Author : Yar Jingau Category : Romantic Hausa Novels
yake cewa ayi masa afuwa domin bashida inda zai zauna abarshi ko a shagonne kan allah ya hore masa.
Dogara wanne suka dauka baki daya,hattara daiiii talaka ,kana gaban manya hukunci anyi shi sai dai wani ba wannan ba.
Cewar sarki aka tambaye ni, Zan iya lamun cewa yaci gaba da zama a shagon gidan;
Dan wani feeling naji a raina kamar nadan farajin tausayinsa,na ce na amince amma da sharadin kar yashiga sabgata , sannan abu nagaba akwai kudade na akansa da yadinga ara har yau bai biya ni ba" kuma Yana da kudin da zai bani Inna tambayeshi sai ya ce babu sai yasamu.
Anan dai aka tsayar da cewar dole ya biya ni dukiya ta ,cewa akayi na lissafo iya abinda nake binsa.
Na ce allah yaja zamanin sarki wasu na rike wasu kuma shine ya rikesu.
Sashi akayi ya fadi adadin abinda na ke binsa ,sai gashi ya na ta lissafi har da ma wadanda ban sansu ba wasu kuma bai fadesu ba,da aka tambaye ni nima haka nadinga lissafosu har sai da ya sunkuyar da kai , abin kunyar ma mafi yawan ni wadanda na fada Ina binsa duk na sabgar data zama dole shine zai nomo ya yi da kansa ne, akwai kuma wadanda na dinga bashi ya yi jari gara gara ma na ce masa akwai dubu dari da hamsin din da dan uwansa ya taba rikewa daga baya dana matsa an biyani.
Sai ga cikakken namiji na share gumi inda kuka San ya hadiyi allura.
Daga karshe dai an tsayar masa duk wata ya tsayar da abinda zai dinga biyana .
Ya ko shiga tashin hankali domin cewa yayi shi samunsa bazai isa ya ciyar damu ba sannan ya dinga biyana wasu dubunnai ba duk wata.
Dana ga za,a dan tausaya masa ,sai na ce ai kwanan ban yasiyi fili kuma har da irin kudina ya hada ya siya.
Wayyo yau shu,aibu yaji barkono,har matsar kwalla yakeyi.
Inda dai muka tashi sarki yabani umarnin in rike filin duk san da yagama biyana na mayar masa.
Zuciyata fari kal nake jinta kamar an yaye min wani dunkulelen dutse a ciki.
Dana dawo gida ai sai na hau hada masa wasu ragowar tarka cennasa duk wani abu in har nasan nasa ne na kwashesu na mika masa cikin shagon.
Cikin farin ciki nake sintirin kai masa ragowar kayansa ,sai bina ya ke da kallo ni kuma Ina kuma juya mala malai da gayya, nazo kawo masa kayan karshe ne ya taso ya tare hanyar ,ya ce karimatu irin karancin da nake Kira miki kenan ;da abinda Zaki saka min kenan;kin kyauta nine fa ,nine mijinki da kika sallamawa komi naki kar kiyi min haka bazan jureba kiyi hakuri mu dai daita kanmu ,kece ni kema Kuma nasan nine ke kiyi hakuri karimata.
Murmushin gefen baki nayi ,sannan na ce ai shanake mun wuce gurin,kai da zaka angwance da sabuwar bazawarar ka, Ina kai ina tsohon hannu wadda aka sakata sabida za,a sami wata, ko ince sabida na taba kudin neman aurenta nacika munci abinci nida diyoyina dan bani dashi ,ai kawai kowa yaje ya yi rayuwarsa.
Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya ,a yau shu,aibu yaci uwar kwalliyarsa domin halartar daurin auren sa da ake yi,nasha tambaya gurin yara cewar ance musu babansu aure zayyi?
E nima haka naji an ce ,nana ce take kuma tambayar to a Ina za,asa a maryar ko a dakin hajiya?
Nayi murmushi na ce a,a ai hajiya takusa dawowa, nima bansan inda zai kaita ba,yo ba sai tambayoyi ba wai meyasa babansu ya koma shagon waje, sunga yadaina shigowa cikin gidan;rasa abin cewa nayi kawai sai nahau muzurai tare da yin shiru,can sai naji na fara ajiyar zuciya alamar raina ya fara baci ,dakar na iya jan jikina zuwa daki aiko duk sai suka kewayeni suna bina da sannu bana iya amsawa sai daga musu hannu nakeyi kawai.
Bansan yadda akayi ba misalin karfe takwasa na dare naji ana guda ,zubawa hanya ido nayi naga nan za,a shigo da amaryar yar ko ina,har kusan mintina ashirin banji motsin shigowa ba sai hayaniya da nakeji ta cikin shagon ,gulma nacina haka na tashi na dan leka cikin shagon.
Abin mamaki katifa ce kwance akasa gefe daya amarya ce ta sun kuyar da kanta kasa,sai wasu akwatina alamar dai nan aka kawo amaryar gefe daya kuma sai Yan kawota da sukayi kungiya annayin kus kus.
Tar kata yarana nayi muka rufe gidan sannan muka hadu daki daya muka kwanta .
Ni dai ranar bacci sai barawo lallai na yarda shidai kishi sunansa kenan dole kuma duk kau da kanka sai ya biyoka har makwancinka.
Dake alhamis ce ranar muna ta sauri zamu tafi makaranta dan munkusa makara sakamakon rashin samun wada taccen bacci danayi ,haka natashi idona ya yi luhu luhu.
Har munzo soro ina kokarin kulle kofa sai nayi karo da mace cikin lillibi ,gaisheni tayi cikin mutunci nima da sakin fuska na amsa.
.bayan nan ne ta ke cemin ita ce amaryar da aka kawo shagonnan jiya,ta ke cew na yi mata alfarmar shiga bandaki,take cewa cikin toilet din shagon babu toilet seat a ciki ita Kuma tana son yin tsuguno ne .
Na ce kinganni kuma aiki zan futa na riga na makara sai dai ko ki leka makota,ta ce kiyiwa Allah na shiga minti biyar ya yi yawayanzu Zan fito,gaskiya kina batan lokaci ki dan shiga gidan da yake jikinnan, dan ko ba aiki zani ba bazan iya bari kishiga ciki ba,dan haka kiyi hakuri kawai.
Har ta juya zata tafi na ce da allah kice wa mijinki matar gidannan tana tsaye ta na jiransa ya sallameta zata futa aiki, bata ce komi ba tashige ta yi tafitarta.
Dan 'kwan'kasawashagon nayi nayi ta kofar soro" zuro kai ya yi yana me sunkuyar dakai dan yama ki yarda mu hada ido .
Ban nuna masa nasan ya kwan da amarya ba kawai sai na ce barka da safiya, dama zan tafi ne najika shiru shiyasa hakkina zaka bani in tafi.
Karimatu babu wata magana me dadi sai wannan ,ke meyasa yanzu duk kin sauya ne ; kiyi hakuri haka mana.
Kaga ni dai zan wuce in bazan samu ba ma hadu a gaba ,janyo ni yayi ya ce dawo ki karba.
Naira dubu daya yadakko yabani kamar yadda yasaba.
Da dan yatsa biyu na rike ta Ina kadawa ,na ce kasan allah zamu koma gaban sarki na gaji da wannan dubun baka ganin yaran sun kuma girma hajiya ma dab take da dawowa dan haka kayimin lissafin abinda zaka dad'a mana dan wannan Karan matakina sai yafi na baya.
Dari biyar ya dakko ya Kara min ya ce to haka ya yi?
Farrrr na yi da ido na ,na ce ai kafini sani kaga tafiya ta kadai samar wa kanka masa laha kan na fito maka da d'aya kalar tawa.
Sannan inason fara karbar kudina wannan watan dan naduba nagani filin daka siya kudina sun nin kashi uku a kanka ,dan haka na shirya kar bar hakina ko kuma mukoma gurin mahukunta.
Kuyi hakuri mun kusa dire labarin mu karasa nima na kagu in kaishi karshe.
*INA BUKATAR COMMENT DINKU INHAR KUNA SO INCI GABA*
π€ *DAGA ALKALAMIN YAR MUTANAN JINGAU* π
[17/03, 4:59 PM] Yar Mutan Jingau: *Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
*π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββ__
π³π³π³π³π³π³
π *ABINDA KE FARUWA* π
*_PART 2_*
*LABARI DA RUBUTAWA*
*BY*
π€ *FAUZIYYA AUWALU ALIN BABA JINGAU* π
*π
Ώ73(U FOR TURNED)*
*πKAINUWA WRITERSβπΌ ASSOCIATION*π€π»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
Amarya dai ta gaji da zaman shago,domin nafara jiyo hayaniyar su, da alama kuma bazata jureba, saboda babu abubuwa da yawa da ta ke bukata aciki,daga gareshi ma baki daya.
Yau asabar muna kitchen Muna hidimar Karin kumallo nake jiyo sautin tafiyar takalmi ,daga baya kuma na ringa Jin ana doko sallama, kullin kosan dake hannu na na ka ra sa sakawa cikin sauri na rage karfin gas din , sannanna fito Ina goge hannu na.
Tsaye na yi ki kam ganin wacce tashigo min,batare da na ce komi ba bayan amsa sallamar da na yi na rike kugu Ina kallonta .
Murmushi ne dauke a fuskarta ta ke gaishe ni ban nuna Mata komi ba na amsa ,da alama kuma gurin zama ta ke nema, na ce Ina fatan lafiya ko; ta ce i lafiya, na dan shigo ne mugaisa, sannan dan allah alfarma nazo nema gurinki.
Na ce amma nake ga kidan jirani na karasa saka kosai ,ita me tayanin aikin zai mata yawa kiyi hakuri ko anjima Kya dawo ko kuma ki jirani in gama in bakya sauri.
ta ce bakomi bara in zauna a kujera in jiraki, kujera Yar tsugune tajanyo ta zauna,ni kuma na koma ciki na cigaba da hada Karin kumallo.
Bayan na tattara Yara na ne kowa na zuba masa kunu da kosai suna karyawa, sai na debi wani a dan flat ,na zuba kunu cikin jug na mika mata na ce gashi ta tafi dashi,
karba ta yi tana min godiya,na ce ina sauraronki Allah yasa lafiya?
Cikin sakin fuska take cewa, dan allah ina neman alfarmar na bude kofar soron gidan nan yazam tanan zan ringa sabgata ,domin zaman a shago bashida amfani ,yariga ya Muna funceni ne tin farko ce min ya yi ya na da gida, daga baya kuma bayan an daura aure ana shirye shiryen kai kaya sai ya zo min da labarin yin hakuri gare ni wai in zauna a inda ya ke kwana kafin yasami gurin da zamu zauna, na kuma tamba yeshi dalili ya ki yi min bayani ,na dai hakura na zauna kan inga in da allah zayyi dani,na kuma yi kokarin ya zo gurin me gidan ya roka mana cewar mu bude kofar soro kan musamu gurin zama ya Yi min shiru, shine yanzu daya shiga wanka na leko da kaina, dan allah kuyi mana alfarmar hakan.
Shiru na yi Ina tinani,wato bai ma nuna mata mudin suwaye din saba lallai zan yi masa kwaba yau dinnan.
Hannunta na kamo na hagu ina kallonta ido cikin ido,na ce me gidan ki bai gaya miki ko mu din suwaye a gareshi ba?
Ta ce bai ce min komi ba ,na dai tamba yeshi sau daya da naga kullum sai kin yi masa magana kafin kifita.
To me ya ce miki?
Shiru ya yi min bai ce komi ba.
Na ce to ki tashi kije, babu wannan damar ta bude min soro ,domin nidin sarki ya riga ya raba mana hanya yin hakan saba umarnin mai martaba ne,amma kisan wannan domin naga alamar kin sakan kance da da namiji, kedin karki zurma da yawa kiyi ta katsan tsan ,sabida kar wataran kiyi dana sani,ki yi kokarin barin shagon nan dan naga kamar kin shiryawa zaman nan din,in kinje kuma ki gaya masa yafara ai komin da sakona, na hakkin da ke kansa, in ba haka ba kuwa zamu gamu a gaban sarki.
Bina ta yi da kallo". sannan cikin mutuwar jiki ta ce kiyi min alfarmar sanin *ABINDA KE* *FARUWA* ban gane zancen ki inda yadosa ba?
Ba lallai kiji mutuwar sarki a bakina ba ,ni dai na doraki akan hanya kije kawai zan shiga ciki.
Ta ban garen amarya kuwa ,cikin daurewar kai ta dauki kununta da kosai ta futa!sanda ta shiga cikin shagon ya futo daga wanka , turus ta yi ganin irin kallon tuhumar da ya ke mata" kayan hannunta ta ajiye ba tare da ta zauna ba ta ce ,sako daga matar gidan nan ta ce ka fara biyan ta hakkinta da ke kanka, kafin ku koma gaban sarki.
Au ban ce miki ba ke ba shiga cikin gidan nan ba; na ce ki yi hakuri cigi yar gida na ke so in sa a nemo min muku ma,babu ruwanki da ita, ki kame kanki gu daya bana son shige shige.
Ai ko wallahi bazan dinga zama cikin shagon kamar muna fuka ba ,babu wanda ya isa ya hanani zuwa in da na so, dama dai cikin gida ne sai in ta kaiwa Ina kawowa amma ka saka ni gu daya kamar wata yar bursin,kuma ina son sanin dan gan takar ka da mutanan gidan; me ye hadin ka dasu ;dan naga kamar gaba ce a tsakanin ku me girma, dan haka sai ka sanar dani ,dan kar in saki jiki dasu kuma daga baya na zo ina danasa ni.
Baki da ruwa da sabgar su dan haka kawai ki bar maganar mayi ta gaba.
Jug din da ta a jiye ya kaiwa dauki"ya ce kunu kika samo mana; bara na tsiya ya nasha ,dama ba son shayin nan nake ba, da allah kidan ringa sabun tama na abin kari kullum ke kenan abu daya.
Harara ta maka masa" ta ce ni ma ai bason nasa nake ba ,dan ba yarda zanyi ne ,ka kawo kayan amfanin mana kaga in ban yi maka ba,to aike kinji ki daga an yi magana sai kice sai an bayar zakiyi ke kodan tema konnan na miji baki iya ba.
Sabida me ko zan iya shi, ka ganni nan naira biyar dita bazan iya taima kawa miji da ita ba, balle inje in kwashi kashi na a hannu domin nayi banji da diba ,dan haka in kana iya zama dani ,ka kula dani kamar yadda miji me zuciya yakeyi to ,in kuwa baka iyawa, tofa ni ko da ko ka wa ne sai na karbi hakki na, bar ganin kana bani ina kauda kai na ,na bakunta na ke yi maka .
Mamaki ne ya rufe shi, domin bayyi tsammanin haka daga gareta ba,a yadda yake tinanin ta ko zata yi rashin kirki bazata fara shi yanzu ba .
Kawar da kansa ya yi bai kuma cewa komi ba, ya bude jug din zai sha kunun ,bata ce komi ba ta dakko kofi ta tsiya ya masa ,ita ma diba ta yi tana kokarin saka hannu ta ci kosan ai ko baki bude ta ke kallon sa ,janyewa ta yi ta ce in kana so ka siyo mu ma muyi ,yaza,ayi na shiga an bani kacinye min! kalli fa saura guda hudu a ciki abun yafi goma amma dan rashin tausayi kacinye min .
Ya bude baki zayyi magana kenan, ya ji ana knocking din kofa,da saurin sa ya mike har ya na hada hanya.
Turus ya yi a bakin kofa .
Karimatu ce ta ce zan iya shigowa?
Cikin kas da murya ya ce kiyi hakuri in na futo zan shigo sai muyi magana.
Kashigo Ina; gidan da mace ta ke ciki ba miji ai sai kasa a fara zargin ko na fara shigo da maza gidan, ko karin shigewa ciki na ke yi ,shi kuma sai babba ke kofar ya ke,a in da ya ganni yasan komi zai iya faruwa, domin a fusace na ke,matsawa baya ya yi na sami hanyar shiga.
Da murnar ta ta taso ta na yi min la le ".ashe kece sannu kara so ki zauna.
Bayan nasami gurin zama ne, batare da na bari min gaisa ba na ce "dazu matar ka taje min da wani zance na zata bude kofar soro domin bukatar ta sami gurin da zata sitir ta kanta, sai na Yyi mamaki ganin alamun baka yi mata bayanin yanayin mu,amalar dazamu yi tare ba, sannan na kara Shan mamaki ganin baka sanar mata da cewar ni din da iyalaina ko su waye dinka ba,ko da ya ke wannan damuwar ka ce, abinda ya kawo ni shine ina alkawarin mu ; sannan term ya taho gan gara yara suna bukatar kudin makaranta , uniform dinsu ma ya tsufa ya kama ta a sake musu , sannan Ina bukatar kudin mota dana magani zan kai nana khadija asibiti na ji jikinta da zafi.
Jigum ya yi ya na kallonna, yama manta da wata amarya a gurin ,can yasaki a jiyar zuciya ya ce "haba karimatu na ,ban san wannan a cikin karancin ki ba ,duk kan ki gayamin kin yi komi kiyi hakuri mu dai dai ta ,bazan juri abu buwan ki ba, ki manta da komi ki yafe min .
Nifa maganar kudina na ke maka ba zan cen shirya wa ba , sannan maganar yara suna bukatar abubuwan dana lissafa maka.
Zanyi kokarin yi insha allah, kiyi hakuri mu zauna muyi sulhu ,kinga sabida ke hajiya ko gaisuwa ta bata amsawa,jiya ma dana je cewa ta yi yau zata dawo gidannan ,amma kar in sake taga kafa ta a gidan da sunan naje gai sheta, ki yafe min nayi nadama.
Kabar wannan zancen mu dora in da muka tsaya,karshen watannan zan fara karbar kudina, dan haka sai ka gaya min nawa zaka dinga bani duk wata,mikewa na yi na ce na barka lafiya,waiwayo wa na yi na ce baka ma sallame ni ba zan tafi.
Hawaye nagani yana zira rowa ta idonsa na hagu ,dauke kaina na yi na ce amarya ban ma tambaye ki sunan kiba?
Leben ta ta cije ta dago Kai ta kalle ni ,ta ce na fahimci abubuwa da dama a gareki na kuma fara daukar darasi sosai, sai dai dake naga wasan kamar ni zan kwana a ciki ,dan haka a fito fili a gayabmin kome akwai, in ba haka ba kuwa zan kai gaba, gurin manya, domin naga kamar haduwa ta dake yana min nuni da ni din ban gama sanin kaina ba ,dan haka ki yiwa allah ki gaya min *ABINDA KE* *FARUWA* ko zan futa daga kokwanto.
Nayi yar karamar dariya na ce, ina son mutum mai saurin fahimta ,na kuma sara miki ,don in wata ce ba zata nuna dakiya irin wacce kika nuna ba ,dan haka ina mara ba dake,ki saka mijinki a gaba ya gaya miki koni din wacece, sannan ki gaya masa ya biya ni bashi na da ke hannunsa ,sannan ya sake halinsa in yana so mu dai dai ta kamar yadda ya ke bukata, ni kuma sai inyi tinani gurin karbar rokon sa,dan babu dole cikin al,amarina yanzu.
Bayan futar karimatu ne daga shagon amarya ne,sai kambun da bai san ta na dashi ba ya motsa, domin wata irin damka ta kai masa tare da cin kwalarsa ,ta ce na rantse in ka mutu na suma yau asirin ka ya tonu ,kana yimin munafunci bazan lamunci hakan ba ,ni ba tam-badaddiyar mace bace,bana