Zafin Rana Book Compelet Novels By Aysha Alto

Author :  Aysha Alto Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   22 / 28

63K to 66K   out of 81.6K words

harareshi tace  Ya Junaid kasan banasan sunan ko?

Dariya yai yace  Bintalo...

Ajiye cup din tai tace bazan maci ba.

Na tuba a yafemin.

Dariya tai tace  sai ka fadi abin.

Yace ah to bari na shirya.

Hanayenta ta hade tana jiransa.

Dariya yai yace  Nana Fadima na tuba. 

Dariya yai sosai shikuma ya hade fuska.

Tace  Ya Junaid dan sake.

Naki din.

Ya fada cikin wasa.......

Ayusher

* ZAFIN RANA *

......................

*Hask e  W rit e rs Ass o ci a ti o n*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*K A$ f[ fV *

{41}

Kallan Azi yai yace  ka fita wajen gari ka yadamin jita jita cewar Sarki Abdulsalam ganin dawowar

asalin dan Sarki Zubair yasa zaiyi Murabus ya ba asalin magajin sarki mulkinsa.

Azi ba tare da tambaya ba yace  To Yarima.

"Nan Ya fita da wasu hadiman Junaid, haka sukai ta yadawa tun daga cikin fada har wajen"

masarauta.

*******

"Sam Abdulsalam ya kasa zaune ya kasa tsaye, afa da marwa kawai yakeyi a cikin kilisarsa."

Isowar su Shamaki ce yasa ya koma ya zauna.

"Cikin tashin hankali suka shigo, Mai Martaba meke faruwa?"

Abdulsalam ya kallesu yace  yaran nan ya san komai.

Galadima yace  taya za ai ya sani abinda akai yana tsimma? Hatta wanda yai maganin fa mun

ga bayansa.

"Abdulsalam yace  to kamar mai aljannu yaran nan hankali a kwance yazo ya sanar dani komai,"

Sabisun kansa baisan abinda ya faruba rabi da kwata in dai har ba aljanu ne dashi ba to ba yanda

za ai ya sani.

Waziri ne cikin nazari yace  ko dai Gimbiya ta fadamai abinda ta sani ne?

Taya zata fadi abinda tasan zai ja mata matsala?

Shiru sukai suna tunanin abinyi.

Jakadiya daga waje ta nemi iso cikin tashin hankali.

Kallan juna sukai sannan sukace lafiya?

Jakadiya ce ta shigo ta zube tace  Allah ya taimaki sarki yanzu labari ya karade ko ina akan wai

zakai murabus.

Hankali a tashe suka kalli juna sannan a tare sukace  Murabus?

"Jakadiya tace  wai zaka maida sarauta inda take, tunda magajin sarki ya dawo. "

Cikin tsakanin tashin hankali sukace  magajin sarki? Junaid?

Jakadiya tace  ka gafarce amma zance ya gama karade gari anata jinjinawa adalcinka.

Sallama tai ta fito.

"Ba karamin tashin hankali bane ya bayyana a fuskokinsu, musammsn Abdulsalam wanda yakeji"

duk duniya ba mai rabashi da kujerar mulkinsa.

"Shamaki ne yace  yanzu ya zamuyi? Ya riga ya samu a karshen layin da babu mabula, yanzu"

"inkace bazaka bashi ba mutane zasu fara zargin halayarka gaba daya mutane zasu bar bayanka,"

sannan inka bashi mu kuma gaba daya tamu ta kare.

Ran Galadima a bace yace  wai yaran nan ba sirikinka bane?

"Gaba daya hucci kawai Abdulsalam yake, yama rasa me zaice."

********

"Zeena na zaune Hajjo ta aiko tazo, tace  ace mata zanzo anjima."

Kafafunta da ake gyara ma farce ta kara mikawa sannan ta kalli Fure tace  waccen matar mara

galihu tana ina?

Fure tace  tana bangarenta ranki ya dade.

Baki Zeena ta tabe sannan tace  Yarima fa? Ta tambaya cikin alamar tambaya mai karfi.

"Fure ta fita da sauri dan dubawa, bata dade ba ta dawo cikin jin dadi tace  bayacan Gimbiya. "

Dadi ne ya kama Zeena tai murmushin farin ciki.

"Hadimar Hajjo ce ta shigo cikin tashin hankali tace  Gimbiya, Hajjo na nemanki cikin gaggawa. "

Zeena ta kalleta tace  kai!

Kamar zata sake magana sai kuma ta mike ta zura alkyabarta wace ke kara mata kyau suka fito.

Mamaki ne ya kama Zeena ganin Hajjo a bakin kofa.

Tana ganin Zeena ta ja hannunta suka shiga ciki.

"Ramlatu, Zubair da kanin Hajjo Suna zaune a kilisar."

Hajjo ta zaunar da ita a kasa a gabanta tace  fadamin dake a ka hada baki?

Zeena cikin rashin fahimta tace  aka hada baki a me?

"Bakin Hajjo ne ya fara kumbura, fuska ta turbune cikin kunar rai tace  uban waye ya isa yasa"

Sarki murabus?wato ke dan hauka mijin da kwata kwata baki dade da aura ba shine yafi

mahaifinki ko?

Zeena tace  nifa bansan me kike cewa ba.

"Ramlatu ce tace  nifa nafi tunanin Azeema ce, matarnan ba karamin shiri ta iya ba. "

"Hajjo cikin tsananin bacin rai ta kalli Zubair dake zaune kamar zaiyi kuka, tace  haka kawai an"

"yada wai Sarki zaiyi murabus yaba asalin magaji mulki, inba Junaid ba wazai yadda wannan abin? "

"Zeena ta mike tace  ni wlh na dauka ma wani abin ne, to in an yada dama ba mulkinsa bane, tun"

asali nashi ne dan yace yana san abinsa laifi ne?

"Hajjo ce ta mike ta daga hannu kamar zata kifa mata mari sai kuma ta tsaya tana hucci, Zeena"

kam kyar take ba alamar tsoro tace  Wai Hajjo sai yaushe zaki daina tunanin ba ya Zubair mulkin

nan? Bayan ke kanki kinsan bashi da abinda Sarki yake dashi?

"Ran Hajjo ya kara kololuwa gun baci, Zubair ne yace  bani dashi kuma a hakan zan amshi"

"hakkina, daga yau Hajjo karki kara kirana ki kira yarinyar nan. "

"Juyawa tai ta fita rai a bace, Hajjo cikin tsananin takaici ta bita da kallo."

******

Barira ta kalla tace  mene?

Barira ta kara sanar da ita tace  yanzu duk abinda yake yawo keman a masarautar nan.

"Komawa tai ta kwanta, saboda zazzabi da ciwon kai data kwana dashi, kallan Barira tai tace"

" Barira ki aika a kiran Junaid, kice a fadamai banda lafiya. "

"Nan Bari tace dakaina ma zani, ta fita."

Junaid na zaune suna dan hirar da shida Sabisu yana bashi labarin Sarki Zubair aka sanar da

isowar Barira.

Sabisu ne ya shiga ciki sannan ya bata dama.

Zubewa tai ta gaisheshi sannan ta sanar dashi aiken Gimbiya.

Kallanta Junaid yai yace  Allah ya bata lfy.

Barira ta dan dago tace  Yarima rabanta da abinci tun jiya shima dakyar tasha kunu.

Kallanta Junaid yai yace  ki koma ki kula da ita tafi kowa sanin bazan zo ba.

"Barira ta bude baki zatai magana Junaid ya mata wani kallo, mikewa tai ta mai sallama ta fita."

Jin yanda sukai da Junaid yasa Azeema tai murmushin takaici tace  nasan nima bazsi taba zuwa

ba sai dai zuciyata na fatan zaizo din.

Barira tace  Gimbiya dukda bansan meke faruwa ba amma dan Allah kici abinci.

Tashi ki fita.

Mikewa tai har zata fita sai Azeema tace  kiramin Binta.

Kallan ta tai da sauri tace  Binta?

Kai Azeema ta daga cikin azabar ciwon da kanta ke mata.

"Binta tana zaune tanata gyara fuskarta, dan itama so take ta dinga fitowa das kamar Zeena."

"Tayi kokari sosai dan tayi kyau, yanzu bata komai saboda jiya Harira ta kawo mata hadimai su"

uku.

Barira ce ta sanar da ita sakon Gimbiya.

"Cikin jin dadi ta mike, kallan Barira tai tace  bari na aikama Yaya Mu tafi. "

"Nan ta tura aka sanar da Junaid, kamar ya hanata sai yaga inya hanata tabbas xatai xargin wani"

abin.

******

Nan suka fito.

Suna kokarin barin kofar Zeena na dawowa daga bangaren Hajjo.

"Kallan Juna sukai ita da Binta, kafin Binta ta gaisheta, Zeena cikin isa ta amsa su kuma suka"

wuce.

Cikinta shiga.

***

"Binta ta shiga cikin daki, Azeema na kwance, hannu Azeema ta mika mata alamar ta matso inda"

"take, mamaki ne ya kama Binta ta kasa matsawa harsai da Barira tace  Binta ki karasa. "

Azeema dake zaune Binta na matsowa ta kama hannunta cikin dana sani da takaicin abinda ta

aikata.

Binta!

Kallanta Binta tai cikin sanyi.

Azeema tai murmushi tace  Junaid fa? Yana nan lfy?

Binta ta daga kai alamar eh.

Barira ta kalla ta mata alamar ta fita.

Nan ta juya ta rufo musu kofa tana mamakin meke

damun Gimbiya? Yau ita ke yima Binta haka???

Nace daga baya kenan

Ayusher

* ZAFIN RANA *

......................

*Hask e  W rit e rs Ass o ci a ti o n*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*K A$ f[ fV *

{42}

"Gaba daya jikin binta ne yai sanyi, yanda Azeema ke rike da hannunta."

Can tace  Mamanki kince ta rasu ko?

Kai Binta ta daga cikin sanyin jiki.

Murmushi tai tace  kiyi hakuri ban dubi maraicinki na jaki a jiki ba. Binta ta share kwallar da ta zubo mata.

Babanki fa?

"Tunda ya koremu bansake komawa ba, sai dai bayan na girma munganshi da yaya shima yayan ne ya kaini sai dai bamuyi magana ba. "

Dayan hannunta ta dan daura a saman hannunta data rike.

"Binta ta kalleta tace  nice mai laifi, na san ko wanene dole yaki amincewa dani, balle dan sarki? "

"Kai Azeema ta girgiza tace  ko kadan san kai da dan zuciya ne irin nawa, a koda yaushe ina"

"dauka nice nake tafiyar da rayuwata sai dai yanzu na fahimci duk rayuwata amfani ake dani, san"

kai dana ke tunanin ina dashi na gane duk shi ya jamin wannan rayuwar dana sa kaina.

Binta bata san me take nufi ba hakan yass ta kslleta ganin yanda Azeema tai shiru cikin wani

"yanayi, daurewa tai ta kalleta tace  karki damu da halin da nake ciki ni nasa kaina a ciki. "

***********

"Junaid ne ya kalli waje, ganin rana tadan fara sanyi ya kalli Azi yace  muje. "

"Nan suka fito, Junaid ya sa kaya wanda ko ranar bikinsa baiyi irin wannan kyan ba, Alkyabar dake"

"jikinsa mai tsananin kyau ce tamai kyau sosai, yayi rawani wanda bayi yake yi ba in ba da dalili ba."

"Tunda suka fito ake gaisheshi, har suka isa fadar sarki."

Sarki wanda ke zaune cikin fada ya kalli manyan masu mukamai dukansu da suka iso akan abinda sukaji.

"Turaki ne ya kalleshi yace  Dolene mu taso jin wannan babban al amari, taya Ranka ya dade"

zaka yanke wannan babban hukunci ba tare da munsan komai ba.

"Sarki ne ya kalleshi, Waziri ya dafa Shamaki wanda yaga yana neman yin magana, Shamaki cikin"

"takaici ya kalli Galadima wanda shima ya cika ya batse, Sarki ne ya kalli Turaki bayan yayi murmushi yace  to mudai wannan magana.  "

Kafin ya karasa aka sanar da isowar Junaid.

"Hankalin Abdulsalam a tashe sai dai baiko kalli kofa ba, isowar Matawalle Junaid ne yasa duk"

kowa ya zubawa kofa ido.

Junaid ya shigo sannan ya gaisuwa ya ja ya zauna.

Sarki ne ya kalleshi yace  Matawalle kaima ka fito?

Junaid yai murmushi yace  munzo ban hakuri ne akan abinda kake neman aikatawa.

Kallanshi Sarki yai a ransa yace  me kuma kake shirin yi?

Junaid ya sunkuyar dakai yace  Tuba nake ranka ya dade amma ina ganin hukunci da umarninka

na ajiye mulkin nan yayi tsauri.

"Kallansa sukai da sarki dasu Shamaki, gaba daya shamaki da Galadima sun bude baki, Junaid ya"

dan kara dagowa yace  kace haka kama Marigayi Sarki Zubair alkawari amma ina ganin a sake dubawa.

Gaba daya kasa magana sukai saboda tsananin mamakin wannan dabaibaiyo daya faru.

"Turaki ya kalli Sarki yace  Amincin Allah ya tabbata a gareka, ashe alkawari kukai da sarki? "

Nan ragowar na fada suka fara jinjina ma imani da adalci irin na Sarki.

"Wale ne ya kalli Sarki yace  gaskiya Sarki Allah yasa ka gama da duniya lafiya, ba karamin"

"mamaki mukai ba da jin wannan abun, da ranmu ya baci amma jin dalilinka yasa mun fahimci"

abinda kake nufi.

Allah ya sa haka ne mafi alkairi.

Nan kowa yace Ameen

"Gaba daya kwakwalwar Abdulsalam ta kulle, kallan Junaid ya shiga yi, Junaid yai murmushi"

sannan ya kallesu yace  ku ba Sarki hakuri taya zan hau mulki bayan da karfinsa?

Turaki ne ya kalli Sarki yace  Takawa kaji abinda yace? Sai dai nasan alkawarin sarakuna ba a

ajiye shi.

"Da kyar Sarki ya daidaita nutsuwar sa sannan yace  To ka gani, dole dai ayi abinda ya dace. "

Junaid ne ya sake yin kasa dakai yace  ku ba Takawa hakuri ba jibi na ya bari sai nan da

shekara.

Jibi? A tare suka fadq harshi sarkin dai baisan ya fadi hakan ba.

"Kallansa sukai jin muryarsa, murmushi yai yace  Jibin dai. "

Turaki yace  Allah ya kara ma yawan rai.

Sarki ne ya kallesu yace  kaina nadan ciwo ina san shiga ciki.

Nan suka kara gaisheshi ya fita.

Waziri dasu Shamaki suka fita suma.

Junaid ya tsaya suna ta gagaisawa dasu kafin ya fito.

Yana sa takalminsa ana sanar dashi Sarki na nemansa.

Bai musa ba ya nufi bangarensa kai tsaye.

"Sarki na tsaye ya juya baya gaba daya hankalinsa ya kai kolokuwa gun tashi, idanunsa sunyi jaaa"

alamar tashin hankali.

Junaid ne ya shigo ya zauna zaman cin abinci a kasa sannan ya daura hannayensa a kan cinyarsa

baice komai ba.

Juyowa yai ya kalleshi Junaid na zaune yana kallansa shima.

Cikin tsananin bacin rai Sarki ya kalleshi yace  me kake shirin yi?

Junaid ne ya kalleshi yace  kai me kake shirin yi?

Baki Abdulsalam ya bude yace  ni kake fadawa magana haka kanka tsaye?

Ya kake so nawa makiyina magana?

"Makiyi? Abdulsalam ya maimaita cikin jin haushi, Junaid na fada maka duk abinda ya faru akan"

mahaifiyarka ne ko? Ko duk ba akanka aka aikata ba?

Wani murmushi yai yace  ita kenan itace zata yadda akanta ka aikata amma ni dakai munsan ba

a kanta ka aikata ba.

Hura hanci yai yace  Kasan ka kiyayeni?

Junaid yai murmushi yace  duk abinda zaka aikata min inaso ka tuna abu biyu na farko kowa

"yasan ni zaka ba mulki jibi dan haka duk abinda ya sameni cikin dayan biyu ne ko kai ko Zubair danka ne, to sai dai matsalar na riga na sanarwa yarka duk abinda ya saman kaine, kaga shaidarta"

ta isa komai naka ya wargaje.

"Gaba daya Abdulsalam ya gama shan jinin jikinsa, ya kalli Junaid yace  to ka fito ka sanar da"

duniya laifin nawa mana.

"Junaid yai dan dariya yace  karka damu komai da lokacinsa, sannan ina duba darajar yarka ko"

"nace wacce ka bani ita saboda kana san boye laifinka ne, hakan yasa bazan fada ba, sai dai wannan shine kashaidi na karshe da zan ma, daga gobe ka tattara ka koma inda aka ajiyeni na zauna ko kuma ka nemi wani gidan ka zauna inba haka ba duk abinda ya biyo baya karkaga laifina,"

inada shaidu da zan lalata ma suna cikin mintina kadan wanda fita ma gagararka xatai.

"Mikewa yai zai fita, ita Azeemar fa? Badai kana tunanin ajiyeta anan ba?"

Junaid bai kalleshi ba yace  duk wani mai laifi sai ya amshi laifinsa ko itace kuwa.

Ya juya ya fita abinsa.

Yana fita Abdulsalam ya saki wani kara tare da zama a kan gado cikin tsananin bacin ran da tunda yazo duniya bai taba fuskan tarshi ba.

*****

Zeena ce ta kalli Fure tace  da gaske hakan ake yadawa?

Fure tace  yanzu ma jinai ance wai jibi Sarki zaiyi murabus.

Shiru tai tana nazari meke faruwa Ya Junaid?

Hajjo kam cikin kumburin baki ta sabi alkyabarta ita da Zubair suka nufo bangaren Sarki sai dai an

sanar dasu bazai gansu ba.

Wannan abu ya kara koma mata rai matuka wanda takeji ko zata kwana a wajen nan bazata tafi

ba sai ta ganshi....

****

Ayusher

* ZAFIN RANA *

......................

*Hask e  W rit e rs Ass o ci a ti o n*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*K A$ f[ fV *

{42}

"Gaba daya jikin binta ne yai sanyi, yanda Azeema ke rike da hannunta."

Can tace  Mamanki kince ta rasu ko?

Kai Binta ta daga cikin sanyin jiki.

Murmushi tai tace  kiyi hakuri ban dubi maraicinki na jaki a jiki ba. Binta ta share kwallar da ta zubo mata.

Babanki fa?

"Tunda ya koremu bansake komawa ba, sai dai bayan na girma munganshi da yaya shima yayan ne ya kaini sai dai bamuyi magana ba. "

Dayan hannunta ta dan daura a saman hannunta data rike.

"Binta ta kalleta tace  nice mai laifi, na san ko wanene dole yaki amincewa dani, balle dan sarki? "

"Kai Azeema ta girgiza tace  ko kadan san kai da dan zuciya ne irin nawa, a koda yaushe ina"

"dauka nice nake tafiyar da rayuwata sai dai yanzu na fahimci duk rayuwata amfani ake dani, san"

kai dana ke tunanin ina dashi na gane duk shi ya jamin wannan rayuwar dana sa kaina.

Binta bata san me take nufi ba hakan yass ta kslleta ganin yanda Azeema tai shiru cikin wani

"yanayi, daurewa tai ta kalleta tace  karki damu da halin da nake ciki ni nasa kaina a ciki. "

***********

"Junaid ne ya kalli waje, ganin rana tadan fara sanyi ya kalli Azi yace  muje. "

"Nan suka fito, Junaid ya sa kaya wanda ko ranar bikinsa baiyi irin wannan kyan ba, Alkyabar dake"

"jikinsa mai tsananin kyau ce tamai kyau sosai, yayi rawani wanda bayi yake yi ba in ba da dalili ba."

"Tunda suka fito ake gaisheshi, har suka isa fadar sarki."

Sarki wanda ke zaune cikin fada ya kalli manyan masu mukamai dukansu da suka iso akan abinda sukaji.

"Turaki ne ya kalleshi yace  Dolene mu taso jin wannan babban al amari, taya Ranka ya dade"

zaka yanke wannan babban hukunci ba tare da munsan komai ba.

"Sarki ne ya kalleshi, Waziri ya dafa Shamaki

22 / 28