ABINDA KE FARUWA HAUSA NOVELS BY YAR JINGAU

Author :  Yar Jingau Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   30 / 31

87K to 90K   out of 92.1K words

daukar rainin hankalin namiji dan haka wallahi ko ka gaya *ABINDA KE FARUWA* ko kuma yanzu in yi maka tijarar da kowa zai zo ya kalle ka.

Dauke ta da mari ya yi, ya ce dama baki da mutunci; ni zaki rikewa wuyan riga ,bazan gaya miki ba, ni nake auren ki ,ko ke kike aure na?

mara mutunci futsa-rarriya ,dama haka kike to ni tinda na ke da mata ta bata taba yi min wannan rashin da,ar ba ,hana ran tsuwa sai sana din kine ta riken riga ,ke ni wannan auran ki ma me na fara karuwa dashi in banda ci baya ,yau satin ki nawa cikin gidannan amma babu wani jin dadi da na fara fuskanta, kullum neman kure ni kike, in abinci na bayar ki dafa sai kinyi korafin bazaki dafa ba babu kaza babu kaza ,dan haka duk abinda zakiyu sai dai kiyi.


Ai ko ta tafa hannu tare da shewa ta ce na gane ,nagane ka, wato matar ka ce ko ; matar ka ce kake zaune gidanta shine ta koroka sabida zaka aure ni ,shine sabida kai din baka da zuciya ka fake anan, har da sakani a shagonta to wallahi bazan zauna ba ,daman hakuri na na meye ;na kar a fara kir gan aure ne,to an dade ba,a kirga ba, dan haka ko ka sake min gida ,ko kuma nayi gaba, na baka wata guda ko in san inda dare ya yi min.


Kallon mamaki kawai yake binta dashi,domin bakin magana ya dauke masa, mutuka ta bashi mamaki,bayyi zaton haka ba kallon me hankali ya ke mata ,dan in aka kalleta zaka yi zaton ko hannu kasa mata baza ta ciza ba, before ya aure ta ko ido bata fiya yarda su hada ba,ashe boye masa halinta ta yi.


Ita ko karimatu ji ta ke kamar salla babu abinda yadameta.


Yau din ko hajiya ta dawo gidan , amma ko kallon shagon amarya bata yi ba ,sanda ta dawo ba karamar murna mukayi nida yara ba ,ita ma ta ji dadin yadda ta zo ta same mu babu wata damuwa tare damu, har take tambaya ta yadda komai ke tafiya ,ban boye mata ba har abinda na yi Wanda bata sani ba sai da na gaya mata,ai ko tasha mamaki ,ta ce nagode miki da kika bi dashi ta haka gaba kinga yashiga tai tayinsa,.


Bayan dawowar sa daga kasuwa ne ,ya yi ta ko karin shigowa gidan amma ya dinga fargaba, domin yana tsoron shigarsa, gargadi biyu ya ke tinawa, gana sarki, gana hajiya ,ji ya ke kamar yadanna kai amma fargaba ta isheshi, bai taba jin nadamar abinda ya yi wa karimatu ba sai a Yan kwana kinnan ,tabbas ya shaida ya zalun ceta ,san zuciya ne kawai irin nasa ,yasan in bai nemi sun dai daita ba tabbas bazai karashe rayuwarsa da salama ba ,yasan karimatu ce rayuwarsa babu wata diya mace da zata iya jurar hali irin nasa, sai ita din da allah yadorawa, kuma gashi ya yi mata butulci dole yasan bazai ga dai dai ba.


Wasu hawaye ne sirara suka zubo masa ,yasa hannu ya share ,da karfin gwiwarsa ya tura kansa gidan ,ko sallama bai yi ba ya tura kansa dakin karimar ,ita kadai ce a ciki yaran suna dakin hajiya .


Juyowar da zatayi tayi kicibis dashi ,taji tsoro ko sosai ,dan batayi tinanin haka ba ,numfashin ta ne ya yi sama har sai da tayi baya zata fadi ,taro ta yayi tare da zaunar da ita bakin gado.


A hankali ta dinga samin nutsuwa kafin daga bisani ta dago kai ta watsa masa idanu,jikinta tajanye baya, ta ce kamanta ne,kamanta nan din ba gidan iyalin ka bane,kamance nidin ba muharramarka ba ce!

Tinda ta fara magana idonsa yake zubar da hawaye ,har takai zancen ta bai ce komi ba, ammafa yashiga taibtayinsa, domin ruko yayi mata na sosai har sai da tayi shiru sannan ya yi kasa da kansa ,ya ce karimatu kiyiwa allah kiyi hakuri ki yafe min abinda nayi miki"na yi nadama ba yar kadan ba, nasan nayi miki butulci ba kadanba ki yafe min bazan kara ba ,zan dawo miki yadda kika sanni, koma fiye da haka ,ban san me yashiga kaina ba har nayi miki butulci, karimatu dake nake kiyi magana".


Shirun ta kara yimasa tana kokarin jan ye hannunta daga rukon da yayi mata.

Ya ce na rantse zan kwanta a kasa ki takani sabida nadamar danayi, kiyi min hakuri mu dai dai ta auranmu: wallahi bazan karaba, kibani wannan damar kigani ,in ki ka ce ma na sake ta bazan musa miki ba, na yarda zan rabu da ita dan in faran ta miki.



Uhmmmmm sabida me zance karabu da ita kamar wadda batasan ciwo da zafin da namiji ba.

In har nadamar ka ta gaske ce zan yarda muko mawa auren mu ,ammafa da sharadin sai kagama biyana kudina da suke kanka sannan zan iya yadda da kai.


Baki yarda da nadama taba kenan; na rantse miki zan shiga dashi saboda in biya ki kudinki kar ki 'ki yarda dani ki bani wannan damar.


Haka dai ya dinga lallabani har sai da muka shirya ,agurin kuma ya yi furucin ya mayar dani ,ammafa ban yadda ba sai da na kafa masa dokokin da nasan ina cutuwa cikinsu ,har mukayi yar jejeniyar ko menene banaso zai kiyaye su,sai batun amarya kuma na ce masa yasan inda zai kai abarsa ni gida babu mahallinta dan bani da in da zansa yarana ciki bare ta shigo in da na ke,na dai bashi shawara cewa ya nema mata gurin zama domin shago babu mutuntawa cikinsa.


Gurin hajiya mukaje mukayi mata bayani ,ta Kuma yi murna da shiryawar tamu ,har ta kara yi mana nasiha kan zaman takewa, sannan ta kara masa da rikon amana dan wannan sakin dayayi min, shi ya ke nuni da cewar amanar ta yi masa karanci.



Sanda ya ke yiwa amarya bayani wacece karimatu a gurinsa da kuma muhimmancin ta gareshi,aiko ta yi tsalle ta dire ta ce bata zama, sabida shidin ba iya rukon gida zayyi ba har ta kara da cewa mutumin da bai iya rike mace daya ba macen ma wacce ta yi masa halarci har zai je ya dauko wata ya hada da ta gida wacce ita take rukon kaso saba,in na gidan a cikin dari ,dan haka baza ta zauna ba ,dan ma shidin lala taccen mijine har sai yadda mace takeso za,ayi in ba tsoronta ya ke yi ba ya bata daki daya mana cikin gidan.


Aiko ya ce wallahi duk in da zata sai dai ta je ,in har baza ta bi maganar da ya ce ba,har yaushe muka hadu da ke da zaki yimin dibar albarka; in zaki zauna a nan ki zauna, tinda ai ke kika ce kinji kin gani kafin allah ya sa asami wani gurin.


Filin taron kowa ya yi tsit an zuba mata ido, duk kuma wanda ka kalla kallon ta ya ke da tausayawa ,shiko shu,aibu ya yi wiki wiki a gurin, gashi dai bakowa ne yasan shiba ,amma ga ni ya ke kamar kowa kallonsa yake.



Tace to kunji *ABINDA YA* *FARU* a cikin rayuwa ta, ko in ce a cikin rayuwar mu nida yan uwa na .


*INA BUKATAR COMMENT DINKU INHAR KUNA SO INCI GABA*


🀝 *DAGA ALKALAMIN YAR MUTANAN JINGAUπŸ™‹*
[17/03, 4:59 PM] Yar Mutan Jingau: *Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€__



😳😳😳😳😳😳



πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™


*_PART 2_*

*LABARI DA RUBUTAWA*


*BY*



🀝 *FAUZIYYA AUWALU ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹





74


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________**Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€__



😳😳😳😳😳😳



πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™


*_PART 2_*

*LABARI DA RUBUTAWA*


*BY*



🀝 *FAUZIYYA AUWALU ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹





74


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________**Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€__



😳😳😳😳😳😳



πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™


*_PART 2_*

*LABARI DA RUBUTAWA*


*BY*



🀝 *FAUZIYYA AUWALU ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹





*πŸ…Ώ74V FOR VERY)*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*__________________________ta daya gefen kuma sadiya ce" ta ke share hawaye ,domin labarin ya tsumata har ta na tinanin lallai ta riga ta gama tafka kuskure cikin rayuwar ta.

Ita ko ameera" tambaya ce cikin ranta kuma ta na da burin yi kafin atashi daga taron ,domin a Kara mata haske.

Har yanzu dai idanunta futar da hawaye su ke yi ,domin ta ruga ta tsokano miki da ya kwana biyu gareta ,dago kanta tayi ta sake kallon mutanen da ke gurin, ta ce kuji tsoron allah kuyi mana adalci a zaman takewarmu, mudin raunimu ya kai "domin allah ne ya ambace mu da haka mu masu rauni ne ,kuma zaluncinku kullum yawa yake gare mu,uhm waifa ni da sauki cikin lamarina, domin Ina da abinda ya ke tallafa min ,to ya kuke so mara abin yi tayi;ya kuke so ta kai rayuwarta; sai an wayi gari an ganta cikin mugun hali sai a ce za,a zageta waye yajanyo?

waya ja mata shiga muguwar hanya,nasha ycin karo da mace da yayan ta sun shiga kasuwa, ko gidajen mutane ,ya yan na dakkowa ita kuma na karba,in banda kun sake mu a titi taya ya hakan zata yiwu ace uwa ce take koyawa diyoyinta sata.


Dan allah ku gyara ku dauke mu da muhimmanci,sai komi namu yazo da sauki.

Sai kuma wani abu guda garemu mata, mu lura da wannan ,ke wacce kika sami dama ki ke wasa da ita" tofa ki kiyayi karshenki ,kina gani miji ko danginsa a hannunki, kice zaki yi abinda ranki keso ,kemafa wata ran uwa ce ,duk kuma abinda kikayi kema za,a yi miki.

kar ki damu da Wai sai an yaba miki,a,a irin wannan keda ubangijinki ne, kiyi komi dominsa.dan haka mudena wasa da damarmu muyi amfani da lokacinmu cikin aminci sai kuga mun wanye lafiya.


Jan hankali,da kuma muhimmin abinda ya taramu a nan .gareku mazaje mun sako kune cikin taronmu domin kusan *ABINDA KE* *FARUWA* garemu a gida janku,tofa mun kai makura ,mun kai karshe ,tin muna yi muku biyayya har kun kaimu matakin da muka fara
fito na fito daku.

Dan haka ki bamu goyon baya ,mucigaba da yi muku biyyayya, mu zauna bisa sunna yadda annabi ya bamu umarnin muyi rayuwar aure gareku.


Ku din kune jigo" kuma dole ne muyi muku biyyayya,domin andllah da kansa ya ce da da akwai wanda zai bada umarnin ayiwa biyyayya tofa ba kowa bane sai miji,kunga kenan matsayinku daban yake kudin dole mu saddakar gareku, muyi biyyayya gareku.


Ta yaya zamuyi :bayan duk wata kofa ta girma da allah ya baku,kun banzatar da ita ,kimar ku garemu kun watsar ,baku yarda mu samu aljanna ta dalilinku ba ,kun mayar damu sha sha shai ,marasa kima da daraja,mun gama cin wuya kar kashinku, sannan bamu samu mun muku biyayya ba saboda taurin zuciyar da kuka saka mana ,idanunmu sun bushe gareku ,bama ganinku a matsayi me girma ,bayan munyi wannan rayuwar sannan mu mutu kuma babu results me kyau,babu sakamako me kyau na bautar auren da mukayi.


Hannunta ta hade guda biyu idanunta na tsiyayar da hawaye hancinta ko sai kyalalar da majina ya ke !!!ta ce na rokeku ku sarara mana ,mu nemi aljanna gareku,karku sa mu zo abanza ,mukoma a wofi,kun riga kun dimau tamu, kunsa mun futa daga hayyacinmu,har Muna kasa gane dai dai da kuma ba dai dai ba.

komi yi muke gareku ,in dai muna ganin zamu sami yancinmu gareku ,dan haka kuyiwa allah da ma,aikinsa mu zauna lafiya.


Ni ko yar mutan jingau ikon allah kawai nake gani ,domin ana cewa maza taurin zuciya ce dasu ,yau to naga hawayensu a bagas ,domin kowa ka kalla hannunsa bisa idanu yana goge guntun hawaye,muko mata da ke rauninmu yawa gareshi har da masu shekar majina sabida kuka ballen tana ko wacce akwai abinda ke damunta.



Dago kanta ta yi saka makon hankicin da rukayya ta ke miko mata,hannu tasa ta karba ta na goge idanunta!


Ban garen mata kuma ta kai idanunta, tace gare ku ma,a bota hakuri.

maganar guda biyu ce, ta farko dai bazai wuce kara jan hankali ba, wannan kokarin da mukeyi wajan kwatar yan cinmu kar yazamto muna yin tufka da warwara yazamto muna shigar da wani abu cikin wani abu.

Sannan kar kuga wata tabi hanya kaza tasami zaman lafiya gidan aurenta, kuce lallai tanan zaku bi domin kusami salama.

A,a kowacce halin mijinta daban sai kuma an bi komi sannu sannu sannan ake cimma gaci.

Abinda na keso na nusarmu shine,mu gane wani abu ,tsakaninmu da mazajanmu ,kowa daga cikinmu akwai hakkin da allah ya dora masa ,kar kiga bai dauke nasa da alla ya Dora masa ba, kice kema zaki tau yeshi, ko kuma kice ni bayyi min ba nima zan rama ta wani gurin ,a,a ki kiyaye kuma ki tina da wannan, in mun mutu an tashi hisabi baza,a ce hakki ya wakilci hakki ba, dole kowa da abinda yayi za,a tuhumeshi,
Baza,a ce tinda bai sauke nasa hakkin ba, to kema kin rama da rashin dauke hakkin da allah ya dora miki ba,dan haka sai munsa lura cikin yin komi.

Cikin kungiyarmu" muna bada shawarwari mafi amfani ,tare da neman yanci ,amma fa bamu yadda kowacce ta ce zata taka dokar ubangiji ba, kodan goben mu ta yi kyau.

Dan haka sai mun saka lura cikin zaman takewarmu,muyi kokari gurin nusar da abe ba dan debe kewarmu ,(wato mazajanmu)in sunji tsoron allah sun gyara ,zasu gani a gobe kiyama da kuma duniyarsu, na biyu kuma muma akwai abubuwan dake janyo mana haka tin farko ,inda zaku kutsa cikin labarina "ko labarin nafisa" ko ramla" ko rukayya" kai da duk wata wadda muka saurari *ABINDA KE FARUWA* gareta kusan abin a bayyane yake, a kwai san zuciya ciki ko garemu ko kuma garesu su mazajannamu,dan haka ko wacce cikinmu sai tayi karatun ta nutsu taga me yafara haifar mata da tata matsalar inda yiwuwar gyara sai a gyara ,in kuma babu dama meye jigo addu,a mika wuya komi ya yi zafi maganinsa allah, shi ya halicce mu "shi zai bamu mafita" mukai kukanmu gareshi "zayyi mana hisabi tun anan duniya.



Shiru ne ya biyo baya, gurin ya yi tsit, bakajin motsin komi sai numfashin jama,a.


Taf taff tafff abinda kunnan kowa ya fara juyowa kenan,aiko sai gurin ya dauka kowa yahau tafa mata .


Ido ta kura masa, shima ya zuba mata nasa ,mikewa ya yi yana tahowa gareta ,a hankali yana cewa lallai kin can canci komi a duniyata ,kece idaniyata ,idaniyar da ke nuni ga kuskuren mutumin da ya saba mata,ma,a bociyar yafiya lallai baiwarki yawa gareta ,nasan ki da karamci gareni, ashe karancin ba a guna ya tsaya ba, har mutanen gari nacin moriyar bai war da allah ya yi miki,ke din tauraruwa ce cikin taurari ,yadda kullum kike kokarin inganta rayuwar al, umma ,na fito gareku mutane ,ku shaida wannan, tin a duniya na daga kafafuna karimatu babu mugunta tsakani na da ita ,aljanna babu ko konta ta bangare na, ta shige babu take kafa gareni har sai takai inda ta ke so ,na gode da karamcinki gareni.



Babu komi dauke a fuskarta sai farin ciki ,kuma hakan ya burge mutane dayawa, domin sun dauki wani karatu da suka dade da mantashi, lallai ana tafka kuskure , lallai kuwa in ba,a gyara ba tofa rayuwar za,a yi ta ne cikin nadama da danasani.

Haka aka bawa kowa dama in yana da abin cewa ya tofa .


Da yawan su in sun tashi yin maganar, jin jinawa al,amarin sukeyi ,sannan kuma su kara jan hankalin mata gurin kwatanta juriya da hikimar da wannan baiwar allah ta yi cikin rayuwar auren ta,sannan suka ringa neman yafiya ga ma,abota rayuwarsu dan sun san akwai kuskure sun yishi sai dai allah ya yafe mana baki daya.


Daga karshe ne ameera ta tashi ta watso tambayoyin da kowa yake son jin karashensu ,tace shin ina labarin amarya da kuma hajiya uwar arziki; wadanda irin su sukayi karanci cikin al, umma, me hali irin na ummana ya labarin ya ke Ina son inji karashensa.


Murmushi karimatu tayi, ta ce labarin amarya bansan yadda ta kasance ba ,domin nawayi gari bata shagon gidan, kuma duk tambayar da nayi domin kawo gyara yaki ya yi min bayani, bare in san halin da ake ciki,sai da aka kwase kusan watanni shida, lokacin da muka tashi da mugun yanayi na rashin hajiya, Hajiyata mutuniyar kirki ,wadda duk halin danake ciki ita tazame min uwa, ban taba zuwa nakai karar mijina ba domin Ina da hajiya ,babu wanda yasan halin dana shiga sai ita ,ita ce ta nuna min hanyar da zanbi domin samun masalaha,sai gashi nashiga gaisheta da safe ,a tsammani na ta yi sallar asuba ta koma bacci,carbi nagani a hannunta alamar lazimi takeyi rai yayi halinsa.

Mun shiga dimuwa ba kadan ba ,rashine na yishi ,wanda bazan maida gurbinsa ba cikin sauki.
amarya sun sami labarin rasuwar sukazo min gaisuwa, anan nake samun labarin ya dade da rabuwa da ita ,na ce ta yi hakuri hankalimu ya dan kwanta sai agyara komi in bazai gagara ba,ta dayyi dariya sannan ta ce ni ai an sake daura min aure, ko banyi aure bama bazan iya auren irin mijinki ba ,to kinji yadda ta kasance.

Sannan kuma tin daga sannan ban sake fuskantar wani bacin rai ta bangarensa ba, wanda ya yi kama da halin dana shiga a baya,sai dai dake dan adam ajizi ne, amma komi yana tafiya yadda ya kamata, kuma duk wani abu da nake binsa ya cika alkawari ya biyani,cikin amincin allah, ya kuma dauki dawainiyar da allah ya dora masa, sai dai dake lamarin rayuwar ko ta Ina ana bukatar taimako ,ta bangaren ciwo na kuwa ba sosai ya ke tashiba dan nakan dade bai waiwaye niba .

Tabangaren sadiya ko dai gashinan yanayinta babu yabo ba fallasa, domin ta dauki darasi sosai ,sai dai kuma nadama ce ta keyinta a sanda komi

30 / 31