Zafin Rana Book Compelet Novels By Aysha Alto

Author :  Aysha Alto Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   14 / 28

39K to 42K   out of 81.6K words

datun randa sukai taron nan amsar da Junaid ya bada ke damun zuciyarsa, sauke"

numfashinsa yai tare da dunkule hannunsa.

"Meyasa jikinshi ke bashi da matsala? lallai kasantuwar Junaid k'ark'ashin fadarsa babban kuskurene, sannan gangancine, danya lura yaron yana tattare da wata fik'ira dashi kansa baisan"

"yana da ita d'inba, me zai faru idan komai ya fito? Ko kuma idan ya nemi amsar mulkin da yake"

nasa?

"Dolene yay azamar yima tufk'ar hanci, yau zai zauna da shamaki da wambai da waziri bisa"

"shawarar daya yanke akan Junaid d'in, dan dolene yasaka Katanga a tsakaninsu."

Azeema fa?

"Wani sashen zuciyarsa ya ambata. Kansa ya dafe, lallai yanda yake haka Azeema take, musamman"

"a yanzu da dukkan motsinta yake akan d'anta da makomarsa, tunda Junaid ya dawo ko gunsa batazuwa sai dai in shi ya aika tazo."

Miye mafita to?.

"Nace,  saiku nemo @&"

****************

AYUSHER 26

****************

* ZAFIN RANA *

......................

*Hask e  W rit e rs Ass o ci a ti o n*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*K A$ f[ fV *

{27}

Barira ce ta shigo ta durkusa tace  Gimbiya Mijin Gimbiya Safiya ya iso.

Junaid wanda ko mosti baiyi ba bashi kuma da alamar tankawa.

Azeema cikin jin dadi tace  Barira akai Mahmud karamin falina na hutawa.

Da sauri tace to.

"Junaid ta kalla, tace  Muje? Ta fada tana mikewa."

"Mikewa yai shima, a hankali ya kalli kofar da zata sadaka da bangaren dasu Binta suke, shiru yai"

"kafin ya kalli Azeema wacce itama kallansa tai, ta fahimci me yake tunani. Muje Ummana!"

"Yanda ya sake kiranta ne ya sa taji wani irin dadi ya kamata, kallansa tai cikin jin dadi sannan"

suka nufi kofa ta baya.

************

"Azeema da kanta tayoma Junaid rakkiya k'aramin falonta Na hutawa, Wanda saika isa d'an gata"

"agareta kake shigarsa, shikansa bai ma san da falan ba."

"Cike da girmamawa Mahmud ya gaida Azeema, sannan suka gaisa da Junaid cikin girmama juna."

"Mahmud cikin jin dadin ganin Junaid yace  Yarima barka da isowa, inata san zuwa dama. "

Junaid yace  bakomai.

Azeema ce takuma yima Mahmud bayani akan mai Junaid d'in ke buk'atar sani sannan ta fito

"daga falan, Barira ta kalla tace  a kai musu kayan marmari. "

"Da sauri tace to, kallo daya zakama Azeema kasan hankalinta a kwance yake da alama zuwan"

Junaid yau da yanda ya ke mata yasata jin wani dadi har ta kasa boyewa.

"Mahmud da Junaid suka k'ara gaisawa, tareda jajantama juna dakuma murnar dawowarsa."

"Daganan Mahmud yafara bashi labarin shud'ad'd'en tarihin masarautar, da sarakunan da suka"

"gabata, da yanda kowa yay mulkinsa da tarihin daya ajiye har zuwa kan mahaifinsa da sarki Abdussalam na yanzu."

"Junaid yacika da al'ajabi, tarihin ya k'ayatar dashi sosai."

"Fuskar Mahmud d'auke da Murmushi yace, ""Yarima wanan shine masarautar a dunk'ule,"

"wad'annan litattafai ne dazaka kuma samun ilimi Na zamantakewa da dabarun mulki, dan sarakunan da suka shid'e sun k'aru da sirrika masu yawa a cikinsu, to lallai nasan kaima zaka k'arun""."

"Junaid yad'an murmusa, ""lallai Na gode da gudunmawarka agareni, zankuma nazarcesu, idan ina"

"buk'atar fad'ad'a ilimi Zan tuntu6eka""."

"""To Masha ALLAH""."

Sun dan sake yin hira kafin suyi sallama.

**************

"Azeema ta kalli barira dake durk'ushe gefenta tai d'an murmushi, ""Barira daga yau kar a sake"

"saka binta aiki""."

"Cike da mamaki barira tace, ""ranki ya dad'e miyasa?""."

Azeema ta gyara zamanta cikeda k'asaita tana wani murmushin da ita kad'ai tasan fassarar

"kayanta, ""karki damu da sanin dalili, kawai inason daraja duk abinda ya shafi Junaid "

"Barira ta jinjina kai cikeda mamaki, tasandai ba banzaba, akwai shirinda uwar d'akin nata keyi ta"

"k'ark'ashin k'asa, dan tasan haka kawai Azeema bazata sauko ta nemi daraja Binta ba."

Harzata mik'e Azeema ta dakatar da ita.

"""Inason ganin jakadiya""."

Barira ta jinjina kai tare da amsawa da to.

****************

"Yau sarki Abdussalam ya gagara fita fadanci, sai aiken yana buk'atar hutawa yay"

"musu, sannan yabuk'aci ganin Shamaki da wambai da waziri."

"Babu 6ata lokaci suka iso, bayan jakadiya ta nema musu Iso suka Shiga."

Duk suka gaida sarki cikin girmamawa.

"Sarki Abdussalam yay gyaran murya idonsa a Kansu, ""kunsan miyasa na aika a kiraku? "

"Wambai yace, ""ALLAH ya k'arama sarki lafiya bamu saniba, sai dai ganin yanda ka kiramu tabbas"

akwai abinda ke faruwa.

Sarki Abdussalam ne yadan sauke ajiyar zuciya ya cigaba da fad'in  me kuke tunani a game da

Junaid?

"Fuskarsu dauke da mamaki suka kalleshi, Junaid?"

"Abdulsalam yace  duk d'inku kunsan minene ma'anar dawowarsa garemu, sannan kunsan"

"makomar hakan, to yarage ruwanmu Neman mafita, domin yaron yawuce zatonmu, na rasa me yasa nakejin ba daidai ba, me kuke tunani zai faru in ya san abinda ya faru a baya? Wanda"

idanunsa sun sa na fara tunanin dole mu san abinyi.

"Hankalinsu ne ya tashi, dukansu suka shiga nazari."

Shamaki ne ya kalleshi cikin mamaki yace  ALLAH yabaka nasara mizai hana mu tuna baya

"kawai?""."

Da sauri Sarki Abdussalam ya kalleshi yace  Baya?

"Idanunsa ya zare da sauri yace  Bazai yiwu ba, kun manta wacece Azeema a gareni? bazanso"

"aikata hakan ga jininta ba, anema wata mafitar. "

Shiru suka karayi.

"""Mafita d'ayace"" cewar Waziri wanda ya fada yana gyara zama."

"""Wacce kenan?"" Sarki Abdussalam yafad'a yana maida kallonsa gareshi."

"""kayi taron nad'ashi Matawalle ko Galadima, sannan kabashi auren y'arka Zeenatu, hakan zaisa"

yai tunanin kafi kowa sanshi sannan yarka zata lura da duk al amarinsa.

"Wani zazzafan huci Sarki ya sauke, ""shawarar k'arshe dama burinace, dukda ban yanke hukunciba,"

"amma jin kalamanka yasa ka k'aramin k'warin gwiwa, ta farko kuwa kasan dai galadima nada ransa da lafiya, zamu sakashi yin murabus ne ko me? Zubair kuma shike rik'e da sarautar matawalle""."

"Wambai yay wata Y'ar dariya ""Ranka ya dad'e anzo dai-dai wajen kenan ai, dan inhar ka tu6e"

"Yarima Zubair ka d'aura Junaid lallai kowa zaikuma girmama adalcin mulkinka, a lokacin kowa zai fahimci kanasan Junaid fiye da yanda kake san danka, uwa uba Gimbiya Azeema wacce zata kara"

ganin girma da darajarka.

"Kai ya jinjina cikin gamsuwa, da alama. Kowa yayi na'am da hakan, nantake suka fahimci matsalar"

"ta warware, suka cigaba da tsara abinda suke tunani."

****************

"Fure dake zube gaban zeena a d'arare tace, ""ranki ya dad'e Azi hadimin yarima ya tabbatar"

"min yaci abincin""."

"Cikeda d'oki Zeena tace, ""da gaske?""."

 Sosai kuwa ranki ya dad'e

"""Kai fure baki ta6a sani farin ciki irin yauba, lallai kinata tukuycin albishir mai tsoka""."

"Fure ta washe baki tace  godiya nake ranki ya dad'e, ALLAH ya mallakama yarima Junaid ke""."

Zeena ta dan harareta tace  me kika sani?

Fure tai kasa dakai tana murmushi.

"Sosai Zeena ke tsallen murna ita kad'ai a d'aki, jitake kamar anmata albishir da aljanna yau."

"Haka ta fito ta gangaro bangaren Hajjo, Hajjo wacce ke kwance duk batajin dadi ta kalli Zeena,"

"kallo daya ta mata ta fahimci Zeena nacikin farin ciki, saidai bata tambayeta ba balle tasani saboda abinda ke damunta ya wuce wannan."

"**************"""

Tunda ya dawo sashensa yake cikin nazarin zamansu da Mahmud da yanda mahaifinsa ya

"gudanar da mulkinsa zuwa sarki Abdussalam. Lallai lokacin dazai fito ainahinsa Na jinin sarauta yayi, yakamata kowa ya fahimci sarauta a jini take ba a ayyukaba."

"Sabon shiri yasake, kafin ya aika Azi sashen mai martaba Neman ison ganinsa. Anyi sa'a shima mai"

"Martaban yana muradin ganinsa, dan haka babu wani janjani yasamu izini."

"A yanda Junaid ya fito dolene kowa ya kallesa, ya rikid'e ya canja gaba d'aya, saika rantse a"

"madarautar ya girma, harira kanta galala tai tana kallonsa, lallai ta yarda mulki a jini yake ba'a ayyuka ba."

"Shi kansa Zubair dake k'ok'arin shiga sashensa la6ewa yai yana kallon Junaid, gaba d'aya saiyaji ya"

"raina ajinsa da girmansa, wai harma yaushe Junaid d'in yagama fahimtar shi jinin mulki ne? Jibifa yanda yake wani shak'ar iska da fesar da ita tamkar shine sarkin, lallai aikine babba agabansu, dan wannan yaron idan basu risinar dashiba to zai 6allo musu ruwa."

Oho Yarima Junaid baisan yanaiba.

"Itama Hajjo tuni labari yakai Mata, ba k'aramin girgiza tayiba dajin batun, zeena dake gefenta ta"

"mik'e da hanzari tafice, saidai tana fitowa Junaid Na shigewa turakar mai martaba."

"Takaici yasata cizon yatsa, takoma da alwashin jiran fitowarsa."

****************

"Sarki Abdussalam dake kishingid'e ya zubama Junaid idanu, mamaki yake a ransa yaushe"

"junaid d'in ya koma haka? Koda yake ba abin mamaki baneba, yasan wacece Azeema sarai, komai zata iya aikatawa akan d'anta domin mulkin nan, amma bai tdammaci hakan da wuriba....."

"Gaisuwar Junaid ta katse tunanin mai martaba, ya amsa masa da kulawa. Shiru ne ya biyo baya,"

"kowa yana nazarin d'an uwansa, zuwa can mai martaba ya nisa yana gyara zamansa,"

"""junaid akwai matsalane, Ka buk'aci ganina?""."

"Murmushi junaid yayi, yad'an girgiza kansa, ""A'a Abba, dama za6in daka bani nazo fad'a maka""."

Murmushi Abdulsalam yai yace  ina jinka me kakeso?

Ya boye damuwarsa dake kasan ransa.

"""Nayi farin ciki da hakan Junaid, amma kafin sannan gawani albishir"".Abdulsalam ya cigaba yana"

kallansa.

"Kallonsa Junaid yad'anyi, saikuma ya murmusa yana maida kansa k'asa."

"Sarki Abdussalam bai fahimci murmushin Saba, ya danne ya Fara magana,"

" Duba da wasu abubuwa danai na fahimci yakamata kayi aure, kai idan masarauta ne, hankalin"

"kowa a kanka yake kana ganin matsalar data afkou wancen lokacin, hakan yasa yai tunani hadaka"

aure da kanwarka Zeenatu.

 Zeenatu?

Junaid yafad'a yana kallon mai martaba fuskarsa dauke da matuk'ar mamaki. Shi kansa mai

"martaba ya fahimci haka, dan haka ya gimtse fuska yana fad'in,"

 Umarnine Junaid dan dan Sarku matarsa ta farko dolene yabi umarnin wacce aka zaba masa.

Jinjina kai junaid yashiga yi yana wani irin murmushi  Sosai ka cancanci nabi Umarninka domin

"matsayin mahaifi kake a gurina, naji na kar6a da hannu biyu""."

"Sarki Abdussalam ya murmusa, dan aganinsa yasamu nasara a matakin farko. ""ALLAH yay maka"

"albarka Junaid, ina sauraren za6inka. "

"""Abba za6in nawa nima bamai wahala baneba, domin duk bisa bigire d'aya muke""."

Bigire daya?

"Gaban sarki Abdussalam ya fad'i, kardai mulkin?. Kafin ya nemo amsa maganar Junaid ya"

katseshi......

"""Inason izinin Auren yarinyar da muke tare acan, binta!..."""

 Binta?

Sarki Abdussalam yafad'a a harzuk'e wanda yau ne karo ma farko da Junaid yaga yayi magana

haka  Junaid maidamin murtani akan rashin kar6ar za6ina yasaka tunanin had'amin yarinya da Y'ar talakawa marar usul ko me? Ni nai tunanin taho maka da ita saboda ganin kana bukatar

"kwanciyra hankali anan, yanzu kuma ka kawo zancen so? "

"Shiru junaid yai yak'i tankawa, yay kuma kicin-kicin da fuska babu alamar fara'a, danmmi za'a kira"

"binta mara usili? To lallai inhar zai auri zeena sai dai da binta, inba hakaba kuma zai 6allo ruwa gaba d'aya kawai, saiya auri wadda basaso d'in da k'arfin mul......"

"""Dakai nake magana"". Sarki Abdussalam ya katse tunanin junaid."

" Dago ido junaid yay ya kallesa, fuskarsa babu alamar fara'a, hakan ba k'aramin razana sarki"

"Abdussalam yayiba, dan ainahin marigayi sarki Zubair yagani a fuskar Junaid d'in, kasa cewa uffan"

"yayi, saiya samu kansa da sassauta fushinsa, yace,"

"""Nabaka lokaci kayi tunani, bani kad'aiba ko mahaifiyarka bazata yarda da za6inka ba, har gwara"

ni zan iya hakura amma kai kasan Azeema bazata taba yadda ba.

"Junaid ya murmusa, ""Tuba nake Ranka ya dade ba binta kawai ba, ko Zeena bazata aminta ba,"

daga zuwana na shaida hakan.

"Yana gama fad'an hakan yamik'e ya fito cikeda kasaita da izza, wadda tasaka sarki Abdussalam"

kasa d'auke ido daga kallonsa. Har yaushe Junaid d'in yay irin wannan canjawar?.

"Junaid na fita ya tsaya a waje a hankalu ya juyo ya kalli bangaren Abdulsalam, bai taba tunanin"

"shima xai zo mai da magana haka ba, juyawa yai cikin isa ya nufi bangarensa."

******************

"Jakadiya ta kwashi gaisuwa wajen Azeema kafin tace, ""Ranki ya dad'e gani""."

"""Na ganki ai"". Azeema tafad'a tare da zuba mata ido. Takuma gyara zamanta tana kallon jakafiya"

dake gurfane.

"""Jakadiya inason bincike akan y'ay'an sarakunan k'asar zazzau, Gumel, kano""."

"""Angama ranki ya dad'e""."

"Jakadiya na fita Azeema ta kalli barira, ""Naji ance jiya mai martaba yayi zama Na mussaman da"

"waziri da wambai da shamaki""."

"""Eh lallai ranki ya dad'e anyi hakan, amma naji k'ishin-kishin akan auren gimbiya Zeena ne""."

"Baki Azeema ta ta6e, saikuma tayi murmushi"

Barira cikin san gulma tace  Gimbiya yanzu wace d'iyar sarkice a cikin ukunnan tadace da yarima

"Junaid?""."

Azeema ta dan harareta.

"Dariyar farin ciki barira tayi, saboda tunowa da binta tace  ranki ya dad'e mu jirayi tarihin"

"kowaccensu saimu d'ora a mizani, dan yarima yafi dacewa da d'iyar bajimin sarki mai ginannan"

"tarihi""."

"""Wannan gaskiyane barira, shiyyasa nakeson kasancewa dake a komaina, ko mai martaba bazai"

"San komaiba akai saina gama da shikansa junaid d'in""."

"""wannan shawara tayi ranki yadad'e""."

*****************

"""Uwar d'akina ga yariman can yafito daga sashen mai martaba, sai dai kuma ransa kamar a 6ace"

kamar yanda na kula.

Kamar Zeena tana bama fure amsa saikuma ta fasa  A bace? Ko muje bangarensa? Ai yayanane

ba wanda zaice wani abin.

 Amma ranki ya dad'e bak'ya ganin yawan zarya sashensa kamar zai  saikuma tai shiru ta kasa

k'arasawa saboda hararar da zeena ta watsa Mata.

Tace  Gun Yayana zani kinada magana?

Fure ta zube tace  tuba nake Gimbiya.

"A falo suka iske hajjo da Ramlah suna magana sai dai da alama ana jinsu akai shiru, harzata"

"wucesu hajjo ta dakatar da ita ""Ina zakije?""."

"Baki ta turo,  zan d'an fita mik'e kafa mana""."

Hajjo taja tsaki tana d'auke kanta. Zeena kuma tafice fure Na take mata baya.

***************

"Gaba d'aya ran junaid a 6ace take, yayinda zuciyarsa kemasa wani sak'e-sak'e akan mai"

"martaba. Ya tuna wadda akeson had'ashi aure da ita, yarinyar data tozartashi farkon shigowarsa masarautar, wadda batasan darajar d'an Adam ba, zai aminta da aurenta kawai domin yasamu damar kasancewa da kwatarwa Binta  yancinta, Ada ba son binta yake amatsayin masoyiyaba, amma ganin matsayinsa da nata ya kawo tazara a tsakaninsu yayi tunanin aurenta, hakanne kawai zai dai-daita matsayinsu tamkar yanda yake gani a tun farko. Yasan kuma babu Wanda zai amince masa da auren Binta kai tsaye, musamman mahaifiyarsa, amma idan ya jingina akan auren Zeena to lallai zai samu yanda yakeso, yanaji a zuciyarsa mai martaba da manufa yake son bashi auren"

"Zeena, inhar kuma yaga bashida mafita dolene ya yarje masa akan auren binta."

Ummana fa!?.

Wani sashen zuciyarsa ya ambata. Kafin samun amsa sallamar Azi ta katse tunaninsa. Azi ya

rissina yana sanar masa da neman iso daga Zeena.

"Wani kallo ya watsama Azi, kafin yace, ""Bana bukatar hayaniya""."

Azi ya jinjinamasa kai cike da girmamawa.

"Takaici ya kama Zeena jin amsar da Junaid ya bayar abata, wannan wulak'anci har ina, takula"

"yarima Junaid yacika tsauri da rik'o, yakamata ya yafe mata inhar akan laifin data aikatane bisa rashin sani, ita ta rasa meyasa take san ganinsa."

Ranta a 6ace tabar sashen.

***************

"Mamaki yakama Binta jin zancen da barira take Mata, wai gimbiya Azeema tace kar asake"

sakata wani aiki.

"Kodai Junaid ne yay magana? To amma jifa yanda ya watsar da ita d'azun, hakan bak'aramin k'ona"

"ranta yayiba, dan har kuka tayi, ita gaba d'aya ya Junaid ya canja Mata, tamkar bashine abokin"

nan nata dasuka tashi tare suka rayu tareba.

"""Ya ALLAH kabani ikon jurewa da wannan sabuwar rayuwa mai cike da rashin ya Junaid a cikinta""."

Ta share hawayen da suka ziraro Mata.

*************

"Mamaki sosai ya Kama gimbiya Azeema ganin yau kwanan junaid uku bai lek'ota ba, Anya kuwa"

lafiya?. Kokuma nazarin littatafan tarihi da Mahmud ya bashine suka d'auke hankalinsa?.

"""Inaga hakane"". Tafad'a a fili tana murmushi da kauda zarginta na farko."

"Sai mai martaba da shima a kwanaki ukunnan Sam bai nemeta ba, baki ta ta6e, dan hakan bai"

"dameta sosai ba, ayanzu burin gyara rayuwar d'anta ne a gabanta, dan nan kusa take buk'atar dawowar mulki hannunsa, tunanin yanda zatai da Abdulsalam ne ya darsu a ranta, dolene ta san yanda zatai."

"Nace, ""turk'ashi, wannanfa shine ga akuya ga kura @&""."

***************

Ayusher 27

***************

* ZAFIN RANA *

......................

*Hask e  W rit e rs Ass o ci a ti o n*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*K A$ f[ fV *

{28}

"Bude idanunsa yai a hankali ya daurasu akan Azi dake durkushe a gefensa, Littafin dayake nazari"

na hannunsa ya kulle.

"Azi yai murmushi yace ""yauma bazaka fita bane?"""

"Junaid ya kalleshi yace ""zuwa yamma."""

"Azi ya jinjina kai cikin gamsuwa sannan ya mike, haryaje kofa ya juyo ya kalli Junaid, Junaid ne ya"

kalleshi kallo mai dauke da tambaya.

"Azi ya kara rusunawa yace ""Binta fa ta zama 'ya, jiya dana ganta, da alama Gimbiya ta zareta"

"daga gun bayi."""

"Kai Junaid ya jinjina bai ce komai ba, Azi wanda ya fahimci jin dadin Junaid ya fita daga falan."

"Shiru Junaid yai a hankali kuma wani lalausan murmushi ya zagaye fuskarsa, baiyi niyyar fita ba"

saboda yana jiran aike daga bangaren Mai Martaba sai dai jin haka yasa ya mike.

"Ciki ya shiga ya fara shirin fita, harya gama shirya wa sai kuma ya koma ya zauna."

************

"Kallan Barira tai tace ""Anji daga gun Junaid?"""

"Barira tace ""tuba nake ranki ya dade amma haryanzu ba labari."""

"Shiru Azeema tai, tace ""Binta fa?"""

"Dazu wai zata fita, Azeema ta kalleta tana mata alamar ina?"

"Kai Barira ta girgiza tace ""bansani ba Gimbiya."""

"Shiru Azeema

14 / 28