Zafin Rana Book Compelet Novels By Aysha Alto

Author :  Aysha Alto Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   10 / 28

27K to 30K   out of 81.6K words

daki daya, shine naje na bincika kuma sai gashi na tabbatar akwai yarinya"

dake kwana dashi.

Idanun Abdulsalam ne ya canza yace  mene?

"Ta sunkuya tace  gafara Takawa, laifina gagarumi ne ni na sani amma bazan bari wani abu ya"

sameka ba.

"Abdulsalam yace  Binta ce amma a bangaren Azeema take, me zaisa kice suna kwana tare? "

Tace  wallahi da gaske Takawa da kaina na bincika.

"Yanda fuskarsa ta nuna bacin rai tsantsa ne yasa ta kalleshi, a hankali ya saki fuskarsa sannan"

yace  a aika Azeema da Junaid suzo. Mikewa tai da sauri ta fita.

"Abdulsalam yai shiru yana tunani, bazai yadda da hakan ba harsai yaji da kansa."

Azeema ta farka taci abincinta Junaid shima an kawo nashi yana ci.

Wani irin dadi take ji wanda tunda taga Junaid bata taba jin irinsa ba sai yau.

Kallanta yai yace  Umma ya akai?

Murmushi tai sannan ta mike zaune tace  mamaki nake haryanzu kana nan.

"Yadan sunkuyar da kansa yace  kiyi hakuri, maimakon na duba yawan shekarun da kikai kina jirana, sai kawai na duba yanayi na na rashin sabawa dake dabanyi ba. "

Kai ta girgiza da sauri tace  sam ba haka bane na fahimceka nasan kuma a hankali zaka saba.

Nagode.

Murmushi tai sannan a hankali ta mike ta shiga toilet.

Tana fitowa tace inka gama muje ka zagaya kaga yanayin gurina.

Zaki iya fita?

Tace  eh gwara nadan zaga ko naji karfin jikina.

Murmushi yai sannan yace to.

"Tare suka fita suka zagaya cikin fadarta, ga gefen shuke shuke, ga hanyar da zata sadata da wani"

"bangare, tace  nan ne asalin bangarenka. "

Kallan gun yai kamar mai shirin tunowa sai kuma yai murmushi yace  a bude yake? Tace  eh muje ka gani.

"Nan suka shiga ciki, tsaf yake kamar wanda akwai mutum a ciki, ga komai akwai a bangaren."

"Kallanta yai, tai murmushi tace  nasa an barshi a yanda yake ne akan tunanin kullum zaka dawo gurinka. "

"Tausayinta ne ya kara kamashi, ya kalleta jiki a sanyaye yace  nagode Umma, Nagode da kullum"

nake ranki.

"Idanunta ne suka ciciko, ta juya kanta gefe tare da saurin fitowa."

"Shima fiyowa yai Barira ce ta shigo gun da sauri, ta kalli Azeema tace  Gimbiya mai martaba na kiranku ke da Yarima. "

 Mai martaba?

"Ta fada tare da kallan Junaid, dakinta ta koma ta kara shiryawa, alkyabarta mai launin ruwan kasa"

"ta saka, Junaid na aiken wata kuyanga akan taje tacewa Binta yana zuwa ta fito, bata kalleshi ba har kuyangar ta tafi sannan suka fito tare."

Bangaren mai martaba suka nufa yana zaune shi kadai suka shigo.

Sai da suka gaisa sannan ya kalli Azeema yace  Azeema meke faruwa?

Tace  name kenan?

Maida idansa kan Junaid yai cikin zargi yace  Junaid a ina yarinyar da muka taho tare take kwana?

Ba tare da wani tunani ba yace  Bangarena.

Da sauri Sarki ya kalleshi yace  mene?

Junaid ya kalleshi sannan ya kalli Azeema wacce ya kasa gane halin da take ciki......

*****

*ZAFIN RANA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

*Shafi Na Ashirin*

Mai Martaba yace  wani irin abu nakeji haka? Taya Junaid zai dinga kwana da ita? Bama a

bangaren Bayi ba?

Azeema ce ta kalli Junaid sannan ta kalli Sarki tace  Nasan bai kamata ba sai dai ganin hankalin

Junaid ya kasa kwanciya yasa na barshi.

 Dan hankalin Junaid bai kwanta ba sai ki bari yai abinda zai barmai tabo? Ke din?

"Junaid ne ya daure yace  Tuba nake ranka ya dade amma haryanzu banga aibu akan haka ba, na farko Binta ba a dakina take kwana ba. "

"Kallansa Mai martaba yai yace  zan ma tambaya, yanzu daka shigo nan a ina kake? "

" Fadar ka, ranka ya dade. "

To waye ya san kana nan ko kana cikin turakata?

"Junaid yai shiru, yacigaba  yanzu inka shiga cikin dakina ko bandaki na waye ya sani? "

A hankali yace  babu.

To fadamin Yarinyar a ina take kwana? Junaid ya kalleshi yace  a bangarena.

 Me kake tunani mutane zasu fassara? Abinda basu taba gani ba?

Junaid yai kasa dakai yace  A gafarceni.

"Sarki ya canza yanayin kallan da yakemai, yace  ka maidata bangaren Azeema ko ta koma bangaren bayi ta zauna, na taho ma da itane jin tare kuka taso, ganinta a kusa dakai zai debe ma"

"kewa, wannan abinda kakeyi bakasan zai iya janyo ta shiga wani hali ba? "

Junaid jiki a sanyaye yace  Tuba nake.

Sarki yace  shikenan jeka huta.

Junaid ya mike tare da godiya ya fita.

"Idanunsa ya maido kanta ya kura mata ido, fuskarta ta hade itama ta kalleshi, yace  me kike"

tunani?

Tace  me kuwa? Na bari ne saboda karyaji ba dadi.

Wani irin murmushi yai sannan yace  ke din?

Kallansa tai tace  tundazu kake cewa nidin?me kake nufi.

Idanunsa na kanta yace  badai kishi kike da yarinyar ba?

Kallansa tai da sauri tace  kishi?

Yace  to fadamin menene na barinta ta kwana dashi bayan kinsan za a yada akan suna kwana tare? Sannan kina ji har gulma ta gama yaduwa ba tare da kin dau mataki ba?

"Ranta ne ya baci ta mike zata fita, mikewa yai ya riko hannunta da sauri, juyowa tai ta kallanshe,"

hannunta yaja ya shiga da ita dakinsa ya zaunar da ita akan gado yace  haushin me kikaji? Haushin na fadi abinda kika shirya?

"Kallansa tai bakinta tadan motsa sai kuma tai shiru, menene ba haka bane? "

Hannunta ta kwace tace  ya kakeso nayi? Yarona ya dawo amma kamar ya sake barina? Bai

damu da mahaifiyar datake jiransa shekara da shekaru ba? Bai damu da yayensa ba? Ba abinda ya dameshi da wace rayuwa nai? Bai damu ya sanar dani rayuwar dayai ba? Komai ka taba zancenshi

"daya ne Binta, ya kakeso nayi? "

Shiru yai yana kallanta a hankali ya zauna kusa da ita ya jawota jikinsa ya rungumeta yace

 hakan da kikai kina tunanin mafitace?

"Tace  bani nai ba, sai dai hakan zaisa ya nesanceta ko dan samun kwanciyar hankalinta, hakan"

zaisa ya maida hankalinsa kaina.

Hannayensa ya sa akan kuncinta yace  shiyasa nace kishi kike.

Dan idanunta ga juya tace  inji wa?

Yace  gashinan kina abinda kika dade bakiyi ba.

"Murmushi tai tace  ka nemomai mata ya aura dan Allah, na tabbatar in akwai mace a kusa"

dashi dole ta kama gabanta.

" Korarta kikesanyi? Kiyi hakurin kwantar da ranki, Junaid naki ne ba wanda zai kwace miki shi. "

Tace  haka da na dauka amma yanzu nasan ba haka bane.

Murmushi yai sannan adan ja kuncinta yace  wannan mamar akwai neman fada.

*************

"Junaid ransa a bace ya shiga bangarensa, Azi ya bishi da sauri, Junaid ya kalleshi yace  wai kaji"

abinda ake cewa?

Azi yai kasa dakai yace  Tuba nake Yarima amma zancen nan ba inda baije ba.

Junaid yai shiru sannan yace  ina Binta?

"Binta? Nan Azi ya mike dan kiranta, Hari na zaune a waje suna hira Azi ya shigo, Hari ta kalleshi"

yace  Binta fa?

Binta? Cikin mamaki tace  tabi yarima tun rana.

 Yarima? Yanzu kuma shiyake nemanta.

"Mikewa tai da sauri suka fito tare, Junaid na zaune suka shigo, kallan Hari yai yace  tana ina? "

Hari tace  ta bika ai.

Junaid yace  ni? Yaushe? Tun rana.

Mikewa yai da sauri tace  bansan waye a gabanta ba amma ba ita kadai ta fita ba.

Hankalinsa ne ya tashi yace  tun rana?

Tace  eh wlh tun rana.

"Da sauri Junaid ya fito Azi da Hari ma suka rufa mai baya, nan suka fito waje, Junaid yce  mu"

"nemeta a hankali, kar hankalin wasu ya kawo kanmu. Sukace to."

"Nan suka fara nemanta sai dai duk inda sukabi babu alamunta ga guri kato, Junaid kam"

"hankalinsa ya tashi ya nufi gun bishiyarnan sai dai ba ta gun, nan jikinsa ya kara sanyi, badai jin"

abinda ke faruwa wani ya mata wani abun ba?

"Kalaman Sarki ne ya fado mai, hankalinsa ne ya kara tashi, Hari dake ta nemanta itama itace ta"

"zo wucewa ta bangaren Raga, kamar zata nufi gun sai ta juya tana tunanin me zai kawota gun, harta juya taji ana dan buga kofar kadan, kasancewar dare ne sai ta kara waigawa cikin dan"

"fargaba, ji tai an kara bugawa kadan, a hankali ta nufi kofar gun, tace  Binta? "

"Daga ciki wacce ta gama galabaita ta kasa komai sai kokarin buga kofa da take da kyar, tace"

 naaam.

"Da sauri Hari ta zari ichen da aka sa aka tare kofar, Binta ta gani a bakin kofa, da sauri ta riketa"

tace  Binta? Me kike anan?

"Kallanta tai a galabaice tace  bansani ba nima, Hari ruwa ruwa.  "

"Hari ta taimaka ta dagata ta ririke hannunta, suka fara takawa a hankali, Hari tace  wani mara"

imanin ne ya kulleki?

Binta cikin dauriya tace  Barira ce.

Da sauri ta kalleta tace  Barira?

"Kai ta daga mata alamar eh, Hari tace  karki fadama Yarima Barira ce. "

Kamar zata tambayeta dalili sai ta kasa saboda karfinta dake tafiya.

"Suna shawo kwana Junaid na shawo kwana, da sauri ya karaso inda suke, kallan Binta yai wacce"

"ta kalleshi itama tare da kokarin yin murmushi, ya kalli Hari yace  meya faru? "

Hari tace  watace ta kirata akan tazo injika shine ta kulleta.

Kallanta yai cikin tausayawa dan ya san shiya ja mata yace  muje ta kwanta.

"Nan suka karasa, suna tafe yana tunani kala kala a kansa har suka isa. Harira tace  bari na wace da ita can. "

"Kai ya daga alamar to, suka wuce."

Shiru Junaid yai harsai da suka rufe kofa sannan ya juya ya shiga ciki.

"Zama yai akan kujera tare da hada hannayensa, tabbas Hajjo ko Zeenatu ne suka aikata hakan,"

sannan dolene ya canza takunsa tunkafin Binta ta rasa ranta a dalilinsa.

"Shiru yai yana tunani, ke din? Kalaman Sarki ne suka fadomai, kai ya girgiza da sauri yace  ba ita"

"bace, wadancan biyu dai a cikinsu ne. "

Inhar yanaso ya kare Binta to lalai dole ya fahimci masarautar nan ya kuma san abinda ya dace

yai.

"Azi? Kiransa yai, wanda ke waje."

"Shigowa yai ga zube a gabansa, Junaid ya kalleshi yace  Azi fadamin me ka sani a game da"

masarautar nan?

Azi yai shiru kafin yace  bansan abubuwa ba saidai nasan kana tsakiyan makiyanka.

Junai ya kalleshi yace  nasan wannan amma me kake tunani a tattare da ita?

Azi yai shiru can yace  karka yadda da kowa.

Junaid yai murmushi yace  tashi kaje na yafe tambayar.

"Azi ya mike yai waje, Junaid ya kalleshi sannan ya mike ya shiga dakinsa........"

Binta kam na shiga ta ci abinci ta sha ruwa dakyar tai sallah ta hau bacci.

"Harira ta zuba mata ido tana kallanta, tana tausayinta sai dai ta tabbatar Azeema tanada hujjarta"

"na kin yadda da ita, sai dai aganinta abin baikai haka ba, gwara tace ta tafi data nemi halaka ta."

******

*ZAFIN RANA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

*Shafi Na Ashirin da Daya.*

"Duk yanda Junaid yaso yai bacci ya kasa, wannan lamarin ya tsaya mai a rai, ance ya taho da"

"mata, ance tanada ciki, sannan an kulleta."

Kenan nan gaba baisan abinda za a iya yima Binta ba? Kawai a dalilinsa.

"Acan bangaren Binta itama sam ta tunda ta farka cikin dare ta kasa bacci, juyi kawai take tana"

tunani metama mahaifiyar Junaid da zata sa a kulleta? Anya zamanta anan alkairi ne? Karfa ace ta

zama wacce a dalilinta Junaid ya shiga wani hali.

"Jitai kamar ana magana a waje mikewa tai a hankali ta leka windown dakin, Harira ce tsaye ga"

"Azi a gefe, Azi yace  kiyi hakuri nasa kin taso. "

"Tace  ban mayi bacci ba dama, abinda ke damuna nasan shine ya hanaka bacci. "

Azi ya kalleta yace  waye ya kulleta?

Shiru tai kafin tace  Barira ce.

Sam baiyi mamaki ba sai dai yace  zance har gun Sarki inaga yaje akan Junaid ya taho da mace a cewar wasu ma tanada ciki.

"Jikin Binta ne ya fara rawa, muryar Harira taji tace  yanzu lokaci ne na Junaid ya cire yarinta da rashin damuwar dake ransa, inba haka ba haka zai zama wanda bashida ra ayin kansa, dan a"

hankali sai Gimbiya ta juyamai ra ayinsa.

"Zubewa tai ta zauna, a hankali wasu zafaffan hawaye suka shiga zubo mata."

******

Me kake tunani? Ke mana Gimbiya ta

"A hankali ta juyo da fuskarsa zata sumbaceshi, idanunta ta bude sannan ta kara maidasu ta rufe, hara budesu tai sannan a hankali ta mirgina akan gadan, saura kiris ta afka kasa ta danna kanta da pillow tare da yin ajiyar zuciya, meke damuna?"

A hankali ta mike zaune sannan ta kalli kofa cikin gadara tace  Fure.

Jin shiru yasa ta sauko daga kan makeken gadan naga sannan ta bude kofa.

"Fure ce keta kokarin nuna musu inda zasu ajiye abinci, jin bude kofa yasa ta juyo, ganin Zeena"

yasa ta taho da sauri.

Zeena tace  Fure zo.

"Fure ta bita suka shiga ciki, zama tai a kan gadonta mika mata kafarta da sauri ta fara matsa mata"

"su, Zeena ta kalleta tace  Fure me kike tunani tsakanina da Yarima? "

Ba tare da wani dogon tunani ba tace  makiya?

"Kafa tasa ta hanbareta, Fure ta fadi, da sauri ta mike ta cigaba da tausar, Zeena ta hade fuska,"

Fure tace  Gimbiya badai kina tunanin wani abin bane bako?

Kamar me?

Fure tace  bakomai dama a shirmenane nake tunani ko kina sanshi.

Kara bigeta tai da kafa tace  ni nake sanshi? Bama shi ba? Tashi ki ban gun banamasan tausar.

Da sauri Fure ta zube a kasa tace  tuba nake Gimbiya sai dai ina ganin in kinassn Junaid ai

"komai mai sauki ne indai yana sanki, inkuwa bayayi ki fadawa Takawa. "

A kufule tace  kina tunanin zan auri wanda bai sona? Kuma uban wa yace miki ina sanshi? Tashi

ki fita.

"Ta zube tana bata hakuri, Zeena a zuciya tasa hannu ta finciketa tai waje da ita ta rufe kofarta,"

"zama tai dabas akan gado cikin kuluwa ta zauna agaban madubi, kanta ta kalla cikin takaici ta mike tai bandaki."

********

"Kasancewar kasa bacci dayai hakan yasashi yin bacci sosai, dan sai da rana ta fito ma ya farka, a"

"zabure ya mike yai sallah sannan ya kara kwanciya, bacci ne ya sake daukarsa sai dai bai dade ba yaji motsin bayi na gyare gyare hakan ya sashi farkawa."

"Fitowa yai ya shiga yai wanka sannan ya shirya ya fito, bangarensu Harira ya nufa, Azi na ganin ya"

"fito ya ajiye ban ruwan da yakeyi ya nufoshi, duk da bayin dake binsa a baya. Junaid ya kalli Azi yace  zanga jikin Binta ne. "

Yace  ko a kirata? Bari naje.

" to Yarima, dama dazu aka aiko kaje bangaren Gimbiya kuyi karin kumallo. "

To kawai yace yai ciki.

"Harira najin an sanar da isowar Yarima gun yasa ta kalli Binta dake kwance tace  Binta, yarima"

yazo.

Kallanta tai tace  Hari kice ina bacci dan Allah.

Cikin mamaki Hari tace  meyasa? Junaid ne fa?

Murmushi tai wanda hawaye suka taru a idanta tace  dan Allah.

"Harira ta kalleta sannan ta mike tai waje, gaida Junaid tai sannan tace mai tana bacci tare da cewa  in ta tashi tazo. "

"Junaid ya kurawa dakin ido sannan ya juya, Binta ce ta share kwallarta Hari ta shigo tace Binta? "

Binta ta kalleta tace  taya yana Yarima zaizo nan? Ba gwara yace inzo ba? Hari bansan ya zanyi ba. 

"Kuka ne ya kunce mata, tausayinta ne ya kama Harira ta matso ta rungumeta, Binta tana kuka"

tace  bankai matsayin da zan wargaza mai rayuwar daya dace da ita ba 

"Harira tai shiru tasan tabbas hakane, amma ya za ayi? Junaid da Binta sun taso tun basusan kansu ba, taya zasu amshi wannan saban yanayin?????"

*********

Junaid kam yasan idan Binta biyu dan tun asali ko rashin lafiya takeyi bata taba kaiwa wannan

"lokacin tana bacci? Sai dai baisan dalilin sa shima nakin tilastawa sai ya ganta ba, yana fitowa"

waje yai suka nufi nangaren Azeema.

Azeema tana zaune akan kujerar ta tasha ado sosai kamar yadda ta saba tana zaune tana dan

"kada dan yatsanta, Allah ne kadai yasan me take tunani a wannan lokacin, barira ce ta matso tace"

 Gimbiya sun dauketa jiyan.

Ba tare da ta bude ido ba tace  iyanzu nasan ya fahimci nisanci da itane kadai kwanciyar

"hankalinta, inba haka ba wayasan mezai sameta gaba. "

Barira tai murmushi tace  banaji tace nice na kulleta.

"Azeema tace  in ta fada kina tunanin shi zai yadda? Bayan yasan kina wajen wanzami lokacin? Kinga in ta fada alamace ta tana neman shiga tsakanina dashi, wanda har gwara tai shiru. "

"Sanarwar isowar Gimbiya Zeena ne yasa Azeema ta bude idanunta a hankali, Zeena kuma?"

"Zeena ce ta shigo tasha kwalliya kai kace wani taro zata,

10 / 28