Zafin Rana Book Compelet Novels By Aysha Alto

Author :  Aysha Alto Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   23 / 28

66K to 69K   out of 81.6K words

wanda yaga yana neman yin magana, Shamaki cikin"

"takaici ya kalli Galadima wanda shima ya cika ya batse, Sarki ne ya kalli Turaki bayan yayi murmushi yace  to mudai wannan magana.  "

Kafin ya karasa aka sanar da isowar Junaid.

"Hankalin Abdulsalam a tashe sai dai baiko kalli kofa ba, isowar Matawalle Junaid ne yasa duk"

kowa ya zubawa kofa ido.

Junaid ya shigo sannan ya gaisuwa ya ja ya zauna.

Sarki ne ya kalleshi yace  Matawalle kaima ka fito?

Junaid yai murmushi yace  munzo ban hakuri ne akan abinda kake neman aikatawa.

Kallanshi Sarki yai a ransa yace  me kuma kake shirin yi?

Junaid ya sunkuyar dakai yace  Tuba nake ranka ya dade amma ina ganin hukunci da umarninka

na ajiye mulkin nan yayi tsauri.

"Kallansa sukai da sarki dasu Shamaki, gaba daya shamaki da Galadima sun bude baki, Junaid ya"

dan kara dagowa yace  kace haka kama Marigayi Sarki Zubair alkawari amma ina ganin a sake dubawa.

Gaba daya kasa magana sukai saboda tsananin mamakin wannan dabaibaiyo daya faru.

"Turaki ya kalli Sarki yace  Amincin Allah ya tabbata a gareka, ashe alkawari kukai da sarki? "

Nan ragowar na fada suka fara jinjina ma imani da adalci irin na Sarki.

"Wale ne ya kalli Sarki yace  gaskiya Sarki Allah yasa ka gama da duniya lafiya, ba karamin"

"mamaki mukai ba da jin wannan abun, da ranmu ya baci amma jin dalilinka yasa mun fahimci"

abinda kake nufi.

Allah ya sa haka ne mafi alkairi.

Nan kowa yace Ameen

"Gaba daya kwakwalwar Abdulsalam ta kulle, kallan Junaid ya shiga yi, Junaid yai murmushi"

sannan ya kallesu yace  ku ba Sarki hakuri taya zan hau mulki bayan da karfinsa?

Turaki ne ya kalli Sarki yace  Takawa kaji abinda yace? Sai dai nasan alkawarin sarakuna ba a

ajiye shi.

"Da kyar Sarki ya daidaita nutsuwar sa sannan yace  To ka gani, dole dai ayi abinda ya dace. "

Junaid ne ya sake yin kasa dakai yace  ku ba Takawa hakuri ba jibi na ya bari sai nan da

shekara.

Jibi? A tare suka fadq harshi sarkin dai baisan ya fadi hakan ba.

"Kallansa sukai jin muryarsa, murmushi yai yace  Jibin dai. "

Turaki yace  Allah ya kara ma yawan rai.

Sarki ne ya kallesu yace  kaina nadan ciwo ina san shiga ciki.

Nan suka kara gaisheshi ya fita.

Waziri dasu Shamaki suka fita suma.

Junaid ya tsaya suna ta gagaisawa dasu kafin ya fito.

Yana sa takalminsa ana sanar dashi Sarki na nemansa.

Bai musa ba ya nufi bangarensa kai tsaye.

"Sarki na tsaye ya juya baya gaba daya hankalinsa ya kai kolokuwa gun tashi, idanunsa sunyi jaaa"

alamar tashin hankali.

Junaid ne ya shigo ya zauna zaman cin abinci a kasa sannan ya daura hannayensa a kan cinyarsa

baice komai ba.

Juyowa yai ya kalleshi Junaid na zaune yana kallansa shima.

Cikin tsananin bacin rai Sarki ya kalleshi yace  me kake shirin yi?

Junaid ne ya kalleshi yace  kai me kake shirin yi?

Baki Abdulsalam ya bude yace  ni kake fadawa magana haka kanka tsaye?

Ya kake so nawa makiyina magana?

"Makiyi? Abdulsalam ya maimaita cikin jin haushi, Junaid na fada maka duk abinda ya faru akan"

mahaifiyarka ne ko? Ko duk ba akanka aka aikata ba?

Wani murmushi yai yace  ita kenan itace zata yadda akanta ka aikata amma ni dakai munsan ba

a kanta ka aikata ba.

Hura hanci yai yace  Kasan ka kiyayeni?

Junaid yai murmushi yace  duk abinda zaka aikata min inaso ka tuna abu biyu na farko kowa

"yasan ni zaka ba mulki jibi dan haka duk abinda ya sameni cikin dayan biyu ne ko kai ko Zubair danka ne, to sai dai matsalar na riga na sanarwa yarka duk abinda ya saman kaine, kaga shaidarta"

ta isa komai naka ya wargaje.

"Gaba daya Abdulsalam ya gama shan jinin jikinsa, ya kalli Junaid yace  to ka fito ka sanar da"

duniya laifin nawa mana.

"Junaid yai dan dariya yace  karka damu komai da lokacinsa, sannan ina duba darajar yarka ko"

"nace wacce ka bani ita saboda kana san boye laifinka ne, hakan yasa bazan fada ba, sai dai wannan shine kashaidi na karshe da zan ma, daga gobe ka tattara ka koma inda aka ajiyeni na zauna ko kuma ka nemi wani gidan ka zauna inba haka ba duk abinda ya biyo baya karkaga laifina,"

inada shaidu da zan lalata ma suna cikin mintina kadan wanda fita ma gagararka xatai.

"Mikewa yai zai fita, ita Azeemar fa? Badai kana tunanin ajiyeta anan ba?"

Junaid bai kalleshi ba yace  duk wani mai laifi sai ya amshi laifinsa ko itace kuwa.

Ya juya ya fita abinsa.

Yana fita Abdulsalam ya saki wani kara tare da zama a kan gado cikin tsananin bacin ran da tunda yazo duniya bai taba fuskan tarshi ba.

*****

Zeena ce ta kalli Fure tace  da gaske hakan ake yadawa?

Fure tace  yanzu ma jinai ance wai jibi Sarki zaiyi murabus.

Shiru tai tana nazari meke faruwa Ya Junaid?

Hajjo kam cikin kumburin baki ta sabi alkyabarta ita da Zubair suka nufo bangaren Sarki sai dai an

sanar dasu bazai gansu ba.

Wannan abu ya kara koma mata rai matuka wanda takeji ko zata kwana a wajen nan bazata tafi

ba sai ta ganshi....

****

Ayusher

* ZAFIN RANA *

......................

*Hask e  W rit e rs Ass o ci a ti o n*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*K A$ f[ fV *

{43}

"Binta tana dawowa daga bangarenta taga Fure a bakin kofar sashenta, da sauri fa karasa."

"Fure na ganinta ta azamo itama ta gaisheta. Binta ce ta kalleta tace ""lafiya?"""

"Fure tace ""Gimbiya ke san ganinki."""

Ba ta kawo komai ba ta bi bayanta suka nufi sashen Zeena.

"Tana zaune a kilisarta Binta ta shigo, sai data gaisheta sannan Zeena ta sallami yan falan, kallan"

"Binta tai sannan tace ""Yarima ya fada miki wani abu ne?"""

"Kallan ta Binta tai cikin rashin fahimta tace ""kamar me kenan?"""

"Zeena cikin isa tace ""koma menene abinda dai ya shafeshi a wannan lokacin."""

"Cikin mamaki Binta tace ""banji komai ba sai dai in ke bansan ko kinji wani abin ba."" Ta fada cikin"

dakewa.

"Mamaki ne ya kama Zeena yanda ta maida mata magana, sai dai yanzu ita duk ba wannan bane"

a gabanta.

"Kallanta tai tace ""Yace yana da abubuwan da yake so ya kammala a kwana uku, yau ne karshen kwana na farko, saura kwana biyu kenan, shi yasa nake san ji ko ya fada miki sama da haka."""

"Basuyi wannan maganar da Ya Junaid ba, kenan ita yake fadawa matsalarsa? Daurewa tai ta"

"kalleta tace ""nima abinda yacemin kenan, sai dai ya kara abu daya."""

Zeena ta kalleta tace mene?

"Shiru binta tai tana tuno abinda zata ce can tace ""Yana san muyi hakuri har saikomai ya kammala sai nan zai samu nutsuwar fuskantar matanshi."""

Zeena ta kalleta rai a bace kenan magana take fada mata akan karyai datai ya kwana da ita?

"Binta ce ta kalleta tace ""Gimbiya bada wani abin ma fada ba ina fada miki abinda na sani ne."""

"Zeena ta daure tadan daga girarta kadan kafin tace ""kinsan zancen Sarkin yanzu zaiyi murabus ya"

"ba Junaid mulki?"""

"Mamaki me karara ya bayyana a fuskar Binta, wanda kallo daya xaka mata kasan tana cikin tsananin mamaki, kafin Zeena tace ""kinsan kuma murabus din jibi ne?"""

"Binta tace ""bashida lafiya ne?"""

"Zeena tace ""a'a lafiyar Abba kalau shiyasa na kiraki dan naji, ko kinji wani abin ne."""

"Dana sani Binta tai da yimata wancan zancen, kanta tai kasa dashi tace ""kiyi hakuri Gimbiya"

"bansan manufarki ba."""

"Kai Zeena ta girgiza alamar bakomai tace ""nina fara sannan ba laifi bane in kin rama, haka ake"

"san matar dan sarki bawai kiyi ta bari ana taka ki ba, gaba daya ni na rasa yanda zanyi nasan abinda ke faruwa, shi yasa na ajiye girmana da matsayina na tambayeki."""

"Binta tace ""Kina ganin akwai dalilin sa na yin hakan kenan?"""

Shiru Zeena tai dan gaba daya tunda taji jibi xa'ai abin ko nutsuwa ta kasayo gaba daya.

Ta tabbatar da abinda ke faruwa amma batasan menene ba.

"Kallan Binta tai tace  shikenan jeki kawai, Binta cikin damuwa tai sallama ta fita."

Fitowa tai ta kalli Fure tace  haryanzu baya bangarensa? Tace eh.

Kallan Fure tai tace  ina san zuwa gun Ramlatu.

Fure tace  dare yayi Gimbiya.

Zeena tai shiru cikin tsananin damuwa.

*****

Binta na fita bangaren Junaid taje sai dai Azi yace mata bayanan tun yamma ya fita.

Shiru tai kafin ta kalli duhun da garin yai bari tai sallah in bai dawo ba ta fita.

Bangrenta ta nufa ta wuce daki.

"Ba karamin tsoro taji ba ganin mutum lulube da bargo, wutar dakin a kashe."

"Tsayawa tai kafin ta nufi gun a hankali, Junaid ne kwance a kan gado ya dukunkune da bargo."

Kusa dashi taje da sauri ta zauna a gabansa tace  Ya Junaid?

Idanunsa ya bude a hankali ya kalleta sannan yai dan murmushi yace  Bintalo ta dawo?

"Hankali a tashe tasa hannu akansa, hannunta ya rike yace  lafiya ta kalau. "

Ajiyar zuciya tai murmushi ya sakeyi sannan ya kalli idanunta wadanda suka ciciko tana neman

kuka yace  karki fara lafiyata kalau.

"Kallansa tai ta kasa magana, mikewa yai ya zauna sannan yasa hannu ya jawota kan cinyarsa ya"

rungumeta sannan ya fita da wata iska daga bakinsa.

Cikin raunin murya tace  Ya Junaid lafiya dai ko?

"Lafiya kalau, me Umma tace miki?"

"Dan juyo da kanta kadan tai ta kalleshi tace  hskiri ta bani, ni duk kunya ma ta kamani. "

"Shiru yai baice komai ba, ta kara cewa  Amma yaya Umma fa ba lafiya kuma naga bakaje ba. "

Kara rungumeta yai yace  ke kinjemin ai.

Tace  taya zanje ma bayan nasan tana san ganin danta.

"Bakinta yakaiwa sumba sannan ya kalli idanunta dake lumshe ya sumbacesu, cikin rada yace"

 kinyi sallah ne?

"Idanunta ta bude tana murmushi, tare sukai sallah ya dade yana addu oi dan har ta jingina da"

bango.

"Junaid ya kalleta sannan ya sa hannu ya kwantar da kanta akan cinyarsa, yatsarsa yasa yana"

shafa girarta yace  me kika jiyo a waje?

"Kallansa tai tace banji komai ba amma naji yanzu agun Gimbiya, meke faruwa da zancen"

murabus?

Zeenah?

"Eh yanzu ta kirani take tambayata ko naji wani abu, da alama tana cikin damuwa."

Shiru yadanyi tare da dakatawa da dan shafa girarta da yakeyi cikin wata murya yace  Binta!

"Naam ta fada a hankali, yace  duk abinda Zeena zata miki kiyi hakuri, batada halayen banza"

"rashin tarbiya mai kyau da ganin ta isa ne yasa take abubuwan da take, amma in kika santa a"

hankali zaki fahimci ba haka take ba.

Kallansa tai duk tadanji zafi wanda kishi ne kowa yanadashi amma murmushi tai tace  insha

"Allah, sai dai ina ganin ka fada mata ko hankalinta zai kwanta, tunda harya kirani ta kaskantar da"

kanta alama ne na ta matsu.

Ba musu yace  Shawararki tayi bari naje yanzu.

"Mikewa tai jiki a sanyaye tana ganinsa ya fita, shiru tadanyi tana tunani dan harga Allah batasan"

daga fada zaice zaije yanzu ba.

Bangaren Zeena ya nufa tana zaune sai dai gaba daya ta rasa abinda ke mata dadi balle tanaso

dare ya kara rufawa ta nufi gun Ramlatu.

Jin sanarwar isowar Junaid ne yasa ta mike zunbur.

Junaid ya shigo ta gaisheshi cikin mamaki tace  Ya Junaid.

Zama yai sannan ya kalleta yace  Tunanin me kike?

Kallansa tai sannan ta karaso ta zauna tace  bakomai.

Binta tace kina cikin damuwa.

Binta?

"Ya kalleta tare da daga kai, kallansa tai tace  Ya Junaid akwai abinda ya faru tsakaninka da Abba ne dan Allah? "

"Junaid daya zuba mata ido baice komai ba, ta daure tai murmushi tace  nasan ba lalai ka"

"fadamin ba, amma ni nasan haka kawai Abba bazai taba yadda yai murabus ba. "

"Idanunsa ya dago ya kara kallanta sannan yace  komenene tsakaninmu ne, kar kiyi bincike kar"

kuma kiso sani.

"Yadan yi shiru kafin yace  wannan umarnine miji yake ba matarsa, in lokaci yayi komai zaki sani. "

"Kallansa tai cikin dakiya duk da rauni da zuciyarta tai sai dai ta daga kai, dan tana san Junaid"

matuka.

Junaid ya kalleta a ransa yace wannan taimakon kadai zan iya miki a wannan lokacin.

Kafadarta ya dafa yace  ki taimaka.

Kai ta daga cikin sanyin jiki.

Sai da safe ya fada sannan ya fita.

*******

"Gaba daya Abdulsalam ya kasa sukuni, balle zance yazo mai har magana ta fara fita wasu garuruwa."

"Sam ya rasa abinda ke mai ciwo, Azeema!"

Ita kadaice zata sa Junaid ya bar abinda yakeyi.

Kallan Hadiminsa yai yace  yi maza ka kiramin Azeema.

Yana fita Hajjo wacce ta gaji da tsayuwa tace  ina zaka?

Yace  Takawa ne yace na kira Gimbiya.

Cikin kumburi da bacin rai Hajjo ta dannu cikin turakar Takawa.

Juyowa yai cikin mamaki dan yasan har baici ace tazo ba.

Kallanta yai yace  Hajjo? Me kike anan?

Cikin masifa tace  koma menake ba damuwarka bace me kake nufi da ni? Wlh sai dai a mutu ai

rai amma duk duniya ba wanda ya ksa kwacema Zubair sarautarsa.

Cikin kuluwa yace  naji jeki dan Allah.

Wai me ka daukeni.......

Tsawa ya daka mata yace  jeki nace ko?

Kallansa tai tana hakkin bakin ciki kamar zatai magana ta fita rai a bace.

******

Gimbiya yana jiranki fa.

Kallan Barira tai tace  banace ace bazanzo ba?

Barira cikin mamaki tace  Gimbiya.

Azeema ta kalleta tace  fita ki kuma rufemin kofar dakina.

Nan ya juya ya fita.......

******

Ayusher

* ZAFIN RANA *

......................

*Hask e  W rit e rs Ass o ci a ti o n*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*K A$ f[ fV *

{44}

Bazata zo ba?

"Dan aiken ya zube a kasa yace ""tuba nake Ranka ya dade, hukuncina mai karfi ne."""

"Abdulsalam hankalinshi ne ya kara tashi, har ya yi hanyar kofa zaije gunta sai kuma ya dawo,"

"zama yai tare da hade hannayensa yana tunani, rana a zaune ya kwana dan duk yanda yaso yai bacci kasa wa yai."

"Junaid kam baccinsa yai karfe hudu ya bude idanunsa tare da kallan Binta, shawarar daya yanke"

"jiya kafin yai bacci ya sake tunowa, tabbas wannan shawarar itace ta dace a wannan lokacin."

"A hankali ya zare jikinsa ya gyara mata kwanciya, kallan fuskarta yai cikin jin dadi sannan ya"

sumbaceta ya sakko.

"Bangarensa ya nufa ya kimtsa suka fito massalaci shi da Azi, bayan sunyi sallah ne ya zauna yai"

"karatu sosai har sai da gari yai haske,ya kalli Azi yace  ka dubo gidan Wazirin? "

Cikin rada yace  eh.

"Tare suka fito suka nufi hanyar waje, masu kula da kofa basu kawo komai ba saboda jalabiya ce a"

jikin Junaid sannan ya sa hula dan kar a ganeshi.

"Gidan Waziri suka nufa kai tsaye, Waziri na soro inda ya maidashi karamar fadarsa."

Yana zaune yana jiran kummalo.

"Bafaden sa ne ya shigo ya sanar dashi yayi baki, Waziri cikin mamaki yace  da safen nan? "

Kallan kofar yai bayan ya musu izinin shigowa.

Zumbur ya tashi tsaye cike da al ajabi yace  Yarima!

"Junaid ya zare hularsa sannan ya kalleshi, hankali a tashe ya fara kokarin shimfida katuwar"

"dadduma akan wata daddumar, yama kasa sawa ayi."

Junaid dake tsaye ne yace  nan ma ya isa. Ya nunamai asalin daddumar dake shimfide.

"Duk ya rasa me zaiyi, Junaid ya zauna sannan Waziri ya gaisheshi."

"Kallansa Junaid yai ya mai alama daya sallami bafaden, nan Waziri ya sallameshi."

Azi ya fita ya rufo musu kofa tare da tsayawa a jikin kofar.

Waziri ne ya kalli Junaid yace  Yarima!

Junaid ya dan kalleshi cikin tsananin kasaita da mulki yace  Zuwa nai nama gargadi da kuma Kashaidi.

"Waziri ya kalleshi gabansa na faduwa, murmushi Junaid yai yace  ka saki jikinka bawai neman"

magana nazo ba nazone na nunama hanyar da kuke nema mai bulewa.

"Kallansa Waziri yai a tsorace, Junaid ya kalleshi yace  idan har kunaso na yafe muku laifinku na"

"hada baki gun halakar da mahaifina da kukai, na yafe muku na cigaba da rayuwar da kuke buri"

bayan rasuwarsa to dole kubi abinda zan sanar dakai a wannan lokacin.

Yawo Waziri ya hadiya cikin tsananin fargaba kenan yasan hadda su?

Junaid yace  kayi gaggawar sanar da  yan uwanka su Shamaki dasu Galadima idan har suna san su da  ya yansu su tsira to tabbas sai kunbi abinda nakeso.

Waziri ya daure yace  me zamubi?

Dukanku kar wanda ya sake zuwa gun Sarki Abdulsalam.

Da sauri ya dago ya kalleshi yace  bangane ba Yarima!

"Junaid yace  duk cikinku nasan kafi kowa fahimta shiyasa nazo gunka, maganar daya ce koya"

"aiko kuje kusan karyar da zakumai karkuje, in kuma har naji labari ko naga daya daga cikinku yaje"

kiran Sarki daga yau zuwa gobe to lalai daga ku har zuri arku ku shirya fuskantar babban hukunci.

"Waziri yai shiru yana mamakin wannan yaran wanda sanda ya dawo yaro kamar bashida ilimi,"

daurewa yai yace

23 / 28