Author : Yar Jingau Category : Romantic Hausa Novels
π
Ώ *9(I)*
π *KAINUWA WRITERS*
βπΎ *ASSOCIATION* π€
Asanda yasa kansa karatun asannan matsatsi Yakuma zuwa rayuwarmu.
Asannanne dukkanin yaran dake gabana suka girma Kuma kowacce tana bukatar abin amfani narayuwa danma wani gida dake daura da gidanmu sun nemi da nabasu yarinya daya taringa zuwa tana Mata dan aikace aikace sai nagayawa megidan ,
Babbar cikinsu wacce take da hankalin sosai ita take zuwa aikatau din da haka muke rage wasu abubuwan Dan matar gidan takan bata Yan tsummo karanta dasu suke da yin gayu ,
cikin amincewar Allah komai ke gangarawa shi Kuma sabo yakan je yayi turin ruwa akalla kullum yakan Sami dubu daya ita Mike tarawa har Allah yasa akasami kudin registration sai ga sabo yafara zuwa University intakai cemuku dai ahaka yayi karatunsa in Yana da lakca yakan hakura da turin kurar sai ya Sami interval sannan yakeyi cikin amincewar Allah ya kammala a hankali cigaba Yake zuwar Mana domin yanzu duk na airar da yaran dake gabana daga mardiyyar har yayan malam tankon danake aure.
asannan Kuma dukkanin wani cigaba yakara zuwarma na dan wuyar da mukaci da yan zun alamu sun nuna muna dad da ketaresu domin sabo yasami aikinyi bakuma nagwamnati ba wani iyamurine yadauke shi Yake kular Masa da kantinsa cikin aminci suke zaune in lokacin tashi yayi kullum Yana bashi dubu daya ga taimakon dayake Masa na sutturu da abinci basuyi shekara biyu ba yafara yimasa zancen sallama .
Yace lokaci yayi dazan sallameka kaima kazama ubangidan kanka akwai kudade danake tara maka kullum inkatashi daga tsarin shago sannan akwai alherin dazan maka domin naji dadin Zama dakai Kai me amanane baka cutata.
Sanda zai sallameshi million biyu yabashi da mota sannan ya zuba Masha Kaya ashago yace yabashi halak malak.
Zokuga umma ranar har suddaja tayi saboda godiya ga Allah .
Aiko kudin dayake tarawa yadakko yase katon fili,
Inda kudi akwai aiki gini yayi amma bai gina gaba dayaba sai yaginawa ummansa iya gun da zata zauna kafin Kuma acigaba , ranar dazasu koma gidan suka tashi da mummunan zance domin gawar mlm tanko akashigo musu dashi ansami wani yabugeshi ya gudu.
Banida caji kuyi hakuri da wannan.
*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA*
*DAGA* *ALKALAMIN YAR MUTANAN JINGAU*
π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββ
π¨π¨π¨π¨π¨π¨
π *ABINDA KE FARUWA* π
*LABARI DA RUBUTAWA*
*BY*
π€ *FAUZIYYA AUWALU* *ALIN BABA JINGAU* π
π
Ώ *10(J)*
π *KAINUWA WRITERS* βπΎ *ASSOCIATION* π€
Sunyi kuka sunyi jimami domin sunyi rashi yatsare musu abubuwa da dama Musamman dayakasance yana tare dasu ya maye musu gurbi dayawa Wanda ko danginsu dasuke dolensu basuyi musuba walau na uwa ko na uba dan sanda yakamata su rungumesu bawanda yake lura dasu ko ta tarbiyya bare na abinda zasuci malam tanko yasha sasu suje su gaida dangin nasu amma ko sunje sukan nuna dasu da babu duk daya .
Bayan anshare makoki da mako daya suka tare agidan kafin sutafine tayi magana da dangin malam tanko akan zaman yaran gurinta to dake sudin sunsan yakamata daman ko lokacin da matarsa ta rasu sunso daukarsu shine dai yaki haka suka tattara yaran suka tafi dasu .
Tayi murna tayi farin ciki bata taba tinanin samun sauyin rayuwaba sai gashi Allah ya musanya Mata da mafificin alherinsa domin duk inda tarbiyya take tsakanin sabo da mardiyya sunsameta sannan ga wannan tagomashin da Allah yayi musu .
basu ritsa shekaraba agidan mardiyya tasamu miji cikin kankanin lokaci akayi bikin batare da bacin lokaciba asannan shima taringa yimasa nuni da yayi kokari yasamo matar aure.
Yakance nifa umma ba yanzu zanyi aureba .
Sai tayi dariya tace toni dai yanzu abinda yaragemin kenan auranka nake fatan Allah ya nunamin .
Zanyi karki damu sonake sai nagama ginin gidannan gabadaya,
To ai wannan mesauki ne mezai hana gidanmu da muka taso kasashi akasuwa sai kakarasa ginin da kudin .
Bayan ansiyar da gidanne ya hada da wasu daga cikin kudin gurinsa aka karasa sannan ya zuba mata kujeru da Yan tarkacen gida .
Duk dai a runtsin Allah ya hadashi da wata yarinya sunje siyan Kaya gurinsa aiko tinda taganshi ta makale masa musamman data shi yaro ga kudi Kuma Yana juyawa shima Kuma dama ya kyasa.
har yafara zuwa gidansu zance tin anan tafara fuskantar irin matsalar dazata fuskanta akalla yaje zance kusan so biyar gidansu bakuma shi da hirar komai sai ta ummansa tin tana biye Masa har tafara Jin haushi takuma fara Jin tsanar matar .
Wata rana yazo yake ce Mata tashirya gobe zaizo suje ta gaisa da ummansa.
Aiko da misalin karfe biyar yazo ba bata lokaci suka tafi gidan
tarya hannu biyu umma tayi Mata tayi Munna da kawota dayayi ta Kuma yaba da hankalinta .
Sai dai kanta tafi sai ta fuskanci irin kallon wulakancin da sadiyar take Mata tare da taunar cingam na rashin kunya har wani hurashi take inyayi billi sai ta tauneshi haka zai bada Kara karasassss.
Bayan yakaita gida yadawo umman tasa yatarar tayi tagumi cikin dagin hankali Yake tambayarta meke damunta?
Ajiyar zuciya tayi sannan take cewa niko sabo wannan yarinyar ko tadace dakai ?
me Kika gani ummana?
Shima ya tambayeta ,
Nayi Mata kallon Mara tarbiyya da farko yarinyar ta kwantamin daga bisani nafuskanci kamar batada tarbiyya.
Murmushi yayi yace haba umma Allah lafiyayyi yace domin ko Ido bata yarda mu hada da ita karshenta shedanne danyaga kin yaba shine zai tinzira minke Allah ki kwantar da hankalinki batada matsala.
Ahaka aka cigaba har Allah yasa yaje gurin Yan uwan mahaifinsa yanemi alfarmar sukai Masa kudin aure sunso su hanashi amma da sukayimar kallon tsaf sai sukaga baya neman tallafinsu aiko jiki na rawa suka karba bai barsuba sai da yabasu har kudin mota tare da kudin dazasusa a aljihunsu sai ko aka hau kirarin addu,a ga mahaifinsa .
Murmushi yayi tare da yin sallama garesu ya koma inda yafuto.
Abinda Yake damun sadiya Bai wuce ganin mahaifiyarsa tarigata Shiga gidannan ba Tasha tsara rayuwarta akan ita kadai zata rayu da mijin ta Bata yarda da iskancinnan nadangin mijiba baza,a takura mataba tayi aurene Dan ta huta bawata Yar kwal
uba dazata rabesu bare azo a hana su walwala bakuma ta bukatar ko wace tace zatazo tashiga hurumin gidanta bare azo ayi Mata kafafar wanane kodan Yar babatane balle su uwar miji suji labari tamafi tsanar ace uwar mijin da zata aura tana raye karshen matsalar kenan in suna hira da kawayenta sukanyi shewa suce nifa uwar miji inda kikasan ciwon dan yatsa haka nadauketa, hhhhhh ke da sauki ma nifa da,ace Ina da uwar miji gara infasa auren ,Medan dama damance takance ni banida matsala da ita matsalar dayace ace tashiga hurumina tofa anan labarin zaisha banban .
dan haka suke da iko kana tare da mijinka cikin kwanciyar hankali sai kaji yace abinda yasa kikaga ban siya Miki ankonnan ba babatace take bukatar wasu kudi shiyasa to Kuma sanda Zan baki sai akasami akasi shine nabata kudin daxanbaki kidan jinkirtamin zuwa wani lokaci toko kunga ai akwai matsala ,shewa suka sake sawa tare da addu,ar Allah yarabu da ciwon ulcer Allah yasa ta kwanta dama Kan mu isketa.
To Kuma sai gashi ita gida daya ma zasu zauna
Inda ta lura Kuma baya hada babar tasa da komi dan ko maganar ta zayyi sai ya kwantar da muryarsa duk saboda girmamawa.
Ansha shagali cikin farin ciki amarya ta tare sungudanar da daransu cikin kwanciyar hankali Dan har makara sai da sukayi hakan Kuma bai hanashi kokarin tayar da itaba domin Shiga kitchen tare da jaddada Mata ummansa tana jiran break fast domin ya lekata da ya idar da sallah har sannan barcin gajiya take shiyasa yakeso kafin tatashi sai dai tatarar da abinci daga sirikarta.
Hakane yasa ta kullaceta domin yadda take karantawa a novel ba hakace tasameta ba memakon tafarka taga ya girka Mata ko Kuma ita umman ta Aiko Mata dashi amma sai sabanin haka ace ita kamar ita amarya ba a temaka mataba har za,ace ta tashi ta girka.
Dafarko taso takai zuciyar ta nesa tana kula da ita Musamman dataga duk duniya bashida farin ciki sama da ya kyautata wa ummansa sai taga abin Yana neman wuce gona da iri abinci bazaici ba sai yaje yaga in taci sannan zaizo ya zauna yaci komai baya bawa muhimmanci sama da ita shiyasa itama taga fa intayi sake za,ayi ba ita.
Ajiyar zuciya tayi tare da juyawa zuwa daya hannun idonta yayi jajir tabbas inta bari sadiya tayi galaba Akan danta to kuwa zuciyarta tana iya bugawa.
Karimatu ce take bawa yaranta umarnin kowa yacire uniform dinsa yasa a ruwan omon data jika.
*INA BUKATAR COMMENT DINKU NA ROKEKU INHAR KUNASO NACIGABA*
π€*DAGA ALKALAMIN YAR* *MUTANAN JINGAU* π
π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββ
π¨π¨π¨π¨π¨π¨
π *ABINDA KE FARUWA* π
*LABARI DA RUBUTAWA*
*BY*
π€ *FAUZIYYA AUWALU ALIN BABA JINGAU* π
π
Ώ *11(K)*
π *KAINUWA WRITERSβπΎ ASSOCIATION* π€
daya bayan daya sukaringa cire kayannasu suna sakawa acikin ruwan omo wannan yazame musu jiki dake tana rigasu dawowa takan dawo gida daya saura sukuma sai daya da kusan rabin suke dawowa,
tana shigowa gida take zazzaga omo cikin roba ta zuba ruwa duk Wanda yadawo takanyimar tinin cire Kaya yasa aciki ita Kuma nana tana dawowa before sutafi Islamiyya saita wankesu ta shanya.
Bayan sungama cin abincine sukayi sallah sai ta dan dimama musu ruwa domin yin wanka dan garin iska na kadawa haka takamasu daya bayani daya tayi musu tayi musu ita Kuma nana tana shafa musu Mai tare da saka musu kayan islamiyya basu Shari awa daya da dawowaba har sun kammala shirinsu yaran gwanin Sha,awa dukkaninsu suna tsaye domin tafiya Nana ce bata fitoba suke jiranta ganin batada niyyar fitowane yasa karimatun takwalla Mata Kira amsawa tayi batare da ta fito ba,
Girgiza Kai tayi tareda mikewa domin binta cikin dakin tana lura da ita tinda ta dawo batada walwala bakuma yarasa nasaba da zancen ko na makaranta ne ,
Sanda tashiga dakin tana tsugune tana lalube cikin Jakarta kudi take hadawa Yan goma gomane birjik da Yan biyar da Yan ashirin agabanta tanayi tana goge hawaye dasike tarar mata
Nana kifuto kutafi kinasawa suna makara shiru tayi sanda taga tana goge hawaye tare da goge majinar hancinta.
Wani abin nayi Miki dakika shigo daki kina kuka ?
Niba kuka nakeba .
To meye kike kenan ko wani abin akayi miki
naga tinda Kikashigo kike fushi kigayamin abinda Yake faruwa , wannan kudin Kuma dasuke gabanki nawaye ?
Shiru tayi batare da tace komaiba ita kanta dan bayar da zata yine tana tausayawa umman tasu dawainiyarta tana yin yawa amma dole sai Dole shiyasa ma takan jure horon da ake Mata narashin biyan kudin term Akan lokaci.
Magana nake Miki inkuma bani da muhimmanci Kan lamarin ki sai inkyaleki.
Dama Kan kudin term ne kullum sai ance inkawo kowa ya biya Ni kadai ce ajinmu ban biya ba yauma koroni akayi to Dana futo titi nayita tsayiwa bansami abin hawaba shine wani malami yazo wucewa ya ganni atsaye sai yasani gaba yamayar dani yace gobe inkawo inba hakaba kar nazo,
Gauron numfashi taja tare da furzarwa tayi murmushin Yake tace auke wannan ne yasa ki fushi kina mace har Dan wannan abin zaisa ki karaya ai ita mace kullum da dauriya akasanta yazamana duk inda Kika juya Zaki jure Amma dan Dan wannan har kike fushi tashi kutafi gobe in Allah ya kaimu babanku zaije sai ya basu abinda yasamu inkuma Basu samu ba sai ya basu hakuri insha Allah duk za,abayar har na kannanki ending this month insha Allah.
Goge fuskar tayi ta amsa da Amin .
Af wannan kudinfa nawane nagansu tirmis a gabanki?
Kudina ne nake tarawa na makaranta Wanda nace miki zamuyi yayin mauludi.
To mezakayi dasu kike ebowa keda Zaki tafi makaranta kinbar Yan uwanki atsaye sai kinsa anyi musu bulalar makara saboda Allah.
Jiyane akayi musu bulala amakaranta sabida basuje da kudin wataba shine damuka taho hanya nace musu zanbasu yau sukai inada kudi agida kirgawa zanyi nagani inzasu Kai sai nabasu inbasu kaiba Kuma ko mutum biyu sai na bawa .
Ido ta zuba Mata tarasa ta inda zata fara komai nema Yake ya kwance Mata inta bullo tanan sai wani abin ya bullo tacan.
Tace nana karkiyimana haka nasan ke yanzu kinfara hankali ko na boye Miki wani abin dolewani Zaki fahimta Daban shigo dakinnan ba Haka Zaki tafi da wadannan kudaden kibasu bansani ba ?
Zaki fara nunawa Yan uwanki gazawarmu ne duk fadi tashin da akeyi dominku yatashi awofi kenan,
Shiru tayi nadan lokuta tare da zubawa yar tata Ido ta hango karaya atare da ita domin kwayar idonta ta nuna balle datayi la,akari da hawayen dake satata a idonta.
Tace ba kuka zakiyi minba magana nakeso kiyi domin inji tabakinki.
Bahaka nake nufiba nidai kawai basu zanyi nasan in sun gaya miki yanzu bakida kudi hankalinki ne zai Kuma tashi shiyasa Zan basu amma bada nufin hakaba kiyi hakuri umma
Shikenan amma karki Kuma haka in ma basun zakiyi kiringa gayamin sai ingaya Miki yadda,zayi shi yaro indai Yana da iyaye baya girma komai zayyi sai yayi Shawara karki Kuma yankewa kanki hukunci kowane irine batare da kingaya minba ,
Ki tashi kutafi kice da malaman zanzo da kaina in anjima nakawo musu .
To umma inba fushi kikayiba kibasu wadannan sukai ko Basu kaiba inyaso inkinzo din Kya cika musu ( tasan dai karshenta ban hakuri zatayiwa malaman kafin asamu akai).
Toke nana Wanda yaje yakai irin wannan kudin biyar da goma ai yanemowa kamsa abin magana yadda wasu malaman suka lalace sai kiji ansa muku suna Akan wannan kudin Basu San da yadda aka hada kudinba gara Baku kaiba da dai Yan hamsinne to da sauki wani yanzu aciki inkuka Kai yaringa kiranku Yan biyar da goma.
Dariya sukayi tare sannan suka fito suka tafi suna muntafi ita Kuma tana yimusu tinin addu,ar fita daga gida sannan ta bisu da addi,ar allah ya kiyaye ya kuma tsareminku, mutuncinku ,kimarku lafiyarku ,sukuma suna amsawa da amin.
Bayan suntafine tacigaba da kujiba kujibarta daki tashiga ta hau bincike wata tsohuwar wayar shu,aibu ta dakko domin yadena amfani da ita ta Dade da lalacewa shine ya ajiyeta da yara sun fara Wasa da ita shine ta dauke ta adanata ,juyata tashigayi tana cewa kozasu siya masu way gata dai da kyanta afuska bansaniba ko za,asiya , haka tadauki waya ta bugawa shu,aibu domin neman iznin fita Gaya Masa takeyi zata makarantar su nana sabida matsalar kudin wata harta ke cewa kozasu Sami wani abun sai arage kodaga bayane acika.
Wai wai wai ita yafara ambata yace anya ko zasu samu toow sai dai ko innadawo din za,a duba amma kije kibasu hakuri za,a biya insha Allah.
Haka ta ajiye wayar jikinta asalube dan duk sanda yayi Mata irin Haka jikin mutuwa Yake kumayi kullum mutum ba karfin gwiwa atare dashi kullum babu haba haba abin Yana neman yin yawa .
Sai Kuma waji wani tinani yashigeta toma mezai bata mutumin da kullum sai ya Kare karfin aljihunsa kafin yabar gidan nemannan dai shine tinkan ya aureta Abu days ake samu gashi har sun tara yara akan kadami guda Aiko hakuri yazama dole inhar tana neman kwanciyar hankali gareta da yayanta dashi kansa mijin Musamman domin bashi karfin gwiwa gurin nemi musi abinda zasi saka abakinmu salati.
Goya nana Fatima tayi ta kulle gidan bakin titi tayi gurin masu Saida ways Basu tayi tace su siya naira dubu da dari daya aka siya ta kirgi Yan ashirin na naira dari ta hada suka Zama dubu da dari biyu dama dari biyune kudin watan aiko saigashi take ta biya tare da Kara basu hakuri najinkirin dasukayi gurin biya.
Alhaji sabo ne azaune gefen ummansa yamayi Mata sannu da jiki adole take amsawa kodan tseratar da sadiya daga kagen cutar datayi Mata.
Yace amma kannaki yadenako ?
Yadena dama Rashin baccine Kuma yanzu sai godiya tinda nafarka sai naji kamar cirar Kaya .
To allah ya Kara sauki,
Amin Allah yayi maka albarka ya tsareka daga dukkan abin ki nasarari Dana boye.
Yanajin dadin adduar nan ya tabbata addu,ar mahaifiyarsa ce take bibiyarsa dukkanin wani abu dayasa agaba Yana ganin haske duk sanda zaizo ya gaisheta sai tayi Masa wannan addi,ar sanda sukaje aikin hajji yanajinta dukkanin wata addu,arta akansu ne baiji tanayiwa kanta addu,aba saisu sai mahaifinsu har sai da yazubar da hawaye saboda irin feeling din dayaringa ji atare dashi kauna ce zir ta mahaifiyarsa.
Sadiya ce tashigo cikin mutunci da mutuntawa ta tsuguna ta gaisheta tare da yimata yajiki abincine a hannunta nakarin kumallo har kwai ta soyo Mata sukasaka ta a gaba Saida ta ci duk wani motsin umman takanyi Mata sannu kotace wani abun ne umma ko kanne haryanzu haka taringayi Mata sanabe iri iri har yatashi yatafi yabarta agurin Yana futa tafara yatsina fuska takuma janyo abinci tace dama nawane nabaki Danni nadena girki da kowa inma za,a koma kitchen a koma Danni ba baiwa bace ko kisashi ya nemo Mana me aiki ehe ta murguda bakin rashin kunya .
Sadiya tanan Kuma Kika bullo ?
Tokiyi kigama zanga karshen wasan naki danii zakiyi niba kishiyarki bace ko kishiya inkana neman girma da mutunci Jan girmanka kake bareni da ko kinci galaba akwai ranar kindillaci,
Tana cikin maganarne alhaji sabo yashigo yaji karhjen zancen amma baiji farkon ba tambaya Yake meyake faruwa yaga kamar ranta abace yake,
Bakomai tace tambayarta yakarayi takuma cewa bakomai ganin bazata fadaba sai sadiyar wadda tajike da gumin fargaba tayi murmushi tare da mikewa tama me bawa umman hakuri tace kyii hakuri bansan ranki zai baci ba umma amma Zan kiyaye insha allah shigewa tayi tafita tare dasa hannu afuskarta kamar tana share hawayen.
Binta yayi da kallo sannan ya kalli umman yace wai menene umma Yake faruwa mnhh bakomi kaidai Allah ya kiyaye Allah ya tsare minkai jeka kasuwa Rana tanayi.
Bai tafiba sai yabi bayan sadiyar domin yanason yaji kome ke faruwa sun daure Masa Kai daga umman har ita sadiyar.
Bara muleka wani gidan miga wata wainar suke toyawa.
Zainab taci kuka takoshi tarasa yadda zatayi da surukar tata ita kyautatawa tanayi Mata amma duk bata futa yanzunma cin mutuncinta tagamayi sabili da tasa sabon dinkin da