Zafin Rana Book Compelet Novels By Aysha Alto

Author :  Aysha Alto Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   27 / 28

78K to 81K   out of 81.6K words

sosai tana"

hidima dan ta gama tsara abinda zata aiwatar a daren yau.

"Sarkin kano bai samu zuwa ba sai dai ya turo babban dansa ya wakilceshi, Sarkin Zazzau ma"

"turowa yai, hidima sosai sukeyi, ta ko ina mutane ke hada hadarsu."

Zeena ce ta kalli Fure tace  kin aikama Hajjo kayan?

Fure ta kalleta jiki a sanyaye tace  tace ma dawo miki dasu.

Kallan kayan tai da bata kula dasu ba da sannan tai yake tace kawo na kai mata dakaina.

"Haka nan suka cigaba da hidima, sosai Binta da Zeena sukai kyau sosai, kayan iri daya ne sai dai"

kowa kalarsa daban.

"Binta da yake ba fara bace sai ta saka sky blue, ita kuma Zeena wace ke fara sosai saboda"

"Abdulsalam tayo ta saka kalar Orange, sunyi kyau sosai."

"Safiya uwar hidima ita da mijinta Mahmud ta ko ina hidima sukeyi, an gama shirya Junaid tsaf"

sannan suka nufi fada danyin nadi.

"Haka aka sha shagali wanda ya kwanta a zuciyar wadanda ke farin ciki, wadanda ke bakin ciki"

kuma ya bar musu babban tabo wanda bazai iya warkewa ba.

"Junaid kam yayi kyau har bansan ta yanda zan muku bayani ba, yo abinka da mai taro lol"

"Haka akai taro aka gama, a kuma daren ranar ne bayan yayi sallar isha i a saban sashensa yana"

"mike saboda gajiyar dayai, tunani yake a kira masa Binta tadan taimaka ta bugamai bayansa,"

"gefensa Azi ne wanda ya kira, ya kalleshi yace  Sabisu ya wuce din? "

Azi yace  ya tafi ranka ya dade

Junaid ya kalleshi yace  Inasan kai tafiya zuwa kauyen nan.

Kallansa Azi yai yace  wani abin za ai?

Junaid ne ya kalleshi yace  Azi girma ya dan fara kamaka kamar ya kamata daga wannan aiken

ka kuma yi aure ka zauna da iyalinka.

Azi cikin kunya yace  ni ka barni a haka Takawa hakan nan kula dakai yafi komai a gareni.

Junaid yace  a a in ka dawo zan nemo ma mata da kaina inkai aure sai ka ajiyeta anan cikin

masarauta.

"Zubewa Azi yai gaba daya ya rasa ta inda zaiyi magana,ya dago yace  ina godiya Takawa Allah ya"

karemin kai a koda yaushe.

"Junaid yace  Ameen, ka shirya ka nemomin mahaifin Binta ka taho dashi. "

Azi ya kalleshi yace  nan?

"Junaid ya daga kai, da sauri Azi yace  angama ranka ya dade. "

"Zagi ne ya fara sanar da isowar Azeema, nan Azi yai sallama ya fita."

"Azeema ce ta shigo bayan an mata iso, Junaid ne ya kalleta har ta shigo, sannan ta zauna,"

kallanta yai yace  Umma?

"Kallansa tai tana murmushi sannan ta ajiye abinda ke hannunta, kaya ne na sarki wanda kana"

"kallo zakasan kaya ne wanda Sarki kadai ke da damar sashi, kallanta yai sannan ya kara kallan kaya."

Murmushi tai tace  zaka tashi na gwada ma?

"Jiki a sanyaye ya mike, da kanta ta taimaka mai ya saka, ganin yayi mai cif cif ne ya sata yin dariya"

"mai hade da hawaye tace  Alhamdulila, na dauka sai mun sake yi. "

"Gaba daya jikinsa ne yai sanyi ya kalleta, kallansa tai tana dariya sannan tace  nagode daka"

amshi kyautata.

 Taya zanki amsa?

"Furucin da taji ya fito daga bakinsa kenan, kallansa tai jiki a sanyaye, murmushi ya mata yace"

 barina kika yanke shawarar yi?

Idanunta ta zaro ta kalleshi jikinta ya sake yin sanyi a hankali tace  ya akai ka sani?

"Nuna mata yai ta zauna sannan shima ya zauna, kallansa tai yace  taya bazan gane ba? Bayan"

kina nufin kin kawomin rigar sallama.

A hankali ta sa hannu a kan fuskarsa tace  Junaid dina ya girma. Ta fada tana kokarin maida

kwallarta.

Sauke hannunta tai tadan ja hancinta tace  Abdulsalam bashi da lafiya.

Na sani!

Kallansa tai tace  yaushe?

"Murmushi yai yace  jiya, ya kirani. "

Yace me? Ta tambaya cikin sanyin murya.

Shiru yai yana tunowa.

Kallansa tai tana nazarin abinda yake tunani.

"Jiya ya kasance kwanan Zeena ne, bai kuma dawo saban bangarensa ba yana kwance a daki"

hadimin Abdulsalam ya zo da sakon san ganinsa da Abdulsalam yake.

"Junaid ya mike zai fita, da sauri Zeena ta rike rigarsa tace  Yaya inzo muje? "

Murmushi ya mata sannan ya dafata yace  yanzu zan dawo.

Kallansa tai jiki a sanyaye ya fita.

Abdulsalam na zaune a bangarensa Junaid ya shiga.

Zama yai Abdulsalam ya zuba ruwa a kofuna guda biyu dake gabansa sannan ya tura ma Junaid

kusa dashi.

"Kallansa Junaid yai sannan ya kalli kofunan, Abdulsalam yace  daya ruwa ne kamar yanda kaka"

"na zuba shi, dayan kuma akwai guba a cikin kofin kafin na zuba ruwan. "

"Kallansa Junaid yai, Abdulsalam yace  ka dau daya nima na dau daya, idan har ka dau ruwa to"

"tabbas zan mutu a cikin dakin nan, kaga shikenan sai a ce kai ne ka kasheni, idan kuma ka dau gubar kaga shikenan daga wannan gun kowa zai san nine na kasheka nima hukuncina kisa ne zai"

biyo.

Junaid wanda ke kallansa ne yai wani murmushi sannan yace  to sai akace kuma dole nasha

ruwan?

Abdulsalam yace  dole ne domin inba haka ba zan shanye duka ruwan kaga duk abinda ya biyo

baya kaine.

"Shiru Junaid yai tare da kuramai ido, Abdulsalam ya kalleshi, Junaid yace  baka da lafiya ne? "

"Kauda kai Abdulsalam yai, yana juyowa yaga Junaid ya dau ruwan ya juyeshi a daya cup din"

sannan ya shanye.

Ido Abdulsalam ya zaro yace  bakada hankali ne?

Junaid ya ajiye cup din sannan ya kalleshi yace  me yasa ka kirani? Nasan ba wai kirana kai dan

kawai kai wannan wasan ba?

Kallansa Yai sannan yai murmushi yace  ya akai kasan bakomai?

Junaid yace  menene abin wahala a cik? Ta ina zaka samu guba a inda ni nasa a killaceka?

Sannan koma ka samu taya zaka sakama mijin yarka? Sannan inka kasheni da wani ido zaka fito?

Sannan babban damuwarka shine Umma ta tsaneka.

"Hannu yasa yana murza idanunsa, sannan ya kalleshi yace  na fadi "

Ya akai?

Abdulsalam yaga ya mike ya sanya gwiwowinsa a kasa.

Da sauri Junaid ya kalleshi yace  lafiya?

Abdulsalam ya kalli Junaid tari ne yadan kwace mai kafin ya tsagaita yace  Junaid na san

"laifina bazai musaltu ba? Sai dai bazanji kunyar tambayarka alfarka guda uku ba, ka dubi girman Allah ka yafemin? Nasan abinda nai har abada bazan taba samun sassauci ba, laifi ne babba wanda na aikatawa Allah, sai dai zan karasa rayuwata agun neman yafiya gun Allah, nasan hukuncina a musulunce mai karfi ne, sai dai ina nemi alfarma kasa a kulleni a gidan daka zauna"

har karshen rayuwata.

"Junaid ne ya kalleshi, Abdulsalam ya kalleshi yace  Sannan abu na biyu ga amanar Zeena da"

"Zubair nan, dan Allah ka kula dasu Junaid, laifina karya shafesu basusan abinda akeyi ba. "

"Junaid ne ya hadiya yawon bakinsa, yana kokarin danne raunin da zuciyarsa ke neman yi."

"Abdulsalam yace  sai na karshe, ka taimaka ka barni na tafi da Azeema. "

Kallan Junaid yai gaba daya dana sani na damunsa.

Junaid me ya kalleshi yace  na farko dana biyu na yadda dasu sai dai na uku banida hakki akai.

"Kallan Azeema yai ya tuno yanda ya fito ya bashi yana hawaye, Azeema tai murmushi tace"

 shikenan.

Ta daure tace  Na fahimci nima zamana anan bazai dada ma komai ba sai bakin ciki. Na

"tabbatar duk sanda ka tuno abinda ya faro sai ka tsaneni, duk kuma sanda ka ganni sai abin ya dawoma, hakan yasa zan bishi, sai dai ina so kamana hukuncin daya dace damu, duk abinda ka"

yanke zan zama mai bi.

Tana kaiwa nan ta mai sallama ta mike.

Kallanta yai yace  Umma!

Juyowa tai ta kalleshi da raunana idanunta.

Yace  bari a kirashi.

Kallansa tai sannan ta dawo ta zauna tace  yanzu?

Azi ya kira yace a kira Sarki.

Hannu yasa a kansa sannan ya rufe idanunsa.

Gaba day jikin Azeema ne yai sanyi zuciyarta na bugawa da karfi da karfi.

Bazata taba yafema Abdulsalam ba sai dai in ta duba ta wani bangaren gani take komai ya faru ne

"saboda ita, ta tabbatar da badan saboda ita ba da duk hakan bazata faru ba."

*

Ayusher

* ZAFIN RANA *

......................

*Hask e  W rit e rs Ass o ci a ti o n*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*K A$ f[ fV *

{51}

"Abdulsalam ne ya shigo gaba daya jikinsa ya kara rarakewa duk ya rame, zama yai Junaid har"

yanzu bai bude idanunsa ba.

Can sai ga Hajjo wacce yasa itama a kirata daga baya.

"Ajiyar zuciya yai sannan ya bude idanunsa a hankali, kallan Abdulsalam yai sannan ya kalli"

"Azeema yace ""daga wannan lokacin na haramtawa Azeema da Abdulsalam shigowa cikin gari, zasu koma kauyen dana nemi su zauna, a kuma can zasu cigaba da rayuwa har karshen ransu, sannan dole su zasu nemi abinda zasu ci su sha, hadima daya da hadimi daya na amince su tafi dasu, sannan idan har Hajjo ta nemi ta bisu itama da hadima daya zata tafi, in kuma mijinta ya nemi zamanta anan ko kuma yana neman sauwake mata? zata koma can karshen ginin kewaye, gefen da Hajiya Inna take ta zauna, sannan itama gudun fitina mai tasowa zata bar shiga duk wani"

"sabga data shafi cikin masarauta."""

"Kallan Hajjo yai sannan yace ""sannan Zubair zan nadashi Hakkimi zai bar cikin masarautar nan ya"

"koma Hakimin garin da na bashi."""

"Maida idanunsa yai yadan lumshe sannan ya sake budesu yace ""inaso a cikin gurin nan maganar"

"abinda kuka aikata ta tsaya, wannan ne kadai abinda xan iya muku."

"Abdulsalam ya kalla yace ""kafin ka tafi gobe kaga nemi ganin 'yarka."""

"Da sauri yace ""to"""

"Yana kaiwa nan yace ""nagama magana."""

"Abdulsalam ya sake zubewa yana godiya, Azeema kam hawaye ne ya zubo mata saboda harta"

"fara rashin dan nata, ita kuma kaddararta kenan, bata taso da shi ba yanzu kuma shn hadu gashi zasu sake rabuwa."

"Kwallarta ta share sannan ta mike ta fita, Abdulsalam yabi bayanta da sauri har yana tuntube."

"Hajjo Junaid ya kalla wacce ta sauke kanta kasa ko tofa kalma daya batai ba, kallanta yai, kallansa"

"tai ta daure tace ""Zubair laifin me yai?"""

"Kallanta yai yace ba laifin dayai sai dai zamanshi kusa dake zaisa ki sashi, in ba abinda zakice zan"

"shiga ciki, sannan kema kiga yarki ta damu."

Ya wuce ciki.

"Haka tafito gaba daya danta a bace, yanzu kam ba yanda ta iya inba so take a turata kauye ba"

"bayan ba ita ya kar zomon ba, rataya aka bata, bataga abinda zaisa tabishi wani kauye ba."

^****

"Abdulsalam ne yabi Azeema da sauri, hannunta ya kamo yace ""Azeema nagode sosai """

"Tari ne ya kwace mai, kallansa tai tace ""karkai tunanin zan bika ne saboda soyayya ko kiyayya,"

"zan bika ne saboda ma kare mutunci da darajar d'ana."""

"Kai ya daga da sauri yace ""koma menene nidai nagode Azeema ke kadai nake bukata a"

"rayuwata."""

"Hajjo wacce ta taho tana jin karshen kalamansa ta tabe baki tace ""sai ka dauki abinka."""

"Kallansa tai bayan ta karaso tace ""kasan dai ni ina nan ko?"""

"Yace ""nasani."""

"Ta maka mai harara ta harari Azeema ta wuce, dan inba su ba da duk wannan abin bakin cikin bazai sameta ba, taga samu taga rashi."

*******

Washe gari a fada.

"Junaid yai gyaran murya wanda yasa kowa sake nutsuwa, kallansu yai dukansu sannan yace"

"""inada muhimmiyar sanarwa, da farko dai Sarki Abdulsalam da matarsa Gimbiya Azeema zasu bar masarautar nan sakamakon izinin hutawa da sukesan yi, abu na biyu kuma Waziri, Shamaki da Galadima."""

"Da sauri suka kalleshi gabansu na faduwa, suma ina neman kowa ya kawo sunan dansa wanda"

"zai gajeshi, ya zauna ya huta a gida, lafiyarku itace anin dubawa."""

"""Sannan abu na uku Zubair!"""

"Zubair wanda dama yasan menene saboda Hajjo ta fadamai, Junaid yace ""na nadaka Hakimin"

"Gabas!"""

"Da sauri mai kiran lafiya ya fara yima sarki kiraki, su Waziri kuwa yanda kasan an musu duka"

"haka sukaji abin."""

Da wannan aka shiga wata hidimar.

"Yana fitowa ya hadu da Azi ya dawo, Azi aya kalla yamai alama da ido akan an sameshi?"

Azi ya daga kai alamar eh.

"Bangarensa suka nufa daga gefen kofa yaga mutumin dake tsaye duk kayan jikinsa a kode,"

kafarsa wani sidaden silifas ne.

Junaid ya kalleshi da sauri ya zube kasa yana kwasar gaisuwa.

Junaid ya kalleshi sannan ya nemi ya shigo ciki.

"Da bakin kofa ya tsuguna gaba daya ya rude, sai da Junaid ya nutsu sannan ya kalleshi yace"

"""kaine Malam Kasim?"""

"Da sauri yace ""eh."""

"Junaid ya kalleshi cikin takaici yace ""ka taba tunanin inda yarka take? Ko a wace irin rayuwa"

"take?"""

'Yata?

"Ran Junaid ne ya kara baci, da sauri Kasim ya kalli Junaid yace ""Binta?"""

"Junaid ne ya kalleshi, da sauri ya sake zubewa yace ""Binta? Tanada rai?"""

"Junaid yace ""ka taba dana sanin abinda ka aikata?"""

"Kuka Kasim ya saka yace ""a koda yaushe cikin dana sani nake, san zuciya yasa na wulakanta yar"

"yarinyar da take marainiya."""

Marainiya?

"Kasim yana kuka yace ""Yarinyar mutumin daya taimakeni na zauna a garin ne, babban mutum ne"

"malami yana zaune da matarsa lokacin da mukazo garin, sai dai yana fama da lalurar ciwon daji, a koda yaushe yana zaune saboda kafafunsa, matarsa nada ciki ya rasu, haka almajiransa kowa ya shiga kokarin auranta dan ya biya hallarcin malam, harnima na shiga ciki, sai dai bansan dalilin Hafsa na zabata ba, nazo kuma ganin na samu dukiyar daya bari nai aure har na koresu."""

"Sake zubewa yai yana wani irin kuka, ran Junaid yakai matuka gun baci yace ""wannan wani irin"

"mugun hali ne? Bayan cutar da mahaifiyarta dakai sannan ka sawa yarinyar kiyayar mahaifi?"""

"Kasimu yana kuka yana neman yafiya, Ran Junaid s bace yasa Azi ya sa a kulleshi."

Ba karamin bacin rai bane ya bayyana a fuskarsa.

****

"Abdulsalam da Azeema haka suka bar masarauta bayan kwana biyu da hawan Junaid mulki,"

"Zeena da Binta sunsha kuka sosai dan Binta tunda Abdulsalam ya kirata yake neman yafiyarta take kuka, dakyar Junaid ya lalabata ta bari."

"Binta kam tasha kuka sosai jin Azeema zata tafi, Sai dai tafi tausayin Junaid dan tasan shikadai"

yasan me yakeji zai rabu da mahaifiyar da ya samu bayan shekaru masu yawa yanzu gashi zai sake rabuwa da ita.

*****

"Hajjo haka Zeena ta taimaka mata ta koma can gefen Hajiya Inna, Junaid yasa aka gyara bangaren biyu, Zeena ta koma bangaren Hajjo ita kuma Binta ta koma na Azeema."

"Da wannan Fada ta samu nutsuwa wanda kowa hankalinsa ya kwanta, sai dai Junaid a koda"

yaushe yana rashin mahaifiyarsa wacce yaso ya kasance da ita sai dai ba yanda ya iya da kaddarar da Allah ya dora musu.

Ba'a dade ba akai rashin Hajiya Inna Allah ya jikanta Ameen

^***********

Bayan watani........

Kwance yake ya juya baya tana matsamai bayansa yana lumshe idanunsa kamar mai shirin bacci.

"Can tace ""Ya Junaid?"""

Hmmmm

Bacci?

Uhm uhm!

"Murmushi tai tace ""ka juyo in ganka tunda ka hau mulkin nan ganinka ma wahala yake mana."""

"Juyowa yai gaba dayansa ya kalleta, idanunsa yana dan lumshe su yana budesu yana saitinta"

"yace ""Binta Allah bacci."" Yai maganar cikin shagwaba"

"Juya mai baya tai tace ""ai bacci lafiya."""

"Murmushi yai sannan ya matso ya rungumeta ta baya a hankali ya sa hannunsa cikin rigarta,"

"idanunta tadan lumshe, hannunta tasa ta rike hannunsa dake kokarin zare mata bra."""

Ya akai?

"Juyowa tai tace ""Yaya Allah Bacci!"" Tai maganar yanda yai dazu, dariya ya saka sosai, sannan yasa"

"hannu ya cakulota bayan ta juya, da sauri ta juyo tana dariya, tana cewa Yaya bari!!!!"

"Ganin yaki bari ta fara ramawa itama, dariya sosai sukai sannan suka kalli juna suna dan numfashi, kan bakinsa ta matso ta sumbaceshi sannan ta koma tana neman kwanciya, hannu yasa ya riko wuyanta sannan ya dawo da bakinta kan nasa, cikin salo da suke sumbatar juna, a hankali yasa hannu ya zare rigarta yana cirewa yana aika mata da sako zuwa bakinta..........."

"Bayan sunyi wanka ne ta kalleshi ta hade fuska tace ""sai yaushe zaka fadamin yanda kukai da"

"Babana?"""

"Idanunsa ya bude yace ""naam?"""

"Ta kwanta itama tana fuskantarsa tace ""Ya kukai?"""

"Bakinsa yadan motsa sannan ya jawota ya rungume nan ya sanar da ita, hawayen dake zubo"

"mata ne sukaki daina zuba, dagota yai yana kallanta."

Itama kallansa take tana kuka.............

"Rungumeta yai yace ""ki mai addu'a daga shi har Umma abinda suke bukata kenan daga garemu"""

"A ransa yace dake da Zeena da alama Allah ya dauramin nauyin zama komai naku, ina rokon Allah"

ya bani ikon kula daku.

"Hannu yasa akan cikinta yace ""sai yaushe zai fito ne wai? Naga na Zeena harya fito."""

Idanunta dasukai jaa ta dago ta kalleshi tasan so yake yasata dariya........

********

Bayan shekara daya.

"A wannan lokaci ansamu canji dayawa, Zeena ta haifi danta namiji aka saka mai sunan mahaifin"

"Junaid Zubair, sai ake kiransa da Baba karami, Binta kuma ta haifi mace aka sa mata sunan mahaifiyarta Hafsa."

"Baba karami yaba Hafsa wata daya, kusan koda yaushe suna bangaren Hajjo wacce zaman kadaici"

"yake

27 / 28