Zafin Rana Book Compelet Novels By Aysha Alto

Author :  Aysha Alto Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   25 / 28

72K to 75K   out of 81.6K words

daga kai alamar to sannan ya juya ya zauna.

Waziri dasu Shamaki ba shakka tsananin tsoron Junaid ya gama kamasu.

"Sarki ya daure yai gyaran murya, da kyar ya samu ya daidaita muryar sa dake rawa yace  abu"

"dai da kukaji haka yake, ina faran zaku bani hadin kai, nima na samu na huta, dama can asalin mulkin nan na shi ne, na rikemai ne saboda mahaifinsa ne wato yayana ya sani, sai dai yanzu"

"Junaid ya girma yayi aure, na tabbatar ku kanku yanzu kunsan Junaid ya cancanci kujerarsa. "

"Zubair kara habaka yai, cikin bacin rai matuka."

Sukam yan fada kowa ya gamsu da maganar Abdulsalam.

"Yau zan ajiye mulkin nan, a wannan lokacin ina fatan xaku ba shi hadin kai, na tabbatar xai yi"

abinda ni da mahaifinsa bamuyi ba.

Wale yai dan murmushi yace  tabbas Takawa samun irinka a duniya sai an tona.

"Junaid ya rusuna sosai yace  Ina godiya Takawa, na gode daka zabeni sama da jininka, wannan"

hallarci naka tabbas abin dubawa ne.

"Kallan Shamaki yai yace  a dako sandar mulki a da kamai, inyaso ragowar abin Sarauta sai ranar"

da za ai nadin sai a bashi.

"Nan Shamaki ya juya ya fita, Waziri ya kalli Sarki wanda yasan Allah ne kadai yasan halin da yake"

ciki a wannan lokacin.

********

"Haka Binta ta zauna sai dataga Azeema taci abinci sosai, sannan sukafara hira sama sama duk da"

rabin hira Binta ce ke bata labarin tasowarsu da abubuwan daya faru a shekarun.

Azeema nata murmushin jin dadi tare da kunyar abinda ta aikata.

*********

Hajjo dake zauna cikin bacin rai ta kalli Ramlatu tace  ya kike ganin zanyi in kamo yarinyarcan?

Ramlatu tace  ai Gimbiya ce in ta dage a abu ba mai hanata.

Hajjo a kufule tace  duk ni na barta haka yanzu ga abinda take neman jawomin ai.

Sanar da isowar Jakadiya da akai ne yasa Hajjo cikin mamaki ta kalli kofa.

Jakadiya cikin haki da alama gudu tai ta shigo ta zube a gabanta tace  Hajjo Hajjo.

Hajjo ta kalleta rai a bace tace  meye kuma?

Jakadiya tace  Sarki ya ajiye mulkinsa.

Mene? Ta tambaya cikin rashin fahimta.

"Jakadiya tace  an dako sandar mulki yanzu an shiga da ita fada, bansan meke faruwa ba. "

Hajjo tace  yauwa Abdulsalam gwara kaga Zubair mulkin kafin wacen mara mutuncin ya aikata

"mana tsiya, ashe shi yasa aka kira Zubair dazu? "

Cikin wata dariyar farin ciki ta tambayi Ramlatu.

"Dariya sosai Hajjo take cikin jin dadi tana jin jina kai, Ramlatu sai kara wasa mata kai take."

tab

****

Ayusher

* ZAFIN RANA *

......................

*Hask e  W rit e rs Ass o ci a ti o n*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*K A$ f[ fV *

{47}

Hajjo cikin tsananin murna ta mike ta fito daga sasshenta Ramlatu na bi mata baya cikin tsananin

farin ciki.

"Daga dan nesa kadan taga kamar Zeena da tata tawagar, baki ta tabe tace  naga bakin ki yanzu"

mai zaice.

"Hajjo tai gaba ba tare da ta kara ko kallan Zeena ba, Zeena wacce yanzu taji abinda ke faruwa ta"

"taso dan san ganin Hajjo da halin da take ciki ta tsaya daga inda take, fuskarta dauke da mamaki, dan bata taba tunanin ganin Hajjo haka ba."

"Kallan Fure tai tace  da alama Hajjo lafiyanta kalau, mu koma tun kafin wani abu ya faru muna"

waje.

"Nan Fure ta amsa dato, haka suka juya Zeenatu na tafe da tsananin mamakin abubuwa biyu, na"

"farko murabus din da gaba daya bata taba tunani ba, sannan da ganin Hajjo hankali a kwance."

Hajjo tana tsakiyar masarauta inda tafiya kadan ne zai hadasu da Fada sukaji masu kirari da busa

"sun fara, sam duk yanda masu kirari Ke magana bataji saboda tsabar zumudi."

"Ramlatu wacce yanzu kunnanta sukaji Junaid akema kirarin, yasa a tsorace ta matso kusa da Hajjo."

Hajjo ta tsaya ganin yanda tadan tare gefen tafiyarta kadan.

Hajjo tace  ya akai?

Ramlatu a tsorace tace  Hajjo ina tunanin mu koma daga nan.

"Mu koma ina? Ai dole muje godiya, Ramlatu a tsorace take kallanta sannan tace  tuba nake"

Hajjo amma dakin danji me masu kirarin nan suke cewa.

"Kallan banza ta mata sannan tace  ina nake da lokacin jin wannan shirman, me suke cewa? "

Ramlatu dai tai shiru kafin tace  mu koma mu kira Yarima Zubair din yazo da kansa.

Hajjo tai shiru kafin tace  bai kamata muje godiyar ba?

Ramlatu tace  eh gwara mu jirashi.

Shiru tai kafin tace  to.

"Juyawa tai suka koma, fuskarnan tata wasai da farinciki, kallan hanya tai tace  waccen yar rainin"

hankalin ta juya ne?

"Ramlatu da batama jita ba tana tunanin yanda zata zame ta gudu, Hajjo ta kalleta tace  me kike"

tunani?

Ramlatu tace  inaji tsabar murna ce tasa kaina ciwo ina tunanin komawa bangarena kafin

Yariman ya dawo.

Hajjo tace  shikenan.

"Nan tai wuf ta gudu da hadimanta, Hajjo tana tafe tana farin ciki, daga sama sama taji kamar sun"

"kira Junaid, sai kuma taji Zubair."

Baki ta tabe tace  wato yayan Junaid? Ni da sunbi ta tawa ko sunanansa basa kiraba.

"Tasa kafa zata shiga bangarenta taga Hadimanta ragowar data bari sun hada kai suna magana,"

suna ganinta sukai shiru.

Wucewa ciki tai ta zauna.

Batafi minti goma da zama ba sai ka bawan Zubair wanda yafi kusanci dashi ya nemi izini ya

shigo.

Hajjo cikin zumudi tace  Aram ya akai? Ina Ranka ya dade din?

Kallanta yai yace  Hajjo! ki taimaka ki aika a kira Yarima kafin wani abu ya sameshi.

Me zai sameshi? Ta tambaya cikin mamaki.

"Aram yace  Hajjo gaba daya ba wanda yake bi takan Yarima murna kawai suke taya Junaid ba wands ya damu da halin da yake ciki, gashi ba damar ya taso kar a dauka bakin ciki yake. "

Bakin ciki? Ta tambaya hankali a tashe.

Yace  bakiji Sarki ya ba Junaid mulkin na?

A zabure ta mike tsaye tace  yaba Yarima me?

"Aram yace  yanzu kam ai kowa yasan abinda ke faruwa, tunda gashi anata busa ana kirarin ana"

sanarwa.

Gaba daya hankalinta ne ya tashi tace  inji wa? Inki ubanwa yace ya isa ya ba Junaid mulki ba

Zubair ba?

Hajjo gaba daya ta rikice hankalinta a tashe take magana........

*****

Zeena sai sintiri take a sashenta kafin ta kalli Fure tace  hankalina ya kasa kwanciya Fure

dubomin Binta.

"Nan Fure tai waje, bata dade ba ta dawo tace  tana bangaren Gimbiya Azeema. "

Zeena tace  tashi muje gun Umman.

Nan suka fito.

Ramlatu tana gudu ta nufi bangaren Azeema.

"Gimbiya na zaune suna hira da Binta, dan Binta yanzu ta sata ta fito falan ta, Barira sai dadi"

takeji.

"Suna cikin hira ne aka fara bushe bushe, Azeema ta kalli Barira tace  Bari duba ki gani meke"

faruwa? Wannan busar busace ta Sarki.

"Nan Fure ta fita, bata dade ba ta dawo ta sanar da Azeema ai wai sarki me yai murabus yaba"

Junaid mulki.

Fuskarta dauke da tsananin mamaki tace  AbdulSalam din?

Barira tace  eh.

"Shiru Azeema tai dan tasan tabbas ba abinda zai sa Abdulsalam yabar mulkim nan da yake so, sai"

dai ta tabbatar Junaid ne yasashi dole saboda abinda ya aikata.

Muryar Binta ce ta katseta datace  Haba Bari sai kace wasa ta ya za ai murabus ba wanda ya sani.

"Barira tace  shine abin mamakin, gun a cike yake dam da alama an shirya dama "

"Azeema tai shiru idanunta suka ciciko,babban burinta ada bai wuce Junaid ya samu mulki ba"

amma batasan meyasa yanzu gaba daya zuciyarta a cike take da tsanar kanta.

"Shigowar Ramlatu ce yasa ta hade fuska, Ramlatu ta zauna ta gaisheta."

Azeema ta kalleta bayan ta amsa tace  lafiya?

" Dama nazo wucewa nace bari nazo na gaisheki, na dade banzo na gaidake ba. "

Azeema ta dauke kai ko tanka mata batai ba.

Ramlatu tai dariya tace  Matar Yarima ce?

"Barira tace eh, Binta ce ta gaisheta."

 Ina Gimbiya Zeena? Allah yasa bata wahalar dake kinsam yarinyar nan Hajjo duk ta gama

sangartata.

"Binta cikin mamaki ta kalleta, dan ita ko saninta batai ba kafin tace  ba abinda take min. "

Ramlatu tai dariya tace  ko dayake yanzu farko ne na tabbatar 

 Ya isa haka nan abinda Azeema tace mata kenan.

"Jiki a sanyaye tai shiru, Azeema tace  inkina gama gaisuwar zaki iya tafiya. "

"Ramlatu wacce taji haushin haka ta mike tana dariya tace  ba laifi, bari na wuce. "

Tana kokarin fita ana sanar da isowar Zeena.

Idanu ta zaro kafin ta dan kauda kai.

Azeema ta kalleta sannan tama Barira alamar ta bata izini.

"Nan Zeena ta shigo, tsayawa tai cikin mamaki ta kalli Ramlatu wacce yanzun nan fa taganta da"

"Hajjo, Ramlatu tai saurin kallanta kafin tace  nazo wucewa ne shine na shigo mu gaisa, naga mun dade bamu ko gaisa ba. "

Zeena tai wani murmushin takaici tace  ko? Wucewar ce naganki yanzu da Hajjo?

Ramlatu tai kasa dakai tace  eh zan wuce bangarenane.

"Zeena ta jinjina kai tace  haka akeso ki bar layin da zai sadaki da bangarenki kiyi zagaye, kin"

kyauta da kika zo gaidata.

"Ramlatu tai kasa dakai, nan tai sum sum ta fice."

"Zama Zeena tai ta gaida Azeema, Binta kuma ta gaisheta."

Kallan Azeema tai tace  Umma Karama dan Allah kinsan meke faruwa? Gaba daya na kasa

"samun nutsuwa, na tabbatar akwai wani abu dake faruwa, duk da Ya Junaid yace kar nai bincike"

kar na tambaya amma sam hankalina ya kasa nutsuwa.

Idanun Azeema ne a dan ciciko tace  kibi abinda mijinki yace sannan dake da Binta ku tashi ku

"koma bangarenku, kar wanda ya sake zuwa nan bangaren har sai Junaid yamin hukunci na. "

"Kallanta sukai a tare, Binta tace  hukunci? "

"Murmushi Azeema tai tace  duk mai laifi dole ne a hukuntashi, kada wanda yasa baki akan"

"abinda ke faruwa, ku tashi ku koma bangarenku. "

Jiki a sanyaye suka tashi suka fito.

Binta suna fitowa ta kalli Zeena tace  meke faruwa Gimbiya? Ance murabus yanzu Umma tace

hukunci.

Zeena tai shiru kafin ta kalli Binta idanunta sun dan ciciko tace  kenan Umma da Abbana sunma

Junaid laifi.

Laifi?

Binta Shiru tai tana tunanin kalaman Junaid na rannan.

Zeena ta kalleta tace  wani irin laifi kike tunani?

Binta ta girgiza kai tace  bansani ba.

Shiru sukai a haka suka koma.

*********

Hajiya inna ta fito daga dakinta dakyar cikin farinciki ta zauna a waje tace  yau ko yanzu na muti

Jakadiya hankalina a kwance zan tafi.

"Jakadiya cikin jin dadi tace  Barka Hajiya inna, wannan lamari yayi dadi. "

Junaid! Hajiya Inna ta fada cikin jin dadi......

******

Ayusher

* ZAFIN RANA *

......................

*Hask e  W rit e rs Ass o ci a ti o n*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*K A$ f[ fV *

{48}

"Fure ce ta shigo da sauri, ta kallai Zeena wacce ta zuba mata ido itama."

Fure tace  Gimbiya baki daga cikin gida sunzo tayaki murna.

 Murna? Ai sa bari sai gobe ko?

Dan tsaki tai sannan ta kalli Fure tace  ke kuma meye? Dan yanda taga Fure ta zuba mata ido.

Fure ce ta kalleta cikin mamaki tace  Gimbiya yaushe kuka zama kawaye?

Harara ta maka mata tace  haka kawayen suke? Tashi ki shigo dasu.

"Nan ta fita, matan kanen Abdulsalam ne da kuma yan uwa dake zaune anan."

********

Binta tana fitowa ta kali Hadimarta tace  Rali kira min Harira dan Allah.

Raliya tai dariya tace  Ranki ya dade in kina san abu ki baku umarni kawai.

Binta tai murmushi sannan ta shiga ciki itama hankalinta duk a dagule.

"Harira ce ta shigo ta gaisheta sannan ta zauna, Binta ta sauko kasa kusa da ita tace  Harira kinji"

abinda ke faruwa?

Harira tace  naji sai dai sam na kasa gane meke faruwa.

"Shiru Harira tai tana kallan Binta tace  Karki damu, Yarima yasan me yakeyi duk abinda kikaga"

ya aikata da dalilinsa.

Binta tace  na sani sosai sai dai ina tsoron yana cutar da kansa ne.

Fuskarta dauke da mamaki tace  kamar ya?

Binta tai shiru dan batasan fadar abinda ke tsakaninta da mijinta duk kankantarsa kuwa.

Harira tai murmushi tace  ki kwantar da hankalinki insha Allah ba komai.

Kai ta daga a hankali sannan Harira ta mata sallama ta fita.

Tanajin yanda ake magana da guda daga bangaren Zeena ita kuma bako mutum daya a

"bangarenta, mikewa tai ta shiga ciki tana tunanin hukuncin da Junaid ke dauka."

**********

Sai yamma kowa ya watse Junaid ya tunkari bangaren Sarki.

"Abdulsalam najin Zagi na sanar da isowar Junaid yaji gabansa ya fadi, sam shi ko sunansa"

bayasan yaji an fada.

Junaid ne ya shigo ya zauna sannan ya kalleshi.

Abdulsalam wanda a yan kwanakin nan har ya rame ya canza ne ya kalleshi.

Junaid ya kalleshi sannan ya saki wani irin murmushi yace  kayi kokari sai dai saura abu daya.

"Kallansa Abdulsalam yai zuciyarsa na tafasa, tari ne ya dan kwace mai yana kallan Junaid."

Junaid yace  a randa akai taron nadi a ranar nakeso ka dau matarka Hajjo ka bar

masarautarnan.

Da sauri Abdulsalam yace  muje ina?

Kafada Junaid ya daga yace  wannan kuma banaji ya dameni.

"Gaba daya Abdulsalam ya rasa me zaice, daurewa yai yasan in ya sake bari yanzu ma galaba"

Junaid zaici a kansa yace  Ragowar matana da kuma Azeema fa?

Kallansa Junaid yai yace  baka taba jin kunyar zama da matar yayanka wacce kai ajalinsa ba?

Abdulsalam yace  ni na kasheshi da hanuna?

Kaikai ajalinsa.

Ita kuma Azeemar fa?

Tanada laifi babba dan haka yanda na ma hukunci itama haka zan mata.

Abdulsalam rai a bace yace  na ajiye mulki yanda kakeso amma duk duniya ba mai rabani da

"Azeema, in har zan bar nan gidan to lalai sai dai na tafi da ita. "

"Junaid ya kalleshi, Abdulsalam yace  in komai ya fito ai ba ni kadai zata kwabe wa ba. "

Junaid yai shiru yana nazari akansa kafin ya mai sallama ya fita.

********

"Bangarensa ya nufa? Yana tafe ana mai buda yana kan doki, mutane na biye dashi, har ya isa"

bangarensa.

"A bakin kofar shiga daga ciki mata ne a cike suna jiransa, Yana shigowa suka fara tayashi murna,"

yana amsawa.

Jakadiya tada wanda har da ita a ciki tace  Yarima au Sarki zance barka da sauka Takawa!

Junaid ya daga kai sannan yai ciki.

"Zeena wacce ta gama daukan kwalliyarta, tana jiran su fita taje gun Junaid."

Azi Junaid ya kalla yace  Sabisu na nan ne?

Azi yace  dazu da kana fada ya fita wai dan kokari zai ga gari.

Murmushi Junaid yai suka nufi ciki.

*****

"Zubair wanda yake tafe Arim na rike dashi, da kyar suka karasa bangaren Hajjo saboda yanda"

gaba daya bakin ciki da takaici suka gama galabaitashi.

A kasa daram yaga Hajjo ta baje ta zauna a kasa hankalinta a tsananin tashe.

"Kallanta yai bayan ya shigo ya zauna a gabanta, wasu zafaffan hawaye ne suka zubo mai yace"

 anya Hajjo ni dan Abba ne? Ace yana mahaifina amma gaba daya bai damu dani ba baya sona?

Hajjo wacce tashin hankalinta ya ninka na Zubair ta kalleshi hankalinta a tashe tace  Zubair gaba

"daya yau ina tunanin kafin dare zan karasa lahira, banaji zan iya rayuwa a haka, ta yaya ma hakan"

zai faru?

"Ta fada kanta na wani irin sarawa, tana rike shi."

"Zubair yace  Goggo ki tashi kije gun Abba dan Allah, wlh ni kam bazan taba yadda ba. "

Ranta a bace ta mike ta shiga dakinta ta kwanta.

Zubair cikin takaici ya mike ya nufi bangarensa.

********

"Kallan Harira yai wacce yasa tazo yace  ki sa a hada mana abinci duka a nan, ki sanar dasu suzo"

nan.

Harira tace  To Ranka ya dade.

"Bayan sallar isha i kuwa Zeena da Binta suka nufi bangaren Junaid, yauma Binta ta yi kwalliya"

"sosai, dukansu sai kamshi sukeyi."

Junaid ya sallami kowa a bangarensa dan yanzu saboda komai ya kusa kammala Sabisu ya

koma bangarensu Azi.

"Binta ce ta fara isowa, Junaid na ganinta ya saki wani murmushin jin dadi, tun dazu yake san"

ganin fuskar nan.

"Binta ta kalleshi, hannayensa ya bude alamar tazo, murmushi tai a hankali sannan ta zo ta zauna"

"kusa dashi bata rungumenshin ba, kallanta yai ya dan turo baki kadan tare da kauda kansa gefe."

"Jiyai ta sumbaceshi a kuncinsa, juyowa yai ya kalleta yace  wannan cin hanci ne? "

Murmushi tai ta dan matso saitin kunnensa tace  in na rungumeka uwar gida ta shigo ince me?

Hannu yasa kamar mai nazari sannan yace  itama in tazo sai ta rungumeni.

Wata harara ta galla mai tace  da cewa nai bazata rungume kan ba?

Yace  ba haka kila ce ba?

Haushi ya kamata tace  Allah zan rama.

Ta fada tare da hade rai.

"Sanar da isowar Zeena ne yasa ya kalli kofa, shigowa tai cikin shiga ta isa da matsayi."

"Tayi kyau sosai, gefen damanshi ta zauna sannan ta gaisheshi."

Amsawa yai fuskarsa a sake.

Shiru suka danyi kafin ya kalli

25 / 28