Zafin Rana Book Compelet Novels By Aysha Alto

Author :  Aysha Alto Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   12 / 28

33K to 36K   out of 81.6K words

Zubair mahaifinka shi kadaine yao tsawan rai a  ya yanta maza, ta haifi maza guda hudu amma duk sun rasu kafin suyi aure shikadai ne har ya hau mulki sannan ya hayayyafa. "

Junaid cikin mamaki da tausayinta yace  ba ita bace mahaifiyar Sarki?

"Tace  AbdulSalam itace ta rikeshi tun yana karami, sai dai ba ita ta haifeshi ba. "

"Junaid ya jinjina kai, shiga sukai ciki, Jakadiya wacce ta sauka ta koma bangaren Hajiya Inna tana"

"zaune a waje suna hira da wasu, tana ganin Azeema ta mike da sauri, dukansu suka hau gaishesu, Jakadiya ta kalli Azeema cikin mamaki, dan rabanta da bangaren nan ita kanta bazata iya tunawa ba."

"Azeema tai gaba Junaid yabi bayanta, Hajiya inna na zaune tana bare goro Jakadiya ta shigo tana"

sanar da ita zuwan Azeema.

"Hajjiya Inna ta dago dayake bata gani sosai, ta kalli Jakadiya cikin muryar tsofafi tace  wace? "

Jakadiya ta kara sunkuyowa tace  Gimbiya Azeema.

" Uban wayace ina nemanta? Karta kuskura ta shigomin nan dan koda wasa bana nemanta, na"

dauka na fada mata ko mutuwa naj kartazo nan?

Jakadiya ta kalleta tace  Hajiya kidan saurara tare take da Junaid kar yaji.

Junaid?

"Ta fada muryarta na rawa, Jakadiya tace  eh. "

"Azeema da Junaid da sukai shiru a waje saboda kalaman Hajiya Inna, Junaid ya kalli Azeema"

wacce itama ta kalleshi tai murmushi tace  karka damu bakomai.

"Jakadiya ce tace su shigo, Junaid ya kalli Azeema sannan suka shiga ciki."

Hajiya Inna ta mika hannunta tana cewa  Junaid!

"Matsawa yai gunta ya rike hannunta, kankame hannun sosai tai muryarta na rawa tace  Junaid! Junaid ashe da gaske sukeyi ka dawo. "

Ido yake kara kuramai? Ta zare hannunta daya tana shafa fuskarsa cikin farin ciki.

Gaisheta yai t amsa tana cewa  ina ka shiga? Kakarka nata addu ar ganinka kafin ta mutu?

"Azeema ce ta gaisheta, bata tanka mata ba ta cigaba da cewa  lale lale Junaid. "

"Azeema cikin sanyin murya takara gaisheta, ran Hajiya Inna a bace tace  tunda na barki kika shigo ai sai kimin shiru ko? Wallahi badan darajar Junaid ba zama a dakin nan bazaki sakeyi ba sai dai bayan raina. "

"Azeema tai kasa da kanta, Junaid wanda kalam Hajiya Inna suka mai zafi, balle daya kalli Azeema"

yaga yanda itma kalaman suka tabata da alama.

"Hajiya inna ce tace  Junaid barka barkan mu, yau Allah ya amsa addu a ta. "

"Junaid ya kalleta yai murmushin yake, Azeema ce ta mike tace  kiyi hakuri Hajiya dama Junaid na kawo miki bari na koma. "

 Idan kina magana kamar mutuniyar arziki wannan mata Allah wadan bakin halin ki da

"tsinanen san kai da san zuciya, yanzu kila in na tambayeki raban dakiyima Zubair addu a ma kin manta, ki fita zai taho da kafarsa."

"Azeema ta kalli Junaid wanda shima kallanta yakey, Murmushi tai mai ta daga mai kai alamar ba"

komai sannan ta fita.

Hajiya inna ta kalli Jakadiya tace  zubamin gishiri a kofar data fita.

Wannan kalma ta konama Junaid rai sai dai baice komai ba.

Azeema na fitowa ta kalli Barira wacce idanta ya ciciko tace  meye hakan?

"Barira cikin konar rai tace  ji fa abinda ta miki, in da kara ai bai kamata ta miki hakan a gaban"

Junaid ba.

Azeema tai murmushi a ranta tace hakan shine ya kamata da batai ba da banji dadi ba

Amma a fili murmushi kawai tai ta fara tafiya

**********

"Hajjo sam ta kasa kwantar da hankalinta, ganin yanda Zeena yau ko shigowa batai ba, kenan da"

gaske san yaran nan take.

Yamma nayi ta mike ta nufi bangaren mai martaba dan ta san lokacin dawowarsa daga fada ne.

"Takawa ya cire kaya kenan Zagi ya sanar da isowar Hajjo, jalabiya ya zura ya bada izinin ta shigo."

"Hajjo ta shigo ta zauna, gaisheshi tai bai amsa ba yace  Hajjo lafiya? Banyi tunanin ganinki ba. "

Kallansa tai tace  me kake nufi da zaka cikama Junaid alkawari akan duk abinda yakeso?

Kallanta yai yace  akan me zan sanar dake?

Kallansa tai ranta ya fara baci tace  Naji bakada hujjar sanar dani amma meye matsayin Zubair

a masarautar nan?

Kallanta yai cikin mamaki yace  Mekikesan ji?

"Tace  Ba abinda nake san ji sai dai nazone na tunama, Junaid ba jininka bane, Zubair ne danka"

"wanda ka haifa, duk yanda kake tunanin san mutum baikai san daya kamata kayiwa danka ba. "

Ido ya zuba mata yana kallanta tace  sannan abu na biyu ka aurar da Zeena ga Sulaiman din

nan dan hankalina ya kasa kwanciya da yanda ta fara maganar Junaid.

"Duk da yayi mamakin jin kalamanta amma bai tanka ba, tace  kardai ka manta nice matarka"

"wacce nasoka tun bamuda matsayi, duk da ba sona kake ba ka auran amma a kalla inada hakki"

akanka.

"Tana kaiwa nan ta mike tamai sallama ta fita, shiru yai yana kallanta, harta fita waje yanayin"

"fuskarsa ne ya canza wanda yasani shiga tunanin abinda yake tunani, ban samo amsarba naji yace"

 waya fada miki?

"Juyawa nai da sauri naga ba kowa agun, da wa yake? Abinda ya fadan kenan, na nuna kaina alamar ni? Lokacin na fahimci wai amsa yaba Hajjo wace ta dade da fita, to me yake nufi da waya"

fada mata?

Hmmmnmmmm

********

*ZAFIN RANA*

......................

*Hask e  W rit e rs Ass o ci a ti o n*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*K A$ f[ fV @&*

"Shiru mai martaba yai kafin yai gyaran murya alamar yanada magana, da sauri bafaden dake jikin"

"kofa ya shigo, kallansa yai yace  A kiran Zeena. "

"Da sauri ya juya ya fita, Zeena dake keance akan gadonta ta rasa ina zata sa kanta, fitowa tai a"

"fussce ta zauna, ta kalli Fure dake zaune agun tace Fure bangaren Yarima nakesan kije ki kiramin Binta. "

Binta? Wacece hakan?

"Fure tai tambayar, Zeenatu ta harareta tace koma wacece meye damuwarki? Kedai ki kiramin ita, sannan ki kirata a boye karki bari Junaid ya ganki. "

Fure tace  Gimbiya taya zani bangarensa na kira wacce bansaniba sannan ba tare da ya ganni

ba?

Ni Fure dan Allah kwakwalwarki tana aiki kuwa? Ke ni meyasa gaba daya bakida irin dabaru da

fasaha ne? Wlh na kusa canzaki ki cigaba damin halin kifi.

"Fure ta juya da sauri tai waje, tsaki Azeema tai tace  bari inga yarinyar da har saboda ita yaje"

gun Hajjo.

Fure na fita aka shigo neman Zeenatu inji mai martaba.

"Mikewa tai jiki a sanyaye dan tasan maganar dai guda daya ce akan aure, shiryawa tai sannan ta"

fito.

Kallan kuyangarta tai tace  in Fure ta dawo kice su jirani.

Tace to sannan ta wuce.

"Mai Martaba na zaune gabansa katan Littafi na fiqihu ne yana dubawa, Zeenatu tana zuwa bakin"

kofar ta canza yanayin fuskarta a nutse ta shiga bayan ya bata izinin shiga.

Zama tai daga gefe zama irin na ladabi.

Abdulsalam ne ya kalleta yace  Mahaifiyarki tazo akan na aura miki Sulaiman.

Da sauri ta kalli Sarki tace  Ranka ya dade tuba nake amma Allah bana san shi.

Wani murmushi yai yace  ni kike kalla kice bakyasan zabina?

"Kallansa tai ta maida kanta kasa tace  Allah da kaima kanaso bazaka tambayi ra ayi na ba,"

"zartar da auren kawai zakayi tunda Hajjo tama magana, amma kiran dakamin da tambayar daka"

min ya nunamin bakaso.

Shiru yai yana kallanta kafin yai wani kalausan murmushi yace  to naji tunda bakyaso sannan

banaso fadamin wa kikeso? Inbaki dashi kuwa na aura miki wanda yamin.

"Kallansa tai da sauri sannan ta maida kanta kasa, yace  baki dashi. "

Tace  akwai amma matsalar ba wanda zai yadda dani.

Wanene?

"Shiru tai gabanta na wani irin faduwa, a hankali tace  Yarima. "

Me kikace?

A hankali tace  Yarima!

Ido ya kura mata sannan yace  Kina tunanin Azima da Hajjo zasu yadda?

"Ta kalleshi idanta ya ciciko tace  na sani, shiyasa nake tsoro. "

 Tashi kije.

"Da sauri ta kara kallansa, yace  kin fadi ra ayinki sannan kinsan bazai yiwu ba, ko kina da wani abin cewa? "

Cikin sanyin jiki ta girgiza kai alamar a a.

Mikewa tai ta fito daga fadar.

"Tana fita Abdulsalam ya mike ya shiga ciki, shiru yai yana tunani, abubuwa guda biyu suna mai"

"yawo akai, me zai faru idan daga baya asiri ya bayyana?"

Sai dai me? Yna tunanin ba abinda Zai faru tunda a lokacin Junaid yana auren Zeenatu in yai sa a ma harda d a.

To amma in kuma asiri ya tuno kafin faruwar hakan fa? Ko kuma Junaid ya rufe idansa akan

komai fa? In kuma abin ya shafi har Zeenatun fa? Wadannan dalilai sun sa gaba daya kansa kullewa.

*******

"Zeenatu na fitowa ta nufi bangaren Junaid, wanda ita kanta batasan nan ta nufa ba sai data ganta"

a kofar shiga.

Da sauri tace  Fure me muke anan?

Da sauri wata kuyanga tace  Fure bata nan ai.

"Zeenatu ta kalli bangaren sannan tai ajiyar zuciya, samun kanta tai da juyawa."

Gimbiya?

"Abinda taji an fada kenan, juyawa tai cikin jin kunya, Azi ne Junaid na gefensa."

Kallan Junaid tai a hankali tai dan yake tace  wucewa nazo yi nai.

"Junaid ya kalleta sannan yace  tanan? Eh, naje bangaren Mai Martaba ne. Oh!"

Yace sannan ya nufi hanyar shiga. Ya Junaid?

"Juyowa yai ya kalleta, tai murmushi tace  bamuje gun Hajiya Innan ba. "

Kallanta yai yadanyi wani tunani akasan ransa kadan kafin yace  zaki shigo?

"Shiru tai tana kallansa, yace  inbakyaso ki barshi. Tace  tunda kai ka gayyacen ina zan ki zuwa. "

"Shiga yai tabi bayansa, zama tai tana kallan bangaren yanda aka gyara shi, murmushi tai tana"

cewa  dole Hajjo taso aba Ya Zubair nan.

"A hankali tai maganar sai dai Junaid ya jita, kallanta yai bayan ya zauna yace  daga bangaren Hajiya Inna nake. "

Cikin mamaki tace  haba? Kai dawa? Yace  Umma ce takaini.

Ido ta zaro tace  Umma karama? Garin ya? Garin ya kuwa? Yai tambayar cikin bugar ciki.

Zeena tai shiru kafin ta kalleshi tace  Hajiya Inna ta haramtawa Umma karama zuwa

bangarenta.

Junaid yace  meyasa? Bayan sirikarta ce?

Kallansa tai kamar zatai magana sai ta fasa.

Can tace  Ya Junaid saboda haka kace nazo? Yace  me? In saboda haka ne bazaki shigo ba? Tace  bance ba amma a kalla nadanji haushi.  Meya hadasu?

Kai ta girgza alamar rashin sani tace  kawai dai nasan batasanta sannan ta hanata shiga

"bangarenta, ita da Mai martaba. "

Junaid ya kalleta yace  hardashi?

Eh shima baya zuwa.

"Murmushi Junaid yadanyi kadan fuskarsa kunshe da tunani yace  shikenan, in kin gama gani"

"bangaren sai ki wuce, zan shiga nai magrib. "

Mamaki ne ya kamata kafin ta tattaro abinda zata fada harya rufe kofa.

Labanta ta cizs saboda takaici sannan ta mike ta bar bangaren nasa cikin takaici.

"Idanunta ne taji suna kara cicikowa, kenan ita duk inda tai ba dadi, cikin jin haushi ta shiga"

bangarenta.

Wata yarinya ta gani a tsaye daga gefe kadan inka shiga.

Kallanta tai a wulakance tace  uban me kike anan?

Binta ta kalleta tace  ance kina nemana ne.

Ni?

Tai tambayar tana kallanta daga sama har kasa.

Binta tace  haka waccen tace.

Ta nuna fure wacce ta taho da sauri.

Binta wacce kafafunta harsun gaji da tsayuwa ta dan jingina.

Fure ta karaso tace  Gimbiya itace .

"Da saure Zeenatu ta kara kallan Binta cikin mamaki, kece Binta? "

Eh nice.

Batasan sanda tasa wata dariya ba wacce ni kaina na saki baki ina kallanta.

A hankali ta fara zage Binta wacce ta nemi ta daidaita tsayuwarta.

"Binta mamaki ya kamata, Zeenatu sai da tagama kallanta tsaf sannan tace  daga bangaren Ya"

Junaid nake.

"Binta ta kalleta da sauri, Zeenatu tai murmushi tace  Ashe abinda ya faru dake kenan? Ayya kiyi"

hakuri kinsan hausawa sunce babban goro sai magogin karfe.

Binta ta daure ta kalleta tace  me ya sameni?

"Zeenatu ta matso saitin kunnent tace  Ya Junaid ya fadamin komai, tundaga sands ya taimakeki har abinda ya faru kwanan nan. "

"Idanun Binta ne suka fara sauyawa, tace  mene? "

"Zeenatu ta shagwabe fuska tace  na tausaya miki, shima Ya Junaid yana tausayinki sosai. "

"Bakin Binta ne ya fara rawa, kuka na neman kwace mata, daurewa tai ta kalleta sannan ta"

"sunkunya tace  tuba nake Gimbiya amma nasan ba abinda kikaji daga bakin Ya Junaid, sannan ko kinji ma nasan yayi maganar ne bada wani abin ba. "

"Zeenatu a zuciya ta kifa mata mari, Binta ta rike gun ta dago tace  menayi kuma? "

Zeenatu tace  tambaya kike? Sai yanzu ma na tuna ashe kece wannan ta rannan.

Sannan yau ya zama rana ta karshe da zaki dinga maida min martani. Tana kaiwa nan tai ciki.

"Binta ta juya ta fita, tana fita tasa kuka, da gaske Ya Junaid ya fada mata komai? Kuka kawai"

takeyi ta rasa ma me take tunani.

**********

"Junaid bayan yayi sallah ne ya zauna akan sallaya yana tunani, ita da Mai martaba? Meyasa? Shiru yai yana tunani, kafin ya mike."

"Waje ya fito yadan tsaya a baranda yana dan kallan kofar da zata sada ka da bangaren bayi, Binta"

ko tana me?

"Shiru yai tare da sakin ajiyar zuciya, ganin ba alamarta ne yasa ya juya kamar zai koma. Jin an bude kofa ne yasa ya juyo da sauri."

"Binta ya gani tana tafe tana share hawaye, tsayawa tai daga bakin kofar itama ta zubamai ido,"

sun fi minti uku suna kallan juna kowa da abinda ke yawo a ransa kafin Junaid yace  Binta!

"Kallansa tai a hankali ta tako, sai dai bata isa inda yake ba tace  Yarima Barka da dare. Ta juya zata wuce."

"Shiru yai ya bita da kallo har ta shiga, meya sameta?"

Umma ce?

Abinda ya fado mai kenan.

******

Ayusher 24

*ZAFIN RANA*

......................

*Ha s ke Writers As s o c ia tio n*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*K A$f[ fV*

*Wannan Littafin Na Saidawa ne ga Duk mai Bukatar siya

ya tuntubi 07084161619 mungode*

*25*

Binta!

"Tana kokarin rufe kofa taji ya kira sunanta, tsayawa tai cak"

"zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, A hankali ta juyo ta kalleshi."

"Murmushi ya sakar mata sannan yace "" magana nakeso muyi."""

"A hankali ta fara taka kafafunta zuwa inda yake, idanunta na kansa, tuntube tai saura kiris ta fadi, da sauri ya zabura yace Binta."

Daidaita tsayuwarta tai ta kalleshi har ya sauko daga

baranda din da yake.

"Kallan juna sukai kawai suka sa dariya, yace ""har yanzu dai sai a dinga tafiya ana neman faduwa."

"Ta karaso tace ""haryanzu dai kafin na fadi an gama"

"razana."""

Murmushi suka sakeyi da tuno da yanda sukeyi acan.

"Karasowa tai ya zauna a kasa ya zura kafafunsa kasan baranda din, kallansa tai sannan ta zauna daga gefe."

"Ya kalleta cikin hasken farin wata yace ""daga ina?"""

"Nadan fitane zagaye."""

Zagaye? Ya maimaita tare da yin sansanyan murmushi

ganin indai zata fita dashi suke fita.

"Kallanshi tai tace ""wacce magana?"""

"""Me kike tunani akan komawa bangaren Umma?"" Kallansa tai da sauri tace ""Naam?"""

"Yace ""eh, ko bakyaso?"""

"Shiru tai tana kallansa, kawar da kansa gefe yai, ganin haka yasa tace ""zan koma."""

"Shiru yai kafin yace ""Nagode."""

"Mikewa tai tace ""zan koma gobe in Allah ya kaimu."" Tafiya?"

"Ya fada ganin ta mike tsaye, juyowa tai ta kalleshi a ranta tace kafi kowa sanin zamana a nan kusa dakai abinda zai haifar."

A fili kam cewa tai na gaji ne.

Ya fahimceta hakan yasa baice komai ba.

Yana nan zaune har ta shiga ciki.

"Mikewa yai ya shiga dakinsac zamanta acan shine kwanciyar hankalinsa ya tabbatar intana gunta ba'abinda ta isa ta mata, sannan hakan ne zai bashi damar kwatar"

mata 'yancinta.

**********

Binta na shiga ta sanar da Harira zata koma gobe

"bangaren Azeeema, cikin tsananin mamaki Hari tace ""Binta hauka kike? Matar da tafi tsanarki kije ki gunta?"

"Kallan Hari tai ta tuno da kawar da kansa dayai, tace"

"""akwai dalilinsa na yin hakan."""

Dalili?

"Harira ta tambayeta, Binta ta kwanta tace ""eh."""

Shiru tai tana tunanin abinda ya faru tsakaninta da Zeena

"yanzu, me Zeena take nufi? San Junaid take kenan ko me?"

"Mikewa zaune tai da sauri ta kalli Harira tace ""Harira ya ake gane mutum na san wani?"""

"Harira tace ""yanda kike san Junaid."""

"Ido ta zaro da sauri tace ""ni Ya Junaid ai. """

"Sai kuma tai shiru, Hari tace ""me?"""

"Kwanciya ta kuma yi da sauri tace ""bacci nakeji."""

"Idanunta ta rufe tana tuno yanda Zeena ke magana, lalai"

itakam tata ta kare dan ta tabbatar ba abinda Junaid zaiyi da ita yana ganin Zeenah.

A haka har bacci ya dauketa.

"Da safe Junaid ya nufi bangaren Azeema, tana zaune a"

"falanta ta lumshe ido tana tunani, ga busar barewa datasa ake mata."

Hannunta daya take dan kadawa wanda duk sands take

tunani haka takeyi.

"A hankali tace ""Barira an kawo rahoton danace?"""

"Tace ""a'a Gimbiya amma nasan Waziri yana hanya."""

Sallamar Junaid ne yasa ta bude idanunta dan batai

"tunanin jinsa ba."""

"Shigowa yai, tai saurin sallamar kuyangar dakeyin busar, tace ""Junaid!"""

"Gaisheta yai sannan yace ""Tuba nake Umma jiya dana"

"dawo bansamu shigowa ba."""

"Tace ""bakomai Junaid nasan kanada dalilinka."""

"Murmushi yai sannan ya kalleta cikin kulawa yace ""Umma"

"wani abu ya hadaku da ita ne? hajiya Inna nake nufi."""

Kallansa tai itama sannan ta sallami kowa dake falan ta

"kalleshi, tace ""Karkasa wannan abin a ranka dan nima ban bari ya dameni ba."""

"Tausayinta ne ya kamashi yace ""amma kin mata laifi ne?"" ""A'a batasona ne saboda tana jin haushi na auri"

"Abdulsalam wanda ta rika bayan rasuwar Mahaifinka."""

Duk da bai gamsu na amma baice komai ba.

"Shiru yai kafin ya daidaita zamansa yace ""Na umarci Binta"

"ta dawo nan."""

"Kallansa tai da sauri tace ""nan?"""

"Ta kalleshi cikin tsananin mamaki, dan bata taba tunanin"

ko ita

12 / 28