Zafin Rana Book Compelet Novels By Aysha Alto

Author :  Aysha Alto Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   28 / 28

81K to 81.6K   out of 81.6K words

neman halakata, shiyasa ana haifarsu ta nemi a dinga kawosu."

"Ramlatu kam ta zama yar sai a hankali, an tasheta itama daga inda take tabar cikin masarauta."

"Junaid ya samawa Azi mata aka auramai suke zaune a nan masarauta, Harira ma tayi aurenta."

"Yau sun tashi ana ta shiri saboda kasancewar yau ranar sallah karama ce, tun safe ake ta hada"

"hada a fada, Zeena ce ta kalli Fure tace ""Zanje na dawo."""

"Da sauri Fure ta taso, Zeena tace ""ki zauna ni kadai zani."""

"Nan ta fito ta nufi hanyar bangaren Junaid, yana zaune yana duba littafin dake gabansa Zeena ta"

shigo.

"Kallanta yai yace ""Zeena?"""

"Zama tai kusa dashi tace ""me kake gani game da yau?"""

"Yau? Ya tambaya, tace ""maganar da mukai"""

"Yanayin fuskarsa ne ya canza yace ""kina ganin yaune kuma ya dace?"""

"Tace ""naga yanzu kowa na hidimar shiryawa, sannan hankalin kowa baya fada har dai zuwa"

"yamma idan za'ai hawa."""

"Yanzu ya fahimci manufarta yace ""na gane, zamuje taren?"""

"Idanunta ne suka dan canza ta girgiza kai tace ""kaje kai kadai yaya ni zan zauna anan harka dawo"

"saboda kauda kokonto."""

"Murmushi ya saki cikin jin dadi, sannan ya rungumeta yace ""nagode Gimbiya."""

"Fita yai ta kofar baya bayan ya kira Azi, suna fita Azi ya zagaya ya fita da mota Junaid ya hau suka"

nufi kauyen.

"Azeema na zaune tana tsince shinkafa, gefenta kuma Barira ce tana fifita ruwan dake kan wuta,"

"Abdulsalam dake cikin dake a kwance rai a hannun Allah ne ya fara tari, mikewa tai ta shiga dakim, tari yake sosai hadda amai, ta rikeshi ya gama sannan aka gyara gun, duk sun canza in ka gansu abin tausai, dan ma Azeema ta taho da kadararta da kayanta su suka saida suka yar gona suna noma."

"Sai daya kwanta ya kamo hannunta yana lumshe idanunsa, yau kam tun safe yake kwara amai"

tsoron halin nan da yake ciki take gashi yasha magani amma abin karuwa yake.

Gimbiya!

Yanda Barira ta kira sunan ta a razane ne yasa ta sakeshi ta fito.

"Daga bakin kofa ya tsaya gaba daya jikinta ya hau rawa, Junaid wanda ke tsaye ne ya mata"

murmushi.

Shigowa yai ya zauna kusa da Abdulsalam.

"Kallansa yai sannan ya kalleta yace ""jikin ne?"""

"Jin muryar ne yasa Abdulsalam ya bude idanunsa, yana ganin Junaid ya fara kokarin mikewa sai"

amai.

Junaid ya maidashi ya kwanta sannan ya kalleta.

"Abdulsalam ya kamo hannun Junaid yace ""Junaid ka yafemi """

"Amai ya shiga kara yi kai kace kayan cikinsa zai amayar, nan hankalinsu ya tashi, Junaid ya rikeshi"

"yace ""na yafema kai shiru ka kwanta."""

"Sai dai ina, jikin ne ya sake rikicewa anan rai yai halinsa."

"Bakaramar firgita Junaid yai ba ganin baya numfashi, hankalinsa ya tashi matuka."

"Azeema kam kasa ko kuka tai, haka Junaid suka mai sallah suka kaishi, nan ya nemi su koma da"

"Azeema amma tace anan take san zama, dole ya taho ya barta."

"Tunda ya shiga moga idanunsa sukai jaaa sosai, tausayin Zeena da Binta su kara kamashi, dole ne"

"ya zamar musu uba, yana fatan Allah ya tayashi rekesu cikin adalci."

"A haka ya isa akai hawa, sai daga baya akaji rasuwar sa......"

Allah ya mana mai kyau Ameeeeeen

****

Ayusher

Ina mika godiya gareku gaba daya wadanda suka sai littafin nan nagode da karamci da kuma

"kauna, kura kuran dake cikin littafin nan Allah ya yafe min su, wanda na fada daidai kuma Allah ya bani ladansu."

"Muna nan haryanzu a tare tunda bamu karasa A GIDANA ba. mu cigaba daga can muji Goggo,"

"Adamu, Zainab da Khalid da kuma Razy "

Love you soooo much

Onelovec'þ

28 / 28