Zafin Rana Book Compelet Novels By Aysha Alto

Author :  Aysha Alto Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   11 / 28

30K to 33K   out of 81.6K words

alkyabar dake jikinta kalar sararin"

"samaniya, Azeema ta zuba mata ido harta zo ta zauna, Fure ce ta ajiye kwanuka guda biyu."

Zeena ta gaishe da Azeema sannan tace  Umma karama jiya nazo gaisheki akace bakida lafiya

"shiyasa nasa a miki farfesu na kawo miki, nayi sa a bakiyi karin kumallo ba. "

"Azeema ta kura mata ido, wanda haryasata yin kasa dakai? Murmushi tai sannan tace  nagode"

"sosai, Allah ya saka da alkairi. "

"Zeena tace ameen, sannan ta mike tace bari naje."

"Azeema bata tanka mata ba sai dai idanunta na kanta, yanda Zeena ke tafiya a hankali ne yasa ta fahimci batasan tafiya, har sai da Zeena taje bakin kofa sannan Azeema tace  ko zakici abinci damu? Duk da nasan ba lalai  "

Kafin ta karasa Zeena ta juyo ta kalleta tace  Ba wani abin? Azeema tai dariya a kasan ranta tace me kike shirin yi?

"Azeema tace  ba wani abin, dama Junaid ne zaizo in ba wani abin ki zauna. "

"Zeena ta zauna suka danyi shiru, sannan ta kalli Azeema tace Umma karama naji ana zancen Ya"

Junaid ko yazo da yarinya ko mata?

Azeema ta kalleta kamar bazata amsa ba sai tai murmushi kuma tace  wace mata ana zaune

kalau? Yarinyace da ya taimaka daga can.

"A hankali tai dan ajiyar zuciya sannan ta kalli Azeema tana murmushi, Azeema cikin zargi tace"

 Hajjo tasan kina nan?

"Zeena tace  a a amma in na koma zan fada mata, dama dubaki nazoyi  "

"Sanarwar isowar Junaid akai, wanda yasa gaban Zeena faduwa wanda ita kanta batasan dalili ba."

"Junaid ne ya shigo, kallan Zeena yai cikin mamaki, Azeema tai murmushi tace  karaso mana. "

"Junaid ya karasa ya zauna a dayan gefen, gaida Azeema yai sannan Zeena ce gaisheshi."

"Kallanta yai sannan ya amsa, Azeema ce tace  ina Binta? Na dauka tare zaku taho? "

Yace  batadan jin dadi ne.

Azeema ta kalli Zeena tace  ashe jiya Zeenatu tazo.

 Eh kina bacci.

Murmushi tai sannan ta mike tace  fara cin abinci bari nazo.

"Ta mike ta shiga dakinta, tayi haka ne dan tanasan fahimtar meke kan Zeenatu."

Zeenatu tana fita ta kalli Junaid tace  yaya na zubama?

"Kallanta yai bai tanka mata ba,tai shiru kafin tace  zamuje yau din? Ina?"

Ta kalleshi .

 ka manta? Nace zan kaika gun Hajiya Inna?

Baice komai ba hakan yasa tace  anjima da yamma sai muje?

Kallanta yai yana tunanin itace? Itace ta kulle Binta?

Yanda ya kalleta ne yasa cikin salo tace  ya Junaid.

 Kinsan Binta?

 Binta? Wacece?

Ido ya zuba mata ganin yanda fuskarta karara ta nuna alamar tambaya take yasa yace

 shikenan.

"Ta bude baki zatai magana Azeema ta fito, kallansa tai bata ce komai ba."

Azeema ce ta kalleta tace  ya naga baku zuba komai ba?

Nan Zeena tadan ja plate ta mikawa Junaid.

************

Mene? Zeena tana ina?

Zubair yace  yanzu naganta ta nufi bangaren Azeema.

Cikin zafi Hajjo tace  jiya mafa ance taje wai uban me ke kan yarinyar nan?

Zubair cikin hasala shima yace  anya Zeena ba akwai abinda ke ranta ba?

"Hajjo ta tuno kalamanta datai rannan, shiru tai tare da dunkule hannunta. "

Zubair yace  akwai ko?

Hajjo ta kalleshi tace  haukarta ce.

*******

*ZAFIN RANA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

*Shafi Na Ashirin da Biyu*

"Azeema ta zauna sannan ta kalli Zeena wacce tai shiru ta kasa ko zuba abincin, Binta? Tunowa tai"

da yanzu Azeema ta tambayeshi ina Binta? Itace? Itace yarinyar daya taho da ita?

"Ganin Azeema na kallanta ne yasa tadan zuba abinci kadan a plate juya cokalin kawai takeyi,"

Fure ce ta shigo tace  Gimbiya ana nemanki.

"Wa? Ta fada tana kallanta, Azeema tace  kije ki gani. "

"Mikewa tai ta kalli Junaid wanda ko kallanta bai kuma yi ba, maida kallanta tai kan Azeema tace"

 Umma karama na wuce.

"Azeema ta daga kai alamar to, Junaid ta kalla tace  Zeena zata wuce  to kawai yace ya cigaba da tunanin da yakeyi, kenan Hajjo ce?"

"Haushi ne ya turnuketa ta juya ta fita, tana fita Azeema ta kalleshi tace  Junaid! "

Dagowa yai ya kalleta tace  baka huce da abinda ta maka bane? Wace?

Murmushi tai tace  shikenan.

Yana gama cin abincin ya kalleta yace  zanje bangaren Hajjo.

 Hajjo? Me zakaje yi?

 Gaisheta zan na fahimci tunda nazo banje ba.

"Azeema kamar zata sake magana sai taga harya mike ma, ganin haka yasa tace  sai ka dawo. "

"Juyawa yai ya fita, Azi ya kalla yace muje bangaren Hajjo. "

Zeena tana shiga bangaren Hajjo ta shiga jiki a sanyaye saboda gaba daya jikinta ya gama sanyi.

Hajjo ce ta buga mata wata muguwar harara sannan tace uban me kikaje yi bangaren Azeema?

Zama tai fuskarta duk ba dadi tace  Hajjo dan Allah ki kyale ni yanzu ni nanida karfin magana.

Hajjo ta kalleta a fusace tace  yau zanje na fadawa Mai Martaba ya hadaki aure da Sulaiman ba

"tare da wani jiranki ba, tunda naga alama in aka barki Allah ne kadai yasan me zaki aikata. "

"Kallan Hajjo tai tace  Sulaiman? Wallahi indai kuka auramin shi sai dai ku gai gawata gidan, ni"

mace ki barni da abinda ke damuna dan Allah. 

"Bata karasa ba ta mike tai cikin daki ranta a bace, Hajjo ta bita da kallo cikin takaici sannan tai kwafa, tace wallahi baki isa ba, ki rasa wanda zakiso sai dan da ya ke neman toshewa yayanki"

gaba?

"Tana zaune tana tunanin mafita taji ana sanarda isowar Junaid, tsantsar mamaki ne ya kamata"

"amma ta daure ta nemi ya shigo, Junaid na shigowa ta saki fuska sosai tace  Junaid? Kaine da kanka? "

Junaid ya gaisheta sannan ya ja ya zauna.

Tunani ta shigayi badai shima Zeenatun yake so ba?

Junaid ne ya kalleta yace  a gafarceni tunda nazo bansamu nazo gaisheki ba.

Murmushi tai tace  ai bakada lokaci ne ni na sani kana ta fama da kokarin daidaita zamanka da mahaifiyarka.

Kallanta yai sannan yace  Eh da jiya naso zuwa to sai banga Binta ba hakan yasa muka shiga

nemanta.

"Yai maganar yana kallan yanayinta, Murmushi tai tace  Binta? Ohhh wace kuka taho tare? Yace  eh. Yadan yi dariya kadan yace  wasu harcewa suke wai na taho da mata. "

"Hajjo tai dariya tace  kasan lamarin masarauta akwai gutsiri tsoma, amma ya Gimbiya taji? Suna"

neman lalatawa danta suna?

"Junaid ya kalleta sannan yai murmushi, baice komai ba."

Tace  irin wannan shi kesa a sa mutum yin abinda bai dace ba in mutum yaga ana neman lalata ma dansa mutuncinsa.

Junaid ya kalleta sannan yace  Yarima Zubair fa?

"Tace  yana bangarensa,dazu ya barnan, Junaid a kokarta a dinga kula da Gimbiya Azeema dan"

ta shiga wani hali sanda baka nan.

Junaid ya kalleta sannan yace  Da a koda yaushe ya kamata yasan me zaiyiwa iyayensa.

"Wannan kalmar taba Hajjo haushi sai dai bata nuna ba tace  hakane, kanasan wani abu a"

kawoma?

Yace  a a zan wuce ma.

"Mikewa yai, jiyai an bude kofa, kallan inda yaji motsin yai, Zeena data fito dan ta wuce"

"bangarenta ne ta zuba mai ido, jitai batasan dauke idanta daga kanshi."

"Junaid na ganin itace ya maida idansa kan Hajjo yace  na wuce, A huta lafiya. "

Tace  to a gaishesu.

"Zeenatu tana kallansa har ya fita ko waigowa baiyi ba, jitai idanunta suna neman cikowa kawai ta"

koma dakin ta rufe.

"Junaid na tafe yana tunanin kalamanta, sannan ya hada da kalaman Mai martaba, yana tafe"

"yana auna kalaman can da komai ya daidaita a kansa, yaja ya tsaya."

Azi ya kalleshi yace  Yarima lafiya?

"Junaid ya kalleshi, sannan yace  mu koma bangarena.  Ba zaka koma gun Gimbiya ba? "

Yace  anjima.

"Juyawa sukai ya wuce bangarensa, bai nemi Binta ba kawai ya shiga bangarensa ya zauna yana tunani, kenan Umma ce ta kulleta dan ta hukuntata akan abinda mutane ke zarginsa dashi? Kenan"

batasan Binta kamar yadda take nunawa?

Fitowa yai ya kalli wani bawa dake gefe yace  kiramin Binta.

Bawan ya amsa da to sannan ya juya.

Tana zaune ta samu tai wanka tana shan kunu da kosai bawan ya sanar da ita Junaid na

nemanta.

Kallansa tai tace  to.

Yana juyawa ta kalli Hari sannan tace  Hari bari naje.

"Ajiye kofin tai sannan ta mike, Hari tace  sai kin dawo. Binta tai murmushin yake ta fita."

"Junaid na tsaye ya juya bayansa a cikin falan yana kallan window, yana kallanta sanda tazo ta"

"wuce, hannunsa daya ba baya, sallama tai, ya amsa ba tare da ya juyo ba. Shigowa tai a hankali ta tsaya daga nesa dashi sosai tace  Yarima! "

Junaid bai juyo ba yace  Barira tazo nan jiya?

Kallansa tai kafin tace  a a.

 Ya akai ke da bakida saurin yadda da mutane kikabi mutum ba tare da kin sanshi ba? Shiru tai kafin Tace  cewa akai inje injika.

"Yanzu kam juyowa yai gaba dayanshi ya kalleta, tana tsaye tana kallanshi itama, a hankali ya fara"

"takowa zuwa inda take, duk taku daya ji take kamar da bugun zuciyarta yakeyi, yauce rana ta farko a iya tarihinta dashi data taba ganinshi haka ba."

"Daf da ita ya matso hartana iya jiyo numfashinsa, gabanta ne ya tsananta faduwa, dagowa tai ta"

kalleshi.

Yace  waye ya jaki?

"Da kyar ta hadiye yawun bakinta sannan tace  koma wanene ya Junaid baya riga ya wuce ba? Sannan laifi nai shiyasa aka hukuntani, dan Allah kabar maganarnan a inda take. "

"Ta fada tare da danyin taku daya zuwa baya, shima taku daya ya kara, ta kalleshi jikinta har rawa"

yadan fara tace  Ya Junaid!

"Yanda tai maganar kamar mai shirin yin kuka, kansa ya juya sannan ya furzar da wata iska ya"

"kalleta yanayin idanunsa ya canza sosai, wanda ya kara tsoratata, tace  Ya Junaid! "

"Bai tanka mata ba yanzun ma sai dai ya kara kallanta, bakinta na rawa muryarta na rawa tace"

 Ya Junaid dan Allah!

"Taku daya yai baya sannan ya kara wani dayan, kallansa tai tace idan harba da kwakwaran dalili"

"ba dan Allah kar kazo bangaren su Harira domin ni, sannan na koma can da zama, sannan"

kuma. 

"Shiru tai tana kallansa, ta daure saboda kukan dake neman kwace mata tace  dan Allah ka rage"

"nemana, in kuma duk hakan ya gagara zan bar gidan nan. "

"Tana kaiwa nan ta juya da sauri tai waje, tana fita tai bayan bangarensa da gudu, ta tsuguna ta"

"fashe da wani irin kuka mai taba zuciya, wannan shikadai ne abinda zata masa dan ta zauna kusa dashi, dan in har aka cigaba da yanda ake ta tabbatar wata ran ganinsa ma bazata tabayi ba, wanda a rayuwa bata tunanin zata iya kwana ta tashi bata ko sashi a idanta ba."

"Kuka take sosai, ta toshe bakinta, gaba daya fuskarta tai jaa, kuka take har iya karfinta wanda duk"

wani mai tausayi inyaga halin datake ciki zai tausaya mata.

"Junaid kam tana fita ya runtse idanunsa shima bai zataba yaji hawaye sun gangaromai, hannu"

"yasa y taba su, sannan ya kalli hannunsa, inhar mahaifiyarsa zata aikata hakan saboda kawai ya damu da Binta to lalai gaba baisan mezata aikata akan hakan ba."

"Kansa ne yaji yana sarawa, ya dauka ganinta zaisa hankalinsa dana Binta ya kwanta me ke shirin"

faruwa?????

Tabbas dolene ya janye Binta daga jikinsa harsai yakai matsayin da zai kwaceta batare da fargaba

"ko tunanin za a mata wani abin ba, yau a wannan lokacin ya dau alkawarin tabbas shi Junaid sai ya ba Binta gatan da babu wace mace data taba samunsa, domin tun yana karami burinsa kenan, akoda yaushe yaganta cikin farinciki, yanzu me zai faru da Basu ganta ba jiya? Haka zatai ta zama"

harta mutu kenan???????

******

Ayusher

*****

*ZAFIN RANA*

......................

*Hask e  W rit e rs Ass o ci a ti o n*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*K A$ f[ fV @&*

*23*

"Azeema tana zaune tana jiran Junaid sai dai har dare ba alamarsa, Barira ta kalla bayan tayi"

sallar isha i tace  Barira Junaid haryanzu? Barira ta sunkuyo tace  ko na je na kirashi?

Azeema tai saurin cewa  a a da alama yana can da yarinyar nan.

Mikewa tai ta wuce dakinta ta kwanta zuciyarta duk ba dadi.

Bata dade da kwanciya ba bacci yai gaba da ita.

"Yanda yake nufota ne fuskarshi tana gumi, gudu take hana binta, hannunsa ta kalla taga jariri a rike, gudu take tana keta cikin dajin nan har takai karshe."

"Juyowa tai cikin tashin hankali tana hakki, hannayenta ta hade tana neman gafara."

Zubair ka tsaya kaji! Zubair ka. 

"A firgice ta farka, da sauri ta jawo bargonta ta gangame jikinta wanda yake rawa, kamar a fili tai"

"gudu nan dan gaba daya jikinta ya jike da gumi, idanunta sun kada sunyi jaa sosai."

"Fitilar kwai dake gefenta ta murda da sauri haske ya dan zagaye dakin, shiru tai hankalinta a tashe ta zauna akan gado ta hade kafafunta, tunanin wannan mafarki, ta tabbatar duk duniya ba wanda yasan wannan sirrin to meke faruwa?"

"Shiru tai tana tunanin kalaman da Jakadiya ta fada mata, da sauri ta girgiza kanta alamar a a."

Da kyar ta samu bacci ya dauketa a xaunen.

"A hankali ta bude idanunta, ganin gari yayi haske ne yasa ta kashe fitilar sannan ta mike ta shiga"

bandaki.

*********

"Fitowa tai bayan ta kimtsa, Barira da ragowar kuyangun ta nata faman gyara bangarensu."

Azeema ta kalli Barira wacce suka zube suna gaisheta suna ganinta.

Azeema tai murmushi tace  Barira kicewa Junaid anjima yazo muje ya gaida Hajiya Inna.

"Cikin mamaki Barira ta kalleta, tace  Gimbiya kinsan matar nan ba sanki take ba karta"

wulakantaki a gaban Yarima.

Wani lalausan murmushi ta saka tace  ki sanar dashi. Ta juya ta shiga ciki.

Barira tai shiru kafin ta aika a sanar da Junaid.

"Junaid kam wanda yau ma baisamu baccin kirki ba, yana zaune yana kokarin karatan wasu"

littafai na tarihi da ya nemi Azi ya amso mai.

"Nan Azi ga shigo ya sanar dashi sakon Azeema, yace  to. "

"Sai daya gama karatawa zuwa inda zai tsaya sannan ya mike ya shiga daki yai wanka ya shirya, a"

ido inka ganshi bazaka taba kawo akwai abinda ke damunshi ba saboda babu yanayin komai a tattare dashi.

"Karin Kumalo yai sannan suka fito shi da Azi, Azi sai binsa yake da kallo, duk da baisan yanda"

sukai da Binta ba amma ya hasasu ganin yanda taci koka shima tunda ta tafi bai bar kowa ya shigo bangarensa ba sai shi daya kaima littafai.

Junaid ne ya kalleshi yace  Azi sai yaushe za a daina kallo na haka?

Azi yai kasa dakai yana dariya yace  wai ka gani? Junaid yace  ba dole ba? Kana neman sani na fadi kasa.

"A tare suka dan murmusa, can Junaid yace  Waccen gimbiyar tace Hajiya Inna batasan"

Umma?

 Gimbiya Zeena?

Eh

Azi ya danyi shiru kafin yace  bansani ba wallahi Yarima kaga ba anan na zauna ba nima. Junaid ya jinjina kai kawai baice komai ba.

"Sun isa bangaren Azeema, ya shiga ciki, zama yai yana jira ta fito."

"Barira ce ta fito ta zube tana gaisheshi ido ya zuba mata kamar bazai amsa ba, Barira ta kara"

"gaisheshi gabanta na faduwa jitai ya amsa, a hankali ta saki wani ajiyar zuciya."

Junaid ya kalleta yace  Ki sanar da Umma nazo.

"Mikewa tai da sauri ta nufi dakin Azeema, da ido Junaid ya bita kafin ya dauke idansa daga kanta."

"Azeema wacce ta gama shiryawarta tsaf tasha kwalliya yanda ta saba, dan dama Azeema yar"

kwalliyace sam baka ganinta ba kwalliya sai dai in bacci take.

"Tana zaune tayi shiru tana tunani, dan yatsanta kawai take dan dagawa take saukewa tayi nisa"

"cikin tunaninta har batasan sanda Barira ta shigo ba, sai da Barira ta matso kusa da ita tana cewa"

 Gimbiya Yarima yaxo yana kilisarki.

"Kallanta tai sannan tai murmushi, mikewa tai ta kara daidaita zaman alkyabarta sannan tace"

 muje.

"Tare suka fito Barira tana binta a baya, gana ganin Junaid ta saki wani lalausan murmushi na"

"farinciki, Junaid."

"Ta fada tana kallansa, Kallanta yai da fuskarsa wacce ita kanta ta kasa meke tattare da ita. Gaisheta yai, amsawa tai tace  jiya inata jiranka. "

Yace  eh dana dawo ne naji banasan fitowa.

"Murmushi tai tace  ka gaji da zirgazirga ne shiyasa, tunda ka dawo kake ta fama. Kasa yai da kansa baice komai ba."

Tace  muje?

Mikewa yai yace  eh.

"Tare suka fito tana nuna mai hanyoyi tare da dan bashi tarihin guraren sama sama, yana biye da"

ita yana kuma jin tarihin harms tambayarta inda bai fahimta ba yakeyi har suka isa.

"Bangaren Hajiya Inna shine daga can karshe karshen ginin, an kewaye mata bangarenta sosai,"

"Azeema suna kokarin shiga ta kalleshi tace  kakatka ce, kayi kokarin sakin jiki da ita. "

"Kai ya daga alamar to, sannan tace 

11 / 28