Author : Yar Jingau Category : Romantic Hausa Novels
ya kwace mata .
Haka aka cigaba da tattauna abubuwa masu muhimmanci har taron ya tashi, sannan sun kafa kungiya ta taimakon kai da kai babu kuma kyashi da nuna ido cikinta an yi ne domin mabukata .
Farin cikinsu baya misaltuwa domin suna ganin a kaso goma cikin burikansu sun cimma mafi runjaye daga ciki.
*BAYAN SHEKARA GOMA* **SHA BIYAR.*
*
abubuwa sun biyo baya na dadi ga wasu ,wasu kuma rashin dadi.
A wannan lokacin karimatu ta cimma burika da yawa ciki ko har da auradda diyo yinta ,a yanzu haka suna kan bukin Muhammad Al,amin buduri sukeyi cikin wayewa da saddakar da komi gurin allah ,bata da fargabar duk surukar da za,a dakko mata ,domin tariga ta gama bawa allah zabi,tin farko bata sake da yiwa diyo yinta addu,r mace ta gari ,tare da abokai nagari,tasan duk wani alheri ta gama rokar musu,sai dai a dora a inda aka tsaya,sai dai ko kuma kaddara wacce ba,a fata.
ta kuma mika wuya tasan bazata wulakanta ba gurin suruka, tana da yakinin ita kanta zata riketa hannu bibiyu domin ance gani ga wane ya isa wane tsoron allah.
Nana kuwa yaranta uku, ga shi ta cimma burinta nazama likita, dan har tafara cin moriyar karatun ta, ta dauke wa iya yanta abubuwa da yawa ,ciki ko har da neman alfarmar umman tasu na ta yi resining.
shima saddiku bayyi aure ba sai da yazama cikakken likita, sannan allah yayi masa kyauta da mace tamkar dubu kyakykyawa me kyan hali ,diya ga rukayya .
Suma sauran yaran kowanne yana kan cika burinsa cikin amincin allah.
In muka leka ta bangaren sadiya kuwa lamarin zai bada mamaki domin itama ta aurar da nata yayan ,yaya mazan da take tutiya wadanda kana kallon lamarin kasan akwai lauje cikin nadi ,warwareshi sai Wanda yasan abin da yafaru tin farko.
Ga jiyya data saka ta gaba domin kunar da tayi, har yanzu tana nan bata warkeba, yazamto inta tayar mata har sai taje kusa da wuta saboda kaikayin da ke mata, dumin wutar ne shi yake sawa tadanji dadi,hakan kuma da take sai kunar taringa futar da mai ,kamar ana gashin nama,idan bala,in ciwon ya motsa haka zatasa hannu taringa barar kunar jini ko haka zai dinga ziyaya kamar
*INA BUKATAR COMMENT DINKU INHAR KUNA SO INCI GABA*
π€ *DAGA ALKALAMIN YAR MUTANAN JINGAU* π
[17/03, 4:59 PM] Yar Mutan Jingau: *Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
*π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββ__
π³π³π³π³π³π³
π *ABINDA KE FARUWA* π
*_PART 2_*
*LABARI DA RUBUTAWA*
*BY*
π€ *FAUZIYYA AUWALU ALIN BABA JINGAU* π
*π
Ώ75(W FOR WORK)*
*πKAINUWA WRITERSβπΌ ASSOCIATION*π€π»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
in tana barar kunar haka jini zai dinga tsiyaya kamar wacce ta yanke a gurin, haka ta rame ta kare ,duk wata nutsuwar ta ta gudu,sai uwar rama da baki da tayi,magani kuwa dama an dena sai na hausa da ake tayi, domin daga baya ganowa akayi daji yashiga cikin kunar shiyasa ko wane magani yaki karbarta.
Ta bangaren ameera kuwa batada wata damuwa domin yanzu babu yara gabanta duk ta aurar dasu , sai dan autanta me shekara takwas duk da ba wai isa tayi da gama haihuwar ba ,amma dai shiru har har yanzu bata kara ba, sai nutsuwa da ta sake samu juya kan sitiyarinta takeyi cikin nutsuwa babu gargada,komi da nutsuwa ta ke yinsa, ta hada kan yaran da na ta da na sadiya duk ta rikesu bisa gaskiya da amana.
badan ita ba sadiya ko kafar yaran nata bazata dinga gani kan lokaci ba,in ma basu zoba ameera ce wacce ta tashi daga ameera ta koma hajiya, ita take kokarin yi musu waya suzo mahaifiyarsu tana bukatar su ,taban garen me gidan kuwa arzikinsa ya dawo dai dai misali, yakuma sami nutsuwa sosai yana kulawa da mahaifiyarsa yadda yakamata ,duk da dai yanzu ta kara tsufa sosai domin ko tafiya umma bata iya i saida sanda ,kafa ce ta ke mata ciwo,so biyu ameera na bashi shawar futa da ita kasar saudiya ana yi mata aiki ko zata Sami lafiyar kafar,amma dake abin ya hada da girma sai dai kawai ace ana samun sauki badai saukin aka samu ba.
Surukan su kuwa dai dai misali suna kwatanta girmamasu ,dan ameera tayi dacen surukai, kamar diyoyin cikinta haka ta dauke su :suma kuma sun dauketa uwa, suna girmama sadiya ammafa a gaban idan mutane in suka kebe babu abinda sukeyi sai shakiyanci ,sufa basa son suna ra barta karnin kuna yayi ta damun mutum, sufa sun kusa ma dena zuwa gaisheta.
Wata rana kuwa da ciwon ya tayar mata sukaje dubata sai susa takeyi dakin kuwa in banda karnin kuna da najini babu abinda ya ke yi,haka suka dinga toshe hanci suna kebe baki ko gaisheta basuyi ba sukayo waje,suna mitar anti ameera badan itaba sufa da bazasu ringa shigowa suna shekar wannan warin me tayar da zuciya ba.
Allah sarki ciwo ashe na ajali ne randa kunar ta tashi da ciwo a ranar wuni akayi a kanta ,dan an rasa yadda za,ayi mata ta dena barewa, hawaye ne yake kwaranyowa ta idanunta guda daya, radadi tare da wata iri yar azaba sune suka sata a gaba,haka ta dinga yagar kunar kamar mahaukaciya, daga karshe dai susa tahau yi tana ihun azaba har sai da jikinta ya Yi sanyi tare da janyewar kwayar idonta sama.
Suna gefe sun zubawa sarautar Allah ido ashe rai ya yi halinsa.(Allah yasa muyi kyakykyawan karshe)
In muka waiwayi shekarun baya da suka wuce ta bangaren zainab.
Tayi iya kokarinta gurin kwatar yancinta,ta bujire musu tare da shimfida nata mulkin na rashin daukar raini,suka ce kuwa dawa Allah ya hadasu bada ita ba,rashin kirki sukeyi mata sosai baga kishiyar ba ,ba kuma ga baban ba.
sun matsa mata lamba sosai har takai in anzo siyan kayan data ke siyarwa suna korar masu siyan ,sai da aka wayi gari kasuwar ta tana neman mutuwa, duk da hakan taki basu goyon baya na cigaba da yi musu bauta.
Ranar wata laraba ne bayan habibu ya gama shirya wa zai futa,har yaje bakin kofa ya juyo ya kalli fuskarta ya ce ki fa kara yin hakuri wannan karan ma aure zan kara dan har nakai kudin aure : hhhhhh yo sai me ai ba yau aka fara ba ,da ka yi !da kar ka yi! ni duk daya ne a gurina bani da wani damuwa akai .
Da jin haushi ya juyo ya kalleta,ya ce au ke har wata magana kike da ita, dan kin samu ma nagaya miki; kar ki damun mana ,dama tinda ba wani alfanu kike dashi a gidan ba ai dole kiyi murna da abinda zanyi,dan haka a hir dinki naji zancan ya futo a cikin gidannan.
He he he he ashe kace zamuyi kallon dambe a gidan nan ,kace muyi Shirin kallon dam ba cewa.
Dawa za,a dambace din an gaya miki itama irin kice shashasha,ita din ai tafiki hankali tinda tana da yara tasan ciwon kanta.
Ni din dabani da su ai ba,ayi shawara da kai cewar za,a bani ko baza,a bani ba .
Hayaniyar muce ta janyo hankalin su baba da khadija sukayo waje.
Da masifa baba ta ke kiran ita fa wallahi tagaji dajin tashin hankali kullum ,dan haka yau dole ko ya korani gida inje in huta ,ko kuma ita tabar gidan taje wani gurin ta huta ,
Kebe baki na nayi na ce ai ba sai ance ma na huta ba, gidan da ba wata karuwa cikinsa sai tashin hankali da rashin sanin darajar dan adam me zan zauna nayi cikinsa.
Aiko kamar tsokana baba tayo kaina gaba daya ta rufeni da duka,kamar Allah ya aiko ta,khadija ko na gefe daya ta na kuma zugata, shikuma sai duru duru ya ke ya rasa wa zai ruke daga ciki.
Dana ji wuya ko nayi wani tsallen albarka sai ga baba a kasa, garin ta yi saurin mikewa ne ta hantsilo da kafar khadija sukayi rubdugu gu daya,
aiko ji kake timmm a kasa khadija ta wado kanta,abin dai duk ya zo da tsautsayi da kuma kiyayewar Allah ga tsohon ciki jikinta,baba ce ta kurma wani ihu tare da rike kafar ta tana ihun khadija ta karya ta.
.jikina a mace na ja baya domin duk bansan abin zaizo a haka ba ,ita khadija in da Allah ya taimake ni bada cikin ta wadi ba da bansan irin tabar gazar da zanyi sanadin ta ba.
Wannan tashin hankalin shine ya yi sanadin aure na har saki biyu,ban wani damu ba sai ciwo irin na kowacce mace data ke ji na in an sake ta.
Haka naci gaba da rayuwa ta a gidanmu cikin kulawar ubangiji da kuma ta iyaye , dole akwai kalubale a zaman zawarci tofa na fuskance shi ,dan ma Allah ya taimake ni nidin me kuzarin nema ce, sai abun yazomin da sauki ,wani abun Inna samu wani fa sai dai in yiwa kai na.
lallai na yarda da maganar karimatu da ta ke cewa in har na dage ne mawa kaina yanci, na gujewa zaman auren da nake yi ,tofa na tina da kalubalen da zai biyo baya, akwai abubuwa da yawa wanda zan wada cikinsu gashi ban Saba ba,ta ce abu na farko hadaka gurin kwanciya da mutanan gida.
Da ni kadaice a dakina yanzu kuwa na dawo gida dole baza,a ce an ware min dakina ni kadaiba,sai dai in da wadatar yin hakan .
Sannan kuma dole a kwai abubuwan da sai na jira an yi min ,sabanin Ina gidan mijina da zan fadi abinda nakeso ayi.(na ce wani mijin ba)
Ga rashin kudin da zasu ringa shigomin,tofa akwai kalubalen da yafi wannan sai dai taimako na ubangiji,abinda yasa ni ban ci karo da wahalarsu sosai ba ,Ina da sana,ata bana rasa kudin shiga shiyasa ban fuskanci wuya me yawa ba a zaman gidan danayi.
Ko shekara banyi a gida ba na sami miji:me hankali da hangen nesa,ban yarda anyi auren mu ba sai da iyayena suka yi bincike akansa,nima akaina sai da na sa akayi min binciken addini sa dadabi unsa da halayyarsa ,ban biyewa dukiyar dayake da ita ba ,ni kawai gobe na nake hangowa ,yazan rayu dashi ,cikin hukuncin Allah sai aka dace ,shidin dan asaline me na garta ,ya tabayin aure amma matar ta mutu gurin haihuwa.
Nayi juyi nayi rawa sanda na fuskanci halin me gidana ,dan baka ramar murna yan kungiya sukayi minba sanda nake gaya musu halin da na fuskanci yana dashi,babu munafunci ,babu mugunta, balle karya dan Sana,ata ma cewa ya yi in hakura yasauke min komi,nice na kiya na ce na riga nasaba yabar ni nacigaba.
Gashi na wayi gari da yaron ciki ,laulayi na keyi cikin amincin Allah Ina kuma samun kulawa gareshi jiyake kamar ya goya ni saboda kulawa.
BAYAN WATA TAKWAS.
nasantalo yar kyakykyawar yarinya ta ,munyi murna tare da jin dadin wannan kyauta da Allah ya bamu, lallai mahakurci mawa daci, tinda a yadda su baba suke nuna min can baya ai bazan haihuba, to gashi dake kyautar ta Allah ce ya bani nawa rabon.
Kungiyar mu kuma sai abinda ya yi gaba domin mun samu tallafin mutane sosai, har yazam to muna hada dan wani abun wanda baifi karfi ba , muna bawa mutane mabukata taimakon jari domin su tallafi iyalansu wasu kuwa shawar warin yadda zasu sarrafa Sana,oi muke basu,kai wasu ma wankau muke cewa suringa yi domin shima yana daya daga cikin hanyar neman abin kai dan haka muna ganin cigaba sosai kuwa,bamuda abinda zamu cewa ubangiji sai dai godiya da wannan baiwar da yayi mana, kota ina muna jinjinawa ga karimatu domin nakan fada na ce komi nazama bazan manta da ita ba, ta bani gudun mawa sosai da shawarwari,ta inda lamarin taq ya ke burgeni nake kuma nutsuwa nadauki wacce zata fishsheni, shine zata baka shawara ammafa zata gaya maka advantage dinta da kuma disadvantage dinta lamarin akwai samun nutsuwa da kwaikwayo aciki.
ππππππππ
Anan nakawo karshen wannan novel din nawa me suna *ABINDA KE* *FARUWA* godiya me tarin yawa ga Allah tare da nuna tsantsar godiya da hikimar da yabani.
Ba wayo na bane ko dabara taba, sai huwa cewa ta ubangiji , Allah ya yi min jagora.
Sannan bazan manta da kuba fans kome nazama kune ,ku kuke karfafamin gwiwa har na cimma gaci da buri na,dan haka Ina gaida kowa da kowa naso na jero koda sunan wasu daga cikin ku ne, amma na hango hakan ba mai yiwuwa bane,kawai nayi jam,i duk wata ko wani fans na *YAR MUTANAN JINGAU* na gode masa da kulawa tare da yabawa Allah yabar kauna,kunsan kanku daku nake na gode sosai domin bakina bazai iya furta komi garekuba,sai dai ince Allah ya barmu tare.kuskuren da nayi kuma Allah ya yafemin wanda na batawa Allah ya bashi hakuri cikin salama.ππππ
Sai mun hadu cikin littafi na na gaba,mai suna *HALAYYAR MU* kuyi kokarin bina ,ko zaku karu ko ki karu ko mu karu baki daya tare da yin kokari muna amfani da darasin dake ciki.
π€ *DAGA ALKALAMIN YAR MUTANAN* *JINGAU* π