Author : Yar Jingau Category : Romantic Hausa Novels
mijin Zaki Fara dubawa,inkun kyautata Zaki gani a kwaryarki inkin Yi akasin haka shi zaki diba, amma dai yakamata Muna kiyayewa Koba muyi Dan Allah ba ,tofa muyi kodan yayanmu,domin karatun rayuwa ,maimaici ne, yadda kika tuka haka zaki kwashe,inma Baki kwashe ba dole cikin zuriyarki wani ya kwashe harda gyara.
Kishiyar ramla ce ta dago da kanta, ta ce lallai na yarda da kowana zance ,tin kan ku gayamin nafara hasasa hakan shiyasa cikin sauki na ajiye komai gefe , amma nima dukkanin abinda nayi nayi be gurin kokarin ,Kar nayi rayuwa irin ta mahaifiya ta wadda sakamakon sai Allah.
Ta ce nidin munga rayuwa nakuma yadda da zancenku ta yarda Mata suke kamar bayi a lokacinnan ,ku saurare ni kuji ,yadda komai yake tafiya acikin namu gidan,da Kuma irin kalubalen Dana fuskanta tin ina yar yarinya ,shine yaja hankali na har nake ganin bazan yadda in zauna da kishiya ba gudun nima rayuwar tazomin a haka.
Aiko dai kafin sadiya ta karbo nanny sai da mukaci tijara,dan har kasa sai da na tsuguna nabata hakuri kafin ta karbeta ,niko hakan danayi nayi shine da manufa,a wannan lokacin zan iya kwantawa kasa sadiya ta taka ni Dan son biyan bukatar dake tare damu.
Ta bangaran yara kuwa ,kamar abakinsu aka rada sunan umma,zancansu kadan umma, da tana yawan za dasu da taji maganganu a bakinsugame da kakarsu da suke yini zancanta.
Shiko me gidan baisan ma suna yiba ,domin yau kwanansa uku bayanan ,ko yananan ma baya tare da nutsuwarsa,kayansa ne aka tare su a boda sai kaiwa ya ke yana kawowa amma futowarsu ta gagara,shine fa yasamu wani da akayi Masa hanyarsa cewar ya bashi wadansu kudade in Allah ya yarda kayansa zasu fita,tofa dai gashi ya bayar dinma abu yaci tura, karshe a Sara ce take neman biyo baya.
Bude get mukaji cikin hanzari yaran suka futa domin sun San babansune yadawo , tin daga bakin motar suke ta bashi labari ,abinda umma ta basu shiko ko takansu ma baibiba,yazo zai shiga gurin sadiya ne Hassan ya ce ummanmu Bata nan tin jiya,cak yatsaya domin Jin zancan yayi daga sama.
Tasha tafiyarta ta kwana batare da ta sanar Masa ba, bai taba Jin komai ba game da hakan, amma yanzu sai yaji abin wani banbara kwai,kallonsa yakai kan Khalil ya ce Ina ta tafi bansani; muma bamu saniba amma dai sunyi fada da anti ameera shine suka tafi da unguwa da anti aminiya,nima bansan inda suka jeba.
Tsintar kansa yayi da juyawa ya nufi gurin ameera da take kare masa kallo tindaga nesa.
Cikin aminci tayi masa sannu da zuwa , sannan ta ce su shiga ciki ya huta gajiyar da ya debo,
Bai wani ji fargaba kamar daba, sanda yake shiga a gurgujeba gudun masifar sadiya ,sai gashi harda kwasar girki ,daga bisani Kuma yayi wanka har yasamu ya zauna suna Dan taba hira ,anan yake sanar da ita irin asarar da yayi ,ga dumbin bashin dake kansa wanda inhar Bai Sami kayannanba tabbas ya kade .
Matsowa tayi kusada shi cikin kwantar da murya take cewa ,nasan haka zata kasance ,Koba dade Koba jima ,ko Bai faruba tabbas hukuncin me girma ne, katana abinda Allah ya hanaka tabawa , tabbas kalubalen rayuwa na neman samunmu,ta daga hannu sama tana me cewa , Allah mun tuba laifi bisa kuskure hukunci tsanani , Allah bawanka kayafe masa baisan yayi ba ,kayimasa sassauci,
Kallonta yake domin shidai baisan abinda take nufiba ,ya bude Baki zai tambaye ta sai ga su Khalil Nan a guje suna musu,anti ameera ai nine umma ta ce angonta ko sai usaini ya ce ai dama ni angon baba iyane ko Hassan ne ya zobara baki gefe ya ce Allah nine angon umma ai kaka ta ce,ba kakarkaba,nusaiba ce take yi musu dariya Yar gidan ameera ta fari ,ta ce to nidai ai umma ta ce ita kawata ce,.....cikin tare zancen nata Khalil ya ce la daddy umma ta ce tana gaisheka Kuma ta yafe maka abinda kayi mata tinda munje mun gaisheta.
Dafe Kai yayi,ya ce ki sallami ya yannan naki Kar su sani ciwon kai,
Sai Kuma yayi wunzur ya mike,kome ya Tina kuma oho ya koma ya zauna,
Ameera ce ta kalleshi ta ce lafiya Yaya Naga ka mike?
Tsaki yadanyi ,ya ce oho nima bansani ba kawai dai wani Abu naji yadan fuzgeni ,ya ce kin shiga ko kin gaida ummana yau;
Kallonsa ta yi cikin kufula ,ta ce wace ummanka ,ni har sai ance inje in gaisheta Kai ne dai zance yau kashiga ka gaisheta.(ita haushinta dashi ma Bai wuce Wai tsahon shekarun da umma tayi Bata gidan Bai taba lura ba )Kuma ko cikin zance Bai taba hasashe ba.
Itako nanny tanacan tana bincike cikin dakunan sadiyar, uban kayan tsafin da ta debo sun yawaita har sai da jikinta yadinga karkarwa ,haka ta debosu Niki niki ta futo ,yayi dai dai da turo get din gidan da sadiya tayi.
*INA* *BUKATAR COMMENT DINKU INHAR KUNA SO INCI GABA*
π€ *DAGA ALKALAMIN YAR MUTANAN JINGAUπ*
[21/01 Γ 12:09] +234 703 197 3585: π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββ
π³π³π³π³π³π³
π *ABINDA KE FARUWA* π
*_PART 2_*
*LABARI DA RUBUTAWA*
*BY*
π€ *FAUZIYYA AUWALU ALIN BABA JINGAU* π.
*π
Ώ50(X FOR* *X-RAY)*
π *KAINUWA WRITERSβπΎ ASSOCIATION* π€
Wani irin furgici ta shiga,a hankali taringa jan jikinta da baya da baya .
Itako hankalita ya na kan motar me gidan balle da hayaniyar yaran taja hankalinta har zuwa falon ameera.
Itako nanny ganin hankalin sadiyar baya kanta ,cikin rawar jiki ta zaga bayan gidan, cikin shirgin dake bayan dakunan gidan ta je ta boye kayan hannunta, sannan ta koma da sauri ta shiga karkade falon ,a kokarinta na azo atarar tana aiki.
Da masifa tashiga falon ,yayi dai dai da sake ambatar kakarsu umma da Hussain karami yayi.
Kamar Wanda aka sake fuzgarshi ya mike, ya ce kumuje mugaishe ta .
Cikin tashin hankali ta dira,ta ce Wai Ina zaka ,Ina zakaje ne naji kana kuje ka gaisheta,
Dake har yanzu Ya na cikin yanayi ,sannu da dawowa yayi mata ya ce daga Ina kike ance tin jiya bakyanan;
Kallon tuhuma tayi Masa, sannan ta bi ameera da kallon da ita tasan kansa,domin inba da wata akasa ba tamance rabon da tayi Abu ya tuhumeta ,ita ko ameera tin da sadiya ta shigo falon gabanta yake faduwa, inbanda ambatan Allah ba abinda ta ke yi.
Tadan fuskanci abubuwa game dashi, musamman da har ya shigo gurin Ameera yazauna ba tare da farga baba.
Cikin basarwa da nuna ba aikomaiba ta hada kan yayanta Dana mijin ta suka fuce,suka bar ameera da bakin ciki.
Wai har yaushe abinnan zaizo karshe ,ita kenan Bata da wani time da zata zauna da mijinta cikin salama sai wata tazo tashiga tsakani,kamar anzun gureta ta mike tabi bayansu.
Suna zaune a falon shiko ya tallafe hannunsa a habarsa ,shiba tinaniba shikuma bawani abin yake ba,uwar ikon kuwa ta kama kofa zata bude bed room domin rage kayan jikinta.
Ba tare da sallama ba ta tura kofar ta shiga,cikin fushi ,ta ce yaya yau nazo ayita ta kare ,shin Wai nidin aure na kake ko kuwa gadin gidanka nake, nifa wannan abun ya isheni bani da damar kashigo dakina sai anbika anfito dakai,to ni nagaji in auren auren ,in kuma bazayyi wuba to kasallame ni inyi gaba inyaso ka karasa rayuwarka da wannan sallamammiyar matar taka.
Aiko kamar zakanya ta juyo afusace,ta ce kuttttt ni ce salla mammiyar to ko kinyi a bakin zamanki a gidannan, zakuma Kiga sallama ganin idonki ,Mara mutunci ,Mara zuciya,in Banda rashin zuciya, aikinsan kedai ba auranki ake ba zamana kike ,to daga yau zan kawo karshen zaman naki ,
Aini nafi karfinki wallahi inkika sake nasakaki agaba wallahi ruwan gidannan sai ya gagareki sha,yo astagfirullah ma ai base na fadaba ,domin tinda aka kawo wannan matsaya na tabbata kina dab da rasa dukkanin wata nutsuwa taki.
Aiko kamar ta Kara tsokanota , keeeeeee kifa ringa kiyayata kina wuce gona da iri ,kina shiga hurumina, ameera kin damenifa,kindaman ki kyaleni,ki rabu dani ,ki rabu da mijina.
Zan rabu dake daga Randa kika ajiye makamanki muka zauna lafiya,kika rabu da yaya yakoma ga mahaifiyarsa.....kamar tsikarin allura yadago ya kallesu, ya ce ameera Wai ummata kike zance ?
E ummanka,umman datayi rayuwa dakai cikin takura da neman daukin ubangiji,umman data raini cikinka har tsawon wata tara ,tayi nakudarka kota rayu kota mutu,umman da Bata bacci sai kaci kasha, Koda zata Kwan Bata ciba, to Katina da wannan Katina da lokacin datake sintirin zuwa gidan hajiya mariya domin bin sahun Al,majirai har sai tasamo maka abinda zakaci, Yaya sabo karka manta ummace muke haduwa tare muyi wankau Dan kasami abinda zakayi karatu kasan kaidin wanene,haba" Yaya sabo" har akwai macen da zatayi galaba akanka Koda da asirine baka taka shegiya Dan mutunta uwa ba,"yaya sabo"Katina me sunan uwa yake nufi,Katina,katina, .
Ke kuma nadawo kanki mara tarbiyya ,wadda batasan me duniya take cikiba ,kalma daya inkika tsinta a cikin zance na maybe ki tsira da sauran imanin da yayi saura gareki,Babu tambaya gareki gaba yayinda komai yagujeki ,Jin Dadi yabarki, zan Baki amsa kafin lokacin tambayar meyasa komai yazamo Miki haka ,sadiya kitina da wannan inhar kina bidar hoton tsufanki cikin iyalanki tare da matan yayanki ,tofa amsar a bayyane take ,sai ki hango yadda kikayi rayuwa tare da mu,amalah da uwar mijinki.
Randa yayanki suka san rayuwar da kikayi da kakarsu ,Ina Dadi gareki susan rashin tarbiyyar da kika aikata,karkiyi mamaki da hukuncin da zasu yanke miki,to ba hukuncin subane, hukuncin ubangijine shine zai hukuntaki ta hanyar diyoyinki sad.......flower ross din dake gefen center table ta makomata a gefen kafarta.
Cikin rashin tsammani yasameta ,Aiko jini kamar Wanda tayi babban yanka ,shi dake zaune kamar medaukar darasi shine yakawo Mata dauki,kafar yarike yana kokarin toshe gurin dake futar da jini.
Sadiya ce ta Kara sautin masifarta yau tabbas sai ta ladaftar da ameera ,Kuma tabbas tayi na karshe domin wannan Karan sai ta bar Mata gida,kansa takoma cikin karaji tace "alhaji sabo" Bai saurareta ba Dan kunnansa ma atoshe yake bayaji baya gani ,ciwonnan dake kafar ameera shine kawai a gabansa,daga karshema hannunta ya kama ya ratsa tacikin yara da sukayi cirko cirko suna kallo, nanny ko tana bayan labule tana leke harda hawayanta.
Muna jinki inji karima .
Ta ce a lokacin Dana taso tabbas talauci yaci karfin gidanmu ,ta yarda ko naira ashirin din siyan kwaki wani lokacin take gagararmu,abin haushin unguwarmu kewaye da mawadata ,masu cin abinda ransu yakeso, uhmmmmm wannan Abu Yana Dagan hankali ,ta yadda kowana lokaci yayansu ne sama damu ,ta ko Ina sun fimu,yawo muke da yunwa tare da rashin tarbiyya,yo Ina zamuga tarbiyya tinda abinci ma musa iyayanmu bamuci mun kishiba bare asami faragar da zasu gaya Mana har muji maganarsu,muzanto yayan da za,a daga murya a kiramu ako ina.mune yawo makota ,mune yawo duk inda mukasan zamu Sami abinda zamu ci ko musaka.
Nidai ban wayi gari ba sai na tsinci kaina Ina me bin maza ,indai zasu bani kudi nikuma Ina manne dasu domin inma banbisun ba tsakanin iyayena da makota bawanda zai dauki dawainiyata ,Kuma fa a haka danake gaya muku Mata biyu ne ga babanmu ,bawata Sana,ace dashiba sai dai yau yaroki wannan gone yaroki wannan,kumafa da Yana dashi shidin Maison yafaran tawa iyalansane ,Dan komai yasamo baya iya ci mu yake kawowa.
Haka nake tara samari a kofar gida bawanda yake kirana yayimin fada ,ko a gida ko a makota ,su gida tinda Ina samun kudi basuda abin cewa,makotafa ai kodan gudun abinda zaije yazo sayimin fada.
Cikin kankanin lokaci nayi fuce , wallahi a lokacin har Yan majalisa daukata suke ,wani time din in suka daukeni nakan share sati a gurinsu,duk da hakan bawanda ya taba yimin fada,sai daifa ko Ina cikin unguwa zance na ake kowa aka tashi hira sai hirata zakaji anayi suko majaifana dasuka ga abin Yana neman wuce inda suke tinani,Aiko suka datseni Niko na ce bansan zance ba.
Haka nadinga hangars rayuwarta wa cikin Allah wadai bankuma taba Jin Wai nayi ba dai daiba,a hankali Kuma da akaga nataso gari sai yayan makota Suma masu karancin tarbiyya suka Fara mannemin,kafin wani lokaci mun dinke da yayansu,sai Kuma akafara bin iyayena da cewar lallai mubar unguwar domin zan lalata musu Yaya.
*INA BUKATAR COMMENT DINKU INHAR KUNA SO IN CIGABA NA ROKEKU*
π€ *DAGA ALKALAMIN YAR MUTANAN JINGAU* π
[21/01 Γ 12:09] +234 703 197 3585: π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββπ€¦ββ
π€¦ββ
π³π³π³π³π³π³
π *ABINDA KE FARUWA* π
*_PART 2_*
*LABARI DA RUBUTAWA*
*BY*
π€ *FAUZIYYA AUWALU ALIN BABA JINGAU* π.
*π
Ώ51(Y FOR* *YORK)*
π *KAINUWA WRITERSβπΎ ASSOCIATION* π€
yo Ina mukaga inda zamu koma,toshe kunnansu sukayi domin basu da abin cewa.
Kaiiii talauci bayyiba ,duk abinda annabi ya ce a nemi tsari dashi lallai ba karamar illa ce dashi garemu ba.
Ciwo ,ciwo ,ciwo, badadi musamman a inda talauci yasamu gu ya zauna, shine yasako babanmu a gaba ,haka muka dinga sintirin asibiti wani lokacin inbani da kudin zuwa sai dai muzauna muzuba masa idanu,domin bamuda yadda zamuyi,gashi anrasa meke damunsa,sai daga bayane ma dayafara yin wani Dan tari Wanda baya sauka ciki ,muka daukeshi mukayi asibitin zana daahi.
Tashin farko aka gano yunwa ce taci karfinsa har take neman ganin bayansa.
Tofa tindaga sannan nadinga bin makota domin su taimaka Mana Koda da kudin maganine,kunsan Allah bawanda ya taimaka ,sai wanine ya tausaya shima dawata manufa ,domin yadade Yana so nakulashi, amma Bai samu ba sai sanadin wannan.
Nidai Dana ga Babu Wanda yadamu da halin damuke ciki sai na fara bugawa samarina waya,cikin kankanin lokaci nasami dauki ta ko ina,kayan abinci munsamesu, sannan nasami kudi sosai.
Bayan yin hidima gareni sai suka Kuma mannemin,niko banida mafita haka nasaki jiki garesu,Dan inma ban yarda ba ,banida yadda zanyi intallafawa iyayena, da kannena,cikin wata tafiya danayi ta wata guda nida wani saurayina cikin garin abuja ,nasamo tsarabar ciki nadi mauce sosai Dan ban tsammaci hakanba,shiko ko a jikinsa,sai kawwameni daya kumayi gu daya ,yamayarni matarsa banida zabi, domin dukkanin dawainiyar gidanmu Yana kokarin dauketa, haka nadinga rayuwa dashi har sai da na haihu, suko iyayena da nasanar musu halin da nake ciki sun shiga Rudu ,har mahaifiyata take ce wa Kar indawo inyi zamana Kar Inja Mata abin kunya,amma daga baya sukabi sahu ba um ba um um ..
Bayan haihuwata ma Bai barni nazo gida ba haka nayi ta rainon jinjirin ,irin gatanannan na me jego duk bansamuba.
Dana gaji da Zama dashi, sai na nemi bujirewa,sai ya nuna shima Daman yagaji soyake mu rabu.
Nayi kwafa nashiga tattara kayana, amma sai yakawomin uzurin in anganni da dafa ince nawaye,jikina ne yamutu duk iskancina bazanso aganni da shegeba,sai nayi waya nasanarwa da babata, halin danake ciki,masifa takama yimin, ai Daman in tururuwa taso lalacewa fuffuke take,tinda dama yadenayo musu aike tasan neman maraba yake ,Dan haka inturo da kudi ayi aiki akansa ta yadda dole ya aureni ko bayaso.
Bayan anyi auran mune komai ya dagule domin talaucinnan yananan a gidanmu,a yarda nakeji wani lokacinma abinda zasu Karya ko subawa yara ma gagara yake,nikuma Ina zaune gu daya , Aiko ciwo ya ce da babanmu salama alaikum ,gashi niba Sana,a nake ba ,kudin da da yake bani yanzu yadaina ,gashi dai atakaice kota Ina ba dadi, Danko kofar gida baya barina in leka Wai beyarda Daniba, ga rashin mutunci kala kala, neman Mata kuwa har gida yake shigowa dasu,karkuce fa ni ce matarsa ta fari a,a Yana da mata ammafa batasan ya aureni ba yakuma ja kunnena kan hakan ,ya ce duk Randa nasake matarsa tasan da zamana abakin aurena.
Waya aka bugomin Allah yayiwa mahaifina rasuwa,nayi kuka nayi kuka kamar bazan bariba,sanda aka bugomin wayar baya gida nayita bugawa Bai dagaba,sai na hakura nafara hada kayana domin tafiya gida, shigowa yayi afusace Yana masifa Bai hanani buga Masa waya ba inya futa,
Dagowa nayi jage jage da hawaye,na ce dole ce tasani baban aiman mahaifina ne yarasu aka bugomin waya,yanzunnan kaga suka bugomin ya rasu Allah yaraba ganawarmu tinda nabaro gida bashida lafiya bankuma ganinsa ba Ashe mun rabu kenan.
To shine Zaki daganin hankali Ina gida ki bugomin waya,har sai da kikasa matata tafara zargin ko budurwa ce takemin waya iyi karki kara.
Na ce dama tafiya zanyi Kuma banida kudin mota,
Au to nizan baki?
Katemaka ko Rance kabani Kar,adaukeshi bamganshi ba.
Aiko sai dai kiyi hakuri Dan bazakiba bada yawu naba ,salon kije adinga cewa Dana shege ,ki hakura kyaje daga baya in an share makoki sannan gidan bakowa sai muje tare.
Wallahi haka bawan Allah nnan ya hanani zuwa ta,aziyyar mahaifina.
A yadda ake bani labarin mutuwar tasa na Yi Allah wadai da makobtaka da masu kudi ,domin basu da amfani ga talaka musamman irin makotan unguwarmu.
Wato yakwan biyu Yana jiyya ,Kuma bakomai bane sai yunwa, haka suke fafutukar neman abinda zasu bawa kannena suci, ta ce cikin ikon Allah ta aika makota gurin wata baiwar Allah ta ranta Mata naira hamsin,sanda aka kawo mata cewa akai ta ce tabarshi,cikin murna ta bayar asiyo Mata kwaki na talatin suger na Shirin,jika musu tayi tabawa yaran susha,shikuma babanmu Yana gefe Yana kallo sai hadiyar miyau ya ke,can sai yadago kai cikin ciwo ya ce Dan Allah kidan sammin kwakin naci yunwa nake ji,kallonsa tayi ta ce ,malam kayi hakuri yara susha kaga yau bawanda ya ci abinci cikinsu innabaka kuma kaga sun rasa kenan.
Ya kwantar da kansa gefe ,ya ce da kinbani na ci yunwa na ke ji,ta ce kadaiyi hakuri,haka ya gyara kwanciyarsa tare da yin salati ya kalli gefensa ,sai bacci yakwasheshi ,haka nima nayiwa Yara shinfida kowa yakwanta,misalin karfe dayan dare yafarka ya na ta kirana,a furgice na mike na kirawo kishiyata muka Yi kansa,cewa ya ke ,ruwa abinci, kubani ruwa abinci,can sai yayi shiru mutuwar kenan da wannan ya mutu ,da wannan yatafi gurin ubangiji alhali....πππππ.
Innalillahi wa Inna ilaihirra,ju,un Yan uwa Ina zamu, Muna Ina Yan uwanmu musulmi suke cikin wannan