ABINDA KE FARUWA HAUSA NOVELS BY YAR JINGAU

Author :  Yar Jingau Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   27 / 31

78K to 81K   out of 92.1K words

se mana nima Ina siya kullum ta Allah Dan baya wadatarmu.


Ke kika sani bata shafeni ba,duk boring kunya kikeyi,Dan haka kije duk inda kika kaimun kudi ki nemosu,in ba Haka ba kishige ki tafi gidanku duk sanda kika Samo kudin kya dawo.


Shu aibu Ina gidannan kake neman yin Dan yen hukunci,to ahir dinka duk Randa kayi kuskuren furta muguwar kalmar da ka kaiwa farmaki to bada yawu na ba,ban maka Baki ba amma na tabbata lalacewarka ce ta zo ,yaki nan diyata futo futo kin wuce wannan in dai ina gidannan shige muje.


A tsaye nake kikam ko motsi na kasa,tsabar bacin rai ,ajiyar zuciya kawai nake saki ,har sai da tashigo dakin tana okarin rike hannuna sannan tafuskanci halin danake ciki, yarana kuwa duk sun shigo ko wanne kallona yake ,nana ce ma take share hawaye ganin Ina tsaye kamar andasa ni ne yasa ta riko ni, yuuuuuu na tafi na kifa kuma shiru ban kuma wani motsin da zai tabbatar da ina da rai ba.


Salati suka saka gaba daya su kuma yaran duk sai kuka sukeyi,nana kuwa itama kamewar ta yi atsaye, shiko shu,aibu rungume ni ya Yi yana jijjigawa,tare da ambaton suna na,hajiya ce ta ce cikata,ai burin duk wani namijin da mace take masa halarci kenan, haka kuke sai kunyi takwabe muku, sannan nadamarku take futowa bani guri butulu.


Haka suka sakani gaba suna tayimin addu,o i su a zatonsu aljanu ne suka Dan shafeni,lura da nana da ita ma ta ke tsaye da sukayi ne ,sai baba ta kamata ta kwantar, sannan ta debo ruwa taringa shafamin a fuska, cikin amincin Allah sai na saki ajiyar zuciya.

Dakar na iya tashi zaune ,domin dukkan raunin zuciya ya bayyana ga gangar jikina, hazo hazo nake kallon kowa,can gefe Naga nana akwance a hankali naja jikina zuwa gareta, kanta na dora ajikina Ina shafawa ,komotsi batayi ba.


Hawaye ne masu zafi sosai suke zubomin, na ce nana ki tashi,kitashi Dan Allah kiyiwa zuciyarki hakuri karki dorawa kanki damuwar Daba taki ba,Koda yake damuwata damuwar yaya nace, amma da akwai lokaci kitashi Dan Allah,wata ran sai labari,daga yau din nayarda nice komanku ,Zan share muku hawayenku ki tashi domin kubani goyon baya nana nana.


Ikon Allah yau naga duniya ,wannan ita ce ranar da ban taba gani a gidan ba,bansan tana da aljanu ba sai a ranar ,buge buge ta hauyi tare da datse harshenta,can kuma sai maganganu wadanda bama gane me take cewa, tsam narike ta a jikina sannan nahau tofa mata addu a cikin ikon Allah sai ta hau nuna babanta da hannu sannan kuma tafashe da kuka ,addu ar natsananta karantawa agareta ,can kuma sai tayi shiru tare da sakin ajiyar zuciya (addu a ce inhar aka tofawa me bugawar aljan zai sami sauki insha Allah,in kuma gurine yaki zaunuwa saboda su tofa in anayinta a gurin insha Allah zasu bar gun).

Tin daga sannan sai na dauke masa wuta a hankali nake tattara kayana domin barin gidan,duk wani shirgin dazaimin amfani na hadesu gu daya ,cire komi nayi a raina domin nafuskanci bakomi ne ya ke Kara jefa mace cikin taskun namijiba illa yayanmu da muke dubawa,har muka sarayar da farin cikinsu dominsu,mukan kira zaman da mukeyi da zaman yaya,haka na tattara komi na watsar na barwa Allah,nasan bazasu ta gayyara ba ,balle ga hajiya a gidan nasan zata kula dasu.


Ta bangarensa kuwa ko alamar nadama,Daman shi mutum ne mara daukar Abu da muhimmanci,ko Abu yayi min dama Bai fiya nuna damuwarsa ba akai,balle yanzu da yake ikirarin nayi masa sata.

Haka ta bangaren aikina lallabawa kawai nakeyi domin su kansu abokanan aikinnawa tambaya ta suke meke damuna; sai dai inyi murmushi ince bakomi,yau juma,a tinda nadawo yara suke tambaya ta wakenmu yakare gashi gobe kosai zamuyi da kunu,na ce kuyi hakuri kusha abinda babanku zai kawo ,abin sabo sai naga Basu ji Dadi ba,kudin nadakko nabasu nace su auno gwangwani uku suyi dashi in Bai Isa ba sai su kara da ko ruwan bunu ne, na ce musu kunga ni yanzu tafiya gidanmu zanyi in kun tashi yin kosan kuyiwa hajiya magana zata soya muku ,karkuce zakuyi da kanku,(lokacin basuyi Girman Haka ba).


Duk sai suka bini da kallo ,nana ce da ta fisu shekaru ta ce fisu gane menake nufi,ta ce umma Dan Allah karki barmu mu kadai ki tafi damu .

Na ce Zan ringa biyowa ta makarantar ku inna taso daga makaranta ,kinga babanku ne ya ce inbar muku gida, kinga dole in tafi tinda ba gidanmu bane.


Titi na turasu suka samomin me adai daita, lokacin magriba ta kawo jiki ,sanda nake futo da kayana a hankali nakeyin komi gudun Kar hajiya taji motsina, amma dake kafin ayi kiran sallah takeyin alwala sai ta fara lazimi kafin atayar da sallar,Aiko sai naci karo da ita ta fito daga bayi hannunta dauke da buta ni kuma hannuna rike da katuwar jaka.



Kallona tayi ni kuma na sunkuyar da kai kasa,ta ce Yar nan yanzu duk hakurin Dana baki bakijiba sai kin tafi,ko wani fadan kuka Kuma yi,yau ni naga ikon Allah,dama zaman da kuke yi kenan ,ko sai da nazo gidan zaman naku yakoma haka,to ki koma Babu inda zakije,nice Zan tattara kayana nabar muku gidan tinda da alamu Ina nema in zama tsohuwar banza.

*INA BUKATAR COMMENT* *DINKU INHAR KUNA SO INCI* *GABA*


🀝 *DAGA ALKALAMIN YAR MUTANAN* *JINGAU* πŸ™‹
[21/01 Γ  12:10] +234 703 197 3585: *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€__



😳😳😳😳😳😳



πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™


*_PART 2_*

*LABARI DA RUBUTAWA*


*BY*



🀝 *FAUZIYYA AUWALU ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹





*πŸ…Ώ69(Q FOR QUESTIONS)*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


sunkuyar dakai na nayi kasa,domin banso taganni ba,inajin kunyar tsohuwar domin kan asami suruka me halayyar hajiya za,a dade ana dubawa,duba da yadda yanzu surukan suka zama sai addu,a.


Ta ce na dauka na Isa dake shiyasa na zaunar dake na Baki hakuri,har na Kara miki da yadda Zaki cigaba da zama dashi,inhar kika tafi kika bar ladanki a gidannan tofa za,ayi bake,inkara miki wani karatun in kinbi shawarata karshe ki dauki riba sai dai shi hakuri wuya ne dashi.

Kin gama gina rayuwarki tare da sabo da diyoyinki ,kin gama karar da karfinki akansa,ba irin wannan mijin ake tafiya abarwa yaya ba,akwai dai wanda in kika bar masa karshe kiga hakan yafi alheri.

Amma inhar kika barwa me irin halinsa yaranki,tofa kece aciki, saboda Bai riga yasaba da wahalar su ba,inda nake karantarku tsakaninki dashi kaso goma na wahalar gidan kece da bakwai shi kuma da uku,da ace shine da bakwan ke da uku Zaki iya tafiyarki kibar masa kodan kitsira da mutuncinki.

Akwai kuma wanda ko shine da ukun in kika tafi kika barmasa,ganin babu idonki sai yadauki dawainiyar dama muguntace,yadanganta da yadda kika karanci mijinki, amma nidai asani na da shu,aibu tinda nina yi goyonsa,halinsa Babu wanda bansani ba nasan tabbas kika tafi Baki sake masa haliba tofa a haka zai rayu da yaranki ba sauyi Dan haka kiyi hakuri kije kibi dashi ta inda nace miki,ni kuma Zan dauke idona daga kanku ,Zan toshe kunne na domin ki karbowa kanki yancinki.


Jakar hannu na na ajiye a kasa ,na ce nagode hajiya zuciya ta ce ta kasa jurar furucinsa gareni, amma zanyi hakuri ,Zan daure insha Allah komi ya wuce nagode Allah yakara girma.


Yawwa ko kefa Allah yayi miki jagora, Allah ya kara miki hakuri, Allah kuma ya doraki akansa.


Salon nasake, karatun hajiya nadauka,tini nafara aiwatar da sabgata.


Na share komi ,nadauke komi daga cikin zuciya ta , jina na ke bani da matsalar komi ,na Kara rungume Yaya na ,basu da Rashi zasu saka me kyau,susha me kyau ,domin gwal dina naje na siyar Wanda nasiye shi wani dashi danayi sanda na siyeshi dubu dari da talatin nasiya ,yanzu kuwa sai da suka karamin dubu sha takwas akai, tini naje na biya kudin term dinsu ,na siyo kayan abinci na ajiye,na biya duk bashin da ake bina ,,sai da nasami rarar kudi masu Dan dama,aiko sai na bazama kasuwa duk wani kaya da nasan za,a siya haka nadinga sararsa ,kuma kudin sunyimin albarka, domin ko atamfa sai da nasaro guda goma masu tsada, sannan na hado da leda atamfa itama guda biyar,sai na shiga kasuwar wambai na sari takalma Yan dari uku da hamsin na dubu biyar, sannan na sari fashion suma,Aiko sai gani natara kaya sosai, dazan tafi makaranta haka na lodasu a adaidaita sahu natafi dasu,cikin ikon Allah sai gashi an kwashe fiye da rabin kayan takalma kuwa ko daya ba,a rage ba saboda kowa yadauka domin zuwa makaranta dasu,duk Wadda tagani takance bani insiyi na zuwa aiki,naji dadin siyo kayan,har wani nishadi nakeyi domin jinake kamar inyi kukan dadi saboda murna.shiko Babu shi a Yan kayana,domin yanzu kusan bashi da kwano a gidan ,domin nadena takura kaina iya abinda nakiyasta cikin kudin daya bani dasu nake amfani, ammafa bawai muna zama da yunwa bane,a,a shidinne dai tsarin yabiyo takansa a haka,Ina girkina dahuwa ko me kyau dan nakan kawata abinci na muci sosai mukoshi, ammafa bana Bari yadawo yatarar inma ya tarar bamu ciba sai na zubawa kowa a wadace in yayi saura in zuba masa,in kuma bayyi ba na ce masa ,baikai ba abincin ya kare,ko kallona baya yi sai dai yayi wani Dan karamin tsaki ya ce ku kuke Jin yunwa gara da kuka cinye ,shi kuma wancan nadakinfa ko bana cibane;ki dafa min ko taliya ce inci.

Sai dai in girgiza kaina ince ai a lissafe kayan abincin suke domin iya wanda na diba iya kudin nake sakawa domin bashi na karbo ban biya ba su nake tarawa in lokaci yayi inbiya,inna wuce geji kuma kudin bazasu kaiba,Dan haka kasiyo sai in dafa maka,

tooo kuzo kuga fushin maza ,ai duk sanda mukayi haka dashi ,daga lokacin sai ya Yi kwana uku Bai kula niba,nima kuma ko takansa banabi.

Yariga ya sauya min sosai ,fiye da inda na sauya masa, Dan aikin da yake tayani yanzu ko kadan yadena ,dama nima bana nema na rabawa yarana kowa abinda zai dinga Taya ni,Kuma cikin ikon Allah suna iyawa .


Sana ata yanzu ta bunkasa domin duk wata sai na sari Kaya,yazamto ma yanzu kafin ayi salary nake zuwa nasaro wasu ina kuma rabawa kafin kuma ayi pay kowa ya biyani wancan kafin kuma ayi wani,yazamto ma yanzu har malamai maza nake sarowa yadiddika suna karba in wata yayi su biyani,wasu makarantun nafara tallata kayana cikin ikon Allah sai gashi ana karba har gida ake biyoni karbar kaya ,har mutanen unguwa ma suka farga suka fara siyaduk kuma a rintsinne yazo min dawani zance tare da kalma mafi Muni a gareni.

Da misalin karfe takwas yadawo ,yayi da ce ranar abincin namu bamu iya cinyewa ba,zubawa nayi na Kai masa,tare da Yi masa sannu da zuwa,Dakar nasamu ma ya amsa,na ce ga abinci Bismillah,wani murmushi yasakar min sannan ya ce yau kuma kudin sun Kai kenan har Allah yasa nasamu; to dauki abunki a koshe na ke bazanci ba,kallonsa nayi na ce wani abun kac;ko banci komi ba bazanci ba kidauke abinki.


Har na mike Zan futo daga dakin domin inason inje inyiwa hajiya shimfida,ya ce koma ki zauna ina da magana da ke,na ce to da shimfida zanyiwa hajiya,kidai saurarenin yanzu Zaki tafi ba wani zance ne me nisa ba.


Na ce Ina saura ranka,ya ce dama zance ne zamuyi kuma kisa fahimta a cikin domin dama da abuna araina, kece kika tsayarmin da komi dan haka karma ki daga hankalinki domin bazan sauya ba ,na riga nagama shirya komi.


Hannu nasa na tallafi habata na ce to Allah ya jishsheni alheri,

Dama aure Zan kara ,bama tin yanzu nagama shirya komi ba, zancen ya dade kudin danake tarawa wadanda kika kaiwa farmaki sune kudin auran daza,akai to duba da yadda kika rusasu shiyasa nadaga zancen auran sai yanzu Dana Gama shiryawa Dan haka ki kwashe kayan dake dakin yaran can domin anan zata zauna Nan da sati biyu zata tare insha Allah,.


Ai ba das karewa nayi ba wannan karan, wani irin fuzgar numfashi nake domin nema yake yayanke daga gangar jikina, ai bama tatasa nakeba takaina nake juya kaina nakeyi tare Dukan kirgina Ina kuma Kiran innalillahi wa,inna ilaihirra ju,un,cikin ikon Allah sai naji Ina samun relief ,nima aljanunne suka hauni kome oho,nima bansani ba, amma dai natsinci hanna ye na bisa rigarsa Ina mezare ido tare da furucin wallahi Bai Isa ba inhar ya Yi aure a wannan halin da muke ciki toko sai dai in bana gidan, hannu yasa ya tsinke ni da mari ya ce dama karimatu Baki da tarbiyya ni kike kamawa riga tare da yimin warning kamar ke kike aurena to kije nibazan iya da wannan musibar takiba ,na sakeki saki daya.


Ya Allah, πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™† *INA* *BUKATAR* *COMMENT DINKU*


🀝 *DAGA* *ALKALAMIN* *YAR MUTANAN JINGAU* πŸ™‹
[21/01 Γ  12:10] +234 703 197 3585: *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€__



😳😳😳😳😳😳



πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™


*_PART 2_*

*LABARI DA RUBUTAWA*


*BY*



🀝 *FAUZIYYA AUWALU ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹





*πŸ…Ώ70(R FOR RADIATION)*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind r readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____GA KYAUTAR PAGE KO BAN FABA KINSAN KANKI_REAL LEEMAT NABAKI KIYI YADDA KIKESO DASHI KIBAWA WANDA KIKE SO KI KUMA HANA WANDA KIKAYI NIYYA.______________________________cak natsaya domin na tabbata innayi cikakken motsi zuciya ta ce zata buga ,bazan iya kwatanta yanayin ba in kukaji ana kiran bacin rai tofa da sauki ni bansan me Zan kira halin danake ciki ba .


Jingina nayi jikin garu na daga kaina sama ,domin insamu numfashina yadinga futa daidai , amma duk da haka baya futa sosai sai jansa danake Yi ciki,Kai na na fara juyawa jinake wani Dan Dano Mara Dadi na ziyartar ruhina ,bana Jin duniyar dai dai ,amma sai na Kuma gyara wa ko zanji dadi, bakin gadona nasamu na zauna cikin ikon Allah kuma sai nahau ajiyar zuciya,Jin nafara samun kaina sai nahau Kiran sunan Allah a fili ,zubamin ido ya yi ganin halin danake ciki sai duk jikinsa ya yi sanyi, matsowa ya yi kusa dani ya rikemin hannu ban hanashiba domin Ina bukatar fiye da haka.


Ganin ya riko ni ne sai na tashi na wada jikinsa tare da rukun kumeshi,Bai hanani ba sai yasa hannunsa duka biyun ya kara matseni ajikinsa,bance komi ba sai lumshe idona da nayi wata katuwar ajiyar zuciya ce ta tahomin wanda har sai da ya dagoni da sauri yana jijjigani.


Bayan nadan Sami nutsuwane nahau tattara kayana tare da na yara na cikin babban buhu,Yana kallona yakasa yimin magana ammafa duk damuwa ta bayyana a gareshi.


Dakin hajiya nashiga tarar da ita nayi har ta kwanta a inda take,shimfida nayi mata sannan natasheta domin tahau ta kwanta,ido tahau mutstsikawa tana cewa lallai bacci haka kamar wadda aka zubawa barkono a ido, murmushi nayi na ce hajiya ki kwanta dare yafara,har na juya Zan futa ta ce ke Yar Nan yaki,komawa nayi na rabe gu daya,ta ce wani Abu akayi miki;shiru nayi,ta ce matsonan me ya faru ki gayamin karki dauke ni ba ubawa ki gayamin damuwarki ko Zaki ji dadin ranki, wannan Jan numfashin naki in Baki Fadi abinda ke ranki ba za,a iya samun matsala.


Matsawa nayi kusa da ita na dora kaina jikinta ,sonake hawaye yadan zubomin kozan Sami sauki cikin raina amma har yanzu Babu alamarsu.


Na ce hajiya shu,aibu ne zayyi aure,dan nace ban yarda ba shine ya sakeni.


A furgice ta dagoni ta ce saki dai na aure;daga mata Kai nayi, ta ce saki nawa yayi miki?


Hannu na na daga na nuna mata, ta ce to yanzu ki saurareni Zan tambayeki, na ce tom, Zaki tafi ko zaki zauna?

Na ce ni har na hada Mana kayanmu tafiya zanyi gidanmu,tayi murmushi ta ce yaro dai yaro ne ,ni ce Zan hada kayana na tafi saboda in Baki goyon bayan Shirin da zakiyi,in kina ganiba bazaki iya yin wani abun ba,karki damu ban tafi ba kenan Zan dawo in kika dai dai ta komi,ki bashshi da halinsa amma kiyi kokarin kwatar yan cinki.


Nan ta gama shiriya min yadda zan gudanar da lamarin ,a Kuma lokacin ta rakata titi tasama mata mota ta shiga ciki domin ya kaita gida,Basu rabuba sai da ta kara Mata karfin gwiwar yadda zata Yi aikinta cikin nasara.


Sanda na koma gidan Yana zaune a daki ya zuba uban tagumi Babu komi a fuskata domin bacin ran yadan ragu da temakon Allah da Kuma shawar warin hajiya,suna na ya kirawo, ban waiwayi ba balle in amsa,ya ce nasan nabata miki amma ke kika fara batamin Dan.....katseshi na yi na ce ai kuma komi yariga yafaru Dan haka shikenan kuma ni a tinanina ko banci tsiran komi ba zanci tsiran ribar da na zube maka ta aure ,ko kuma na ci tsiran shekarun da muka samu tare shekara goma sha takwas Muna tare sun wuce wasa Dan haka na barka lafiya ,karka kuma cewa komi tinda Naga karshen game din.


To ki saura reni mu dai dai ta ,na ce dawa futa ma nayi na shige dakin yara da suke bacci nayi kwanciyata,jinsa nayi ya futo ya na kirana ban amsa ba bare in futa.


Jinsa nayi ya futa nasan Kuma bread zaije yasiyo, na ce yanzu wasan zai fara,tashi na Yi maje na kulle kofar gidan na ce mafuta kenan wannan gidan badai in barmaka shiba sai dai mu kabar mana ,niyyarka in tafi inbar wadannan diyoyin da baka daukar lamarinsu da girma toko sai dai kaje ka sake sabuwar rayuwa kaida amaryar taka.


Sanda yadawo daga siyo bread din bugu yadinga yi inzo inbude masa,amma sai nayi kunnan uwar shegu dashi ,a kalla ya shafe awa daya Yana bugu har sai da yafara tasarmin Yara daga bacci,tashi na Yi nashiga cikin shagon gidan na leka ta taga na ce Wai waye yake buga gidan mutane da darannan?


Da zafinsa ya matso kusada tagar Yana cewa wannan wane wulakanci ne kika rufemin kofar gida ki budemin na share sama da awa daya Ina bugu kina Jina Dan wulakanci ,ko ke kike rufe gidan Daman ko kuwa nema

27 / 31