Zafin Rana Book Compelet Novels By Aysha Alto

Author :  Aysha Alto Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   8 / 28

21K to 24K   out of 81.6K words

mai lale lale da dawowa, duk yanda"

yaso ya hango Binta abin yaci tura saboda yawan mutanen dake ta matsowa gunsa.

"Safiya ce tazo ta nemi da kowa ya tafi gun taro suma gasunan tahowa, nan kowa ya sa takalminsa"

ya fita.

Safiya tsayawa tai tana kallan Junaid hawaye suna gangaro mata.

"Jiki a sanyaye ya kalli Azi, da sauri Azi ya matso ya radamai cewa yayarsa ce."

"Junaid ya matsa kusa da ita, murmushin farin ciki ta hau yi tana goge hawayenta."

Nuna mata yai da yatsarsa akan ta goge nan.

"Nan ta goge tana dariya, tace Junaid Barka Barka"

"Murmushi yai, fitowar Azeema ce ta sa suka maida hankali kanta."

"Fadar uban gayun da Azeema tai ma bata lokaci ne, dan ta kashe lokaci ganin ta fito a yanda"

takeso.

Junaid ya matsa ya gaisheta.

"Fuskarta dauke da fara a tace  Yarima muje mutane na jira, dan wasu komawa zasuyi a yau. "

Kallan cikin gidan yai sannan yace  Binta fa?

"Tace  muje yanzu zasu taho da bata karasa shiryawa bane, kasan mu mata akwai wuyar shiri. "

"Nan suka tafi yana sake waigawa, barira tai daki da sauri dan su fito suma."

"Sai dai me? Ba Binta ba alamun ta, idanu ta zaro a tsorace tai kofar baya dan nemanta."

"A waje kuwa Binta tana tafe tana neman gidan Junaid, tun abin na mata dadi hartazo ta gaji, sai"

neman gun take gashi duk wanda ta nema dan ta tambayeshi daga yaga yanayinta zaiyi gaba.

Tana tafe tana share hawayenta dan itakam batama san inda take ba.

"Daidai nan ne lokacin dasu Zeenatu da Hajjo suka taho ta kan layin, Binta na share hawayenta"

"sam bata gansu ba, sai jitai an bigeta ta baya."

Da sauri ta nemi juyawa wanda hakan ya bugi hannunta.

Da sauri ta ja baya sannan ta kallesu.

"Zeenatu ranta yakai kololuwar matuka gun baci, tana huci ta daga hannu ta sharara mata mari,"

wanda ya gigita Binta.

Tace dago.

Binta ta sake dagowa ta kara kifa mata wani marin wanda sai dayasa ta tafadi.

"Ta daga wani zata kara mata, Zubair ya riketa yace  ya isa muje. "

Hajjo ta makama Binta harara sukai gaba.

"Wani irin kuka tasa tana kiran Junaid, dan tabbas raban da a mareta haka harta manta."

"Kuka take sosai, ta kasa ko mikewa."

"A can gun tro kuwa duk wannan abin da ake hankalin Junaid baya gun, ganin Binta taki zuwa"

yasa ya mike ya kalli Azi yace  muje naga taki zuwa.

Azeema dake zaune kusa dashi ta kalleshi tace  ina zaka?

Yace  naga haryanzu Binta batazo ba?

Haushi ya kamata amma ta murmusa tace  yanzu zata zo ko kuma Azi yaje ya dubo ko basu

"gama ba, hakan yayi? "

"Junaid ya kalli Azi yamai alama dayaje, nan Azi ya juya."

************

Ayusher

***********

*ZAFIN RANA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

Shafi na Goma sha Shida

"Azi na fita su Hajjo na shigowa gun, duk inda Zeenatu ta gifta zakiji ana gimbiya kinyi kyau, kanta"

ne ya kara fasuwa ta tabbatar abinda ke kwance a kasan ranta zai karbu.

Azeema tana ganinsu ta mike dan tarbar Hajjo wacce kowa keta gaishewa.

"Azeema na karasowa Zeena ta matso ta wani riko hannunta, duk da suna shiri da Zeenatu amma yau ce rana ta farko data taba riketa haka."

"Zeenatu cikin farincikin tace ""Umma karama barka barka."""

"Azeema tai murmushi duk da daurewa kawai tai saboda mutanen dake gun, sannan ta zare"

"hannunta suka gaisa da Hajjo, tare da nuna mata gurin zamanta."

"Hajjo ta kalli Zubair tace ""muje ka gaisa da kanin naka."""

Ta fadi haka ne dan ta batawa Azeema rai.

"""Oh hakane fa ashe Yarima Zubair baiga kaninsa ba."""

A tare suka jera inda Junaid ke zaune mutane duk wanda yazo sai ya gaisheshi sannan yake

komawa ya zauna.

"Suna karasowa Azeema ta kalleshi tace ""ka gaida Uwar gidan Sarki."""

"Junaid ya gaishe ta fuskar sa a daure, murmushi ta sake tana cewa lale lale Junaid."

"Kallan Zubair tai tace ""babban dan sarki."""

"Junaid ya mika mai hannu, suka gaisa."

"Ta bude baki zata gabatar da Zeena tai saurin cewa ""ni ai ka sanni."""

"Junaid sai yanzu ya kula da ita, kallo daya ya mata ya juya."

"Wannan abu ya bata mamaki, dan har kasa boyewa tai tace ""Ya Junaid!"""

"Kallanta ya sakeyi tace ""baka ganeni bane? Duk da nasan na bata maka amma a karshe ai"

"nice. """

"Hajjo ce ta tabata alamar tai shiru, fuskar ta ce ta canza dan da a nishadance tazo gun amma"

abinda ya mata yasa taji ranta ya baci.

"Azeema ce ta nuna ma Azeema gefen Junaid ta zauna, Zubair ya zauna a gefenta, ita kuma ta"

"zauna a dayan bangaren Junaid, Zeenatu na gefenta."

"Zeena sai cika take, me mutumin nan yake nufi da kallan da ya mata? Kamar irin yaga shara? Ai"

ko me tamai bada saninta bane balle ya tuhumeta.

"Haushin kayan data saka da bata lokacin datai gun kintsawa ne ya kara kular da ita, meyasa to"

takesan ta birge Junaid? Tambayar data zo mata kenan.

Da sauri ta kalleshi ya zubawa shirin dawakan da ake ido sai dai inka kula dakyau zakaga idansa

ba a gun yake ba.

"A hankali ta bi inda yake kallo, hanyar shigowa taga yana kallo, a fili tace ""wani yake jira?"""

"Azeema ta kalleta tace ""wa?"""

"Zeenatu tai murmushi tace ""naga kamar kofa yake kallo."""

"Azeema ta kalli Junaid sannan ta kalleta tace ""wasa yake kallo"""

Zeena ta kara kallansa tace hala ni naga daban. Ta fada itama tare da kallan masu wasan.

Gaba daya hankalinsa ya kasa nutsuwa sam abinda ake ma bai sani ba.

Busa da taken isowar mai martaba ce yasa Azeema cikin wani farinciki.

"Kallansa tai tacemai ""mai martaba ya iso."""

"Hajjo ta kalli Zubair tace ""me yake anan shi kuma?"""

"Zubair yace ""Hajjo karki nuna wani abin."""

Kallan Azeema tai wacce ke murmushin jin dadi.

"Shigowar mai martaba ya dau hankalin mutane,dan ba wanda yai tunanin zuwansa."

"Kusa da Junaid fadawan suka je, Azeema ta mike tana godiya, Sarki ya kalli Junaid yai gyaran"

murya wanda yasa kowa yin shiru.

"Kallan Junaid yai yace sai kuma ya dan murmusa yace ""ganin bansan me kake so ba yasa nai"

"tunanin abu daya."""

"Ya kalleshi yace ""nama alkawari a wannan guri na baka izini ka zabi duk wani abu guda daya da"

"kakeso, ko menene shi ni kuma na ma alkawarin yimakashi indai inada hali."""

"Junaid ya mike yai godiya nan aka hau tafa musu ana taya Junaid murna, Hajjo kam ta cika harta"

"gama batsewa, yanzu kam ran Zubair ma ya baci dan hannunta ya dunkule da karfi."

"Kowa ya gama sanin mezai faru domin abu ne mai sauki, Junaid zai nemi abashi mulki kuma dole"

"ne Sarki ya bashi tunda alkawari yai, wannan al'amari ya batawa magoya bayan Hajjo da danta rai, Azeema kam wani dadi ne ya kamata ta sake yima Sarki godiya."

"Sarki ya juya ya bar gun, Zeenatu tai shiru itama tana tunanin abinda ya faru a lokacin, me"

mahaifinta ke nufi.

"Sarki na juyawa Junaid ya kalli Azeema yace ""bari ma duba Azi da alama wani abin ya samu"

"Binta."""

"Bai ko jira tayi magana ba ya juya da sauri, bayin dake kula dashi sukabi bayansa."

"Kallan Junaid mutanen dake gun sukai, ina zaije bayan wannan taran anshiryashi ne saboda shi?"

"Safiya dake gefe ta mike da sauri dan ta tareshi, sai dai kafin ta karasa yabar gun, ganin kar"

"mutane su ankara da halin da ake ciki yasa ta wayance da zuwa gun Azeema wacce ta cika fal a kasan ranta, Zeenatu ce ta mike da sauri tana kokarin fita daga gun, da alama binshi take san yi"

"taga ina zashi haka, muryar Hajjo taji tace  ina zaki? "

Kallan Hajjo tai sannan tace  kaina ke dan 

"Gun zamanta ta nuna mata da kanta, hakan yasa ta koma ta zauna fuska a hade."

"Azeema ce ta mike, cikin nuna jin dadinta da wadanda suka hallari taran sannan ta sanar dasu"

wasani kala kala da za a gabatar nan gaba tare da basu hakuri akan Junaid yadanje ganin wanine amma yanzu zai dawo.

Azeema ta kallo Safiya tace  Barira har yanzu bata zo ba ita ma?

Tace  eh bari na dubota

Kiyi masa kafin a ganshi da yarinyar.

"Yarinya? Safiya ta tambaya, Azeema ta mata alama dataje kawai, juyawa tai ta fita, Zeena da"

kunnenta ke makale agun taji kalmar yarinya da aka ambata amma bata fahimci me ake nufi ba.

Yarinya? Abinda ke yawo akanta kenan......

"Junaid kam yana fita bangaren Azeema yaje, sai dai ba kowa a bangaren, hakan yasa ya nufi nashi"

"bangaren, yana zuwa a bakin kofar shiga ma yaga Hari yace  Hari tana ciki ne? "

Hari hankali a tashe tace  Yarima an rasa inda take.

"Idanunsa ne suka fito alamar tsantsan mamaki, hankalinshi a tashe yace  ba a ganta ba kamar"

ya? Yanda yai maganar kadai zaka san hankalinsa ya gama tashi.

"Harira tace  ina zaune Azi ya shigo shida Barira tagun Gimbiya wai suna neman Binta, ganin"

bata nan shine suka rabu zuwa nemanta ni kuma na tsaya anan ko zata zo.

"Bai kara tofa komai ba ya juya hankali a tashe, Hari na kiransa amma inaa baibi ta kanta ba,"

bayinsa ne suka bishi a baya.

"Yama rasa ta ina zai fara neman nata ganin yanayi guri ba kadan ba, tunda gashi ko Azi bai gani"

ba bare Bari.

"Haka sukai ta bi suna nemanta, itama Safiya ta fito da tata tawagar suna neman Junaid su kuma."

"Gaba daya jikinsa ya gamayin sanyi gani yake ma ta bar masarautar ne, yana tafe yana dana"

"sanim dawowarsa nan, danshi bai ga amfani dawowarsa cikin daula ba ita kuma ta koma ita kadai."

"Wata bishiya ya gani, ya tsaya tare da kura mata ido yana tunanin yanda suke zama a bayan gari,"

yana saman bishiya ita kuma tana kasa suna hira.

Baisan sanda murmushi ya bayyana a fuskarsa ba dan gani yake kamar a wannan lokacin akeyi.

Harya juya yaji alamun ana cilla dutse karami.

"Da sauri ya leka bayan bishiyar, tana zaune rike da kananan duwatsu tana cillawa daga inda take."

Wata nannauyar ajiyar zuciya ya saki tare da jingina da jikin bishiyar.

Binta jin yanda yaja ajiyar zuciya ne yasa ta juyo ta kalleshi.

Idanu suka kurama juna yana daga jikin bishiyar ita kuma tana zaune.

Kuka?

Me akamin da zanyi kuka? To ya naga idanki haka?

Tace  kawai na gaji ne.

Me kike anan?

Tunani?

A tare suka saki murmushi wanda ya bayyanar da begen juna da sukey. Matsowa yai kusa da ita ya zauna yace  bata kikai?

Ta dan harareshi tace  eh mana garin neman wani.

Dariya yai yace  Ahhh yazanyi da Bintar nan banaji zata ita yini bata ganni ba

Dariya tai itama tace  Ahhhh ya zanyi da Ya Junaid banaji inyaga bai ganni ba zai samu nutsuwa.

Yanzun ma a tare sukai dariya kafin tace  Allah yaya wannan gidan naku yai girma.

Yace  bakya sanshi mu koma?

Kallansa tai a ranta tace ta ina zan sake rabaka da iyayenka?

A fili tace  in nace mu koma zaka yarda?

 Kina musu? Kin dai sanni ko?

"Da sauri tace  wasa nake Yarima, ban isa ba. "

 Kin tsorata kenan?

Tana dariya tace  tuni ma.

Mikewa yai yace  muje.

"Mikewa tai suka fara takawa a tare, suna tafe suna hirarsu yana bata labarin abinda akai batanan"

duk da shima bakomai ya fahimta ba.

"Suna shawo kwana Safiya ta hangoshi, da sauri ta karasa, tace  Junaid kazo ka koma, mutane"

"na nemanka, karsuyi zargin wani abin. "

Kallanta yai yace  Ba a gama ba?

Tace  eh karkasa mutanen da sukazo dominka suji ba dadi.

Ta karasa tare da kallan Binta.

Yarinyar dazu?

Junaid ne ya kalli Binta yace  muje?

"Kayan jikinta ta kalla, sai a lokacin ta kula da irin shigar dayai da kuma irin shigar da Safiya tai,"

"jitai tasha jinin jikinta, ta kalleshi tai murmushi tace  a a kaje ni zan jiraka a inda ka ganni yanzu. "

Kai ya girgiza alamar a a sannan yace  sai dai in mu tafi tare ko ki zauna gun Hari.

"Safiya ta kalli yarinyar itama cikin rashin jin dadin wannan abu, wacece? Ina ya samota? Da"

"alama soyayya ce mai tsananin karfi tsakaninsu wanda ita kanta ganinsu na farko tare yasa ta fahimci haka, tab lalai da matsala......"

Muryar Binta ce ta katseta tace  zan jira gun Harira.

Nan suka karasa bangarenshi sai dayaga ita da Harira sun rike hannu sun shiga sannan ya juya.

"Harira na rufe kofa ta jawo Binta ta rungume, wanda jin haka yasa Binta sakin kuka, tabbas"

"yanzu kam jikinta ya fara bata Junaid ya mata nisa, yafi karfinta........."

*Ayusher *

*ZAFIN RANA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

*Shafi Na Goma Sha Bakwai*

"Azeema ce ta zauna a bakin ta wuce ciki bayan ta gama sallamar da jama ar ta, tana shiga ta"

zauna a gefen gado cikin bacin rai.

"Safiya ce ta turo kofar a hankali ta shigo, kallanta Azeema tai tace  ya wuce? "

Safiya tace  nayi nayi ya taho nan yace ya gaji ne amma ni nasan saboda yarinyar nan yake san komawa.

Safiya ta karaso tace  wacece wai?

Azeema tace  ina ma na santa? A can inda suka taso ya hadu da ita.

 Yanzu haka zamu bar yarinya mara asali tana juya Junaid? Taya zamu dawo da abinda muka rasa hannunmu yana haka?

Azeema ta kalleta a hankali ta saki wani lalausan murmushi wanda Safiya tace  Umma me kike

tunani?

Kallanta tai tace  ke a naki tunanin Junaid nada wayau a wannan lokacin?

Tace  bangane ba.

"Azeema ta murmusa sannan ta mike tsaye tace  baisan komai ba, banda ita a wannan lokacin, me kike tunanin zai faru in aka kamata da gagarumin laifi? "

"Safiya tace  bangane ba, hankalinsa ne zai tashi? "

"Azeema ta kalleta sannan tai ajiyar zuciya tace  basu kwana biyu zan dau mataki a na ukun, kwana biyun zan barshi ne yai bankwana da ita. "

Safiya ta kalleta dan sau da dama in Azeema na magana ba komai take ganewa ba.

Jin kamar ta sauke nauyin dake kanta ne yasa ta mike ta shiga toilet. Safiya ta bita da kallo.

********

"Binta ce zaune Hari na taje mata kai, Hari tace  hanzu kin ware da kikai wanka? "

Kai ta daga tana murmushi tace  Bansan ya akai naji kuka yaki daina zuwa min ba dazu. Hari tai murmushi tace  Binta!

Naam

"Hari tadanyi shiru kafin tace  sai kinyi hakuri dan rayuwar masarauta ba daya take da rayuwar da kika sani ba, sannan dole sai kinyi hakurin janye jikinki daga gun Junaid inba haka ba daga ke har"

shi kuma bazaku tsira ba.

Kallanta Binta ta juyo tai tace  bangane ba Hari.

"Hari ta daure mata kanta tace  bazaki gane ba duk bayanin da zan miki sai dai inaso ki kula da mutanen masarautar nan, karki yarda da kowa inba Junaid. "

Binta ta daga kai alamar fahimta sannan tace  Mahaifiyarsa fa?

"Hari ta kalleta tace  itace mace ta farko da zaki kula da ita, dan kowa ansan cikinsa amma ita ba wanda yake sanin nata, sannan ba sarauniyar dazatai murna da danta ya kwaso mata mace wacce"

ba yar mulki ba irinki

Binta cikin rashin fahimta tace  ni ai tare muka taso.

Hari ta mike tace  da alama an gama taran naji masu busa sun daina.

Binta na kokarin fitowa Junaid na shigowa bangaren.

"Daga nesa ya kalleta cikin jin dadi, gashi tai wanka ta sa kaya duk da kayan ta ne nacan amma tayi kyau."

Fuskarsa dauke da murmushi yake kallanta harta karaso inda yake.

Tace  wai harkun gama?

"Fuskarsa ya canza yace  ko na koma? Yai maganar yana neman juyawa, da sauri tace  wasa nakeyi. "

Kallanta yai yace  Muje?

Kai ta daga suka nufi cikin kilisarsa yana nuna mata.

Sannan yace  dazu na tafin miki da abu amma Azi ya manta inda ya ajiye saboda nemanki da akai tayi.

Tace  ina binka bashi.

Dariya sukai a tare.....

**********

Ran Hajjo yakai matuka gun baci dan abinda akai a tarancan ba karamin bata mata rai yai ba.

Kallan Zubair tai tace  kaga abinda nake ce maka ko? Idan har bamuyi da gaske ba yan kallo za a barmu a gidan nan.

"Zubair ya kalleta shikanshi abinda ya faru ya bata masa rai, yace  Amma Hajjo abinda mai"

martaba yai dazu ya kyauta?

Ramlatu wace ta biyesu ce ta kalli Hajjo tace  sai fa mun dage inba haka ba komai zai lalace ne ba tare da mun shirya ba.

Hajjo ta kalleta sannan tace  Zubair jeka zan nemeka.

"Nan Zubair ya mike ya fita, Hajjo ce ta maida dubanta kan Ramlatu tace  kin samo yanda za "

ai?

Ramlatu ta kalleta tace  karki damu ina tunanin ido zamu zuba komai zai wakana ne in muka sa

hannu kadan.

Hajjo tace  me kike nufi?

Murmushi ti sannan ta kara matsowa tace  kinsan ya taho da yarinya daga can inda ya taso?

Cikin mamaki Hajjo tace  yarinya kuma?

" Eh dazu bakiga ya fita ba ana taro, haka kawai jikina yaban akwai wani abu shine na tura abi bayansa. "

Hajjo cikin kaguwa tace  sai akai ya?

Ashe yarinya yake nema

Hajjo mamaki karara ya bayyana a fuskarta tace  meye tsakaninsu?

Ramlatu tai dariya tace  meye tsakanin mace da namiji ai ko daga yanda ya mike yabar gun

alamace ta tanada babban matsayi a gunshi.

"Wata irin dariya Hajjo ta saka wanda ki kaina ban taba jin tayi dariya haka ba, har kwallace ta"

taru a idanta sannan tace  zanso ganin halin da Azeema ke ciki.

Ramlatu tai dariya itama tace  shiyasa zamu taimaka kadan muja baya muyi kallo.

Hajjo tace 

8 / 28