Zafin Rana Book Compelet Novels By Aysha Alto

Author :  Aysha Alto Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   19 / 28

54K to 57K   out of 81.6K words

tace  ana jiranka.

Mikewa yai yace  bari na shirya

"Ya fita, da kallo ta bishi sannan ta zauna abakin kujerar daya tashi cikin sanyin jiki."

*********

"Junaid na fita ya wuce ya shirya, sanye yake cikin dakakiyar shadda kalar gajinare hula ya saka"

sannan ya saka takalmi yayi kyau kwarai da gaske. Yana fitowa ya kalli Azi yace  ki kira Binta.

Azi ya kalleshi sai dai ganin yanda ya hade fuska yace  To Rankanya dade.

Nan ya kalli dayan bawan nasa yace  yima Zeenatu magana.

Nan shima ya jiya da sauri.

Junaid ya karasa sa takalminsa sannan ya fito ragowar hadiman na biye dashi.

"Binta dake zaune inda aka barta Azi ya sanar da ita sakon Junaid, cikin jin dadin hakan yasa ta mike da sauri ta shiga daki itama ta zura alkyabarta, kasancewar karta tsaya kwalliya ta bata ran Junaid yasa ta fito."

"Zeena ce tsaye kusa dashi da alama magana sukeyi, kallan Zeena tai taga tasha uban kwalliya."

Dan murmushi ta kakaro sannan ta nufo su.

Agun Zeena da Junaid kuwa kallansa tai tace  bangane Binta muke jira ba?

Wani kallo ya mata yace  batada hakkin zuwa ne?

 Ba haka bane amma ai 

Yace  badai haryanzu a matsayin wacce batada matsayi a gidan nan kike kallanta ba?

"Ranta ne ya baci ta kalleshi, yace  karki manta kishiyarki ce matar Junaid, a ynzu in aka"

"wulakanta matata kamar ni aka wulakanta, kuma ke ma kamar ke aka wulakanta. "

Shiru tai saboda tama rasa me zatace ta ina dan an wulakanta Binta aka wulakantata?

Isowar Binta ne yasa t mata wani banzan kallo.

Junaid wanda haryanzu fuskarsa a hade take yace  muje.

Haka suka taho suka nufi bangaren Azeema.

"Kallan Zeena yai bayan sun dan yi tafiya mai dan tsayi jefi jefi suna daga hannu in an gaishesu,"

yace  ni Shamaki yaushe ya samu mukaminsa?

"Kara matsowa tai kusa dashi hakan yasa Binta tadan ware kadan da su, tace  sanda Abba ya"

hau mulki. Shamakin da fa?

"Tace yayansa ne saukeshi akai, Junaid yace  Galadima fa? "

Tace tunda shine haryanzu kum 

"Baya tai tana neman faduwa, da sauri yasa hannu yariko hannunta."

"Binta ta kalla wacce gaba daya takeji kamar an wareta, wacce ganin Zeena da Junaid a haka ya kara sa taji gaba daya komai ya tsaya mata."

"Wani murmushin wulakanci ta watsama Binta, sannan ta dago."

Junaid yace  Kina Gimbiya bakya ganin hanya. Ya fada yana saketa.

"Gyara tsayuwarta tai tana  yar dariya kadan, tace  tafiyarce bakaga yau wahala takemin ba? "

Cikin rashin fahimtar me take nufi ya maida kanshi kan Binta wacce ita ta fahimci me take san

cewa.

Junaid ne ya matsa kusa da ita yace  Binta!

Kallansa tai sannan tai murmushin yake tace  Naam.

"Muje, naga ne kin tsaya, kai ta daga alamar to."

Haka suka isa bangaren Gimbiya Azeema wacce take ta jiransu. Da hanzari Barira ta karaso tace  sun iso Gimbiya.

Nan ta kara gyara zamanta tasa aka musu iso.

Junaid ne ya fara shiga sai Zeena sannan Binta.

Gaisheta suka fara yi ta amsa.

"Kallan Zeena tai wacce take ta wani iyayi wai ta kasa zama daidai, sannan ta kalli Binta wacce tai"

"shiru, ta kalli Junaid wanda kamar kullum yanzu fuskarsa daf take."

Nan ta kalli abincin da aka jera sosai a gun tace  kuci abinci zan shiga ciki.

"Nan ta mike tai ciki, Zeena ta kalli Fure tace  Fure zubamin. "

"Fure ta taho da sauri, Junaid ya kalleta yace  ku bamu guri. "

"Nan kowa ya fita, cikin mamaki Zeena ta kalleshi, kallanta yai yace  ki zuba da kanki. "

In zuba?

Ta fada tana nuna kanta.

Dauke kai yai daga kanta yace  Binta bismillah.

Yanzu kam bazata kara bari a maidata  yar kallo ba.

"Da sauri ta jawo plate ta zuba mai abinci, sannan ta zuba nata."

"Spoon ya mika mata shima ya dauka, dariya yai yace  naki wayan shine aka cikamin? Itama dariya tai tace  ya kamata kai kaci dayawa dan Allah nasan yunwa kake ji. "

" Ahhhh na manta ashe kina gane in cikina ya rarake, lalai zanyi dabara yanda bazaki dinga"

ganewa ba

Dan Kallan Zeena tai ta gefen ido wacce ta cika ta batse ko abincin ma ta kasa sawa.

Kallan Junaid kawai take dama yana dariya haka?

Binta ce ta kalleta tace  Gimbiya na zuba miki?

"Zeena tai shiru tana nazari kafin tace  basai kin zubamin ba, tunda ya Junaid yace nashi yamai"

yawa bari muci tare.

"Cikin mamaki Junaid ya kalleta, Binta ta zuba mata ido itama."

Junaid ya kalli Binta sannan ya nuna mata plate da idanunsa alamar t zuba nata ya dauke kai.

Cikin kufula ta jawo plate ta zuba.

Safiya wacce sanda sukazo tana hada kayanta taga Azeema ta shigo.

"Kallanta tai tace  Umma ya kika shigo kika barsu, bayan kinsan mata biyu lokaci daya akwai"

hidima?

Azeema ta zauna tare da cewa  hakan ne yasa na taso.

"Safiya tace  ni Binta nakeji, itada bata magana sosai, Zeena nasan haka zataita kunsa mata"

haushi.

"Azeena ta gyara zamanta tace  intaga ana neman kwace mata miji ta kwaci kanta, zama ka"

"fadawa mutum karya bari amai kaza da kaza bata lokaci ne, in taga mijinta na neman yin nisa da"

ita ta mike.

Safiya tai dariya tace  Umma kenan komai naki sai kin hasaso kike aikata shi.

A falo kuwa haka kowa yai shiru kowa da abinda yake sakawa a ransa.

"Zeena na jin haushin abinda Junaid ke mata, Binta na kishin yanda Zeena da Junaid ke maida ita"

"yar kallo, Junaid kam tunanin Shamaki da Galadima yakeyi, kallan Zeena yai sannan yace  Waziri fa? "

Fuska ta hade tace  shima tun lokacin Marigayi.

Junaid yai shiru yana tunani.

"Binta ce ta zuba ruwa ta ajiye kusa dashi, kallanta yai sannan ya sakar mata murmushi yace"

 Nagode!

Itama murmushin ta maidamai tare da nunamai wata kwanon agun.

Kallan robar yai sannan yace  a a

Tace  kai Ya Junaid!

Yace  Allah karkici kin manta abinda ya saki?

Da sauri tace  na hakura ba sai ka fadaba.

"Zeena ta kalli kwanon dake cike da gwaza, sannan ta haraeta tare da tabe baki."

***********

Sarki ne ya kalli Shamaki yace  ka gano inda Sabisun yake?

"Shamaki ya girgiza kai yace  haryanzu ranka ya dade, amma wai me yasa kake nemanshi"

yanzu?

"Sarki yace  haka kawai nakejin hankalina ya kasa kwanciya, ni gaba daya yaran can gani nake"

kamar kallan mu yake yana nazari akan mu.

Dariya Shamaki yai yace  karka damu Ranka ya dade na tabbatar yanzu da yke danka kuma

sirikinka bazai kawo wannan a ransa bama.

Sarki ya jinjina kai alamar gamsuwa yace  haka nake fata.

******

Ayusher

* ZAFIN RANA *

......................

*Hask e  W rit e rs Ass o ci a ti o n*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*K A$ f[ fV *

{36}

"A bangaren Azeema ya barsu, fitowa yai ya nufi bangaren Hajiya Inna."

Daga baranda ya tsaya yana amsa gaisuwar Jakadiya.

Junaid ya kalli Jakadiyar yace  Jakadiya ina san magana dake.

A tsorace ta kalleshi tace  To Yarima.

Fitowa tai tabi bayansa har bayan ginin Hajiya Inna.

"Su biyu ne agun, ya kalleta yace  Jakadiya shekararki nawa kina aiki anan gidan? "

Dan murmushi tai tace  tun ina Yarinya nake anan.

Junaid ya kalleta yace  meyasa Hajiya Inna batasan Umma?

"Da sauri Jakadiya ta kalleshi, Junaid cikin yanayin maganarsa ta kasaita ya kalleta yace"

" tambayarki nake, dalilin zuwa na da kaina dan karma kiyi tunanin boyemin wani abu ne, zan iya shiga na tambayi Hajiya Innan da kaina. "

"Hankalin Jakadiya ne ya tashi, ta zube a kasa tace  Yarima! "

Junaid yace  menene dalili? Na tabbatar ba akan ta sake aure bane.

Shiru tai sai da Junaid yai gyaran murya alamar bacin rai.

Da sauri tace  Yarima ka gafarceni amma Hajiya In

"tace tun Marigayi nada rai Gimbiya da Sarki suna san juna, tace san mulki ne yasa Gimbiya taki"

auran Sarkin yanzu ta zabi Sarki Zubair.

Junaid ya kalleta yace  dan tana sanshi ta auri yayansa menene na tsanar?

"Jakadiya gabanta ya sake faduwa, hankali a tashe ta kalli Junaid tace  wannan Hajiya Inna ce"

kawai tasan dalilinta.

Ido Junaid ya zuba mata sannan a hankali yabar gun ba tare da yace komai ba.

"Gaba daya kansa ne ya kulle, dan har bibiyu yake gani."

"Dakewa yai harya isa bangarensa, a daki ya zauna yana tunani, in tana sansa kenan Hajiya Inna"

tana zarginsu da kebencewa bayan anyi aure ko me? In haka take zargi kenan shima haihuwarsa

"akwai ayar tambaya? Wani murmushin takaici yai yace  ta yaya? Ai da ba wanda zai kawo maganar aure na da Zeena a cikinsu, to menene? "

Sai can bayan Magrib Azi ya shigo yace  Yarima lokacin zuwa bangaren Binta yayi.

"Junaid ya kalleshi sannan ya mike jiki a sanyaye, Azi cikin mamaki ya kalleshi, ya dauka zumudi"

"zai hana Junaid mantawa, meke faruwa?"

*******

"Zagaye take tayi a cikin dakinta, gaba daya hankalinta nakan bangaren Binta dan ta tabbatar"

"Junaid nacan tunda kwananta ne, zama tai a bakin gado ta harari kujerar daya kwanta daren jiya, mikewa tai zumbur ta sa mayafi ta fito falo."

Fure da sauri ta taso tace  Gimbiya lafiya?

Zeena ta kalleta tace  Bangaren Maman Rabi zani.

"Ramlatu? Abinda ya fado ran Fure kenan, tace  Gimbiya me zakiyi acan? "

Wani banzan kallo ta mata tace  mu biyu zamu koma banasan kowa yasan inda muke.

Da sauri Fure tace to.

Fitowa tai ta aiki kuyangin dake waje suka wuf suka fice.

Ramlatu na zaune suna hira Fure ta shigo.

"Zubewa tai ta gaisheta sannan ta mata alama data sallami mutanen dake gun, nan Ramlatu ta sallamesh."

Kallan Fure tai tace  lafiya?

"Gani tai an bude labile kallan mai shigowa tai, mamaki ne ya kamata ganin Zeena."

Da sauri ta mike tsaye tace  Gimbiya?

"Zeena ta karaso ta zauna sannan ta kalleta, sallamar Fure tai sannan ta maida hankalinta kan"

Ramlatu tace  Ramlatu kun samo inda Sabisu yake?

Mamaki karara ne ya bayyana a fuskar Ramlatu tace  Sabisu?

Zeena ta hade fuska tace  kunsamo inda yake?

"Cikin mamaki tace  ai bangane bane, me zaki mai? "

Zeena tace  Zaki fadamin ko sai na fita na nufi bangaren Umma karama na fada mata kin amso

magani?

Hankalin Ramlatu ne ya tashi a tsorace ta kalle Zeena tace  bamu sameshi ba amma munji

labarin yana wani kauye wai Bukul.

Bukul?

Zeena ta tambaya.

Ramlatu tace  eh amma da alama Hajjo ta hakura dan bata sake sawa a nemeshi ba.

Zeena ta kalleta tace  kar wani mai numfashi yasan nazo gunki balle yasan maganar da mukai.

Ta mike ta fito.

Suna isa bangarenta ta kalli Fure tace  da gari yadanyi haske kadan kije bangaren Binta kice

Yarima ina bangarensa ina jiransa.

Kallan mamaki Fure ta mata sai dai batace komai ba sai to.

"A can bangaren Junaid kuwa, bayan sunyi sallah tare ne akan sallaya ta kalleshi cikin kulawa"

ganin yanda yai shiru yana dan nazari.

"Hannu tasa a hankali ta kamo hannunsa, kallanta yai sannan yai murmushi."

 Meke damunka Ya Junaid?

Wani sansanyan murmushi ya sakar mata yace  zuciyata ke sanar dani wani abin wanda kuma

bansan kwakwalwata ta amince dashi.

"Hannunsa tadan murza kadan tace  in har bakasan amincewa dashi ko tsoron tabbatar da abinda kake zargi, ka hakura dashi mana. "

Kai ya girgiza mata alamar a a yace  abu ne da dole sai nayi.

Kai ta daga alamar ta fahimta.

Kallanta yai yace  shiyasa nake neman alfarma.

Alfarma?

"Ta tambayeshi, yace  zaki iya jirana? "

"Kallan mamaki tamai na rashin fahimta, yace  zuciyata gaba daya bata nan gun, sannan ina"

"tsoron abinda zan binciko wanda kila ya shafi tsatsona da rayuwata, zaki jira na gama abinda nake?"

Banasan na shiga hakkin daya daga cikinkin ku.

Gaba daya jikinta ne yai sanyi duk da batasan me yake nufi ba amma tasan tabbas abinda yake

tsoro yanada waya a ransa wanda har yasa yake tunani haka.

"Kai ta daga alamar to hannu yasa ya jawota jikinsa ya rungume, tsoron abinda zuciyarsa take rayamai yakeyi."

"Kwanciya ya fara yi ya jawota jikinsa ya rungume tsam, in har mahaifiyarsa nada wani tabo"

baisan ya zaiyi rayuwarsa ba.

Yanda ya matse binta ne yasa a hankali tace  Yaya!

Kallanta yai sannan ya sassauta rikon yace Yahkuri Binta.

"Murmushi tai ta dago kanta ta kalleshi, ganin yanayinsa ne yasa ta kwanta a kafadarsa cikin"

tausayamai.

A hankali bacci ya dauketa.

Junaid kam kasa bacci yai sai can wajen dayan dare ya samu bacci ya daukeshi.

Yana sallar asuba ya kalli Azi bayan sun fito daga masallaci zai mai magana kenan Hadimin sarki

wanda ke jikinsa ya iso gun da suke.

Junaid ya kalla bayan ya gaisheshi yace  Yarima Mai Martaba yace da rana ka shigo fada.

Junais yace to.

"Yana tafiya ya kalli Azi yace  Azi inaso ka tafi neman Sabisu, karka bari kowa ya san abinda kakeyi. "

Da sauri Azi yace  to Yarima. Daga nan ya fita.

Junaid ya shiga bangaren Binta tana zaune kan sallaya tana wa Junaid addu a da fatan dacewa.

Zama yai a bayanta a hankali yasa kansa akan bayanta.

Murmushi tai bayan ta kammala addu arta a tare suka shafa sannan ta gaisheshi.

Kallanta yai yace  Binta kin tashi lfy? Cikin jin dadi tace  lafiya kalau Ya Junaid.

Murmushi yai yace  Da alama Bintata ta fara dawuwa.

Dariya tai tace  Da ina naje?

Yace  kin bari masarauta ta cinye rabinki.

Dariya ta sakeyi shima yana dariya yace  ba haka bane?

Zatai magana sukaji ana magana.

Cikin mamaki ya kalleta ganin yanzu gari ya waye.

Binta ta fito ta bude kofa.

Fure ta gani cikin mamaki tace  lafiya?

Fure tace  Gimbiya ce tace acema Yarima tanada magana tana bangarensa.

"Tsayawa Binta tai cikin tsananin mamaki, Fure ta juya."

"Binta jiki a sanyaye ta nufi ciki, kallan Junaid tai wanda yace  waye? Wai ya akai bakida hadimai"

ne sai wata guda daya da na gani jiya?

Binta ta kalleshi tace  Gimbiya ce ke jiranka a bangarenka.

"Cikin mamaki ya kalleta, Gimbiya?"

Tace eh.

Yanda tai maganar kana gani kasan taji haushi.

"Shiru yai yana tunani, ta samo wani abin ne? Kamar bazai tashi ba har Binta taji dadi sai taga"

zumbur ya mike.

Kallansa tai da sauri tace  ina zaka yaya?

Yace  bari naje zan dawo.

Mamaki ne ya kamata dako magana bai sake mata ba ya fita.

"Kasa motsi tai a inda take, shiru tai tana tunani, yace bazai kwanta da ita ba bayan jiya ya kwana"

"da Zeena, yanzu kuma ya tafi ya barta? Anya Ya Junaid dinta ne?"

Junaid ne ya nufi bangarensa.

Zeena na zaune a falo ya shiga.

Zama yai daga kujerar dake kallan tata yace  ya akai?

Kallansa tai sannan ta dan lumshe ido tace  magana nakeso muyi.

Kallanta yake baice komai ba.

Tace  na samo inda Sabisu yake.

Kallanta yai da sauri sai kuma yace  taya zaki san inda yake a yini daya?

Tace  Shikenan tunda baka yarda ba.

Ta mike zata fita.

Hannu yasa da sauri ya riko hannunta.

Cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba yace  Yana ina?

A hankali ta juyo ta kalleshi tace  Yana Bukul.

"Mikewa yai da sauri, yace  inane Bukul? "

"Tace  bansani ba nima haka kawai akacemin, sai dai yanda nasamoma inda yake nima sai ka amince da abinda nake so. "

"Kallanta yai baice komai ba, tacigaba  Kamin alkawarin bani dama nima. "

Dama?

Ta cigaba  Zuciyara zata hakura da rashin san da kakemin kafin aure amma bazata iya daukar kiyayyarka ba bayan aure.

Kallanga yai baice komai ba.

Shiru suka danyi.

"Cikin jin haushin aikar Azi dayai, ya shiga tunanin abinyi."

Kusa da shi ta kara matsowa tace  Meyasa kake nemanshi wai? Kai Da Hajjo bansan me kuke

nema dashi ba.

Junaid ya kalleta yace  Inaji dole na fita da kaina.

*******

Ayusher

* ZAFIN RANA *

......................

*Hask e  W rit e rs Ass o ci a ti o n*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*K A$ f[ fV *

{37}

"Kallansa tai hankali a tashe tace ""ina zaka?"" Ta fada tare da riko hannunsa."

Kallanta yai ya kura mata ido yana nazari.

"Gani tai ya saki wani dan siririn murmushi wanda ya bata tsoro, tace ""ya akai?"""

"""Ba sai naje da kaina ba, tunda bansan ya yake ba balle inda zan sameshi takamaimai."" Gaba"

"daya batasan me yake nufi ba shi yasa ta kasa cewa komai, hannunsa ya zare cikin nata sannan ya fita."

Kasa tsaidashi tai saboda tana tunanin abinda yake nufi a kanta.

"Junaid na fita hadimansa suka biyo bayanshi, bangaren Azeema ya nufa."

Tana daga kwance ana dan matsa mata kafarta.

"Barirace ta shigo ta sanar da ita isowar Yarima, kallan Barira tai tace ""Junaid?"""

"""Eh Gimbiya."""

"Mikewa zaune tai ta sallamesu, Junaid ne ya shigo ya zauna a kasa."

Sai daya gaisheta ta amsa tare da tambayan kwanan matansa.

Suna lafiya ya fada yana kallanta.

"Kallansa tai tace ""da wani abin ne?"""

"Junaid yace ""matsalarku da Hajiya Inna, bakya tunanin ya kamata ki bata hakuri? Halin rayuwa"

"shi ake

19 / 28