ABINDA KE FARUWA HAUSA NOVELS BY YAR JINGAU

Author :  Yar Jingau Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   23 / 31

66K to 69K   out of 92.1K words

khadija wadannan ma ba fiya dasu yayi ba Dan ko anan ya ke wani lokacin can ya ke shiga ya debo kayansa inzaisa,hatta gajerun wandunansa sai da ta tarkata masa ta ajiye gefe, bayan ta gama shara ne ta Debi kayan wankinta ta hau sabewa, ada takan dibi kayan su hasiya ta hada dasu ko ba dukaba in taga bata gajiba ,har na baba Dana habibun ta ke hadawa haka ta ke wuni akansu inzatayi wanki,yau ko cikin mintina tagama abinta ta na Yi ta na wake wake ,har sannan kuma bata waiwayi Wai me aka dafa a gidanba .



Bayan gama ayyukan da ta ke dasu ne ta dakko tsohon rishonta da ta ma manta rabon da ta yi amfani dashi,ta wanke shi kal ta shanya, daki tashiga ta dauki kudi ta leka makota ta sami yaro yatafi siyo mata kerosene.



Bokitin da ta ke ajiyar kudin cinikinta ta zazzage ta tarkata cinikin da akayi bayan ta kirga ta watsasu jaka,gurin kulle kullen kayan nata ta nufa daya bayan daya ta dinga dubawa wanda Babu kuma ta debo tahau kullawa cikin awa biyu ta Yi abubuwa masu yawa wanda ada ko tanaso ta yi Bata fiye samun dama ba.


Suko mutanen gidan sun saba da baccin hantsi har zuwa karfe daya ,kan sutashi daga bacci ita ko ta gama Yi musu komai,yauma hakance ta faru abinka da sabo,ki wacce tasaki jiki ta Yi baccinta sun manta tsarin gidan angaya musu ya sauya.


Yunwa ce ta fara tashin khadija daga bacci ,mika ta ke yi da alamar Jin dadin hutawar datayi ,kamshi ne ya daki hancinta Aiko Dan dake cikinta ya kara juyawa Dakar tasamu ta yunkura tayo waje sai murxa ido ta ke yi,can gefe zainab ce zaune sai warbar indomie ta ke yi wadda ta ji kayan hadi ga wani nar keken kifi daga gefe cikin wani sosa na hango yankan da tayi wa cucumber da kabej timatr da albasa wanda ta cakudesu gu daya da cokali ta ke diba tana hadawa da wannan indomie din tana ci hankalinta kwance ga jug dinta nan wanda ta hada tiara dinta domin warware yunwar data nade mata hanji.



Ameera kiyiwa Allah ki bayyana min *ABINDA KE* *FARUWA* domin nakasa tunowa, Ina jina kamar baniba , kamar kuma wasu abubuwa sun faru dani wanda kuma nakasa tinawa.


Na ce Haka ne amma yanzu bazai yiwu ayi komai a gaggauce ba, kabarwa anjima ko gobe domin kaga yara suna bukatar abinci tun da na dawo baka barni nasami nutsuwar da Zan sallami wadanda suke jirana ba ,ka yi hakuri inshiga kitchen in fito sannan koma meye sai mu tattauna.


To ameera ta nagode Dan Allah kanki tafi kitchen din kigaya min in kinsan inda ummana ta ke jinake kamar zuciyata zata fashe kigayamin Dan Allah.


Kabarni din dai indawo,bani mintina dan Allah.

Sadiya ce take goye da hannunta a baya yaranta duk sun kewayeta , khalil ne dake yafisu wayo ta ke tambayart, amma ko kallonsa batayiba,azabure ta dakko waya bugu daya aka daga batare da jiran komiba ta ke cewa aminiya kina ina kizo ki kawomin dauki komai ya lakace komi ya kwabemin,to to to inajiranki Dan Allah kiyimin sammako bansan mezai faruba inya fuskanci Nike da alhakin komi.


Sanda karimatu ta koma gida karfe biyar harda mintina ,da sallama tashiga gidan nana ce a tsakar gida tanayin tatar kunu, Dan gobe asabar dama Kuma duk asabar da lahadi shine tsarinta sukanyi kunu da kosai ko Kuma koko da kosai,shikuma saddik yana sunkuye ya na sharar tsakargida,aminullahi kuma yana tace shinkafa,su kuma sauran yaran suna dakin kakarsu wadda ta dade da rasuwa suna yin kallo.



Da sallama tashigo gidan Aiko sukayi kanta da tambayar yau ina ta tsaya; hhhhhh Kai sai kace Yan jarida wannan tambaya haka, aminullahi ne yayi saurin cewa kin manta Da ni kenan momi ,au au au ashefa zanyi shuka a idon makwarwa ga jaridar kanta a gefena,to kaikuma fa doctor ya sharar yau kaita titsiye kenan da shara ;dariya sukayi duka nana ce ta ce a,a wallahi aikinne yayimin yawa shine ya ce zaimin tata ni nayi sharar to Kuma kinsan tatar saddik gobe dusa zamu dinga hadiyewa guda guda kamar curin kosai.


Aiko ya wullar mata da tsintsiyar ya ce to ko kyayi abarki ni zanyi tatar in yaso ke kiyi sharar ki in yaso in an dama ki ki Sha,kici kici suka kama bakin rariyar tare da hayaniya har sai da sauran Yan uwan nasu suka fito,yar autarta data taho da gudu gunta ta cafe, tare da sakar wa yaran dariya,ta ce nidai na banu nafa dawo kenan ba sarki sai Allah Koda da ba na nan kunyi fadan oho.


Aminullahi da ke gefe Yana kwasar dariya ne ya sa ke kwashewa da dariya domin dagaske ko kawar karbar rariyar sukeyi ga junansu,ya ce wallahi momi wadannan Yan rainin hankaline sanda bakyanan hademin Kai sukayi harda dunguremin Kai Wai sai nayi girki amma daga dawowarki har sun fara fada.



*INA BUKATAR RUWAN COMMENT DINKU INHAR KUNASO INCI GABA*


🀝 *DAGA ALKALAMIN* *YAR MUTANAN JINGAU* πŸ™‹
[21/01 Γ  12:10] +234 703 197 3585: *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€__



😳😳😳😳😳😳



πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™


*_PART 2_*

*LABARI DA RUBUTAWA*


*BY*



🀝 *FAUZIYYA AUWALU ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹





*πŸ…Ώ61(I FOR IMMEDIATE)*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*



Dariya ta yi ta ce to Kai dinfa ; yanzu nima dazanyi magana haduwa zakuyi ku hademin kai kamar Baku sanni ba,Dan haka bakina kanin kafata,kunga shigewata.



Aiko ta bakin nata ta na barin gurin suka sa santa,nana ce ta fara cewa to tsaya kaji kabarni na karasa inyaso Kai sai kadama Mana kunun gobe ,ni kuma sai inyi sharar Kai har dakinku zansharo kaji Dan kanina hh,ya ce a,a wallahi sai dai in saka kosai ke ki dama, kuma kwasar farko tawa ce inkin yarda,e naji jeka ka karasa na yarda kaga magriba ta kusa Kar aikin yayi mana dare gashi ko markade ba,a dakkoba ga momi ta dawo Kuma nasan zata bukaci abinci karmu bata mata lokaci.



Ta na ciki ta na jinsu ,Dan murmushi ta yi najin dadi domin ta na Jin dadin kulawar yaran nata gareta,iya kulawa ta basu tare da dawainiya dasu wanda bazai misaltu ba ita din wani bango ne na diyoyin nata wanda suke jingina suji dadi ,domin Nan duniya sun tabbatar basu da sama da ita, gadai baban nasu suna kallo amma taurarinsa a kullum Basu fiya haskawa a fuskarsu ba ,har kullum sudai mominsu,wani abu da zai burgeka da yaran shine ,basason ganinta cikin kowane yanayi inba farin cikiba ,ko Zama ta yi Bata aikin komai tausaya Mata suke Dan ko juyi tayi da sunan gyara zama kwaji sunce momi sannu,balle ta tashi ta na kaiwa da kawowa aiko sannan zakuji yadda diyoyi suke kaunar uwarsu sun dinga momi sannu ki zauna ki huta karki kaji,momi sannu aikin su kenan zallar tausayi da soyayya ke futa agunsu ,zokuga wani daga cikinsu yasami wani abun anan ake kafsa Yar haushi da kishi ,domin kowa karinsa ya mallaka mata dukkanin abinda yasamu har sai ta na cewa kaima ka rage wani abun kozaka amfana,


A,a momi Babu abinda zanyi dashi kirike ko ki cinye in Ina so nazo kibani wani,tofa sai kowa kishinsa ya bayyana Wai Dan bashi ya bataba,sai kuga suna kokarin lalubo kome ke garesu domin Suma su Bata taji dadi,Kuma daga manyan har yaran haka suke,gashi dukkanin abinda zasuyi basayi batare da umarninta ba da wuya su dakko mata magana domin ta bi matakan da zasu gujewa hakan.


Ta na cikin tunani ne nana ta yo sallama,bayan ta amsa sallamar ne,ta ajiye mata abinci,tare da yiwa momin ta su sannu da hutawa, ta ce me na samu hajiya nana ; dariya ta Yi ta ce shinkafa da miya mukayi da salat to kuma sai yanzu na Dora miyar shine na zubo Miki da manja kafin agama sai mutuminki Dana zubo miki,bude flat din abincin tayi shinkafa ce kuwa da manja taji gyanye dasu cucumber ta ce hakan ma nagode sannunku da aiki Allah yayi muku albarka Allah ya baku ikon jurewa .


Cikin farinciki nana ta ce Amin momi dazu abba ya aiko da nama amma ban gyara shiba sai dai ko innagama , Allah sarki shiya kawo ko kuwa; a,a me nama ne ya kawo na bayan layi,to mun gode ki ce akwai cin dadi kenan; aiko momi ki gyara bakinki dan sai kinci kin more Zan bawa kowa ya ci,dariya ta Kuma yi ta ce haba nana Ina kika bar wanda ya kawo din ai sai an diba masa sannan mu kuma asallamemu,yanzu dai tashi kije kafin in taso sai in tayaki naga dare na Shirin lillibe garin ,a,a momi ki ci abincin sai kidan huta kafin ayi Kiran sallah in kikayi sai ki kwanta kyafi huta gajiya nasan kin gaji ko momi sannu bara naje kici abincin sosai.


Bin yar tata ta Yi da kallo wani siririn hawayen kaunar yayan na ta ne ya ziraro mata ,ta sa Dan yatsa ta dauke ita har kullum cikin tausaya musu ta ke shiyasa har kullum kokarinta ta dorasu kan tafarkin da bazasuyi nadama ko danasani ba,tana hango kalubale garesu yayinda Babu ita dan haka ta ke musu tattalin da baza,ace sun Gaza tallafar rayuwarsu ko batanan ba ,tasan dai akwai Allah amma fa dole akwai wani shiri gareka Dan adam kafin Allah yasa cigaba yasame ka,Haka kuma duk sanda ta kalli diyoyin dake kaiwa suna kawowa har kullum tausaya musu ta ke Koba nata bane domin ko ta ina anbar gini tin ran tibani, shiyasa yanzu ko ta ina Yaya suke neman bujirewa iyayansu Dan sun rasa tallafi mafi girma a rayuwarsu,Baga uban ba,bakuma ga uwar ba ,kuma har gara fa na uwa domin ita tare da ita ake cikin wuyar rayuwar, takan hango ita kanta dabadan Allah yasa tanada aikin yi tare da kujiba kujiba ba,da batasan yanayin rayuwar dazatayi ita da yaranta ba,gashi dai a haka komi sai godiya musamman ma da Allah yasa tayiwa tufkar hanci har ta kwato yancinta dakar tare da neman mutuwar auranta a wancan time din ,wanda badan ta Yi dagaske ba da tini rayuwar iyalanta ta wargaje.


E mana ai in akace uwa bata tare da yaranta ai taga banu ,suma yaran sun ga Banu ganin idonsu ,domin dukkanin rashin gata yasamesu,dan Shi uba fa kafin ki hango me hangen nesan matsalolin yayansa Zaki dade kina laluba, kefa ko me kular kika samu kedin dai ke ce shakudin me abin mamaki shiyasa wanda ya rasa uwa ya ke da wani miki mara warkewa har sai randa ransa ya rabu da gangar jikinsa.



Ta na cin abincin ta na tinanin yadda rayuwar kullum take kuma tabar barewa,har kullum kuma komi akanmu ya ke karewa mu mata , uhmmmmm mata mata Allah ya tallafa mana, zainab ce ta wado mata a rai ,ta ce ko ya su ke ciki yanzu, Allah dai yafitar da ita domin ta na cikin matsala sosai ,in banda ma abin wasu iyayenna mu da basa duba yadda rayuwar take, da kuma yadda diyoyinsu su ke rayuwa ,ai Bai kamataba kamar zainab da ko haihuwa daya batayi da mijin ba, a ce anbar ta cikin wannan hali ba, intayi magana a ce ta Yi hakuri har yaushe hakurin zai kare ,kodai an sai mata tikitin dawwama cikin bacin rai,girgiza kai ta yi ,ta ce ya kamata fa mu fadada wannan kungiya ta mu domin Kai dauki ga Yan uwa masu fama da bakin cikin namiji,abincin dake gabanta ta ture gefe ji tayi ranta ya kara baci sosai nan da nan zuciyarta ta tsananta bugawa fat fat jitayi kamar ciwonta na neman tashi ,nana ta kwallawa kira amma dake ta na kitchen batajiyo taba ,sai saddik ne ya shigo dakin ya na cewa momi ta na kitchen aiki ta ke wani abun za,ai....da sauri ya karasa ciki cakumarta ya Yi dasaurinsa ya na cewa momi tinanin me ki ke yi me yake damunki sannu momi me ya ke damunki...hannu ta daga masa ta ce Yi a hankali Kar ya ra su jiyoka maganina zaka dakkomin Yi sauri kabani.

Da sauri ya mike ya nufi cikin bedside dinta ,wasu tarkacen magunguna ya debo Yana dubawa guda uku ya diba daga ciki sannan ya dakko ruwa ya mika mata, ita kuma ta karba ta zuba a baki shikuma ya saka mata ruwan abakinta ta hadiye magungunan,sannu ya ke ta jera mata sannan ya ce ta kwanta ta huta ,gyara mata gurin yakara yi yana ta kara jera Mata sannu bayason ciwon Nan na mominsu ciwon ya na daga musu hankali sosai inda ma Allah ya taimakesu yanzu ta kan dade Bai tasar Mata ba.




Kai kai kai komi Dan Allah yafi sabaninsa, domin Al,amuran a bayyane suke yau in kuka kalli sadiya duniya tayi mata gwatson mage ,abubuwa ne suka tarar mata Dan wani zubin takanyi kamar ta dora hannu aka ta ce wayyo Allah.


Miji ba yayi da ita ,ga babu data samesu Dan yanzu akaso goma cikin arzikin dayake dashi Babu shida ,iftila,I kala kala ya wadawa dukiyar, ga yayanta ma da basu dauketa da muhimmanci ba ,komi zatayi basa sauraranta kota kanta basa bi ,ko korafin su ameera da babansu ta ke gaya musu abin baya wani damunsu , musamman ma khalil Dan dashi yaran suke kwaikwayo,shikuma yaro ne da Bai damu da uwar saba ,sabgarsa yakeyi ko ta kanta baifiya biba,ya kance nafasan halinki umma tinda kika yiwa kakarmu ma to wazaki kyale kawai in ma anyi miki kiyi hakuri a wuce gun Dan ke kika fara Yi musu.


Ameera ko da umma kamar Basu taba tsintar kansu cikin wata damuwa ba, lamuransu sukeyi sosai cikin kwanciyar hankali,gadai babun data hauro musu gida amma ko a jikinsu ta rungumi mijinta da uwar mijnta .


Tabangaren mu,a malarsu kuwa daga sanda komi ya bayyana, aiko bakaramin duka ya yi wa sadiya ba, sannan ya dankara mata saki daya ,yar korar tata kuwa aminiya, randa yarutsa ta ta jibgowa sadiya wadansu kayan tsafi, cikin wani irin bacin rai yayi kanta ,baima duba cewar ita din wacece ba ya shaki mako goronta,ya ce dama ke ce munafukar da tayi silar komi ko, yau kin shigo hannuna menayi miki kikeso ki rabani da rayuwata, janta yayi ya kumata jikin garu sannan yadauki tafin hannunsa yamaka mata a fuska, Aiko ta kwallara ihu Dan Marin yashigeta sosai ,ihun da tayi sai ya kuma fusatashi ya maka Mata hannunsa a bakinta ,wayyo aminiya yau tashigo hannun maza ,domin da ihunta da hakoran bakinta nagaba suka yo waje,duk wani tsoron sadiya ya Kara bayyana sai mazari takeyi dan ta tsorata da lamarin.



*INA BUKATAR RUWAN COMMENT DINKU INHAR KUNA SO INCI GABA*

🀝 *DAGA ALKALAMIN YAR MUTANAN JINGAUπŸ™‹*
[21/01 Γ  12:10] +234 703 197 3585: πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€



😳😳😳😳😳😳



πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™


*_PART 2_*

*LABARI DA RUBUTAWA*


*BY*



🀝 *FAUZIYYA AUWALU ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹





*πŸ…Ώ62(j FOR job)*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*




Ihun da ta Kuma kurmawa ne yajanyo hankalin mutanan gidan ,har Yar rige rigen shigowa suka dingayi, domin ganin meke faruwa,yayi daidai da kara tsula mata wayar socket da yayi a gadon bayanta ,wani irin gantsarewa ta yi har sai da ta hantsila ta baya.


Umma ce ta Kai mata dauki,ta ce lafiya meke faruwa ka ke Dukan matar mutane; Babu amsa sai uban huci da ya ke faman Yi,idonsa yadago yasauke su Akan sadiya ,wacce ta Yi tsumiii kamar munafuka,kamar anhankada shi ya yi tsalle ya isah gabanta, da saurin ta ta ja da baya, Aiko ya sa kafa ya fardo ta ,wayyo sai ga ta ta zube jikin aminiya ta na rike kugu,ta ce kayiwa Allah ka yi hakuri wallahi sharrin shaidanne bazan sake ba.



Ki ma sake, ba sai kin gan ki cikin gidanba sannan Zaki sake yun kurin cutar Dani ba ,Dan haka ki je na sake ki, kinga in kin hada da wancan biyu kenan kafin in ciko mi ki cikon dayanki ,kinga kenan ba kare bin damo.


Ameera ce ta ke tafa hannu ta na cewa Kai ,kai,kai Yaya me ke nan ,me kenan Dan Allah kayi,ya mukayi da Kai wancan karan me Kuma ka ce min ; to Dan haka tafiyar sadiya daga gidannan tafiya ta ,Dan bazata gama rashin mutuncinta tare da cin galaba akan kowa ba sannan ka ce Wai ta karkade yayanta tabarminsu ita kuma ta tafi ta wataya ba ,Dan haka ko ka mayar da ita ko nima inbita gara ka rabu da ita a gidannan ta kwashi ribarta a hannunta bame tayata.


Umma ce ta ce, kenan ban isa da Kai ba da na ce karka Kara sakinta ba ko,sha na ke mun gama wannan maganar ,kome ne sai ka Sanar da ni, Dan haka ka je ka Yi duk yadda yayi ma ka dadi tinda har yau ba ka dawo hayyacinka ba.



Da sauri ya juya gurin umman ta sa ya na me ba ta hakuri, sannan ya kamo hannun ameera ya na cewa kema kiyi hakuri ameera kingafa kamasu na yi da wadannan kunshin tarkacen, har ta na ce mata ta zuba ma na a abinci muci ,kalli, kallesu ameera , umma ke ma matso kigani asiri ne ta kuma kawo mata za ta kuma rabamu.


Murmushi umman ta yi ta ce lallai kam ka dake ta, amma ko sadiya kinyi Girman banza duk darasin da ki ka fara dauka bai isheki ba,to daga yau za mu zama Yan kallo tsakaninku, amma kai abinda na ke so da kai kamayar da ita dakinta ta ci gaba da rungumar yayanta ,ni ko ameera ba me rike mata diyoyinta ita din dai ita ce jigonsu .


Waiwayawa ya yi ya kalli ameera ya ce je ki ki kirawomin baba me gadi .


Cikin mintina ko sai gashi ya zo.


Tambayar lafiya ya fara Yi musu ganinsu cikin wani hali duk kowa a furgice ,gefe daya kuma uwar dakinsa ce da aminiyar ta a zube sai a jiyar zuciya

23 / 31