Zafin Rana Book Compelet Novels By Aysha Alto

Author :  Aysha Alto Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 28

15K to 18K   out of 81.6K words

Azeema tace  duk garin nan ba"

"wanda ya isa ya marar min da, duk matsayinsa kuwa. "

"Ta juya, Zeenatu ta zube kasa kawai tasa kuka, dan taji marin nan har kanta."

Tare suka tafi har inda aka kulle Junaid gaban Hajjo sai faduwa yake tana fatan Allah yasa yanada

rai.

"Bawan da ya rakosu ne ya bude kofar, ido Hajjo tadan runtse dan jikinta y gama bata ya margaya"

lahira.

"Ana budeshi Azeema ta hango danta a yashe akan yayi, hankalinta a tashe ta shiga ciki da sauri"

"tasa hannu ta dagoshi, jin yana numfashi ne yasa ta saki wani ajiyar zuciya hawaye ya biyo baya."

"Kallan Hajjo tai wacce tai tsuru. Azeema ta shiga jijigashi tana hawaye a hankali yadan bude ido,"

baya gani sosai sai yaga kamar Binta ce kusa dashi dan sam bai kawo Azeema mahaifiyar sa ba.

A hankali yace  bin.....bin. 

"Idanunsa ne suka rufe wanda ya kasa ko bude ido, Azeema ta kalli bakinsa duk ya tsage alamar"

yunwa da kishin ruwa.

Wanda ya bude kofa ne yazo ya daukeshi suka fito.

Azeema ba abinda tace sai hawaye da takeyi.

Bangarenta suka nufa Hajjo zata shiga Azeema tace  mun gode da rakiya.

Tana fada ta kalli Bari wace ta rufe kofa.

"Hajjo tabi kofar da kallo tashin hankali, yanzu a wani hali zata tsinci kanta? Ita? Zeenatu? Da"

Zubair dan tasan yanzu ko za a mutu Azeema itama cewa zatai Junaid ne zai gaji mulkin nan.

"Suna shiga Binta na tsaye a waje tana shan ruwa saboda gaba daya jikinta ba karfi, tana ganin an"

"shigo da Junaid ta yadda kofin, da sauri ta isa gun tace  Junaid. "

Ciki ya shiga dashi ya kwantar dashi dakin Azeema.

"Binta hawaye kawai take ganin yanda duk ya canza, ta kara cewa  Junaid. "

Azeema ce ta kalleta tace  Yarima Junaid.

"Binta ta daga kai alamar to, Bari ta kalla tace  yi maza ki kira wanzami. "

"Nan bari ta fita da sauri, Azeema ta fito falo dan bada umarnin abincin da za amai da kayan"

sawa.

"Binta suna fita ta tsuguna gefen gadon tana kuka, dagowa tai tana kallan yanda duk ya canza,"

"hawayen da takeyi ne ya diga a kan fuskar sa, a hankali ya dan bude idansa sama sama."

Kallansa tai tace  Junaid!

Binta? Ya fada tare da kokarin murmusawa sai dai a hankali idanunsa suka koma suka rufe.....

"Tausayinsa ne ya kara kamata hankalinta ya kara tashi, hawaye kawai take."

*Ayusher*

*ZAFIN RANA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

Shafi na Goma Sha Biyu

"Azeema ce ta turo kofa, dauke da kofi a hannunta, kallan Binta tai tace ""bamu guri."""

"Mikewa Binta tai zat fita, a hankali yace ""Binta!"""

"Juyowa tai ta kalleshi, murmushi ta sakar mai hawaye suka gangaro tace ""Yarima kagane ni?"""

"Kai ya daga sannan yace ""Yarima?"" Dan yaune rana ta farko data kirashi da haka."

"Azeema ce ta kalleta wanda ya sa juyawa zata fita, mikewa ya shiga kokarin yi yana cewa ""Binta"

"ina za. """

"Kallan mahaifiyarsa a gabansa ne yasa ya kalli dakin da yake ciki, sake kallanta yai cikin mamaki,"

"kofin hannunta ta mika mai wanda madara ce a ciki ta shanu, mikamai tai saboda yanda yakejin jikinsa ne ya amsa ya kafa kai bai sauke kansa ba sai da ya shanye ta duka."

Ajiye kofin yai sannan ya kalleta yace  meke faruwa?

Kallansa tai cikin tausayawa ta zauna a gefen sa tace  Junaid!

"Shiru yai yana kallanta yana san jin abinda ke faruwa, hawaye ne suka zubo mata ta gogesu tace"

 kasan kullum dakai nake kwana nake tashi? Amma Junaid kana ganina kaki sanar dani kai wanene?

"Abinda ke bakinsa ya hadiya, kallanta yai kamar zaiyi magana ya fasa, mikewa ya shiga kokarin yi"

yana cewa  ni zan wuce ni da Binta.

Hankali a tashi ta mike tace  Junaid zaka koma ina?

Kallanta yai yace  yanda kike rayuwarki hankalinki a kwance nima a can hankalina a kwance

"yake, tunda kin gani na ganki zan koma. "

Da sauri tace  kana tunanin zan barka ka koma wani gun? Junaid? Baka tausayin mahaifiyar

data rasa danta tun baigama wayau ba? Shekarata nawa rabona dakai? Ka rasa abinda zakacemin

sai zaka tafi?

"Juyowa yai ya kalleta, zuciyarsa ce ta karaya, shi kanshi yana kewar mahaifiyarsa amma gani yake"

kamar mantawa sukai dashi.

"Karasowa tai inda yake tace  ka koma ka huta na sa akira wanzami ya dubaka, Junaid bansan"

"meke yawo a ranka ba anma ni mahaifiyarka ce, babu uwar dazata ajiye danta a wani gun tai"

rayuwar datakeso.

"Shiru yai baice komai ba, ganin haka yasa tace  kana san wani abu ne? "

Kai ya girgiza alamar a a yace  Binta tana ina?

Kallansa tai tace  Junaid 

Sai kuma tai shiru tace  ka huta inka tashi sai a kirata.

Kai ya jinjina sannan yace  ina bandaki?

Nuna mai tai da sauri sannan tace  nasa a kawo ma kaya.

"Kaya? Ya tambaya cikin mamaki, tace  eh na tura gun masu dinkin mu na masarauta, nasan"

baza a rasa wanda suka ma Zubair ba.

"Baice komai ba dan baisan ma me zaice ba, juyawa tai ta fita, zama yai a bakin gado yai shiru"

"yana tunanin wannan lamari, wai meya faru ne daga sanda aka kulleshi?"

"Azeema ce ta turo kofa dauke da kaya, mika mai tana cewa  me kake tunani? "

"Shiru yai yana kallanta, murmushi ta saki tace  inada abubuwa dayawa danake san tambayarka"

sai dai ganin yanayin da kake ciki yasa nake jurewa.

"Yanzu kam shima murmushin yai, tace  Junaid! "

"Kallanta yai tace  Nagode daka jure abinda ya faru,nagode wa Allah daya barmin kai da rai. "

"Tausayinta ne ya kamashi, juyawa tai da sauri tabar dakin."

"Junaid ya dafa kansa, lalai bai kyauta ba da yake jin zafin mahaifiyarsa bayan abar tausayi ce."

"Mikewa yai jikinshi duk ba karfi, wanka yai tare da alwala sannan ya fito, kayan ya saka sannan"

ya tada sallah.

"Bari ce ta kwankwasa jin shiru yasa ta koma, kara dawowa tai ta kwankwasa Junaid ya bata izinin"

shigowa.

"Abinci ta shiga jerawa a kan karamin carpet din dake dakin, haka tai ta shigowa dashi tana"

"jerawa, data ajiye na karshen ne ta zube a kasa tace  yarina barka da dawowa. "

Kallanta yai yace  ina Binta?

"Tana dakinmu, taci abinci ne?"

"Cikin mamaki ta kalleshi, tace an kai mata."

Ki duba nasan bata fara ci ba kice mata ta dawo nan.

"Cikin tsananin mamaki ta kalleshi, shima kallanta yai yace  da wani abin ne? "

Da sauri tace  a a

Mikewa tai ta fito kilisar Gimbiya Azeema wacce ke bada sako akan a sanar wa Safiyah halin da

ake ciki.

Gaba daya Azeema ta kasa zama sai ake take gun yan uwanta na kusa dana nesa.

Bari ce ta matso kusa da ita ta sanar da ita abinda Yarima yace  shiru tai cikin rashin jin dadin

zancen tace  kice taje

Da sauri Barira ta kalleta tace  Gimbiya.

"Azeema ta juyo ta kalleta tace  ki bar Junaid yai duk abinda yake so, ni zan san abin yi. "

Barira ta jinjina kai sannan tai dakinsu.

"Kamar kuwa ya sani tana zaune sai jujuya abincin take taki ci, Barira ta sanar da ita sakon Yarima"

da sauri ta mike ta dau kwanan tai dakin.

"Barira ta bita da kallo, cikin takaici."

**********

"Hajjo kam sai matse hannayenta takeyi daga zaune, tabbas gaggarumin matsala na neman"

afkowa a tare da ita.

Zeenatu wacce ke zaune itama tayi shiru tana tunanin abinda ke faruwa.

Zubair ne ya daure yace  wai da gaske yaran nan ne Junaid?

"Hajjo tace  da gaske wlh, yanzu ya zamuyi? Dan wlh akwai gagarumin matsala. "

"Zeenatu ta kalla wacce tai shiru kafin wani murmushi ya bayyana a fuskarta, Hajjo cikin mamaki"

tace  ke kuma fa?

Zeenatu ta kalli Hajjo da sauri tace  ya akai bamu gane ba Hajjo? Yaran nan wlh sam baiyi kama

"da bawa ba, ko daga yanayin maganarsa zakasan jininmu ne, ya akai idanunmu ya rufe? "

Ran Hajjo ya baci tace  to ke yanzu ana zancen abinda zai biyo nan gaba wato ke abinda ya faru

a baya kike maimaitawa?

Zeenatu ta sake murmusawa tace  abin ne abin birg 

Uban hararar da Hajjo ta maka mata ne yasa ta kalli Zubair tace  yaya wai meye na damuwa?

Milkin nan fa kowa yasan naka ne meye na wani tada hankali?

Zubair ya kalleta yace  kinba Sulaiman din hakuri?

Tace  kai yaya ana cikin wannan yanayi wake zancen wani Sulaiman?

Hajjo tai dan tsaki tace  aiki Fure ta kiramin Ramlatu.

"Nan Zeenatu ta mike, Hajjo ta kalli Zubair tace  Zubairu karka kuskura adan tsakankanin nan kai"

"laifi, kabi kowa a sannu, kai luf kamar baka nan kafin na samo mafita, dan wallahi barin yaran nan"

daidai yake da ajiye matsayinka.

Zubair ya kalleta yace  Hajjo kisan yanda za ai.

"Tace  karka damu, in ta gama rama abinda aka ma danta sai musan abinda zamuyi. "

Yace  kina nufin sai ta rama?

"Hajjo tai wata dariya tace  bakasan Azeema bane, ita a tarihinta bata barin ta kwana ko a mutu"

ko ai rai amma sai ta fanshe.

Zubair yai shiru yana tunani.

*****

"Suna cin abinci yana tambayeta abubuwan da suka faru tana fadamai, ko mai ya bude sai ya turo"

gabanta yace  binta ga kaza kin taba ci kuwa?

"Dariya tai tace  Ya Junaid nifa bamu shirya bama wlh, ka taho ka barni. "

"Ahhhh ya rike ciki wai ciwo,"

Hankalinta a tashe ta kalleshi tace  Ya Junaid?

Ganin yanda ta rikice yasa ya saki dariya yana cewa  yanzu mun shirya?

Hade rai tai tace  Ya Junaid.

Tai maganar cikin shagwaba.

Azeema dake jikin kofa rike da kofar ta kalli Wanzamin dake gefe kansa a kasa tace  ko zaka bari

sai anjima?

"Yace to ya juya tare da mata sallama, shiru tai tana tunanin wannan yarinyar, itafa danta bazai"

"zauna yana biyewa yarinyar nan cikin masarautar nan ba, wanda tasan yanzu idan kowa kansa zai"

koma.

*Ayusher*

"Dan Allah ku daina min sharing din littafi, ina iya bakin kokarina na ganin an zauna lafiya da kowa,"

dan Allah wannan littafin na kudi ne ku daina yadamin shi.

Nagode

*ZAFIN RANA*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*NA Ayusher Muhd*

Shafi na Goma sha Uku.

"Haka sukai ta hirar su kamar ba wata matsala a gabansu, wanda hakan ba karamin batama"

"Azeema rai ba, zama tai a kilisarta tai shiru tare da zubawa kofar ido."

Barira ta sunkuyo tace  Gimbiya haka zamu barsu?

Kallanta tai tace  kinsa a gyara bangaren Yarima?

"Tace  eh na tabbatar ma sun gama, badai tare zaki bar  "

Wani banzan kallo data mata ne yasa ta yin gum da bakinta.

Azeema ta mike ta shiga dakin.

"Suna dariya suna ganin ta sukai shiru, Junaid ya kalleta, Binta kam saurin mekewa tai tsaye ta ja"

baya.

"Azeema ta kalleta tace  Gashi ganinki yasa Junaid ya ware, angode. "

Binta tai kasa dakai tana kallansa.

Murmushi ya sakar mata.

Azeema ta zauna a bakin gado tace  Junaid!

"Yanda ta kira sunan nashi ne ya sa shi kallanta bayan ya amsa, tace  an gyara maka ban garenka,"

"zamuje yanzu ma kaika, dan gobe za ai taron murnar dawowarka."

Ta danyi ajiyar zuciya sannan ga cigaba  Sai dai inaso kai da Binta ku rage nuna mu amalar ku

cikin jama a.

"Kallan Binta tai sannan ta kalli Junaid, Binta!"

"Junaid ya kirata, nan bamu guri ya fada yana kallan Azeema."

Binta ta mike tai waje.

"Azeema ta kalleshi tace  Junaid kai yarima garin nan ne, idan kowa akanka yake, me kake"

tunanin za ace in aka ganka da mace budurwa?

Junaid yace  menene damuwata akan abinda zasuce? Binta kanwa tace wacce na taso tare da

"ita a lokacin da banda kowa, ban fahimci dalilin da zaisa na ja baya da ita ba dan yanzu na zama"

wani abin.

"Azeema tai murmushi tace  ba haka nake nufi ba, in kana cikin mutane ne sannan Junaid ko ba"

dan kai ba ko dan ita ya kamata saboda inba haka ba mutane zasu takura mata.

"Shiru yai bai ce komai ba, tace  ka barta anan sai su dinga kwana da su Barira in yaso da safe sai"

ta dinga zuwa.

Junaid ya kalleta da sauri tace badai tunani kake ku zauna tare ba?

Yace  me zai haka? Bayan haka muka taso?

Tai shiru kafin tace  Junaid kayi hakuri ka barta anan.

Kamar zai sake magana sai kuma yaga kamar bai dace haduwarsa ta farko da mahaifiyarsa ba ya

dinga bijire mata haka ba. Shikenan.

Azeema tace  Nagode Junaid Nagode.

 Ga amanar Binta nan.

"Tace  ni na taho maka da ita karka damu zan kula da ita, sannan Azi da Hari da ragowar bayin"

da mukace su taho sun iso su suka gyara ma bangarenka.

"Cikin jin dadi ya kalleta, tace  Junaid! "

Naam

" Kai jinin mai Martaba ne karka yadda wani ya kawo ma raini, sannan duk wanda ya nemi yima"

zancen banza. 

Sai kuma tai shiru ganin kamar bayasan maganar duba da yanayin da fuskarsa tai.

Murmushi tai tace  Junaid yaushe zaka ban labarin rayuwar dakai.

" Ba wani labari, mun daiyi rayuwar mu tundaga yarinta har kawo yanzu. "

Kai ta jinjina tace  Alhamdulila.

"Shiru suka danyi saboda rashin sabon dake tsakaninsu, kafin yace  meye dalilin sarki na kaini"

can?

"Kallansa tai da sauri saboda batai tunanin tambayar ba, tace  bansani ba wlh, sai dai nasan"

yayi hakane dan hankalin ka ya kwanta.

" Bawai ina inajin haushi bane, sai dai haryanzu ina ganin akwai dalili bayan waccan. "

Shiru Azeema tai jin kalamansa yasa itama ta fara tunanin tabbas dan kawai Junaid yai rayuwa

"hankali a kwance bazai zama dalilin da zaisa ya dauke danta bada saninta ba ya boyeshi, tabbas akwai wani abin kenan? To menene?"

Junaid ne ya kalleta yace  karki damu nayi maganarne ba tare da nazari ba.

Murmushi tai cikin jin dadi a kalla yana da dogon nazarin da akesan mai mulki ya kasance dashi.

Mikewa yai yace  Su Harin suna ina?

Tace  bari nazo muje.

"Dakin huta, ta mikr tana cewa muje na fara nunama hanya."

"Nan suka fito, Binta bata gun hakan yasa yace  Binta fa? Barira tace  ta shiga bandaki. "

Yace  bari na jira ta fito.

Azeema ta kalleshi tace  muje Junaid in ta fito sai Barira ta kawota.

Ya kalli Barira wacce tai saurin cewa zan fada mata inta fito.

"Nan suka nufi waje, a hanya sai kallan Junaid ake ana gaisheshi, Suna kokarin yin kwanar dazata"

sadasu da bangaren Junaid ne sukaji ance  Barka da Yamma.

"Juyowa Azeema tai, ta hade fuska tsam tare da binta da kallo, Zeena ta karaso fuska a sake,"

Junaid kam ganin ba dashi ake ba bai ko juyo ba.

Zeena tace  Nazo bada hakuri naga zaku fita.

Azeema tace  hakuri? Laifin me kikai?

Tace  Tuba nake na yi abinda na bata miki rai.

"Azeema ta juya batace komai ba, dan bataji zata hakura tabbas sai ta fanshe."

Zeena ta bi bayanta tana kallan Junaid tace  Yarima kayi hakuri bansan kai wanene ba lokacin.

"Juyowa yai ya kalleta, tsayawa tai tare da kura mai ido, maida kansa yai hanya baice mata komai"

ba.

Shiru tai bata kara daga kafarta ba wanda hakan yasa du Azeema sukai gaba.

Fure ce tace  Gimbiya menene?

"Zeena ta kalleta da sauri sannan ta kalli gun da su Junaid suke, haushi ya kamata tace  uban me"

kike da har suka wuce mu?

Fure tace  tuba nake Gimbiya.

Takaici ya kamata tace  meye ma amfanin fitowar? Ko so kike na bisu kamar jela?

Fure tace  tuba nake Gimbiya.

Cikin takaici ta juya ta koma bangaren Hajjo.

Azeema kam wani irin dadi ne ya kamara dataga kallan da Junaid ya mata wanda ta san hakan

ne ya tsorata ta tabbas jinin sarautar na nan na yawo a jikinsa.

Yana shiga ya hango Azi na gyra harabar waje.

"Azi na ganshi ya matso cikin tsananin jin dadi, kasa yai da kansa yace  Yarima. "

Junaid ya kalleshi cikin jin dadi yace  Azi kunzo lafiya?

Azi yai saurin zubewa a kasa yace  tuba nake yarima na barka cikin wani hali.

"Junaid yai murmushi yace  nina umarceka ka barni ai, ina su Hari? "

Suna ciki hala dan da suna nan.

"Kai ya jinjina sannan suka shiga ciki, yanda aka gyara gun me gashi kato sosai ya birgeshi."

"Azeema tace  Junaid nan asali da bangaren Mai Martaba ne, anan mahaifinka ya zauna, sai dai"

shekaru biyar da suka wuce aka kara fadada masarautar wanda aka sakema Takawa wani ginin

"shine ya tashi, dazu ya turo akan abude maka. "

Junaid ya kalleta yace  amma hakan ba matsala?

Tace  ba wani matsala tunda umarnin Sarki ne.

"Junaid ya jinjina kai alamar gamsuwa yana kara kallan gun, Azeema ta shiga nununamai yanda"

gun yake.

***

Zeena hartaje zata shiga bangaren Hajjo ta kalli Fure tace  Fure ni me zasuje yi bangaren Takawa na da?

"Fure tai shiru, Zeena tace  kin fadamin ko kuwa?"

Fure tai kasa dakai tace  Sarki ya bar ma Junaid.

Ido ta zaro tace  mene?

Kallan Fure ta karayi tace  Hajjo ta sani?

Fure ta girgiza kai alamar a a.

Zeenatu tace mu koma bangarena baza a huce a kaina ba.

*******

"Da sauri Binta ta shigo, sannan ta kalli Kuyangar data jata wai akan an aiketa, Barira ta kalleta"

tace

6 / 28