Yi kwalliya gwanin Sha,awa kai ka ce amarya ce ,Dan kayan data saka sun amsheta sosai, sannu da zuwa ta Yi masa ta ce ango kasha kamshi daga ina da tsakar ranar nan; (dama da sunan ta ke kiransa tinda ya Yi aure) a,a ke Zan tambaya ina zuwa; ta Dan yi dariya ta ce gani Nan dai Sona ke indan Kara Jin karfin jikina kafin in fuce zanje wani taro ne,ya ce to Allah ya kiyaye, bara nadan karasa in huta na kwaso gajiya ga yunwa da na kwaso.


Ta na tsaye gaban wardrobe dinta tama rasa kayan da zata saka, domin duk kayan nata sunyi sanyi,babu wanda zata daga ta ce shine futacce wanda zataje taro dashi, da sallama dauke a bakinsa ya shiga ,waigowa ta Yi tare da amsawa,ta ce barka da dawowa,Bai amsaba sai bin jikinta da kallo da yayi ,gajiyar daya kwaso ajikinsa yaji kamar an sauke ta shi har kullum jikinta na burgeshi baya saurara mata inhar ya na cikin dakinta, hannu yakai yajanyo ta jikinsa ,turo baki ta yi alamar bata so , amma da ke ita ce a karkashinsa duk kin da tanuna masa sai gashi ya rinjayeta an wada ruwa.

Bakin ciki ne ya turnike ramla,domin yanajin kokarin ta na kwace daga gareshi,sai Kuma can ta ji sunyi shiru alamar sun dai daita kenan,ta ce lallai yarinyar nan sai ta gyara mata zama sosai kuwa,mijin ya fuce yabarta ba abinci amma Dan iskanci bayan kin koshi yadawo ya sake kwashe albarkatun da nabaki kika zuba acikinki.


Daki ta shigewar ta duk haushi ya isheta, jitake kamar taje ta makure su,

Ko tsayawa jiranta ma batayi ba ta dauki mayafinta zata fuce,

yayi daidai da futowar Amina daga cikin daki, turus ta yi tare da sunkuyar dakai kasa tayi sanda sukayi kicibus ,jitayi duk kunya ta rufe ta ,jitake kamar ta aika ta wani laifi ,a hankali cikin Jin kunya ta ce,Dan Allah anti ki yi hakuri kitsaya ni Dan Allah,


Jitayi yarinyar tabata tausayi, lallai dole sai an Sami wanda zai sata a hanya,in ba haka ba kuwa burin kungiyarsu bazai cika ba ,in dai zasu ga irin wannan su zuba ido,dole ta kara a jiye kishi a gefe ta yi domin Allah.

Cewa ta yi shikenan na baki minti goma,in kika wuce haka zakiji na Yi gaba.

Bayan aminan tashiga wanka ne,

ta kira me gidan, Dan yau da sunansa ma ta kirashi tabbacin serious dinta ta ke.

Lekowa yayi daga shi sai gajeren wando,ya na murmushi tare da cewa inkaji Kiran uwargida tasamu,kebe baki ta yi ta ce e lallai kam tasamu,dama matar ka zaka bani aro ta yi min rakiya,


Galala ya bita da kallo domin ta bata masa budget dinsa,so yayi inda zata futa dinnan yabarje guminsa har sai ya bawa uku lada ,gashi yara sun tafi makaranta amma zatayi mas...cin kunu ta kumayi ta ce ko in tafi bazaka barta ba dama nasan ai ita amarya har kullum bukatar me gida ce ,banda wadda aka dakkowa domin debe kewa,Dan haka kaga tafiya ta, ka rike abarka ango mijin amarya.


Ganin ta Yi fushi da gaske,sai ya sha gabanta ya ce ba haka na ke nufi ba ,nufina Wai kar yara su dawo ba kowa shine na cek...nifa ban ce komi ba tinda bazata raka ni ba ai shikenan.


Tom shikenan kuje sai kun dawo amma dan Allah karkuyi dadewar da kikeyi a waje kinga yau bake kadai bace.

Murmushin takaici ta yi sannan ta ce na sani ai bazan dade ba tinda na tafi da matar so matar kishi,niko ai nasan duk inda na ke Allah na tsare ni kuma yana tare da ni.


Gum ya yi domin yasan in ya tabo ta bata da kyau ,gashi dama sun Kwan biyu basu haura ba musamman ma da ta dena tsayawa jiran sai ya bata.



Suna tafe a hanya ta ke cewa, ammafa amina in halinki haka ya ke bazamu shirya ba.


Kallon ta ta yi ta wutsiyar ido ,ta ce ki Yi hakuri anti Zan gyara insha Allah.


Ba komi na ke nufi ba,in baki ba ni hadin kai ba ,bazan Sami damar gyara mujinmu ba , hakan da kike shi yake kuma bata komi,ki saura reni, sannan Kuma ki fahimci abinda na ke nufi.


Yadda Bai baki kinci kin koshi ba,Bai kamata daga zuwansa, ba wani Jan aji ba komi sai ki wage masa kafa ya shige,tofa dole kin bashi lasisin da gobe zai hanaku ko ya hanamu abinci,Dan yasan bashi da matsala.


Dan haka in Zaki gyara,ki gyara,in kuma kinki Allah Zan rabu da ke mu koma yar gidan jiya.


Ta ce to ai ni bansan yadda zanyi masa ba ko naki yarda dole ya ke min ta karfi.

Ta ce to ki saurare ni kiji da kyau, ki cire ni a zuciyarki matsayin kishiya,ki dauka yayarki ce ta ke ba ki shawara,daga yanzu duk randa Bai baki abinci ba karki kuma yarda dashi,

kisami gajeran wando guda biyu kisaka a ciki sannan kisami dogon wando ki dora a kai karki kwanta a haka dauki zani ki dora a kai ki nemi guri ki kwanta ,koda yaci gala akanki ,aikinga sai da ya wahala, amma kiyi kokarin kwatar yancinki, in ya matsa miki,kice masa inda darinsa,ya daro,in Babu kuma ya dara , Ina nufin in ya baki abinci ki yarda, inkuma Bai baki ba ya Kama gabansa,ki tabbatar duk ran girkinki kinyi wannan Shirin, nima ta bangarena Zan yi kokarin dai dai ta komi, maybe yadan gyara ko kadanne, amma bari muje gurin taron sai muji ta bakinsu,Wala, Allah asami sauyin shawara.




*INA BUKATAR COMMENT DINKU INHAR KUNA SO INCI GABA*



🀝 *DAGA ALKALAMIN YAR MUTANAN JINGAU* πŸ™‹
[21/01 Γ  12:10] +234 703 197 3585: πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€




😳😳😳😳😳😳



πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™


*PART 2*

*LABARI DA RUBUTAWA*

*BY*



🀝 *FAUZIYYA AUWALU ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹.


*πŸ…Ώ64* *(L FOR LOVE)*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*___________________________________



cikin sanyin jiki da tsarin da ramla tazo mata dashi ,ta ce Tom anti Zan kiyaye insha Allah.



Yana zaune sai aika kosai bakinsa ya ke ,har wani lumshe ido ya ke yi sabida dadin da ya Yi masa.girgiza kanta ta yi ta na ayyana lamarin da namiji acikin zucitarta, lamarinsu dole duk tsaurinka gurin kwatar yancin da ka ke tinanin nema garesu, dole wani time din kadan saki kodan tina ranar da su ke da ita a gareka,abin zai bada mamaki, inda za,aji yadda a kayi dashi kafin a fara suyar kosan,nana ce ta ce da momin nata,momi ba bu fa man suyar kosai;dafe Kai ta yi tinawa da cewar daman yakusa karewa,jakarta ta dakko ,domin bayarwa asiyo,sake tinani tayi sai ta dakko dari uku gefenta ta ce da shu,aibu Wanda ya yi kunnan uwar shegu da su ,ta ce in za,a samu cika mata dari da hamsin ta bayar Yara su siyo Mai kosai zata soya.


Cikin kebe fuska ya ce kawai ta Yi da wanda tasamu ,cikonnan dakar zai samu .cikon daza,a siyo kwalbar man da za,a karya ne bazai samu ba ;na tambaya. to ai kudinne Babu a aljihuna ban shigo da kudiba shiyasa.


Ok shikenan bayar asiyo gwangwani ukun kinji, in yaso arage min ragowar kullin ayi alala dashi.haka mukayi dashi ,kuma har ta tafi bashi da alamar bayarwar.


To kuma abin dariya yafi kowa cin kosan, har zuba masa ake ya tafi dashi kasuwa, saboda son da ya ke masa, murmushi ta yi domin ta kulla masa tsiyar da za ta shuka masa.


Bayan yagama shiryawa ,zai futa kasuwa ne, sai yaran suka shigo domin sanar masa da sakon hukumar makaranta .

Bai ce komi ba sai dauke kansa da ya Yi gefe daya,momin tasu ce ta ce kutashi kuje zai bayar, sai Allah ya kaimu litinin.

juyowa ya yi ya kalleta bayan sun bar gurin,Wai banayi Miki bayani ba me kikeso Kuma ince miki?



Juyowa ta yi ta sake kallonsa, tare da kada idanta, sannan ta Yi murmushi ta ce haji shu,aibu kenan,

shu,aibu nawa, kaidai Allah ya kaimu litinin din, aje a Dan lalubo, ko Rance ne ayi ,a warware daga baya,to ke a ina Zan ranto, kowa yana fama da kansa, waye zai baka rance a wannan lokacin; dariyar kasa kasa ta yi ta ce a inda ake aro na baya har a biyasu bamu Sani ba,sai a daure a koma nasan zasu kuma bayarwa tinda ana biyansu.


Tsaki ya yi ,ya ce kinga ni karbi wannan,tafiya zanyi Dan zubomin kosan in tafi dashi,hhh ai kosai ya kare sai kullu ,sabida man bai wada ceshiba ,sai dai in zaka jira adafa alala sai katafi dashi.


To ai da ansan an Dan ragen wanda Zan tafi dashi, tinda ansan Ina sonsa,la ai da ragowar kullin, manne dai bazai kaiba,sai dai ko zaka bayar sai asiyo sai a soya maka ragowar.

Shiru ya Yi mata tare da shurar ta kalmansa ya yi waje,ita kuma ta bishi da murmushi,ta ce ai kuma daga yau sai dai kaci na gida,
kadena tafiya dashi gara inba makota marasa shi tinda Kai baza,a Kari da kaiba.


Da misalin karfe daya da rabi,bayan ta sallami diyoyin nata zuwa tahfiz ,Dan dab manyan suke dasuyi sauka,

ko waccensu daya bayan daya ta bayyana,

a gidan karimatu suke

24 / 31