Zafin Rana Book Compelet Novels By Aysha Alto

Author :  Aysha Alto Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   13 / 28

36K to 39K   out of 81.6K words

tace ba zai yadda da hakan.

"""Eh, sannan inasan sanin yanda yanayin masarautar take"

"tun lokacin da suka gabata."""

"Azeema ta kalleshi cikin jin dadi tace ""ba matsala, zan sa Mahmud mijin Safiya wanda yake Hakimi ne shi ya sanar"

"dakai komai."""

Muje? Ta tambayeshi.

"Yace ""Eh amma akwai dalilin kiran ne?"""

"Tace ""lokaci lokaci yakan kira mata da yaransa a tattauna."""

Junaid ya jinjina kai kawai.

"Mikewa tai suka fito, a bakin kofar fita suka ga Binta wacce ke kokarin shigowa rike da ledar kayanta."

"Da sauri ta rusuna ta gaisheta, Azeema ta kalleta tace ""Binta kin taho?"""

Eh.

"Shiru tai tana wani tunanin, kafin ta kalli Junaid tace ""Junaid me kake tunani in ta bimu?"""

Ina?

"Murmushi tai tace ""Su Barira ma suna zuwa dan taje itama bana ganin akwai matsala."""

"Junaid yai shiru duk da ya tabbatar akwai wani abin a ranta sai dai rashin sanin menene ya hanashi musawa. Barira ta kalla sannan tace ""Bari a ajiye kayan ku biyomu."" Nan suka shiga ciki."

"Kayan kawai suka ajiye suka fito, Binta na tambayar Barira akan ina zasuje."

"Barira ga shareta kamar ba da mutum take magana ba,"

hakan yasata yin shiru.

Bangaren Mai Martaba Sarki Abdulsalam suka nufa.

"Fadar sa aka bude musu kofa, Zagi ya sanar da isowarsu."

Jakadiya na tsaye a bakin kofar tana musu barka da zuwa.

"Hajjo, Zeena, Zubair da su Ramlatu da ragowar matan"

sarki da yaransu sun hallara da alama sune sukazo karshe.

"Hajjo ta hade fuska, Azeema ta zauna a inda aka ware"

"dominta sannan Jakadiya ta nunawa Junaid inda zai zauna,"

zama yai su kuma su Binta da ragowa bayi suka koma gefe

"suka tsafsaya, Binta tana tunanin me take anan?"

Azeema kam kallanta tai kadan tace gwara ki fahimci

Junaid ya miki nisa hakan ne yasa na kawoki.

Zeena ce ta zubawa Junaid ido cikin jin dadi da mamaki halim da take neman tsintar kanta a ciki.

"Gani tai ya dago ya kalli wani gun, idanuntanr suka kai kan"

"Binta, wani irin kululun bakin ciki ne ya kamata."

Sanar wa isowar Mai Martaba da Zagi yai ne yasa kowa ya

daidaita.

Abdulsalam ya shigo ya zauna tare da kallan su.

Kowa an ajiye kayan marmari da abinsha a gabanshi.

"Bayan an gaida Mai Martaba ne ya kalli Junaid yace ""Dafatan Junaid ka fara warewa da zaman nan?"""

"Junaid yace ""Alhamdulila."""

"Andansyi shiru kafin Sarki yace sannan yace ""Bari mu fara gwada tambaya kamar yanda aka saba, dan a tattauna a"

"kara rike sanin juna."""

"""Idan akace za'a sai Sarki nawa kuke tunanin ya kamata a"

"siye shi?"""

"Hajjo ce ta kalleshi tace ""Rankanya dade wannan tambaya"

"ta ina za'a nemo amsarta?"""

"Sarki bai kalleta ba yace ""wannan tambaya inaso Zubair ya"

"bani amsarta"""

"Zubair ya kalleshi yaga yanda Sarki ya hada rai yace ""ta ina za'a sai sarki? Ai wannan sai dai bayi, idan kuma har akaje ga siyan sarki to lalai sai dai a kwashe duk tattalin arzikin"

"garin a sai shi."""

"Wani kallo Sarki yamai yace ""idan aka kwashe arzikin kasar sai kuma ai rayuwa dame?"""

"Zubair yai shiru, Ran AbdulSalam ya baci saboda haushin"

"amsar daya bashi, kallan Zeena yai wacce itama taji haushin ansar."""

Zeena me kike tunani?

"Kallansa tai tace ""indai za'a sai sarki to kenan ya zama ba"

"sarki ba"""

Yace haka ne indai har aka siye shi ai ya tashi daga

"matsayinsa, Junaid kai fa me kake tunani?"

A siyeshi a silai

Silai?

"Azeema ta kalleshi da sauri tace ""Junaid!"""

"Nan kowa ya fara yan kananan maganganu, Zeena ce ta"

kalleshi itama hankalinta a tashe.

"Binta kam idanunta kawai ta runtse dan tasai halin Junaid duk abinda ke ransa fada zai, yanzu me ya kawo zancen"

"silai? Karamin kudi?"""

"Sarki wanda shi kansa ransa ya baci matuka ya dunkule hannunsa sannan ya dan murmusa yace ""me yasa kace"

"haka?"""

"Junaid yace ""A tunanin mutane dayawa Sukai ba wani kudi bane mai daraja sai dai a gun talaka wanda yake neman ci dasha dakyar silay tafi komai daraja a gunsa, kafin a samu wanda baisan darajar sulai daya ba za'a samu"

"talakawan da suka san darajarta ashirin, hakan yasa Silai"

"ta zama kudi mafi daraja a ciki kudi, sannan sai ka hada silai dayawa ne zaka samu kudi mai daraja da kake nema. Idan har za'a sai sarki to sai a siyeshi a abu mafi daraja"

"wanda talaka da mai kudi sukafi sanin darajarsa."""

Yana kaiwa nan yai shiru bai kara tanka komai bs.

"Ido Abdulsalam ya zubamai, tabbas koshi bai taba kawo hakan a ransa ba, wannan shi ake kira magana da hikima wanda ake neman Sarki da ita, tabbas dawowar Junaid nan"

ba karamin matsala zai jawo masa ba nan gaba.

"Azeema wacce dadi ya kamata ta kalli Abdulsalam,"

hannunsa ta kalla dan ta gama saninsa duk wani abu dayake tunani rabi tana ganewa daga kallansa.

"Ganin hannunsa a dunkule yasa ta kalli fuskarsa, da sauri ya sake hannunsa sannan ya kalleta cikin nuna tsantssn jin dadinsa yace ""Masha Allah! Tabbas wannan shi ake kira"

"magana cikin hikima."""

"Zeena ce ta kalleshi tace ""Mai Martaba ni kaina na tsorata"

"jin Ya Junaid yace silai, sai dai jin bayaninsa yasa na"

fahimci me yake nufi sannan na fahimci Silai yafi komai

"daraja kamar yanda Sarki yafi mutanen gari."""

"Hajjo ce ta sa hannu ta bige Zeena dake gefenta, sannan tace ""amsoshi duka sunyi ma'ana kowane da nashi"

"fahimtar."""

Azeema ta dau kofin dake gabanta ta kurbi ruwa.

"Binta wacce tai shiru tana kallan Junaid wanda ya daure fuska sam ba alamar fara'a a tattare dashi, tabbas Junaid dinta jinin sarauta ne, wanda ita kuma take wacce"

mahaifinta ma bayaso........

Zeenatu ce ta kalleta ganin yanda take kallan Junsid cikin

"rauni yasa tace ""Binta!"""

Kafin ma Binta ta amsa Junaid ya kalli Zeena.

"A ranta tace au ashe zaka kalleni, Binta ce ta matso da"

"sauri, Sunkuyowa tai Zeena ta mika mata kofinta tace ""dan daurayomin naga kamar kura."""

Binta ta kalli Junaid wanda ya dauke kai kamar baisan

tana gun ba.

"Sai dai gaba daya hankalinsa na kansu, Binta ga amsa tai"

"waje, Azeema ta bita da kallo."

"Zubair ne ya kalli Hajjo cikin kunar rai, alams tamai da"

karya nuna jin haushinsa.

"Sarki yai murmushi yace "" Junaid kayi tunanin abinda"

"nace ka zaba?"""

"Junaid yai kasa dakai yace ""zan sanar dakai Ranka ya"

"dade."""

"""Sirri ne kenan?"""

"Zeena ta tambaya, bai ko kalleta ba sai dai Azeema datace"

da alama.....

**********

* ZAFIN RANA *

......................

*Hask e  W rit e rs Ass o ci a ti o n*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*K A$ f[ fV *

"Nanma shiru yay yak'i tankawa, yakumak'i kallon kowa."

"Binta ta dawo da kofin da zeena tabata ta d'aurayo, rissinawa tayi ta mik'a mata, d'agowar da"

"zatayi suka had'a ido da Junaid, saurin janyewa tayi, shima ya basar."

"Azeema da Idonta ke kallon duk motsinsu taji zuciyarta ta k'untata, amma saita had'iye fushinta"

tamkar babu komai.

"Sarki yacigaba da jeho tambayoyinsa ana bashi amsa, Junaid kam tundaga ta farko bai kuma"

"tankawa ba, sai dai tsaf yake nazari akan amsar kowa da motsin kowa."

"Bayan taron ya tashi kowa ya nufi sashensa, Azeema taso Junaid yakoma sashenta dan tanason jin"

miya tanadi zaba bisa ga k'yautar sarki na abinda yakeso.

*****************

"Tunda Junaid yadawo daga sashen mai martaba saiya kasa zama, sai safa da marwa yake a"

"falonsa yana cud'anya wasu abubuwa daya danganci masarautar tasu, a yanzu mafita d'ayace dashi, nutsuwa wajen jin sirri da tushen masarautar tasu, haka kawai jikinshi na bashi ba dalilin dazaisa mahaifinsa ya kaishi can gefen gari ba tare da sanin mahaifiyarsa ba."

Ta wannan hanyarne kawai zai samu amsar tambayarsa akan wanene yasa a fiddashi a

masarautar zuwa ke6antaccen waje?.

Ajiyar zuciya ya sauke da addu'ar samun kwarin gwiwa akan samun warwarar cud'ad'd'en

al'amari da zuciyarsa ke hangowa gameda abubuwa masu yawan gaske.

*****************

Suna isowa sashenta ta kalli zeena rai 6ace.....

" Hajjo nikam wannan kallon naki tsoro yake ban, nidai nasan banyi wata kato6ara a"

"wannan taronba, banda abin arziki danai. "

"Hararta Hajjo tayi tana hura hanci, murya a cinkushe tace,  wani lokacin saina ringaji inama bani"

"Na haifi Zubair ba, kwata-kwata k'wak'walwarsa bata ja yanda ya kamata, dolene na nemo"

malami ya koyar dashi hikimar zance .

Dariya Zeena tayi sosai dukda kallon da hajjo ta watsa Mata bai hanata fad'in  To Hajjo ke da

"kanki kin kirashi mai kwakwalwar kifi tayaya ko kin d'akko malami masanin hikima kan Yaya zai iya bud'ewa? Da dai kunyarda da shawarata kawai dayafi muku, danni inaji a jikina Yaya bazai mulki"

masarautar nanb. 

"Hannu Hajjo ta kai mata, Zeena tai azamar matsawa da baya.  Nifa umma gaskiya nafad'a, idan"

"baki haifi sairkiba ai kin haifi wadda zata haifa miki sarki, ki zauna kiyi tunani akan hakan? ."

" Lallai ashe ba Zubair kawai ne mai kwakwalwar kifiba? Kekam ai saita jakuna, shashasha kawai,"

"idanma barci kike ki farka, babu yanda za'ai jinina ya dunk'ulu dana Azeema ."

"Baki Zeena ta ta6e ta mike tai hanyar d'akinta da k'unk'uni tana fad'in  Ashe zaki mutu kuwa ayi,"

"Danni koza'a maida masarautarnan birnin sin saboda rikici saina mallaki ya Junaid matsayin mijina uban y'ay'ana, yau na tabbatar shikadai ne ya dace dani dan haka ba wanda ya isa ya hanani"

mallakarsa.

"Hajjo najin k'unk'unin Zeena, amma batajin mitake fad'a, dan haka ta zuba tagumi tana binta"

"da kallo. Takula inhar tayi wasa za'ayi sukuwar irganmun dokuna a masarautar nan batareda ta d'aurama nata sirdi ba. Kai ina ALLAH ya kikaye, koma mizai faru kam sai dai ya faru, sai Zubair yazama *SARKI!*."

hummm to maji magani an binne tsohuwa da ranta

***********************

"Gaba d'aya zama sashen Azeema bayama Binta dad'i, amma tayi alk'awarin jurewa"

"kodan farin cikin Junaid. Yanzu haka buk'atar ganinsa takeyi, koda bazasuyi maganaba ta gansa tasami nutsuwa, dan talura lallai yamata nisa, ta k'ara fahimtar hakane bisa mizanin fahimtar gayyatar da azeema tamata zuwa taron jiya."

"Da farko bata fahimtaba, saida suka dawo ta zauna tayi dogon nazari, ta umarci tabisune saboda a"

"nuna mata iyakarta, murmushin takaici ta saki tana had'iye kukan daya fara taho Mata. Lallai dolene ta sake takunta, dan ta lura mahaifiyar Junaid kishi take da ita. Babbar magana, ina ita ina kishi da matar sarki, mahaifiyar Wanda tafiso aduk fad'in duniyarnan, insha ALLAH cikin ruwan sanyi zatabi matakan da mahaifiyar Junaid zata fahimci ba burinta rabata da d'antaba."

"Sam bata iya ko fitowa, daga daki sai takar gida na baya, haka zata zauna tai shiru tana mamakin"

"wannan rayuwa data tsinci kanta a ciki wanda bata taba kawowa ba, ada ta dauka samun inda iyayen Junaid suke shi yafi komai mahimmanci a gareta sai dai yanzu batasan me ke ma ranta ba. Dan wani sa in takanji dama bai gansu ba......."

In hakan yazo ranta sai tai saurin yin istigfari tare da fatan Allah ya kauda mata wannan mumunan

abin da zuciyarta ke raya mata.

**************

"Sai dayai kwana uku bai fita ko ina ba, ya zauna sosai yayi karatu akan abinda yake san fahimta."

"Yau da wuri ya shirya, dan yanason zuwa sashen Umma akan maganarsu ta jiya Na"

"sanin tarihin masarautar, dakuma yagama ji yana buk'atar ganawa da mai martaba akan za6in damar daya bashi."

"Shiga yai ta alfarma, daka gansa kaga jinin sarauta na asali, dan akwanakin da yayi a masarautar"

"komai nashi ya canja, ya canja d'abi'unsa sosai tamkar yanda ya lura mahaifiyarsa Na buk'ata. Shi kansa kuma ya gamsu da tsarin nata d'ari bisa d'ari."

"Da mamaki yake bin kayan karin kumallo da aka shirya masa a falonsa, yay tsaye ya zuba musu"

ido kamar yay gamo da abin kallo. Ganin yarasa amsa saiya kwala kiran Azi.

Da hanzari Azi ya k'araso yana risinawa  Barka da safiya yarima .

"Kai Junaid ya jinjina masa, sannan yay masa nuni da shiryayyun kwanikan abincin batare da yayi"

magana ba.

Azi yad'an kuma risinawa yana murmushi  Ranka ya dad'e ai gimbiya ce takawo tare da

kuyanginta .

 Gimbiya? Junaid yafad'a cikin sigar rashin fahimta .

"Fahimtar hakan da Azi yayi saiya fad'ad'a murmushinsa Ranka ya dade Gimbiya Zeena nake nufi,"

dazu aka aka kawo.

"Bak'aramin ware fararen idanunsa yayi akan Azi ba, yabud'e baki zaiyi magana saikuma yay shiru,"

ya kauda idonsa ga kwanikan yana fad'in  Muje sashen Ummana . Da sauri Azi yace  Yarima Abincin fa?

Kallansa Junaid yai wanda yasa shi yin shiru.

Kai Azi ya jinjina.

*********

"Tunda suka fito bayi keta zubewa suna gaisheshi, iyakarsa d'aga musu hannu. Sun kusa shiga"

"sashen Umma yace,  Har gulman ya ishesu? ."

"Azi dabai fahimtaba yace,  Yarima gulma kuma? ."

 Uhm

Yafad'a a tak'aice.

"Murmushi Azi yayi, dan yanzu ya gane miyake nufi, kafin yabashi Amsa sun iso sashen Umma."

Babu dad'ewa da sanar da isowarsa barira ta sanarmasa da izinin shiga inji Azeema.

Yayi taku biyu zai shiga rumfarta idonsa ya sauka ga Binta dake hidimar gyaran falon.

"Wani Abu yaji ya gangaro tun daga mak'oshinsa zuwa yatsun kafarsa, yaushe raban da ya"

"ganga?amma saiya danne, yakuma basar tamkar bai gantaba."

"Hakan yabama binta mamaki, sannan yayima barira dad'i. Kamar yanda sauran bayin suka zube"

"suna gaisheshi haka itama binta tayi, hannu ya d'aga musu kawai yay gaba, hankalinsa duk yanakan binta daya lura yanayinsa ya tsoratar da ita."

"Har cikin d'akin Azeema yashiga bisa jagorancin Barirah, Azeema na kishingid'e bisa dardumar"

"tsakar d'akin, littafine da abin rubutu a hannunta."

Zama yay d'an nesa da ita kad'an yana fad'in  Barka da safiya ummana

"Tai k'asaitaccen Murmushinta danjin yanda ya kira sunanta, hakan namata dad'i ainun, cikin"

"lumshe idanu ta amsa da  barkan ka dai Junaid, ina fata katashi lafiya? ."

 Alhmdllh .

"Zamanta ta gyara sosai tana kallonsa, saikuma ta d'auke kanta tana kiran barira."

"Da sauri Barira ta shigo, batare da Azeema ta kalleta ba tace,  Yauma ahad'amin karin kumallo"

tare da Junaid .

" Angama ranki ya dad'e, amma a ina za'a shirya? ."

Kallon Junaid Azeema tayi alamar jin ta bakinsa. Ya d'an murmusa sanann yamata alama da nan

cikin d'aki.

"Itama murmushin tayi, sannan ta kalli barira, nuni taimata da nan ta d'auke kanta."

"Bayan fitar Barira Junaid ya gyara zamansa, kansa a k'asa yace,  Ummana idan abu nada daraja"

bai kamata a daraja duk abinda ya dangancesa ba? .

"Shiru Azeema tayi tana kallonsa da juya maganarsa, saikuma tai murmushi cikeda k'asaita, tad'an"

"sauke numfashi tana kuma kishingid'a  Gaskiyane Junaid, lallai za'a gyara ."

"Baice komaiba sai d'an d'ago ido dayay ya kalleta, tai masa murmushi."

Tsaf barira da kuyangi biyu suka kammala shirya abinci a gabansu. Bayan fitarsu Azeema ta kalli

Junaid taimasa nuni da Bismillah.

"Murmushi yayi yafara k'ok'arin zubawa, itadai tana kallonsa. A mamakinta koda yagama saiya"

"matso gareta, fuskarsa d'auke da murmushi yace,  A tsarin masarautar nan Ko inada hurumin cin abinci da matar sarki umman yarima Junaid? ."

"Wani k'asaitaccen murmushi ta saki, wanda akan dad'e ba'a gansa a fuskarta ba, ta d'ora"

"hannunta dayasha zobunan azurfa da lu'u-lu'u akan nasa,  Wannan shine yanayi da girmamawa mafi soyuwa ga matar sarki kuma Umman sarki insha ALLAH ."

"Junaid yay murmushi mai sauti, Wanda ya bayyana fararen hak'oransa sosai."

"Ahankali suka fara cin abincin cikin nutsuwa da tsintar kai a yanayin nishad'i, gimbiya Azeema"

"najin lallai ta Isa kuma ta cancanta, kaso mafi yawa Na fargabar tazarar dake tsakaninta da d'anta ya ragu, harma tad'anji ta rage jin zafin Binta, balle tunda ya ajiyeta taga ko nemanta baiyi ba gashi yau yazo yana faranta mata rai wanda bata taba tsammanin samunshi a yanzu ba."

Azeema ta kalli Barira tace  Wazirin ya fada miki?

"Tace  eh Gimbiya yace akwai Gimbiya Zainab a masarautar Zazzau, akwai Gimbiya Nafeesa a masarautar Gumel, akwai Gimbiya Kadijah a masarautar Kano. "

Azeema tai shiru tana tunani kafin tace  zansa a bincika mun su kafin nawa Mai Martaba

maganar.

Barira cikin gulma tace  Mata zaki nemowa Junaid?

Azeema ta kalleta sai dai bata ce komai ba ta juya tana tunani.

***********

"Tunda aka dawo daga kai masa abincin takasa zaune ta kasa tsaye, burinta da addu'arta shine ace"

yaci dan ta tabbatar idan har yaci to ya fara saukowa kenan. Ganin lokaci yaja ta kwala kiran fure.

"Jiki Na rawa Fure ta iso d'akin, ta risina tana fad'in  gani uwar d'akina ."

"Wani kallo Zeena tamata, cikeda k'asaita tazauna bakin gadonta,  Fure! Inason kije sashen ya"

Junaid ki bincikamin yaci abinda muka kai masa? .

"Fure ta had'iye yawu tana gyad'a kai, har zatayi magana Zeena ta katseta ta hanyar watsa mata"

harara....

" to mai kan kifi, halan zakice tayaya zaki sani? Lokaci kad'an yarage na canjaki fure, ko kad'an"

baki dace da zama hadimata ba sam .

" ALLAH ya huci zuciyarki uwar d'akina, a gafarceni gimbiya ."

"Banza Zeena Tamata, ta d'auke kanta gefe kawai. Ganin haka sai Fure ta mik'e a sanyaye zuwa"

sashen Yarima Junaid.

*************

"Bayan sun kammala cin abincin su barira suka kwashe komai, Junaid ya kalli Azeema"

saikuma ya duk'ar dakai.  Ummana yaushene zaizo? .

"Cikin nuna jin dad'inta da yanda hankakin Junaid yafara tasiri akan mulki ta amsa masa,"

" Nan kusa zaka ganshi, sai dai kafin zuwansa ga tambaya? ."

 Ina sauranki . yafad'a batare da ya d'agoba.

 Meka tanada zaka za6a bisa Umarnin mai martaba? .

"Murmushi yayi batare da ya kalleta ba, a ransa yace Umma za6ina bazai saki farin cikiba, dan naji"

"a raina bashine burinki ba. Amma a fili sai ya fad'ad'a murmushinsa  Ummana ina nan Ina nazari dai, kinsan yanzu nake fahimtar komai ."

 Gaskiyane . Ta fada cikin jin dadi.

"Daga nan shiru ya biyo baya, shi duk hankalinsa nakan me binta takeyi yanzu? Amma ya kamata"

Umma ta sa Binta aiki kamar Bakwa? Bayan ita ba baiwa bace? Ta ajiye aikin taci abinci? Kokuwa har yanzu tana can tana bautar?

**************

"Sarki

13 / 28