ABINDA KE FARUWA HAUSA NOVELS BY YAR JINGAU

Author :  Yar Jingau Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   21 / 31

60K to 63K   out of 92.1K words

hidima tasake samuna har nake neman dauki kodan tallafar rayiwarmu nida diyoyina,bazan nuna rashin godiya ba,Yana yimin abubuwa sai dai wadatuwa ne bamayi musamman danake da yara,Ina bukatar tallafi sosai,domin ko gun sittira nawaiwaya tofa Muna bukatarta ,duk kudinnan dayake samu tsakaninmu dashi sittira sai shekara shekara yake mana Dani da yara ,yakan dinka musu kala bibbiyu wani sa,ilin sukan samu uku uku ,tofa sai wata shekarar ammafa bawai Gama garin kayabane masu tsadane wadatarmune dai kawai dabasayi,


Nikuma yakan gwada bajintarsa anan yakan zage damtse gurin gwangwajeni da sitturu masu tsada Dan har Holland Yana sayamin ,kudinsane dai Bai yarda su gilma ta hannuna ba,a yanzu dazance yabani naira dari tofa sai Bala,i na tsoka no wa kai na,kumafa Ina da takar duna na shaidar Gama karatu, guyin duniya yabarni inyi aiki yaki domin Ina da bukatar abubuwa sosai atare Dani ,Wanda shi bazai mallaka minba sai dai ni innemesu da kaina.



Abinda yakuma sani Sha,war yin aikin kodan diyoyina domin Suma suna da bukata daga gareni,ace Babu ni Babu saiwa wani yaro nawa abu ,nasan da Zan tsurasu ince sununa min abinda nataba sai musu bazasu iyaba,tinda banida hanyar dazan sai musu nayi kokarin yin Sana,a yahana ni,Toya zan,hankalinna bai Kuma tashiba sai da mamana ta ke Kuma kwatan tamin,cewar shifa da har kullum yakanbi zabin ransa ne ,meye zabin rannasa shine ,me Faranta masa ,ta ce har kullum insun tashi kallon fuskarki data mahaifinsu Dole akwai banbamci Kuma da ban ban cinnan zasu rayu azuciyarsu, inzaki mike kinemi Sana,a ki nema kodan fuskarki tarinka haskawa a idanunsu,kafin kukai munzalin dazasu ce mahaifinsu yafiki say ba adadi.


Lokacin datake gayamin sai nakarbi shawarar hannu biyu, domin Koba ta fada ba zan can a bayyane yake ,don nasan masana sunce sadakin so kyauta ,balle Kuma ga yaya da kake rayuwa dasu ko yaushe.


Ta ce keda kina cikin wannan halin bakizo kin gayaminba shekara da shekaru sai da damarki ta ke neman kwacewa ,kinsan mena keso da ke; girgiza kaina nayi, ta ce Yi kokarin sau yawa kafin damarki ta wuce.



yanzu Banda wannan meye matsalar gaba,na ce ai daman kowacce matsala data faru a karkashin wannan tafuto ,kuma innasamu Wannan ta Wu ce tofa ni komai yayi daidai.

Na ce umma nidamu wata ma mafi daukaka, dayake iya kallona ya ce Wai banason yayanshi ,har yakance Dana no na haifesu ba wallahi cewa zayyi banasonsu, ta ce meyaja hakan;baki nadan tabe na ce bansan meyasa ,amma nakan danganta hakan da rashin hidimata garesu.


Allah sarki kinji zancen ko ko anan dazaki Yi wani karatu sai kiga shikansa daya tauyeki yakan nuna bacin ransa na rashin hidima garesu ballanta kuma su yayanki da kansu ,nidai karshen zancena zanbaki jari me tsoka ,kije kisami Sana,ar dazata taumakeki inkuma kinjebkin Kuma bashi kudin tofa ke kika sani,Kiki yaye.


Tofa umma bansan yarda Zan Masa ba kinda San namiji irin wannan inhar ya kyalla yagano ka da kudi yakan yanke hidimarsa gareka me har sai yaga bayan kudin.


Ta ce to kinemi wata a min tacciyarki ,kibata taringa siyar miki da abinda kika yanke gurin siyarwa,ko kuma kiringa sarin kaya kina turo dasu nan sai Yan uwanki suringa siyar miki ,kinga suma har sa sami wani abun kin karu sun karu.

Na ce Tom umma Allah ya kara girma.


Haka ko nayi abin sai yazama nafara asa,a domin tin Ina sarin kanan abubuwa sai nakoma sarin kayan danasan ana bukatarsu acan Ina turawa,haka nadinga taimakon yayana nima Ina taimakawa kaina har da ma wanda zai rabeni.


Intakaice miki labari dai wannan Sana,ar ita ce nadin gayi har sai da ta shahara yazamto na Sami hayar wani shago batare da sanin megidana ba Kuma dasu ne muka kawo iyanzu har yazamto na mallakawa diyoyina Sana,ar a hannunsu, basu da damuwar Wai jinginuwa jikin wani komai nasu nawane, Kuma abina abunsune,dakuma wannan nawanke kallon danake samu na banbanci tsakanina da babansu,nazamto tauraruwa a idon yarana, shiko yadda akayi nadawo gidannan .


Yasamo asaline daga sanda babansu yagano irin dukiyar dasuke juyawa ,munsha tashin hankalinsa sosai, har Saida nayi Masa bayani Bai Kuma gamsu ba ,Yi yake yana karawa Dan me Zan dauki kudi inbasu ,ai shiya kamata yadauka yabasu nayi masa shishshigi Dan haka in inason zaman lafiya tofa inkarbi kudinnan inbashi.



Yaufa akeyinta yinayi kamar Zan ari baki Dan fada, bude idona nayi ,hnagaya masa duk irin cutar da yayimin Bata isheshiba Sai yakara da wata sai da mahaifiyata takara ginani sannan zaice inbashi,na ce inkaga kudinnan sun dawo hannunka tofa sai dai inbani da rai,na ce kaifa ni wallahi akan kudinnan sai dai komai yafaru.


Au Haka kikace to shikenan nidai aurena dake mutu karabane bare kiyimin wata togaciya, kudi kuma saikin kawosu Kona waye, lallai naganeki batin yauba nema kikeyi sai kin zo dai dai dani ko ina ke Ina rike kudi oho bare Kuma irin wannan.


Haka mukaringa Zama dashi kullum fada ,daga baya kawai sai nawayi gari yarana sunce inzo muje Inga wani abu,ban musaba suka daukeni a mota wani dankareren gida sukayi fakin ,koni yabani Sha,awa balle a ce Wanda Bai taba ganin kerarren gidaba.



Masha Allah yayi kyau sosai, Haka nadinga cewa,cikin farin ciki sukace a irin alherin dasuke samune suka siyeshi ammafa haryanzu basu Gama biyan kudinba ,Dan Haka inyi zamana zasu tattaromin kayana su biyoni dashi duk Randa baba yagama fadan Kya komamasa ,Aiko cikin kankanin lokaci yadinga nemana har sai da yatayarwa dayaran hankali suka kawoshi inda na ke, mun dai daita tsakanin mu ,ammafa naji dadin gidan, na ce ko bani komawa Dole shima ya tattaro kayansa muka tare .



Bayan shekaru kamar biyar babban Dana yayi aure,cikin da ce da yarinyar arziki Yar gidan dattako, nidai nayi dacen suruka ,koyar dana haifa sai Haka gurin mutuntani,Kuma tsakaninta da Allah take ,Dan da da wata manufa ta ke da tini asirinta tonu ,bana nuna mata wani hali a matsayinta na surukata ,duk abinda yasamu ni ,Dan ko Abu yasiya mata wani lokacin takan nuna Masa muhimmanci na agareshi,bata yarda ya fifitata akaina ba,kuma na tabbatar gobenta zatayi kyau ,samun akasin Haka kuwa sai dai kaddarar Allah tinda shi komai rubutaccen lamari ne daga Allah.


Tokinji takaitaccen tarihina ,nakuma Baki komai atakaicene domin bamu da lokacin dazamu dauki dogon labari.

Umma ce taka doguwar ajiyar zuciya ,itako ameera tini takuma kulawa duniyar tunani mkomar sadiya take hangowa , tabbas samun rayuwa medadi gareta sai wani hukuncin ubangiji.


Daga nesa sukejin kwada sallamar da akeyi,


Baba iya ce ta ce yawwa gashinan yazo angode Allah.


Kai kai kai yau kunji dadinku kun matseni kunsami har raed more uku .


(Karimatu na miko gaisuwa ta gaida kowa musamman da addu oinku suka Isa gareta, )(

Sadiya ko ta ce duk sai tayi maganinku da ita kuke zancen😜Dan ta ce ...... uhmmmmm baruwana)

*INA BUKATAR COMMENT DINKU INHAR KUNA KUNA SO INCI GABA NA ROKEKU*



🀝 *DAGA ALKALAMIN YAR MUTANAN JINGAUπŸ™‹*
[21/01 Γ  12:10] +234 703 197 3585: πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€



😳😳😳😳😳😳




πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™

*_PART 2_*


*LABARI DA RUBUTAWA*


*BY*

🀝 *FAUZIYYA AUWALU ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹.





*πŸ…Ώ58(F FOR FREEDOM)*





🌈 *KAINUWA WRITERS✍🏾 ASSOCIATION* 🀝






Kiyi magana kike hararata, yaya katambaye ta ita tasan inda umma ta tafi, tasan inda ta ke, domin dukkanin kulawar umma kasan ita kadankawa bani ba, ban taba karbar wani Abu gurinka domin in kaiwa umma ba ,ita ka nadawa wannan nauyin.


Bin sadiyar da kallon tuhuma yayi,ita kuma dukkanin wata rashin kunyarta tayi kasa domin ga dukkan alama karyarta tana neman karewa.


Ya ce sadiya Ina ummata ?

Tsuru tsuru tayi takasa magana,matsawa gabanta ya dinga Yi a hankali har sai da yaje daf da ita, hannunta yarike cikin lallami ya sake cewa, sadiya Ina ummata; ganinsa cikin yanayin kaskan da kai agareta sai tayi tinanin ko har yanzu yanayinsa na da yananan.


Funcike hannun nata tayi , sannan ta nunasu da Dan yatsa ta ce ban Sani ba ,katambayi uwar kitifin data kawoka, da can bakasan umman Bata gidanba sai da wannan munafukar ta Tina maka, duk Wanda zai San inda uwarsa ta ke ai barin dane Dan......tas tass tasss,yasakar mata kyawawan Mari guda uku a fuska,cikin zare idanuwa bakinsa cike da masifa ya sake Kai mata bugu, da zafin Naman daba tasan tana dashi ba ta kauce ,



Cikin fargaba ta dafe kirji sannan ta kwalalo ido waje,ta ce " alhaji sabo"nika mara,nika mara agaban yaya na; na ce bansan inda ta ke ba ,kabani a jiyarta ne bare ka tambaye ni inda ta ke , Baki bude yake kallon ta tinani ya ke yaushe sadiyar ta koma haka ,dama haka ta ke Bai sani ba.


Dan yatsansa manuni ya daga yana nuna ta , da mamaki ya ke cewa , sadiya kin mance umma wacece a gurina,kin manta banida sama da ita,kinmanta zaman lafiya ta shine zaman lafiyar mahaifiyata;sad... ameera dake gefe daya kuma da alama suna neman mantawa da ita,ta tareshi cikin murmushi ta ce ai yaya takaicinka kadanne ,bakafara shiba, sai sanda kaji rayuwar da kayi da mahaifiyarka ,katuna, koma shekara tara ko goma da suka wuce,tuno sanda kake tseren ceton rai inkaga umma ,katuno lokacin daka Dena ciyar da umma a cikin gidannan,kamanta, Inka manta bara natina maka ,in kuma baka neman tini kayi tinani ,katuno rabon da kaga umma ,katuno na ce inkuma baka Tina ba ,Zan labarta maka kadan daga cikin halin da umma tashiga "yaya sabo"kataba kwana da yunwa bakaci abinci ba ;kataba wuni da yunwa bakaci ba shin kataba rasa gidan da zaka Dora duwawunka domin neman masalaha a rayuwarka nasan tinda ka mallaki hankalinka a iya sanina baka taba wuni cikin kunci da sunan umma ce tasaka ba,to kaduba wannan,kaduba ka gani duk abinda na lissafa maka tofa rayuwar da umma tayi kenan,Kuma sanadin wa; na ce sanadinwa, ka ce min kaida matarka ka ce ku kukasa umma tayi rayuwar bakin ciki,to ingaya maka daga sanda kajuyawa umma baya bata taba wayar gari ta wuni batare da bakin cikin sanadin da wannan matar tayi Mata ba.


Shegiya munafunka ,duk me irin halinki bazai gama lafiya ba.

Batada bakin magana domin ameera nema take ta ballo mata ruwa,


Shiko gurin yaransa ya dosa wadansa suka cure gu daya ,kamosu yayi gaba daya ya rungume su, hawaye ne masu zafi suka zubo masa domin shidai yasan da hankalinsa bazai aikata hakaba ,to me yasame shi da yadinga yiwa ummansa haka, lallai shidin me laifi ne,to yanzu a Ina zai ganta ,Ina zai dosa domin nemanta, lallai sai ya tubarwa Allah, tuba me tsanani domin hakkin uwa Babu wasa a cikinsa , tabbas bazai taba ganin da kyauba domin yariga ya lalata ayyukansa, rungumesu yakumayi domin yanajin kewa atare dashi, yanajin inshine haka ta faru a gareshi zai iya rasa abubuwa da dama, ciki ko harda farin cikinsa na din din din.

Sadiya ce ta matso kusa dashi ta tsuguna, nadama takejin kamar zata shigeta ammafa har zuciyarta tana kulla ce da ameera da umma.


Kallonta yayi baisan meta aikataba ,baisan ita ce da alhakin dukkanin matsalarsa ba , amma Kuma yanajin Bai yarda da ita ba, bangaran da ameera ta ke ya kalla ya ce mata shige muje Ina son magana da ke, kiyimin wannan alfarmar Dan naga kinfusata dani kiyi hakuri bisa laifin dabansan na aikata shiba.



Zainab ce tafe cikin farinciki ,jitake dukkanin matsalarta ta yanke,danko gani ta ke duk Wanda ya ce mata kule zata ce masa casss.


Da sallama dauke a bakinta tashiga gidan duk suna tsakar gida a zaune,bakuma wanda ya amsa mata sallamarta.


Ko kallonsu batayi tafara kiciniyar bude kofa,khadija ce ta ce to Yar karoro kijiraci dawowar me gidan, domin yatafi Samo mana abinda zamuci ,hukuncinki me girma ne ,saboda rashin mutunci baki bamu dumame ba ,Baki bamu na Rana ba ,kinsa kafa kinfu ce yawon gantalinki, kin barmu da yunwa to inya dawo zakiyi bayani.



Kallon wulakanci na watsa mata tare da juyowa gareta ,na ce kitaka a hankali domin nidin banida kyau karki so mugauraya, wallahi
bazatayi Miki dadiba ,Dan haka da babbar murya ki iya bakinki.


Baba ce tayo tsagal ta ce to rasa kunya beran tanka kindawo din Zaki addabemu bayan wunin damukayi da yunwa yanzu kuma kin dawo Zaki bimu da rashin kunya ,to zanyi maganinki Yar banza da bata girmama manya,koda yake nasan bakinciki kike da cikin da ta ke dashi shiyasa kike hanamu abinci to duk abinda yasamu cikinta ke ce ,muguwa me mugun hali,ke baki haihuba kuma kinawa wata bakin ciki.





*INA BUKATAR COMMENT DINKU INHAR KUNA SO INCI GABA NA ROKEKU*


🀝 *DAGA ALKALAMIN* *YAR MUTANAN JINGAU* πŸ™‹
[21/01 Γ  12:10] +234 703 197 3585: πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
πŸ€¦β€β™€



😳😳😳😳😳😳




πŸ™ *ABINDA KE FARUWA* πŸ™

*_PART 2_*


*LABARI DA RUBUTAWA*


*BY*

🀝 *FAUZIYYA AUWALU ALIN BABA JINGAU* πŸ™‹.





*πŸ…Ώ57(E FOR* *EVECTION)*





🌈 *KAINUWA WRITERS✍🏾 ASSOCIATION* 🀝



Dan wallahi da tini na gudu da kafafuwana,


Kema batare da bin ra,ayinmu ba ,sai dai kiyi kokarin daukar wadda zata fishsheki, a matsayin ki da kike da karancin shekaru, duk da kina da naki shekarun amma dai nasan kasa kike damu ,dole fa ki alkinta rayuwarki, karki bari wani Dabe San ciwonki ba ya mayarki shara abar wulakan tawa, kiduba darajar da Allah yayi miki, sannan kiduba kedin mace ce ,ita Kuma diya mace tana da limit Dan haka dole kiringa tattalin rayuwarki.


Yanzu kinje kin zauna kin kwashe wasu shekaru dashi ,ke ba dan kida bare Dan rawa,bakuma Kya tinanin kiyi gaba ko Zaki dace,shikuma baya Miki tinanin neman mafitar meya hanaku haihuwa tare,bare kisan matsayinki, shiko dake da right akan Al,amarinsa kinga kotakanki baibi ba yasamowa kansa mafita, tinda bazai iya jiranki har sanda Allah zai Baku rabon da yayi niyya ba,ba,anan matsalar take ba duk da wannan ma matsala ce kuwa babba ,domin Yaya sune cikakkiyar ribar aure ,kefa har yanzu a alakoro yake ganinki ,kinsan ko alakoro bawani daraja ne dashi ba ,domin dashi da Babu duk daya,

dago Kai tayi ta kai kallonta gareta ,ta ce kiyi hakuri Zaki iyajin fiye da haka, domin innaga mace tazauna namiji na waharta yadora mata dukkanin zaluncinsa kanta, sai inji kamar inkwatota daga gareshi, banasanin irin kalmomin dake futa daga bakina,saboda bacin rai.


Kinsan meyasa na ce Yana Miki kallon alakoro,girgiza Kai tayi tare da cewa a,a bansani ba,saboda har yau baki bashi riba ba,Baki bashi ribar auran da ake bayarwa ba, ke Kuma bakya tinanin kisamu, Allah shike bayarwa a Kuma lokacin daya gadama ,
yake Yar uwa kiringa hangen gobe a rayuwarki me gobe zata haifar miki,


Wai shin bakya bukatar kema kisami farinciki, ko Baki Sami farin cikin me gida ba in kinada diyoyinki ,kin wuce wani mataki Daba kowa ke zuwa gareshi ba,na tabbata da kina da yaro a gabanki kin wuce wani wulakancin,ko ba a gurin uwar mijiba Kya wuce shi a gurin kishiya,,wataran inbata kyaleki Dan Allah ba zata kyaleki Dan danki daga randa ta kalleshi taga kwarjinin mazantaka tare dashi,ko taga mammora atare dashi,toke a cikin wannan Wana tanadin kikayiwa kanki,ko kin hakura kin sallama kin dorawa kanki abinda Allah bai dora miki,kin zauna kina wahalar kishiya da surukar da take neman ganin bayanka ta kowacce hanya,to duk meyajanyo kika hakura ,kawai Dan kina gudun karki zama bazawara ,ko Kar a Fara kirga Miki aure,sai kije kinemi guri kizauna wani can da baisan ciwonki ba ya tauye Miki hakki ke ba kya tinanin kema kisamarda iri wanda Zaki fatan asami shekaru tambarinsu na alheri yana bugawa,

Niko kinganni Nan duniya tare da cikar burina Inga ranar da Dana ko yata zasu Zama wani abu, Ina addu,ar Allah yasa Al,umma su amfanesu, ko su amfani gabarsu, ko dukiyarsu,kinsan ance da d'a da dukiya ba Wanda yasan me morarsu sai Allah, tofa ni har kullum ina mefarin ciki a ce Dan da na haifa duniyar musulunci su amfana dasu.

Ke bakya wa kanki fatan Haka,kodai kin hakura kin sallama kishiya tayi ta haihuwarsu ke Kuma kina fama da wahala,
Dan haka ki sauya kiduba wannan zaurancen nawa ,kiduba ki dauki Wanda zai amfanarki ,karki dauki Wanda Zaki zo kina Dana Sani,domin komai sannu sannu ake binsa.


Zainabbbbb takirata da babbar murya kitashi ki koma gida ,ki sauya daga yau kidena yiwa wadanda basu dauke ki mutum ba bauta ,ki hakura da mijin nan naki,ki hakura da farin cikinsa,karki ringa hango matsayin dazaki shiga yayin kwatowa kanki hakki,ki hakura da so,ki hakura da so,ki hakura da so,mazanmu yanzu basa dubashi ,duk sanda zasuyi miki rashin kirkinsu tofa yi suke ,da da akwai sonnan namu garesu na gaskiya da munci arzikinsa garesu, daga sanda kika Zama saniyar tatsarsu gurin sex sun gama yin so dake ,domin sun mayarmu baiwa sun mayarmu bayinsu ,babu alfaninmu da suke dubawa zuwa garesu, kalilanne daga cikinsu suke duba muhimmancin mu garesu ,Dan haka kitashi tsaye domin neman mafita, ko baki nemi sallama daga gareshi ba dole ki gyara Al,amuranki dolesu sauya kinuna masa kema cikakkiyar mace ce me kima,karki Kuma daukar cin mutuncinsu gareki,yoma keda kike da Sana,a macen da Bata da abinyi itace me fargabar daukar mataki ,biyayya ai kinyi musu ,to yanzu kije ki gwad baiwar da Allah yayi miki ta diya mace,ki kwatowa kanki yanci,nabarki da wannan inda me Yi mata Karin bayani kuma sai ya dora domin zuciya neman bugawa take dan haushi.



Malama ramla ce ta ce kamar yau kika sabajin *ABINDA KE FARUWA* a gidajen mutane.


Aini duk sanda naji ,nakanji lamarin kullum sabo,domin har yau sunki su sauya mukuma munki mu sauya su Dan haka dole muyita ganin abubuwa daga garesu.


Mlm nafisa ce ta ce to aike mlm karimatu lamarinki ai ya sauya,ko ba duba ai kinci ribar farautarki, sai ki godewa Allah Dan kowa ya kalleki ,ya kalli yaranki ai ya San jiya da yau badaya ba,duk da jiyan batayimiki muniba ,kodan jajircewarki,Dan haka sai dai mukara dagewa da addu,a Allah ya kara lamuce

21 / 31